Showing 27001 words to 30000 words out of 80926 words

Chapter 10 - YAR KISHIYA Book Complete BY Zee MD.pdf

Zee MD   

10 Jul 2025

4187

sukayi karo da Hisham yana k'ok'arin fita , yana ganin d'an
uwan nasa yafara fara'a yana fad'in " Soja mazan fama saukar yaushe ? Huneed yayi
murmushi yace " saukar yanzu dan ko cikin barrack bashiga ba nataho gida , Hisham yace "
sannu da zuwa ya anshi jakar hannun nasa ya juya suka shiga cikin gidan tare.......


Fahad yanemi parking space ya ajiye motar sannan ya shigo cikin gidan , karo sukayi da
Hajiya Nafeesa lokacin Sanam ta hau sama sai ita kad'ai a zaune , Kusa da ita Fahad ya
zauna yana fad'in " ina 'yar mulkin take ? Hajiya Nafeesa tayi masa nuni da baki alamar tana
sama , tab'e baki yayi sannan yace " wallahi wannan yarinyar bata da mutunci ko kad'an , wai
ni zata kallah ta kirani da direban ta , Hajiya Nafeesa ta dube sa tace " Sanam d'in ce tace
maka direba ? Fahad cike dajin haushi yashiga bawa Hajiya Nafeesa labarin duk yadda sukayi
a airpot , sannan yace " wanda yaje gun nata da zumar yana sonta shi ta turo wai ya kira mata
direban ta , murmushi Hajiya Nafeesa tayi sannan tace " k'yale ta kawai iya yaune duk rashin
mutuncin nata , dan mahaifin ta tana juya mata baya zata dawo k'ark'ashin ikon mu , a lokacin
zaka shigar da manufarka nasan auren ta kaga babu ta yadda za'ayi tak'i ka saboda bata da
majin gina , dama kuma kaga bata damu da wannan saunar uwar tata ba , hasalima sai da
nasan yadda nayi ta tsani mahaifiyar tata , kaga bata da inda zata nufa dole sai wajen mu dai ,
wani dad'i sosai Fahad yaji har da murmusawa tare da jinjinawa yayar tasa , dan yana mugun
jin sha'awar Sanam , tunda yake mu'amala da mata bai tab'a cin karo da mace me k'irar jikin
Sanam ba , komai na jikin ta ya had'u sosai , hatta da faratan hannun ta da k'afa abin kallah ne
, nan yafara hango shi yana jikinta yana sarrafa ta yadda yakeso......

Sanam na shiga d'akin ta taci karo da wani k'amshin na musamman , lumshe ido tayi tana
bud'e hanci tana shak'ar k'amshin , toilet ta fad'a danyin wanka , nan ma karo tayi da turaren
wanka me k'amshi ta tsiyaya a cikin abin wankan ta , cikin ranta ta furta " gaskiya matar nan ta
iya turaruka masu k'amshi , ga k'amshin me sanyi da kuma dad'i da sanyaya zuciyar me shak'a
, tana shiga cikin ruwan wankan tafara lumshe ido tana wani sirtaccen murmushi.......


Koda Sanam tagama wanka tafito , shieyawa tayi cikin wasu riga da wando masu kyan
gaske , gasu da rashin nauyi sosai sunyi kyau , wayar ta ta d'auka ta fito daga cikin d'akin ta
sauko k'asa abinta.......

Tana sakkowa idon Fahad k'ur akanta yana kallonta , wani yawu yake had'iya jikake k'utt.
duk kallon dayake mata kwata kwata bata kula dashi ba , dan ta tattara hankalinta akan
wayar ta tana nemo lambar Daddyn ta , tana k'arasowa taja kujera ta zauna tafara magana "
Mumy me kika dafa min dan nayi missing din girkin ki , Murmushi Hajiya Nafeesa tayi sannan
cikin kissa tace " abincin da kika fiso my Shalele , dan nasan dama dole zakiyi missing din girkin
nawa , Sanam zatayi magana kenan sai Alhaji Abba ya d'aga wayar yana fad'in " welcome my
queen dafatan kindawo lafiya ? Sanam tace " lafiya lau my Daddy , nayi Missing d'inka inason

inganka , nan tashiga zabga masa shagwab'a tamkar wata yar k'aramar yarinya , da k'yar ya
lallab'ata sannan ya sheda mata gashinan yanzu zai taho , murna tashiga yi sosai tana niyyar
kashe wayar ya dakatar da ita , cike da lallab'awa yace " kin manta baki tambayi Mumyn taki ta
biyu ba , Sanam tamkar tana gaban su ta tab'e baki sannan tace " nifa Daddy banda wata
Mumy bayan tanan gidan kuma ai ita gata muna tare , Hajiya Maimuna dayake wayar Hands
free take tana jin abinda Sanam d'in tace , Murmushi tayi na takaici batare da tace komai ba ta
mik'e tabar wajen , shima kuma Alhajin bai wata nuna damuwa ba game da jin maganar Sanam
d'in , Kashe wayar tayi sannan ta fara janyo kulolin da Hajiya Nafeesa ta jera mata su , tuni
Hajiya Nafeesa tafara wani shu'umin murmushi , duban Fahad tayi suka had'a ido sannan suka
murmusa....
[9/27, 09:52] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
‍♀️‍♀️


*NA*
*Zee* *MD*


*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046

✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨


*Bisimillahir Rahamanir Rahim*




Chapter 20.


Sanam tana bud'e kular taga sakwara sosai taji dad'in ganin nata , janyo d'aya
kular tayi tabud'e miyar agusi da ta wadatu da naman rago sai k'amshi ke tashi , d'auko guda
d'aya tayi tasa a filet tare da zuba miya tajanyo tana fad'in " Mumy tamkar kinshiga zuciya ta
kinsan inason cin sakwara , tunda naje Turkey nake kewar cin ta amman bansamu ba , cike da
kissa Hajiya Nafeesa tace " haba my luv kinsan komai da nasan zai faran ta miki ai shinakeso ,
yanzu dai bari nashiga d'aki na fito nasan lokacin kin gama ci sai kibani labarin Turkey , Sanam
tayi murmushi tace " wanne labari Mumy ? sai dai ko labarin bikin da akayi zanbaki , Hajiya
Nafeesa tace " ai daman shi nakeso kibani bari na fito....
Fahad shima tashi yayi yabi bayan Hajiya Nafeesa yana fad'in " Aunty ina key d'in motar ki
zanfita ? ...

Sanam lomar ta d'aya taji muryar Diyana tana sallama , da gudu Diyana ta taho tana
fad'in " Oyoyo my Besty ta , nayi missing d'inki sosai tunda kika tafi ko nemana bakyayi ,
murmushi Sanam tayi sannan tace "kinsan biki naje dole kimin uziri amman kina raina nima ,
zama tayi ta janyo filet d'in sakwarar dake gaban Sanam tace " kice nazo asa'a anyi best food
d'inki , Sanam tace " wallahi kuwa Mumy ce tamin na murnar dawowata , lomata d'aya kika
shigo zaki samin rani kawai , Murmushi Diyana tayi tana fad'in " naji d'in ai nima kinsan inason
Sakwara sosai , Sanam tace " to gatanan ai sai kiyi ta fama , zata sake magana wayar ta
tashiga ruri , d'auka tayi tana duba screen d'in wayar number Huneed tagani , da sauri ta mik'e
tana cewa " Diyana ina zuwa , da kallo Diyana tabi bayan Sanam da kallo tana fad'in " a lallai
Besty kinyi kamu wannan rawar jiki haka ,.....

Sanam can bayan gida ta fita sannan ta d'aga wayar , tana d'agawa tayi sallama tamkar ba
ita ba , Huneed najin muryar Sanam ya lumshe ido yanajin saukar wani nishad'i , a hankali ya
furta " My speacial ya kike ? Sanam sauke wayar tayi daga kunnen ta tana k'ara duban wayar
, dagaske Huneed ne yakira ta da My Speacial ko dai kunnen tane ? maganar dataji ya kumayi
ne yasa ta maida wayar kunnen nata , ci gaba yayi da magana yana cewa " andawo lafiya ?
sai sannan mamaki ya kama Sanam taya yasan ta dawo ma ? murmushi yayi me sauti tana
jiyowa yace " kina mamakin ta yadda akayi nasan kindawo ko ? to kibar mamaki kawai dai na
tsoka ne kine , murmushi tayi itama sannan tace " yakake ? lafiya lau nake dafatan kindawo
lafiya , Sanam tace " lafiya lau nadawo kaima ina fatan nasameka lafiya ? Huneed yace " lafiya
lau nake sai dai kawai inason ganin kyakkyawar fuskar Mata ta , Sanam tace " ai sai ka koma
gida ka kalleta ko zaka samu sauk'i , batajira yace wani abun ba ta kashe wayar sabo da wani
kishi da yataso mata , kwata kwata idon Sanam ya rufe ko gaban ta bata gani ta nufi cikin
gida da gudu ta haye sama d'akin ta......

Hawaye ne ke zuba a idon ta ta fad'a kan gadon ta , cikin ranta tace " me yake nufi dani
ne ? daga munfara magana sai yadunga min maganar matar sa ina ruwana da ita , sosai
Sanam keyin hawaye saboda wani mugun *Kishi* dataji yana taso mata......
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
‍♀️‍♀️


*NA*
*Zee* *MD*


*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046

✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨

*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*



Chapter 21.


Huneed tunda yaji yadda Sanam ke magana k'arshe ma ta kashe waya yake mamaki
, to shifa yasan har yanzu bai furta mata yana sonta ba , amman taya take da wannan kishi
haka ? to kodai itama kamar yadda yakamu da sonta haka itama ta kamu da nasa ne ? idan
kuwa hakane to tabbas zai yi rawa ya juya dan daman fargabar sa ita , kuma abinda yasa
yasan ta dawo shine ' Diyana ce tazo wucewa d'azu suna tsaye da Hisham , tana ganin su ta
k'araso tazo suka gaisa anan take shedawa Hisham ai Sanam tadawo , murmushi yayi sannan
a hankali ya furta ai dole na shirya zuwa lallashi , tashi yayi ya nufi toilet dan watsa ruwa.......

Kwata kwata Diyana bataga shigowar Sanam ba , hankalin ta na kan cin sakwara da miyar
agusi ta , dama Diyana akwai shegen kwad'ayi gashi gidan su basu da wani k'arfi sosai ,
sanadin k'awancen su da Sanam ma a sch suka had'u , Yayan Baban Diyana yana da kud'i
shine ya d'auki nauyin karatun ta shiyasa tasamu tayi sch d'aya dasu Sanam , ga Diyana akwai
gayu da gwalli dakuma shish shigi , ta duk'ufa tana ta cin Sakwarar ta taji muryar Hajiya
Nafeesa tana fad'in " Diyana ina kuma Sanam d'in ? sai sannan ta saita kanta dan gudun yarfi ,
dan tasan halin Hajiya Nafeesa akwai wulak'anci da jin kai , gaishe ta tayi tace " Mumy barka
da yamma dafatan kin wuni lafiya , Hajiya Nafeesa a tak'aice ta amsa da cewa " lafiya ina
Sanam ? Diyana tace " naga ankira wayar ta tafita waje ta d'aga shine bata dawo ba , Hajiya
Nafeesa da sauri ta dubi Diyana tace " taci Abincin nan kuwa ? Diyana tace " e nashigo
nasameta tana ci daga nan muka fara magana sai kuma aka kira wayar tata , wata ajiyar Zuciya
Hajiya Nafeesa tayi idon ta ya rufe kwata kwata tace " Alhamdulillah , sannan ta kuma kallon
Diyana tace " kin tabbata dai taci ko ? Diyana cike da mamaki tace " ea na tabbata Mumy ,
cikin ranta tace " meyasa Mumyn Sanam takeso taci Abincin nan haka ? kodai akwai abinda
takeso tayi mata ? ganin Diyana ta tafi Nazari yasa Hajiya Nafeesa ta saita kanta tace " kinsan
k'awar taki batason cin Abinci shiyasa nadamu , kuma kinga daga tafiya tadawo yakamata ace
taci abinci kar Daddyn tq yayi fad'a , dayake Hajiya Nafeesa ta k'ware wajen kissa da kisisina
tuni ta shigar da Diyana.......


Sanam tuni bacci yayi awon gaba da ita , daman agajiye take ga kuma kuka da tasha ai
tuni tayi nisa a bacci....


Diyana ganin shuru shuru Sanam bata dawo ba yasa ta mik'e dan ta lek'a , dai dai lokacin
Daddyn Sanam ya bud'e k'ofar palor ya shigo shima , sunayin karo da Diyana yaji ya tsani
ganinta ya had'e fuska sosai , Diyana ta rissina tana gaidashi , wata harara ya wurga mata

yatsa tsaki batare da ya amsa ba yayi gaba , duk abinda yafaru akan idon Hajiya Nafeesa ba
k'aramin dad'i taji ba ganin maganin yafara aiki , cikin ranta tace maganinki ai kwad'ayayyi yar
banza da wofi , Diyana tunda taga kallon da Daddyn Sanam yayi mata da kuma k'in kula ta
dayayi jikinta yayi sanyi , Daddyn da inya ganta har tsokanar ta yake tare da wasa da dariya ,
amman yau ko kallo bata ishe shiba sai ma harara da tsaki , tabbas inajin akwai abinda yafaru
dole tasamu Sanam suyi magana , sai dai tana fitowa harabar gidan bataga Sanam ba , ba
inda bata duba ba amman babu Sanam babu dalilinta , cikin ranta tace " to ita kuma ina tayi
haka ? gashi duk motocin gidan suna ajiye bare tace fita tayi , har zata koma cikin gidan wata
zuciyar tace " karki shiga kuma yanzu Daddy yasa miki duka , tuni ta fice daga cikin gidan
batare da ta kuma bi takan neman Sanam ba ....


Alhaji Abba yana k'arasowa Hajiya Nafeesa tafara murmushin kissa tana fad'in " wato anji
shalele ta dawo shine aka taho a ganta ko , murmushi yayi yana mejin dad'in yadda Hajiya
Nafeesar ke nunawa 'Yar tasa tilo soyayya , ko ba komai hakan yana sawa yaji yakuma santa
sosai , zama yayi a d'aya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun falor yana fad'in " wai ina take
ne ? Hajiya Nafeesa cike da murmushi tace " inajin tana d'akin ta , amman bari naduba nagani
ko bataji shigowar kaba , da sauri ta nufi sama dan ganin Sanam d'in ko tana nan , dan ta
matsu taga sun had'u yayi mata yadda yayiwa Diyana , wata dariya tayi tare da furta " Sanam ki
shirya yau kinzo hannu , sai na rusa miki farin cikin ki saina saka kinzama abar tausayi kuma
mak'ask'anciya , haka ta k'arasa cikin d'akin Sanam d'in .....

Tana tura k'ofar tasamu Sanam kwance a gado tana bacci , gashin kanta ya rufe mata duk
ilahirin fuskar ta , tsayawa rayi tana mamakin meyasa Sanam d'in bacci a irin wannan lokacin ?
tunowa da tayi in Sanam na bacci ba'a tashin ta yasa ta tsaya , dan tabbas in ta tashe ta to
rarrashin ta ma sai yazama aiki kafin tayi shuru , har ta juya zata fita taga Sanam d'in ta motsa ,
da sauri tace " My luv kin tashine ? Sanam ta bud'e idon ta a hankali tana duban Hajiya Nafeesa
, a hankali ta furta " natashi Mumyna akwai wani abin ne ? Hajiya Nafeesa tace " Daddyn ki ne
yazo yakeson ganinki shine nazo kiranki naga kamar bacci kike , Sanam jin ance Daddy yasa
ta mik'e zaune tana fad'in " ganinan zuw Bari nayi wanka dan jikina ciwo yake min , Hajiya
Nafeesa tayi murmushin yak'e tace " to shalele inkin fito kisamemu a k'asa , Sanam tace " to
tana mik'ewa ta nufi toilet.......


Bayan Minty 10 saiga Sanam ta sauko sanye da riga da siket na wata babbar atamfa ,
sosai kayan suka amshi jikinta suka mata kyau , kanta babu d'an kwali sai wani k'aramin gyale
da ta yafa kalar jikin atamfar , sai kuma filet shoe d'in ta datasa , sosai tayi kyau sai k'amshi ke
tashi ajikinta ta ko' inah , tana k'arasowa Daddyn ta yafara murmushi yana fad'in " your welcome
my love , a hankali Sanam ta k'araso jikinsa tana murmushi tare da murnar ganin Mahaifin nata
, tabbas 'Da da Mahaifi sai Allah wata k'auna ce a tsakanin su me zafi , Alhaji Abba yana
mutuk'ar ji da tilo d'in 'Yar sa , dan haka a koda yaushe bayason yin nisa da ita , sundad'e a
manne da juna suna murnar ganin juna kafin Sanam tasamu guri kusa da Daddyn nata ta
zauna , gaishe shi tayi cike da girmamawa dan Sanam duk iskancin ta tasan darajar gaida

iyaye , amsawa yayi cike da so da k'auna yana cewa " kinga yadda kika rame

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login