Showing 24001 words to 27000 words out of 109227 words
Chapter 9 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf
Watannin cikin Khadija 9 da kwana 9 tafara nak'uda, tasha wahala matuk'a wajen wannan
haihuwa, da k'yar ALLAH yabata ikon haihuwar yaro namiji, sai dai tana haihuwarsa koma
ganinsa bataiba ALLAH ya d'auke kayansa, ta rasu.
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, fad'a muku rud'anin da Muhammad yashiga 6ata lokacine
ma, murnar haihuwa tazama kukan rasuwar Khadija da rud'anin da Uncle M.A ya tsinci kansa.
yaronma kwanansa uku a duniya yakoma.
Halinda uncle M.A yashiga sai da yakaishi ga kwanciya asibiti, kusan tsawon sati biyu
sannan aka sallamosa, suka cigaba da masa addu'ar ALLAH yabashi dan gana.
Tundaga wannan lokacin rayuwar uncle M.A ta canja baki d'aya, yazama silently, maganama
bayasonyi, inkaga maganarsa babane kokuwa isma'il Baban Ama.
Shima Baban Ama a 6angarensa lokacinne kawu mahaifinsa ALLAH yamasa rasuwa, wata
d'aya tsakaninsa da Khadija, shima kan yashiga rud'ani sosai, Dan yana k'aunar mahaifinsa,
shikad'ai ya rage masa, gashi kuma yatafi.
Aifa rasuwar kawu takuma rikita Uncle M.A, dole baba yaymasa shiri yabar k'asar, yakoma
Ghana da zama wajen wani abokin Baban.
Uncle M.A yacigaba da zama a Ghana har tsawon shekara uku, ganin karyayta zaman
banza sai kawai yafara karatu na wani cause.
A Ghana Uncle M.A yahad'u da Aneesa, anan makwaftan abokin baba take, tunda tagansa
tarikice, sai dai takula yana cikin matuk'ar damuwa, wannan yasata d'aura d'ammarar dawo
masa da farincikinsa, musamman data samu cikakken bayani akan tarihin rayuwarsa.
Tasha matuk'ar wahala kafin tasamu kan Uncle M.A, kafin komai ya dai-daita Soyayya mai
k'arfi tashiga a tsakaninsu.
Aneesa k'yak'yk'yawace sosai gaskiya, gata nitsatstsiya, ga kuma ilimi, (kunsan dai 'yan
Ghana suna karatu sosai), k'yawwawan halayen Aneesa ne sukajawo k'aunarta mai k'arfi a
zuciyar Uncle M.A.
Sai dai kuma lokacin da Uncle M.A yashirya yazo Nigeria danya fad'ama baba a kai kud'in
aurensa saiya tarara an saka masa ranar aure shida Fateema d'iyar kawu yakubu k'anin innani,
hankalinsa yatashi, amma bashida yanda zayyi, danshi mutumne dabai k'etare maganar
iyayensa, dasunce yayi yakeyi, Dan haka ko'a fuska bai ta6a nuna bayason auren Fateema ba,
sai dai yasanarma mahaifinsa abinda yazo dashi shima.
Baba yaji dad'i sosai, babu kuma 6ata lokacin aka d'aura aurensa da Fateema, bayan sati
uku sukaje Ghana kai kud'i, sai dai iyayen Aneesa basu wahalar dasuba sukace kawai a d'aura
auren ya d'auki matarsa, tunda abune ba k'asa d'ayaba, su baba sunyi farinciki dakuma jinjina
dattako irinna iyayen Aneesa. A kwana biyu akayi komai aka gama, aka basu amaryarsu.
Uncle M.A bai gayama Aneesa aurensa da Fateema ba saida suka iso Nigeria.
Ai kuwa Aneesa tayi matuk'ar birkice masa, sai da yasha bak'ar wahala kafin yasamu kanta
lokacin.
Aneesa da Fateema ba gida d'aya yahad'asuba lokacin, Dan gidanshi da yazauna da
Khadija ginin mace d'ayane, kuma bashida k'arfin yin gini, dole yakamawa Aneesa haya anan
cikin anguwar, babu nisa da gidansa Inda Fateema take.
Dukkan hidimar bikinsa biyu Isma'il ne tsaye, (Baban Ama), Dan zumincinsu nan, duk da
yanzu yanayin aiki kansasu yin watanni basuga junaba, amma kullum suna mak'ale da waya.
Bakuma ko yaushe iyalansu ke zuwa gidajen junaba, saboda Saliha ta girmi su Fateema, kuma
batawani saba dasuba sosai kamar Khadija, amma suna girmamata gaskiya. Baba ya tattara dukkan kasuwancinsa ya mik'ama Muhammad gaba d'aya, yace yacigaba
da juyawa kawai, tundaga lokacin uncle M.A yakoma kasuwa baki d'aya, dukda yana wani aiki a
nan B.U.K
Ubangiji ya sakama kasuwancin hannu, dandanan shagon atanfofi ya bunk'asa, har suka
bud'e wani. Shekara d'aya da auren matansa duk suka haihu, amma Fateema Ce tafara
haihuwar Namiji, aka saka masa Ahmad suna kiransa (Abulkhairi) saboda sunan babane,
Aneesa ma ta haihuwa, sai dai d'iyar batazo da raiba.
A cikin shekara biyu Uncle M.A harkar kasuwa takuma fad'ad'a, dan zuwa yanzu sunada
kusan shaguna Hud'u, sunada shagon atanfofi, shaddoji, materials, gale, kaya 'yan kanti,
dakuma kayan yara, kowanne nau'in sittira kaje saika samu a shagonsu.
Zuwa lokacin Aneesa ma ta haihu, Namiji, Wanda yaci sunan Abdul'aziz (Saifudden),
sunan babanta.
Shekara d'aya tsakani itama Fateema tasake haihuwar Namiji Isma'il (yayma Baban Ama
takwara), yana cemasa Sahibi, (Sahib) kenan.
A lokacinne kuma yagama ginin gidansa daya d'auki tsawon shekaru uku yanayi, ya had'e
matansa duka a waje d'aya.
Had'uwar Aneesa da Fateema kam bata zama da sauk'iba, Dan rikici sosai akaita sha,
Aneesa tanada kishi sosai, bata k'aunar ganin abinda zai ra6uda mijinta ko kad'an.
Itama Fateema a kwai kishin, amma tafi Aneesa wayau Na 6oyewa. Sai da yaymusu
zagir-zagir sannan yasamu sauk'in yawan rikicinsu, daganan aka koma kishin kissa, to duk
masu ilimi aka tara, dolene salon kishinsu yayi matuk'ar bigeka gaskiya, Dan kowa sotake
tazama star a wajen boss. Zuwa yanzu Fateema Nada 'ya'ya uku, Ahmad (Abulkhairi) Isma'il (Sahib) Ai'sha mai sunan
mamanta (Ummita).
Aneesa nada biyu, Abdul'aziz mai sunan babanta (Saifudden), Sai Zainab mai sunan Innani
(Siddiqa).
Shekaru uku dasuka wuce ciyo yasamu baba, kad'an-kad'an abin ya fara masa, tun suna
magani a tsaitsaye harya kwanta rijuf, sosai Alhaji Muhammad ke tsaye akan ciwon baba, sunje
asibitoci da dama Nigeria amma lamarin sai dai addu'a kawai, ciwon koya tafi saiya dawo,
saboda yahad'a da girma, ciwon baba dakuma harkar kasuwancinsa daya bunk'asa, ga aiki
yahanashi ziyarar jos, sai dai koyaushe Baban Ama Na hanyar duba jikin baba, wani lokacin
suzo da Ammi wani lokacin shi kad'ai, Amatallah kam bata biyosu, tun wani zuwa datayi ita
kad'ai Hutu su Aneesa sukayi fad'a a kanta itada Fateema tace bata sake zuwa.
Koyaya su Ammi sukayi da ita saitak'i biyosu, in zasuzo saitayi tafiyarta gidan ka kanninta
iyayen Ammi, Dan zuwa lokacin tafara zama budurwa, tana secondary kusan js 2, duk da
yakamata acema taje SS, amma yawan rikin da jihar jos ke fuskanta yasaka karatun yana
samun koma baya a jihar sosai. Kullum zancen Uncle M.A ina best daughter d'insa? yakamata tazo masa Hutu.
Amma k'iri-k'iri Amatallah tak'i.
Hak'ura yayi yabarta saboda shima ciwon Baban da dawowar nauyin gidansu gana iyali ya
gama d'auke hankalinsa, ga kuma aiki dayakeyi duk da ba kullum yake a office ba dai.
Kwatsam sai Baban Ama yasamu wani mai Maganin gargajiya, ya d'aukeshi sukaje har Kano
domin duba baba, Alhmdllh kuma aka dace, Dan baba nasamun sauk'i sosai da wannan
Magani, bayan yak'arene Uncle M.A yazo jos kuma kar6awa baba wannan Magani.
Anan yaga yanda Amatallah ta girma, duk saiya rikice da mamaki da al'ajabi, Dan yanzu tana
shekara 19, SS 3 kuma a Secondary, sune zasu zana SSCE a wannan shekarar.
ya d'aukko hotunanta dan nunama matansa suga yanda ta koma, amma sai kishi ya rufe
musu ido, suka fara tunanin ko sonta yakeyi, saboda motsi kad'an yace, "my best daughter".
Shikuma kawai mamakin yanda tayi girmane ya tsaya masa a zuciya bawani abuba. amma
matansa sun hau sun zauna sonta yakeyi. To kuma ga yanda al'amarin ubangiji ya kasance,
Ashe ALLAH ya k'addarata acikin matansa Na aure.
Wannan shine asalin labarin wad'annan brothers guda biyu.
Hummmm koya zata kaya kuma idan matan Uncle M.A sukaji a gaske Amatallah tazama
matar mijinsu, kishiyarsu, tabbas a kwai cakwakiya.
Ku dai Ku kasance dani bilynku kawai.
*_WASA FARIN GIRKI!! My fans_*
Mukoma labarií ½í±Ží ¼í¿»
_____________________________
Hankalin Uncle M.A yatashi, yanda yaga rikicin ya fad'ad'a har zuwa wasu jihohin, bak'amin
ta6a zuciyarsa lamarin yay ba, musamman daya tuna babu brother d'insa yanzu a doron k'asa,
dama a wajensane yasamu kwarin gwiwwar kafa k'ungiyar dazata farkar da matasan, a yanzun
kam baisan ta Yaya zai tunkari lamarinba, sai dai insha ALLAH zaiyi k'ok'ari wajen hana kansa
rashin k'warin gwiwwar aikin alkairin daya kulla niyya, shawarar da amininsa brother d'insa
yabashi itace zata zam jagora wajen k'aiminsa da wanzuwar himmarsa........
Ringing d'in wayarsane yasashi sakin ajiyar zuciya, hannunsa yasa yafara lalubenta a
gefensa, Dan kwance yake a kan gado, tunda yadawo sallar asubahi yakuma d'an kwanciya,
saboda tunani baya barinsa samun isashen barci, tunanin jikin baba da rashin d'an uwansa, ga
kuma Amatallah da aurenta, Dan har zuwa yanzu bata farfad'oba, iyalansa kuma basusan da
aurenba.
Ganin sunan doctor Shu'aibu yasashi d'aga wayar da hanzari, ko gaisawa basuyiba doctor
Shu'aibu ya shaida masa Amatallah ta farfad'o, kuma Alhamdllh cikin hayyacinta, sai dai tanata
kuka da kiran iyayenta.
Da hanzari ya diro daga kan gadon, jallabiyarsa daya dawo masallaci ya d'auka ya Sanya,
ya d'au key d'in mota yafita da sauri.
A falon k'asa yaci karo da Fateema dake k'ok'arin had'a break fast saboda yara zasuje
makaranta.
"A'a lafiya kuwa Nurri? Saurin mikakeyi haka?".
Bai ko juyo ya kalletaba yace, " zanje asibiti ne, Amatallah ta farfad'o".
Duk da tana matuk'ar tausayin yarinyar, amma sai da zuciyarta ta sosu, taraka bayansa da
kallo harya fice daga falon, wani takaici yadaki zuciyarta akan mazarin da mijin nasu keyi. (Wata
zuciyarta tace, aiko baikamata kiji haushinsaba, Dan babu Wanda ya cancanci damuwa da
lamarin yarinyarnan sama dashi, kiduba halin data shiga mana). A sanyaye Fateema tace, "hakane kuma, ALLAH kabani hak'urin jure duk abinda zan gani".
Nace, " to amin uwargida".
********
Uncle M.A a rikice ya isa asibitin, tun a k'ofar d'aki yay karo da gwaggo Rakiya tana kuka, bai
ce komai ba yashiga d'akin da Amatallah take.
Doctor Shu'aibu Na tsaye kanta, sai Nazeefa dake zaune gefen gadon rungume da ita, kuka
takeyi rurus da fad'in a kaita taga babanta da Amminta.
A hankali Uncle M.A ya sauke ajiyar zuciya, ya k'araso gaban gadon idonsa akan
Amatallah. d'ayan gefen gadon yaje ya tsaya, ya kalli doctor Shu'aibu a raunane.
Jin jina masa kai doctor Shu'aibu yayi, tareda masa nuni ya lallasheta da idanu.
Uncle M.A ya jinjina kansa, sannan yay k'ok'arin maida kwallar idonsa yana cije le6ensa Na
k'asa. Alama yayma Nazeefa ta barta ta fita itama, saboda doctor Shu'aibu shima yafitan.
Nazeefa ta zare jikinta daga Na Amatallah, ta sakko daga gadon.
Hakanne yasaka Amatallah d'ago jajayen idanunta, tana ganin Uncle M.A tak'ara k'arfin
kukanta tana fad'in "Uncle ka kaini naga babana da Ammina Dan ALLAH".
Bai ce komai ba har Nazeefa tafita. Sannan ya zauna a bakin gadon kusada ita, hannu yasa
ya jawota kusadashi ya rungumeta kawai, tuni idonsa suncika da kwallah, harsun fara taruwa a
gefen idonsa.
Rud'anin da Amatallah take cikine yahanata mamakin rungumar da uncle yaymata, Dan
tunda tafara girma da wayo ya daina rik'e koda hannuntama. jinta a jikinsa yasakata kuma
fashewa dawani kukan mai tsuma rai.
d'an yatsa d'aya Uncle yasaka ya d'auke hawayen dasuka taru masa a gefen ido, ya k'ara
rungume Amatallah sosai ajikinsa, cikin daidaita muryarsa yace, " Khadija! ".
Yanda yakira sunantane yasakata tsaigaitawa da kukan, amma bata amsaba.
Ya kuma fad'in " Khadija! Kina jina?".
Cikin da shashshiyar muryarta ta amsa da "Na'am uncle"..............âœí ¼í¿»
í ½í±Ží ¼í¿»
Inaga maybe gobe idan ALLAH ya kaimu bazaku ganniba gaskiyaí ¾íµ°í ¾íµ°í ¾íµ°í ¾íµ°.
Idan kuma naga comments yanzu idan nadawo anguwa nayi muku.
One Luv my fansí ¾íµ°
*_ALLAH ka gafartama iyayenmuí ½í¹í ¼í¿»_*
[1/16, 1:29 PM] Aysha Galadima: *_Typingâœí ¼í¿»_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*í ½í²¡
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* â‰
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ceí ¾í´™í ¼í¿»_*
____________________
*_Number 12_*
____________________
Shiru yad'anyi Na wani lokaci, kafin yagyara mata kwanciya a jikinsa, murmushi yayi mai
ciwo sannan yace, "Khadija duk duniya wayafi kowa a halittun ALLAH?".
'Dan d'agowa tayi ta kalleshi kad'an, sai kuma ta maida kanta a gefen hannunsa, muryarta
a dusashe tace, " MAZON ALLAH (S.A.W) Uncle ".
Lumshe idanunsa yayi yana fad'in " masha ALLAH Khadija, yanzu yana ina?".
Yanzun kam tashi tayi sosai tabar jikinsa, jingina tayi dagadon
idonsa Na kanta.
"Uncle ya koma ga Ubangijin sammai da k'assai".
''Alhmdllh Khadija, yakikeji darashin kasancewarsa a duniya".
Mamakin tambayoyin Uncle suka fara bata, amma saita dake tace, " inajin babu dad'i,
amma nayi hak'uri tunda ubangijine ya tsara hakan, ina dai Addu'ar ALLAH ya sadamu dashi a
ranar ceto".
Kansa yakad'a mata, muryarsa takuma sanyi fiyeda sanyin datake dashi, yakamo
hannayenta biyu yarik'e a nasa, "Khadija ke musulma ce kuma mumina, kinsan k'addara da
jarabawa, duk wani mumini akwai irin jarabtar da ALLAH kanyima rayuwarsa, wani yabashi
dukiya mai tarin yawa, amma bashida lafiya, wani talauci amma yanada lafiya da 'ya'ya, wani
ilimi amma sai ya jarabceshi da hatsabibiyar mace ko shi d'in ya kasance hatsabibin, ko cikin
'ya'yansa, wani haihuwace ALLAH bai bashiba, wani ya haihu 'ya'yan sun zame masa fitina,
wata macen gidan mijine jarabtarta, wata rashin aure, wata rashin lafiya, wasu kuma saikiga
ALLAH ya had'a musu komai Na rayuwa, sai dai kinsan wani Abu?".
Amatallah ta girgiza masa kanta.
Yacigaba da fad'in kowanne irin matsayi ka taka a rayuwarka inhar bakajin tsoron ALLAH ba
to kaifa ba komai baneba, duk k'ask'ancin waninka inya kasance mai tsoron ALLAH toya fika
agareshi, ubangiji shika d'ai yasan iya adadin halittun daya halitta masu numfashi a duniya,
kuma shine ya tabbatar mana duk sai ya d'and'ana mana mutuwa, wad'anda suka rigamu tafiya
ba sauri sukayiba, muda muka rage bamuyi jinkiriba. A wannan ga6ar ina mai baki hak'uri, da
rok'onki akan kizama cikin bayi masu ambaton Alhamdullahi ala kulli halin aduk yanayin dasuka
tsinci Kansu a rayuwa, ki kar6i jabawarki da hannu biyu dankizama cikin salihan bayi
muminai..........."
Hawayene masu zafi suka fara zarya a kumatun Amatallah, tabbas bayanan uncle namata
nuni akan babu babanta a duniya, ahankali tace, "uncle babana yarasu ko? Karka 6oyemin,
kafad'amin, insha ALLAH zuciyata zata iya d'auka, domin ubangiji baya jarabtar bawa da a
binda bazai iyaba. namaka alk'awarin kasancewa cikin bayin ALLAH masu hak'uri da kar6ar
jarabawa ko wacce iri".
Da k'yar ya iya had'iye wani kulutu daya tokare masa k'irji, sannan ya d'aga mata kai a
hankali shima hawaye nabin nasa kumatun.
Jikinsa kawai tafad'a tasaki kuka mai tsuma rai, hannu biyu ya kar6eta ya rungume, suka
cigaba da rairawa a tare, abin gwanin ban tausayi.
Sun d'auki tsawon lokaci ahaka kafin Amatallah cikin kuka tace, " uncle Ammina fa?".
"Sai hak'uri Khadija, Saliha tama rigayi brother ra..s....u...wa...".
yak'arashe maganar da k'yar, saboda wani d'aci dayakeji a zuciyarsa.
Sunyi kuka mai isarsu shida ita, kafin doctor Shu'aibu yazo yana lallashinsu, dole akama
Amatallah allurar barci danta samu nutsuwa.
*_One week later_*
Alhamdllh a sati d'ayannan daya gabata abubuwa masu yawa sun faru, ciki harda rud'ani mai
rikitarwa da Amatallah ta shiga, dole aka d'akkota daga asibiti aka maidota gida wajen innani.
Basu 6ata lokaciba aka dage mata da addu'oin dangana da hak'uri, Alhmdllhi ansamu
nasarori kam, Dan addu'a takobin mumini Ce.
Nutsuwa tazo mata sosai, sai dai yawan kuka datakeyi, sannan maganama yanzu kam saita
wunima batayiba.
Kullum uncle Na hanyar gidansu innani.
Nazeefa da Innani suna matuk'ar k'ok'ari wajen rage mata kewa da yawan damuwa, hakama
jabeer, Shehu kam sai a hankali, danshi dama bayajin magana, zaman gidamma bayi yakeyiba,
danma yana masifar tsoron uncle Muhammad d'inne yake rage wani abun.
Har zuwa yanzun daga Amatallah har matansa babu Wanda yasan da zancen aurensu,
innani da babane kurum sai jabeer da maijiddah suka Sani, ko Nazeefa batasan komaiba.
Bayan sati uku da rasuwarsu Ammi cif baba yace yakamata asanarma Amatallah zancen
auren, karya zam saita saki jiki kuma akuma maidata ruwa, gamma taji