Showing 1 words to 3000 words out of 80926 words
[9/27, 09:36] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee* *MD* ✍
*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
_Dasunan Allah me rahama me jin k'ai , tsira da aminci su k'ara tabbata ga Shagaba Annabi
Muhammad S.A.W ,_
_Wannan littafin nawa k'agaggene banyishi dan cin zarafin wata ko wani ba , duk wanda
yayi dai dai da rayuwarsa to yazo ne a kasi , banyadda wani ko wata ya juyamin labarina ba
batare da izinina ba , Yin hakan doka ce Akiyaye_
_Wannan littafin sadaukarwa ne gareki Masoyiya Hafsat Abdurrahman_ *Allah yabar
k'auna*
Chapter 1.
A garin Abuja yau antashi da ruwan sama kamar da bakin k'warya , hakan yasa
garin yayi tsit kowa yana cikin gidan sa , wani katafaren gida nagani ana wangale k'ofar gate
d'insa , wata motar ce ta danno kai da gudun tsiya tamkar zata tashi sama saboda gudu .....
baka hango wanda ke cikin motar saboda bak'in glass d'in dake jikinta , amman kasan duk
wanda ke cikin motar basai anfad'a maka irin rashin jin shiba , saboda irin gudun dayake
sharawa ga kuma wani kid'a na tashi tamkar dodon kunnen mutane zai tsage , a k'ofar wani
katafaren gida motar ta tsaya ta danna hon. Da gudu megadi yazo ya bud'e dan yasan waye
ko ba'afad'a masa ba , da gudu motar ta kuma shiga cikin wannan gidan kuma har a lokacin
ba adaina ruwa ba , anfi minty biyar ba'a fito daga ciki ba sannan aka bud'e murfi aka fara zuro
k'afa , wata had'addiyar Budurwace wacce tagaji da had'uwa ta fito daga cikin motar sanye da
glass a idonta , ga wasu matsatstsun kaya datasa duk ilahirin jikinta a matse yake , takalmin
dake k'afarta irin hill d'in nan ne , tana fitowa me gadi ya k'araso da gudunsa yana zubewa
gabanta yana fad'in " sannunki da zuwa ranki shi dad'e Hajjaju mutan makka da madina , ko
kallon arzik'i batayi masa ba ta wurga masa lemar data d'auko bayan motar ta , da sauri ya
mik'e yana bud'e lemar tare da rik'e mata dai dai kanta gudun kar ruwa yatab'ata , shigewa tayi
tana wani irin taku tamkar wahainiya har suka k'araso k'ofar wani had'add'en falor , shigewa
tayi ciki shikuma me gadi ya tsaya a wajen saboda bin umarninta......
Tana shiga cikin falor tasamu 'Yan aikin gidan sai faman gyare gyare suke a falor , suna
ganinta dukansu suka zube k'asa suna gaidata , kallo basu isheta ba bare ta amsa musu , step
tafara hawa alamun sama zata hau , saida ta haye saman sannan dukan su suka mik'e suna
girgiza kai kafin suci gaba da aikin gabansu......
Wani d'aki naga tashiga ko sallama batayi ba , wani Magidancin mutum ne a zaune yana
danna cumputer lapton akan wani katafaren gado , sai kuma wata mata wacce ke had'a masa
cofee a gefensa , kana ganinta kasan matar sace saboda yadda suke hirarsu cikin farin ciki da
raha , jin anshigo yasa dukansu suka dubi k'ofah dan ganin waye ? koda suka ganta Mutum
yafara fara'a yana fad'in oyoyo My luv , zonan naji waya tab'amin ke naga sai had'e rai kike ?
Hajiya Maimuna tadubeshi tace " Alhaji nagama aikina zan'iya tafiya ? dubanta yayi tare da
canza fuska yace " Haba Maimuna wai meyasa duk lokacin da *SANAM* zatazo sai kin bar
wajen ? Hajiya Maimuna tace " kafi kowa sanin halin 'yarka batason kowa ya rab'eka mutuk'ar
ba ita bace , dan haka duk lokacin data tafi zaka iya kirana inyi maka duk abinda kakeso , bata
jira cewar saba tayi hanyar fita tafice abinta.......
Sanam ta rakata da Hara sannan tayi tsaki taci gaba da taunar cingum d'in ta , Alhaji
Abba yadubi tilon 'yartasa wacce yake mutuk'ar k'auna a duniya kuma akanta zai iya yin komai
mutuk'ar za'atab'a masa ita yace " Sorry my luv k'yaleta kar ranki ya b'aci akanta , Sanam tayi
wani k'wai da cingum d'inta har saida yatab'o hancinta tace " Daddy nazo ne akan maganar
canzamin motar , kasan cikin account d'ina kwata kwata bakai adadin kud'in dana ke buk'ata ba
, duk wannan maganar da Sanam takeyi a Shagwab'e takeyinta tamkar K'aramar yarinya ,
dubanta yayi yace " My luv ina ganin fa motar nan taki kwata kwata batafi kwana goma ba ,
kuma ace har ank'ara siyan wata , da bari kikayi wannan ta kwana biyu sai insa ayi miki order
wata daga Jamus , had'e rai tayi sannan tace " Daddy yanzu kana so muyi anko motar da
Zahra ne ? itama fa daga ganin wannan tawa tasa Daddyn ta yasiya mata irinta , nikuma
gaskiya bazan dunga hawa motar iri d'aya da wata ba saboda banson Ajina ya zube , Murmushi
yayi yana dubanta sannan yace " to shikenan nawa ne kud'in waccen motar d'in ? wani
murmushi tayi wanda har sai da dimple d'inta ya lotsa tace " 50.Million ce kawai Daddyna ,
murmushi yayi yace " indai akwai ta sama da haka ni ita nakeso nasiya miki My luv , tashi tayi
da sauri ta fad'a jikinsa ta rungumesa tana murna , ganin ta a farin ciki yafi masa komai a
duniya , shima samun kansa yayi da farin ciki sannan ya sumbaci goshinta , Nan yatura mata
80.Million a accaunt d'inta yana fad'in " sai munzo celebrition my luv , ta shagwab'e fuska tare
da manna masa kiss a kunci tace " thanks my special papa proud of U My Daddy , da sauri ta
d'auki jakarta tajuya ta fice daga cikin d'akin ,..
Lokacin da ta sauko sukayi karo da Hajiya Maimuna , Sanam wani dogon tsaki taja tare da
tsartar da miyau tana bin gefe harta fice daga falor , wannan Abun datayi wa Hajiya Maimuna
ba k'aramin harzuk'ata yayi ba , taya yarinya k'arama zata dunga yi mata wannan abu ? tabbas
wannan hali na Sanam yafara damunta zata iya ci gaba da zama da Alhaji Abba kuwa ? Sama
ta nufa wajen sa ranta a mutuk'ar b'ace , tana shiga d'akin nasa ko sallama batayi ba tafara
fad'in " a gaskiya Alhaji nagaji sosai da halin wannan 'Yar taka , a koda yaushe tazo gidan nan
saita yimin abinda zuciyata zatayi min rashin dad'i , yau saboda iskancinta har miyau ta
tsartamin dashi haba Alhaji , idan anyi magana sai kace ana takura mata ansa mata ido , a
gaskiya indai zamu ci gaba da tafiya akan haka tabbas zanbar maka gidan ka dan hak'urina
yafara kaiwa k'arshe , a fusace Alhaji Abba ya mik'e yana kallon Hajiya Maimuna yace " nasan
dama dole sai kinzomin da wata sabuwar magana akan zuwan Sanam gidan nan , Maimuna
ina d'aga miki k'afa sosai aka Sanam saboda wani Abu , amman duk randa kika isheni wallahi
zaki gane waye ni , tsaki yaja tare da d'aukar mukullin motar sa yafito ......
Hajiya Maimuna tuni hawaye ya wanke mata idanuwa , fad'awa kan gado tayi tana kuka tare
da fad'in " yaushe ne matsala ta zata kawo k'arshe a kan wannan yarinya ? yaushe ne zanyi
zaman farin ciki a gidana koda yaushe indai zata kawo ziyara to tabbas sai tabar mata tabo ,
lallai hausawa sunyi gaskiya da suke cewa *'Yar kishiya rik'on me hak'uri* Allah yabasu ikon
cinye jarrabawar nan......
Koda Sanam ta fito har a lokacin megadi na tsaye ruwa yayi masa duka , ga lema a
hannunsa amman yasan indai yasake yashiga cikinta to tabbas yagamu da jaraba , tana fitowa
yayi saurin bud'e lemar yana rufa mata aka suka wuce har gun motar ta , tana shiga ya nad'e
lemar yasa mata ita a bayan motar tare da kwasa da gudu yayi wajen gate. Bud'e wa yayi tazo
ta fice da mahaukacin gudunta tamkar zata tashi sama , gudu take sosai titi ko wanne me
motar matsawa yakeyi inyaganta , tana shiga estet d'in Airea 11 dai dai wani k'ofar gida wani
matsahin saurayi ya fito a k'afa sanye da jallabiya jikinsa , kana ganinsa kasan sauri yake
yasamu sallar Azzahar ta wanke sa da ruwan cab'i dukansa , kuma ta fiki motar ta tamkar
batasan abinda tayi ba..............
*Comment* *d'inku* *shine* *zai tabbatar min da karb'uwar da littafin zaiyi*
*Dafatan wannan salon shima zai k'ayatar daku*
Kardai kumanta Alk'alimin *'Yar Mutan Kanawa* _Ce_ ✍
[9/27, 09:36] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on_ _Me_ _Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
Chapter 2.
Bin motar yayi da kallo har ta k'ure sannan yadubi jikinsa , duk jikinsa a b'ace da
cab'i , wani takaici yaji ya kamashi sosai tabbas duk wanda yake cikin wannan motar ba
k'aramin mara mutunci bane , amman tabbas saiya gano ko waye a cikin motar tunda acikin
Estet d'insu yake , juyawa yayi ya nufi cikin gidan su ransa a b'ace ga takaicin rasa jam'i
dazaiyi....
Wani mahaukacin Hon Sanam ke dannawa a k'ofar gate , lokacin megadin su yatada sallah
, babu shiri ya sallame daga sallar saboda sanin hali , da gudu ya bud'e k'ofar gate d'in yana
fad'in "sannu da zuwa hajjaju , dawani mugun gudu ta shigo tamkar zata bi takansa , da sauri ya
buga wani tsalle yana jan baya tare da dafe k'irji saboda razanar dayayi , tafi minty goma kafin
tafito daga cikin motar ta dubesa a wulak'ance tace " mekakeyi da har yafi hon d'in motar ta
muhimmanci ? da sauri ya zube yana fad'in " tuba nake ranki shi dad'e wallahi sallah na tayar
shiyasa , wani tsaki tayi sannan tajuya ta nufi cikin gida......
Hajiya Nafeesa tana cikin kitchen tana ta k'ok'arin had'a Abincin dare taji shigowar Sanam ,
k'wala mata kira taji tanayi tamkar k'aramar yarinya , da sauri tafita daga kitchen d'in ta nufi
Falor , Sanam naganinta ta taho da gudu tana fad'in " Mumy Kitayani murna Daddy yabani
kud'in yace in canza motar , Hajiya Nafeesa tace " shiyasa nafad'a miki kije kisamesa kinsan
komai kikeso yana faranta miki , Sanam tayi murmushi sannan tace " Mumy nasan Daddyna
yana sona fiye da komai a duniya , Hajiya Nafeesa wani abu taji ya tokare mata a k'irji na
takaici amman saboda bariki irin tata sai cewa tayi " in bai soki ba Baby wazaiso ? ke kad'ai
Allah ya mallaka mana a duniya kinga kuwa dole musu farin cikin ki , k'ara shiga jikinta Sanam
tayi tamkar wata k'aramar yarinya tana jin dad'i , Hajiya Nafeesa cikin ranta take fad'in " duk
yadda zanyi na raba wannan soyayyar taki da Mahaifinki sainayi , a koda yaushe na bud'e ido
naga yadda yake sonki yake kulawa dake wani takaici ne yake min yawa , a fili kuma tace " bari
nakoma kitchen dan kinsan yau girkin da kikeso shinake miki , Sanam ta d'ago tana fad'in "
shiyasa nake sonki Mumyna kina sakani farin ciki sosai , ba kamar waccen matar Daddyn ba
yauma danaje saida ta b'atamin rai , da sauri Hajiya Nafeesa ta dubi Sanam tace " me Hajiya
Maimunar tamiki haka ? Nan Sanam tafad'a mata yadda sukayi da Hajiya Maimuna , wata
dariya suka saka tare da tafawa Hajiya Nafeesa tace " kin kyautamin walllahi dakika tofah mata
miyau , nan Sanam ta haye sama d'akinta tana fad'in " ai ko gobe naje gidan nan saina kuma
mata kalar wani rashin mutunci mutuk'ar zata shiga gonata .....
Hajiya Nafeesa kitchen ta nufa tana fad'in " banza wawiya wacce bata san ciwon kanta ba ,
Wai har dad'i takeji dan tayiwa Uwar ta rashin kunya , yarinya zakiyi bayani ne sannan gaba ,
duk wannan soyayyar danake nuna miki badan Allah bane kawai saboda dukiyar Ubanki nake
lallab'aki , dasannu zaki gane cewa duk inda kishiyar uwa take to tabbas kishiyar ce , tun
zuwanki duniya nakeshan wuyarki kawai ina dannewa ne saboda lokacin baki wuya baiyiba ,
saina sa kinsan cewa rik'on danake miki shine wanda hausawa suke cewa *'Yar kishiya rik'on
me hak'uri* zanci gaba da hak'uri dake tare da nuna muku tawa kalar siyasar......
Wani had'ad'd'en d'aki Sanam tashiga sai k'amshine ke tashi , komai na cikin d'akin kalar
pinky ne har fentin d'akin , toilet d'in dake manne jikin bed d'inta tashige , bayan minty 15 tafito
daga toilet d'in d'aure da tawul iya guwa sai k'amshin turaren wanka take , zama tayi gaban
mirror tana goge jikin nata tare da janyi mansha fawa tafara shafawa , Sanam nada kyau sosai
kana ganinta kaga zallar shuwa arab , tana da kyau na nunawa sa'a ga dirin jiki tamkar itace
tazab'i ayita hakan , farace sol fatar jikinta har shek'i takeyi saboda hutu da gyara , wayar tace
tashiga ruru amman ko kallo wayar bata isheta ba har kiran ya katse....
Shiryawa tayi cikin wasu matsatstsun kaya riga da wando , duk wata sura ta jikinta sai data
baiyana , ta d'auki wani tsadadden turare ta fesa ajikinta , tuni k'amshi ya gauraye ko inah na
jikinta abinka da 'yar gayu , wani filet d'in shoe d'inta ta d'auka tasaka tarae da d'aukar jakarta
swuga tarik'e tafice daga d'akin....
Lokacin data sauko k'asa dai dai lokacin Hajiya Nafeesa take jera abinci a daining ,
k'arasowa tayi taja kujera ta zauna tana fad'in " Mumy yunwa nakeji plss kiyi seving d'ina ,
Hajiya Nafeesa tace " to my Babyna bari nagama d'akko sauran Kayan sai na zuba miki , turo
baki tayi sannan tashiga dannan wayarta , sai a lokacin taga me kiran nata k'awarta ce Diyana ,
da sauri ta dannah calling d'in number , bugu d'aya aka d'aga ana cewa " Baby Sanam wai ina
kika shigane yau kwata kwata bakizo an had'u ba ? kinsan fa yau Zahra take celebrition d'in
siyamata sabuwar motar da Daddyn ta yayi , kuma kinsan da gayya takeyin hakan saboda ke ,
tab'e baki Sanam tayi sannan tace " k'yaleta kawai Diyana banda lokacinta amman ko saboda
kar ace ina mata bak'in ciki anjima zanshigo , katse wayar tayi batare da tajira me Diyana
zatace mata ba , lokacin Hajiya Nafeesa ta k'araso tana ajiye kayan hannunta sannan tafara
zubawa Sanam Abincin , Faten doya ne wanda yaji Naman kaji sai k'amshine ke tashi , Sanam
tuni tafara zubawa cikinta tana wani danna waya , Saida takusa cinyewa sannan ta ture wai ta
k'oshi , lemo ta tsiya tasha sannan ta mik'e tana duban Hajiya Nafeesa tace " Mumy nidai
zanfita kibani mukullin motar ki da ita zanfita , Hajiya Nafeesa tace " yana kan dirowar mirror
d'ina kije ki d'auko , sannan karki dad'e dan kinsan anjima Kad'an Daddyn ki zaizo , Sanam tace
" to Mumy kikulamin da kanki bye bye , Hajiya Nafeesa ta raka ta da harara tana fad'in "
shegiyar yarinya tamkar Aljana dan kyau..
Sanam tana fitowa tashiga motar Hajiya Nafeesa , da sauri megadi yaje ya bud'e mata gate
yana fad'in adawo lafiya Hajjaju , ko kallonsa batayiba tasaka kai ta wuce abinta.....
tunda Huneed ya shiga gida canza kaya yake cika yana batsewa , dubansa Hisham yayi
yace " wai mutumina ya akayi naganka haka naga jallabiyar ka ta b'aci da cakwali saikace
k'aramin yaro , gashi kuma naga sai faman had'e rai kakeyi ? Huneed yace " wallahi nafita
sallar Azzahar d'azu kawai wani wawa yazo wucewa a motar ya feshe ni da cakwali , murmushi
Hisham yayi sannan yace " duk cikin Estete d'in nan bawanda yake irin wannan gudu sai wata
yarinya me suna Sanam , itace take gudu da motar