Showing 48001 words to 51000 words out of 80926 words

Chapter 17 - YAR KISHIYA Book Complete BY Zee MD.pdf

Advertisement

Zee MD   

10 Jul 2025

4242

)
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/





*Bisimillahir Rahamanir Rahim*




_Inayiwa d'aukacin Masoyana Barka Da Sallah , Dafatan kowa yayi sallah lafiya Allah ya
maimaita mana_
*Masu k'orafin bana typing dayawa da masu cewa sai na dad'e nake Typing , ina mai baku
hak'uri akan hakan duk zangyara amman kudunga yin uziri , sannan duk wani marubuci yanaso
yaga ana yi masa Comment duk lokacin da ya turo da book d'in sa , Amman dayawa a cikin ku
basayin Comment , dan Allah munaso inkuji dad'in Book kudunga fitowa kuna yabawa
Marubutan dan suma suji dad'i ,*


*Nagode Sosai Masoyana* _nima ina k'aunar ku tamkar inzo in sace ku mu rayu
tare_




Chapter 32.


Koda Huneed ya fito daga cikin gidan su Sanam neman ta yayi yarasa , da sauri ya
shiga motar ya fice daga cikin gidan....

Hanya ya dunga dubawa ko zai ganta amman harya fita daga estete d'in Anguwar bai
ganta ba , haka ya dunga ware ido yana kallon titi ko zai ci karo da ita , can ya hangota a tsaye
tana kallon titi ranta duk a b'ace , dayake Unguwar babu masu Napep sosai sai dai in Allah
yasa sun shigo da wani , wannan yasa Sanam bata samu abin hawa ba har wannan lokacin ,

yana k'arasowa ya kashe motar tare da fitowa daga ciki , Sanam ganin sa da tayi yasa ta
kauda Fuskar ta gefe tamkar bata gansa ba ,...
Murmushi Huneed yayi sannan ya k'araso wajen da take , duban ta yayi yaga idanun ta
sunyi ja tamkar ma kuka tayi , da sauri yace " Baby me yafaru dake haka naga idonki yayi ja ?
Sanam jitayi tamkar yazo mata da rainin hankali , komai daya faru ai shine ya janyo mata , inda
bai takura mata tazo ba taya zasu ganta bare su gaya mata magana , cike da jin zafin sa tace "
dama sai da nace maka bazan zoba amman ka takura min nazo , ko kad'an basa k'auna
sannan sun tsani Mumyna to meye amfanin inje inda suke , Huneed yayi murmushi sannan ya
rik'o hannun ta yace " sud'in sunfi kowa sonki da k'aunar ki , kintab'a ganin uwar da zata
durk'usa ta haifi d'a a cikin ta sannan tace bata k'aunar shi ? tamkar k'aramar yarinya haka
Sanam ta gyad'a kai alamar a'a , Huneed yaci gaba da magana " To kidaina cewa basa sonki
dan dukan su nagano tsantsar soyayyarki a idanun su , kece dai bakya son su tunda naga
hakan atare dake , Sanam ta d'an dubesa kad'an sannan ta kauda fuskar ta , har wannan
lokacin Huneed na rik'e da hannun Sanam d'in , k'asa yayi da murya sannan yace " inaso
Babyna tadaina fushi da Mumyn ta kuma Mahaifiyar ta wacce takawo ta duniya , nasan zaki
d'auka cewa Mumy Amarya tafi sonki fiye da Mumyn ki , to ba gaskiya bane dan duk duniya
bayan Allah daya halicceki ba wanda ke sonki sai Mumyn Twins , karki manta itace tayi rainon
cikin watakila ma bata iya cin komai , a haka har tayi nak'udar ki ta haifeki ta shayar dake har
kika kawo wannan matakin , kinga kuwa duk wanda zai nuna miki soyayya bayan ta yake ,
tunda Huneed yafara magana jikin Sanam yayi sanyi sosai , ganin hakan yasa Huneed yaci
gaba da yi mata nasiha tare da nuna mata girman iyaye musamman girman uwa , har suka
shiga motar suka tafi yana kuma yi mata nasihar wanda yake da tabbacin tana ratsa Sanam
har sassan jikinta.......

Hajiya Nafeesa tunda ta fita gidan Hajiya Harira suke shirya makircin su , har maganar
Maryam da yadda suka shirya ita da Fahad sai data gaya mata , Hajiya Harira kuwa taci gaba
da ingiza Hajiya Nafeesar akan hakan da sukayi yayi dai dai , sannan ta d'ora da cewa " kinga
inkika samu ta haihu ta baki d'an shikenan dama kafin lokacin kin raba Sanam da Alhaji kinsa
masa tsanar ta , Hajiya Nafeesa ta tab'e baki sannan tace " ai yanzu ko Alhaji ya daina son
Sanam ba muci riba ba , tunda gashi yanzu ta kuma haifo masa wasu , yanzu haka maganar
dana ke miki baki ga yadda yake rawar k'afa ba tamkar akansu aka fara masa haihuwa , Hajiya
Harira tace " suma dole atashi tsaye akan su dan sonake dukan su ya tsanesu har ita uwar
tasu , Hajiya Nafeesa tace " kin manta wannan shegiyar matar batajin asiri , wanne irin boka ne
ba muje gunsa ba akan araba ta da gidan amman kina kallo kamar dasa ta ma akeyi , Hajiya
Harira tace " kibani lokaci zan samo mafitar yadda za'ayi masu dukan su , haka suka yini suna
k'ullah yadda zasu tarwatsa Sanam da Hajiya Maimuna.......


Huneed yaso su biya ta gidan su Sanam ta gaisa da Hajiyar sa , amman ganin duk
Sanam d'in bawani walwala take ba yasa ya wuce da ita gida , suna shigowa Harabar gidan
suka ci karo Jaydeen a tsaye jikin motar sa yana danna waya , Huneed na kallon sa yaji wani
kishi ya kamashi dan ko ba'afada masa ba yasan wajen Sanam yazo , Sanam ta kalli Huneed
lokaci d'aya taga ya canza fuska yana kallon wajen da Huneed yake , tamkar tasa dariya haka

taji ganin yadda ya had'e girar sama da k'asa tamkar bashine ke lallab'ata ba , a zuciyar ta tace
bari nayi tsokana yanzu , kallon sa tayi tace " My dear ni zan shiga gida sai munyi waya ko ,
Huneed yadubeta sannan yace " zaki shiga gida ko kuma zakije wajen bak'on ki , to in kingaji da
ganina ni bangaji da ganin ki ba kuma bayanzu nakeso ki tafi ba , wani murmushi Sanam tayi
najin dad'in yadda Huneed ke san ta , dan tasan so ne kesawa a dunga jin kishin mutum , ta
karyar dakai tana duban sa cike da shagwab'a tace " haba My dear daga ganin mutum sai kace
bak'o na ne ? kasani ko bak'on Mumy ne ni bani dawani wanda mukayi dashi zai zo , Huneed
yace " to koma waye dai bazaki fita ya kallemin mata ba , Jaydeen tunda motar Huneed ta
tsaya yaji ajikin sa Sanam na ciki , dan dama me gadi ya sheda masa ta fita ita da wani ,
kishine ya kamashi tuni ya nufo wajen motar Huneed d'in , b'angaren da Sanam ke ciki ya shiga
bugawa , Huneed ransa ya b'aci shima ya bude murfin b'angaren sa ya fito , Duban juna sukayi
dukan su sannan Huneed yace " Malam lafiya zaka zo kana bugamin glass d'in motar ?
Jaydeen ya kalli Huneed cike da isa yace " wacce take cikin motar nakeson magana da ita
Malam bakai ba , Huneed ransa ya sake b'aci yace " meye had'in ka da mata ta dazakayi
magana da ita ? Jaydeen yace " matarka kuma ashe har ka aureta batare da sanin iyayen ta
ba , inaso kasani Sanam bata dace da namiji irinka ba ka kalleka ka kalli motar da kake hawa ,
wannan kad'ai ya isheka kasan ita ba sa'ar auren ka bace , Huneed yayi murmushin takaici
sannan ya kalli Jaydeen yace " sannu d'an gidan k'aruna rainon biskit da chocolate , inaso
kasani tunkafin in canza maka kalar fatar jikinka , Jaydeen ya kalli Huneed yaga lallai inyace
zasuyi fad'a to tabbas sai ya doku a gunsa , dan jikin sa ko ina a murd'e yake , amman duk da
haka Jaydeen bai karaya ba ya ci gaba da gayawa Huneed magana ....
Tuni Huneed yayi kansa yafara kai masa naushi a fuska , dai dai lokacin hancin motar Hajiya
Nafeesa ya sako kai cikin gidan , da sauri ta fito daga motar ko kashe ta bata tsaya yi ba , tana
zuwa tafara fad'in " meye hakan zangani kai meyasa baka da hankaline kasan dan waye kake
duka haka ? Huneed yanajin abinda tace kuma yasan dashi take , ko waiwayo ta baiyi ba yaci
gaba da dukan Jaydeen ,

Sanam tana cikin motar tana kallon duk abinda yake faruwa , sai dai ko ajikinta tunda dama
ita bawani k'aunar Jaydeen d'in take ba , dan dama yadameta da yawa ga uban kiran waya ga
kuma turo mata test kullum, Marin da Hajiya Nafeesa ta d'auke Huneed dashi shine yasa
Sanam katse tunanin ta tana mai bud'e murfin motar ta fito ........... [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
‍♀️‍♀️


*NA*
*Zee MD*



*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )

✨ (W.W.A) ✨

https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/






*Bisimillahir Rahamanir Rahim*



_Wannan Page d'in gaba d'aya sadaukar wane gareki , Aysha Fulani Happy
Anniversary One years, Allah yakaramuku zaman lafiya keda Oga Allah yakawo mana
yara nagari masu Albarka Ameen_



Chapter 33.


Tana k'arasowa ta dubi Hajiya Nafeesa wacce ke uban sababi akan dukan da
Huneed yayiwa Jaydeen , Sanam tace " amman Mumy meyasa zaki mari iya Huneed shi
wannan sakaran bazaki maresa ba ? duban ta Hajiya Nafeesa tayi baki sake tana mai maita
kalmar da Sanam d'in tafad'a , batare da Sanam tadamu da yanayin kallon da Hajiya Nafeesar
keyi mata ba taci gaba da magana " Na ruga na zab'i wanda zanyi rayuwa dashi meye zaka
dunga damuna , inaso kadaina zuwa wajena domin bazan tab'a saurarka ba , ta kalli Huneed
wanda ransa yake a mutuk'ar b'ace tace " dan Allah My Dear kayi hak'uri da Hukuncin Mumy a
gareka , Huneed jin abinda Sanam tace masa da kuma irin magan gun datayi yasa yaji zuciyar
sa tayi sanyi , yasan ko iya haka ta nuna shine acikin zuciyar ta bawani ba , Huneed yace "
Bakomi Baby indai akanki ne komai za'amin zan jure , abinda bazan iya jurewa ba shine wani
banza yadunga kallemin ke ko kuma ya furta miki kalmar so , Jaydeen da hancin sa ya fashe
da bakin sa tuni ya juya rai a b'ace ya shige motar sa yabar harabar gidan , shima Huneed
sallama yayiwa Sanam sannan ya koma ciki motar yaja ya fice daga cikin gidan .....

Sanam ko takan Hajiya Nafeesa bata bi ba tashige cikin gida abinta ........

*Bayan kwana biyu*

Kwata kwata Hajiya Nafeesa ta d'aukewa Sanam wuta , ko hanyar bata bari su had'a ko da
yaushe sai wasan b'uya take , in Sanam taje ganin ta sai ta tadda me aikin ta ta shaida mata
batajin dad'i , ahaka tagaji da zuwa itama tashiga sabgogin gananta , ....

Soyayyar Huneed da Sanam sai k'ara yawa take , kwata kwata yanzu Huneed nema yake
yakasa tafiya aikin sa , koda yaushe suna tare a waya kuma ko yaushe indai zasuyi waya sai ya
mata maganar Mumyn twins , yana kuma nuna mata matsayin ta a gunta da kuma cusa mata
soyayyar ta , yauma kamar kullum suna cikin waya da ita ya shiga tambayar ta wasu littattafai
tasani na addini ? shuru Sanam tayi batare da tace masa kanzil ba , jin hakan ya tabbatar
masa ko kad'an Sanam batayi islamiyya ba , murmushi yayi sannan yace " sai nemo mata
malamin da zai dunga koya mata karatun alk'ur'ani da wasu littattafan na addini , batare da
musu ba Sanam ta yadda dan itama tanaso tasan wasu abubuwan ,.....

Bayan kwana biyu da maganar su Huneed yasamo mata malamin kamar yadda yayi mata
alk'awari , a sati zai dunga zuwa sau uku kuma Huneed ya gaya masa sunayen littattafan da
zai koyar da ita , tuni Malam yafara zuwa kuma ba laifi Sanam tana bashi had'in kai......

Hajiya Nafeesa da Fahad zaun suna tsara yadda shirin su zai kasance , Maryam wacce
itace cikon ta ukun su tuni tasamu ciki wanda bazaka ce ga namijin da yayi mata shi ba , mazan
da take bi Ita kanta baza ta tantance ba , tuni Hajiya Nafessa tasa mata 2milloins a account ,
Maryam sai murna take dan itama zata faso gari kwana nan , Duban Hajiya Nafeesa tayi
sannan tace "Hajiya inaso in badamuwa zan dawo gidan nan da zama , Hajiya Nafeesa tace "
babu damuwa amman inaso kibari me gidan nan yatafi dan jibi zai bar k'asar nan , kuma zaiyi
kamar wata tara ko goma bai dawo ba , dan akwai wani aiki dazaije koyowa , Maryam tace "
nagode sosai Allah yanuna mana lokacin , Hajiya Nafeesa ta tashi ta haye sama abinta tabar
Fahad da Maryam zaune , suna ganin Hajiya Nafeesa ta mik'e suka matso jikin juna suka fara
tab'a juna da shafe shafe , Fahad yace " Babyna kisamun 1m. A account d'ina tunda kinga nine
nasamo wannan aikin , Maryam ta d'an turesa tana fad'in " gaskiya bazai yuwuba Dear , kaifa
Auntynka ce koda yaushe ka tambaye ta zata baka , nikuwa iya rabona zanci kafin inyi gaba ,
dan haka kayi hak'uri zan baka 200 Hundrend in sunyi maka , Fahad sosai yaji haushin abinda
Maryam d'in tace , sai dai ba yadda zaiyi tunda nema yake kuma shi bawani kud'i Hajiya
Nafeesa ke bashi ba , .....

Tunda ga ranar Hajiya Nafeesa ta tsiri cutar k'arya , haka ta k'i zuwa tayi barkar Twins har
Akayi suna , koda Alhaji Abba yayi mata magana sai tace bata da lfy yanzu daga ta mik'e jiri
take gani , amman da zarar taji sauk'i zata shirya taje taga yaran , ganin lokacin da take
maganar ma tana kwance yasa yarda da ita kuma yace dole ta shirya taje taga likita , dama
tuni ta biya likitan ta kud'i akan in sunzo ita da Alhaji lallai yace ciki gareta , aikuwa suna zuwa
akayi gwaje gwaje likita ya sheda musu tana da ciki , sosai Alhaji Abba ya shiga murna yana
mata addu'ar Allah ya sauketa lafiya , bakin sa ko rufuwa bayayi dan murna da baiwar da yake
ganin yasamu , haka suka taho gida sai lallab'a ta yakeyi yana wani ririta ta , ita kuwa sai wani
langab'ewa take tamkar me cikin gaske , Alhaji Abba yana shigowa palor yafara k'walawa
Sanam kira , dan yasan zata fi kowa farin ciki da wannan ciki tunda kullum burinta Mumyn ta ta
haifa mata k'anne , Sanam ta sauko daga sama tana fad'in " Daddy lafiya kuwa naji kana
k'walamin kira ? Alhaji Abba yace " bani goron Albishir kafin infad'a miki , hannu ya mik'o mata
yana murmushi , kallon Hajiya Nafeesa tayi sai wani ya mutsa fuska take ita ala dole me ciki ,

sake duban Mahaifin nata tayi sannan tace " Daddy nidai kafad'amin inji sai nabaka ko me
kakeso , Murmushi ya sake yi sannan yace " Mumyn ki zata haifo miki k'ani ko k'anwa nan da
8Month , wani tsalle Sanam ta doka tana matsawa kusa da Hajiya Nafeesa "Mumy dagaske
zaki haifo yaro daga cikin ki kema ? Murmushi Hajiya Nafeesa tayi sanna tace " Ea My luv zan
haifo miki k'ani me kama dake wanda zaki dunga d'auka kina yawo dashi kema , nan Sanam ta
shiga murna sosai , da sauri ta hau sama tana d'aukar wayar ta ta shiga kiran Huneed , yana
d'agawa tafara cewa " My Husbee Katayani murna Mumyna tasamu ciki itama , Huneed yayi
murmushi sannan yace " congrat My Baby kice dai yanzu zaku k'ara yawa kinzama Babba
tunda gashi kina ta samun k'anne , Allah yarabata dashi lfy yasa watarana Albishir zakimin
gashi kina d'auke da cikina , Sanam najin haka ta kashe wayar tana mejin kunyar maganar
tashi......

Diyana ta kira tashiga gaya mata itama , murna ta taya ta tare da cewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login