Showing 30001 words to 33000 words out of 80926 words

Chapter 11 - YAR KISHIYA Book Complete BY Zee MD.pdf

Zee MD   

10 Jul 2025

4196

kuwa ? nasan ba
lallai kina cin Abinci ba acan , shiyasa nafison muyi tafiya tare saboda baki kulawa , Hajiya
Nafeesa tamkar gunki haka ta koma tunda Sanam ta fito da yadda taga Daddyn nata ya tare ta
, cikin ranta take fad'in " wato da alamar Sanam bataci maganin nan ba kenan ? tabbas bata ci
ba tunda gashi Diyana taci kuma taga Yadda Daddyn Sanam d'in yayi mata , tayi nisa cikin
tunani taji muryar Alhaji Abba yana fad'in " Hajiya Nafeesa ko bakyaji ne ? firgigit tace " inaji
Alhaji kasan in muna tare da Sanam bana iya sauaran komai sai sautin ta , murmushi yayi
sannan tace " ai gatanan ta dawo sai kitajin sautin muryar ta ta , nan suka saka dariya wacce
a b'angaren Hajiya Nafeesa yak'e ceb, dan ji take kamar ta mik' e ta shak'e uba da yar saboda
takaici , sukuwa ko ajikin su sai hira suke cike da nishad'i , tuni Hajiya Nafeesa ta mik'e tace "
zataje d'aki tadawo ...
Tana shiga d'aki ta d'auko wayar ta ta shiga kiran Hajiya Harira.......





*Rashin Comment* *shine yake sani typing kad'an*‍♀️‍♀️


_Indai zanga Comment to kuwa zan muku typing me yawa_



*Dan Allah kugyara kudunga Comment*



*'Yar Mutan Kanawa* _Ce_✍�
[9/27, 09:54] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
‍♀️‍♀️


*NA*
*Zee* *MD*



*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046

✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨

*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*




⚜️ *BU'DA'D'DIYAR SOYAYYA*


Jameey yar' mutan kankia


*Promo* *Promo* *Promo*



Daga yau 21/5/2022 promo dinmu zai fara , har zuwa 30/5/2022 inshaa Allah , ga yanda
promo din yake.


#300-sau biyu a rana
#500-sau ukku a rana
#700-sau hudu a rana



kiyi man wannan number magana danjin yanda zaki biya 08160508316




Chapter 22.


Kuka Hajiya Nafeesa ta fashewa da Hajiya Harira , da sauri Hajiya Harira tashiga
tambayar ta " lafiya kike irin wannan kuka haka ? waye ya mutu kuma ? Hajiya Nafeesa tace "
wallahi wanda ayi mutuwa da abinda yafaru , dasauri Hajiya Harira tace " sakin ki Alhaji Abban
yayi ne ? da sauri Hajiya Nafeesa ta dakatar da kukan tace " ki rufamin asiri ba sakina yayi ba
shirin mune dai ya lalace , wani guntun tsaki Hajiya Harira tayi saboda takaici , taso ace ma
sakin Hajiya Nafeesan akayi tasamu tayi wuff da Alhajin , a fili kuma tace " garin yaya akayi
hakan kuma ? kinfi kowa sanin irin wahalar da mukaci kafin musamu wajen wannan bokan , ga
mak'udan kud'in da kika kashe , Hajiya Nafeesa ta goge Hawayen ta tace " duk tarin kud'in

dana kashe bashine yada meni ba , kawai ina tunanin yadda zamu kuma komawa wannan dajin
me nisan tsiya , gashi bokan nan kwata kwata bashi da imani wajen cewa sai ya kwanta dani ,
Hajiya Harira tace " wannan ma me sauk'i ce mutuk'ar buk'ata zata biya , sai dai kar mukoma
kizo kisake yin sakaci wani abun yafaru kuma , wai garin yaya hakan tafaru shirin namu ya
lalace , nan Hajiya Nafeesa tashiga gayawa Hajiya Harira duk yadda abin yakasan ce , wata
ashar Hajiya Harira tayi tana fad'in " shegiyar k'awar tata ce me kwad'ayi munafika , wanda ma
da Alhajin ya tsaneta kinga zata rage zuwa gidan sai muyi yadda mukeso , nan Hajiya Harira
tashiga kwantar wa da Hajiya Nafeesa hankali har da k'ara tinzura ta akan lallai sukoma wajen
bokan , abinka da wacce tayi nisa zuciyar ta ta k'e k'ashe tuni takuma jin wani k'arfi yazo mata ,
take suka shirya randa zasu koma wajen boka me doki.....

Sanam sai hira suke da Daddyn nata cike da so da k'auna , anan yashigo mata da
maganar taje ta gaida mumyn ta Hajiya Maimuna , Sanam take fara'ar dake fuskar ta ta
dakushe , cike da shagwab'a tace " Daddy nifa kasan matar nan taka ba sona take ba , koda
yaushe naje gidan nan bata da aiki sai yimin fad'a tana yimin wa'azi , murmushi yayi sannan
yace " haba Baby kinsan duk duniya bayan ni babu wanda zai soki tamkar ita , ko kin manta
itace ta haifeki kinga dole zata soki fiye da saninki , Sanam tamkar wata yarinya tace " wallahi
Mumyn nan gidan tafita sona sosai kuma kaima kasan hakan Daddy , shuru yayi yana nazari "
tabbas yasan Hajiya Nafeesa nasan Sanam tamkar itace ta haifeta , sai dai yasan baza ta tab'a
yi mata irin son da Mahaifiya kewa 'ya'yan taba , amman saboda kar yaja zancen yace "
shikenan Baby abar zancen duk sanda kika samu lokaci kije sai ku gaisa da ita , turo baki tayi
tana fad'in " to Daddy .......


Huneed tuni ya shirya cikin wani yadi me tsadar gaske , ga wani had'edd'en turare daya
fesa sai tashin k'amshi yake , yana fito yashiga falor Hajiyar su d'auke da sallama a bakin sa ,
amsawa tayi cike da sakin fuska tare da nuna kulawa ga d'an nata , durk'usawa yayi a k'asan
cafet yace Hajiya ta barka da wannan lokacin , cike da fara'a tace " Barka kadai My son ,
wannan wanka daga gani nasan wajen sirikata za'aje , sunkuyar da kai yayi yana dariya kafin
yace " Hajiya ta inaso kiyimin addu'a yau zanje na sanar da wacce nakeso inason ta , murmushi
tayi sannan tace " koda yaushe ina maka addu'a kai da d'an uwanka , Allah yazab'a muku
mataye nagari masu k'aunar ku , Allah yayi muku Albarka tare da sauran 'Yayan musulmi baki
d'aya , sannan inaso inkaje kagaida min da ita kace ina maraba da zuwan ta gidan gwarzon
d'ana , murmushi Huneed yayi yana mejin dad'in maganganun Hajiyar tasa , mik'ewa yayi
yana fad'in " zataji insha Allah Hajiya ta sai nadawo , yasa kai ya fice daga falor cike da farin ciki
fal a zuciyar sa , ......

Hajiya Maimuna ce zaune ita da Mahaifiyar ta tana hawaye , share mata hawayen nata
Mahaifiyar ta tayi tana fad'in " kici gaba da addu'a Maimunatu insha Allah komai zaizo k'arshe
duk tsanani yana tare da sauk'i , wata rana zata gane muhimmancin ki kuma saitayi nadama
sosai , yanzu kici gaba da mata addu'a dan addu'arki tafi komai tasiri a wajen ta , muma muna
yi miki kuma duk daren dad'ewa komai zai zo k'arshe , da irin wannan dad'a d'an kalaman
Hajiya Rabi take kwantar wa da 'yar ta ta hankali duk san da taje gida , yauma tun fitar Daddyn

Sanam ta hau motar ta tayo gidan su dan kawo kukan ta da Mahaifiyar ta ta , Tabbas duk
wanda yarasa *Uwa to yayi rashin Babban jigo a rayuwar sa wanda babu madadin ta* , *Allah
yajik'an iyayen mu wad'an da suka rigamu hidan gaskiya* , _wad'an da suke a raye kuma Allah
kabamu ikon yi musu biyayya_
Sosai Hajiya Maimuna ranta yayi mata dad'i da yadda mahaifiyar ta ta ta kwantar mata
da hankali , nan tasaki jiki taci gaba da hira da Hajiyar ta ta har lokacin da tayi mata sallama ta
koma gida .......

Hajiya Rabi sosai take tausayin 'Yar tata ganin yadda akayi mata fin k'arfi akan 'yar ta , ita
kanta batace ga randa ta tab'a ganin Jikar tata Sanam tazo gidan nata ba , amman haka take
kwantar mata da hankali har tasamu ta sauko......

Sanam hirar su suke akan komawar ta sch dazatayi , Hajiya Nafeesa ce ta fito daga
b'angaren ta tamkar babu abinda yake damunta , tana zuwa tasamu guri ta zauna hirar suka ci
gaba dayi har ita , cikin ranta tana fad'in " kuyi duk abinda zakuyi nan da kwana hudu zan raba
ku da farin cikin dake fuskokin ku , sallamar da megadi yayi ita ta katsesu , cike da girma mawa
yace " ranki yad'ad'e ana sallama dake a waje , Sanam tasan da ita yake amman ko kallon sa
batayi ba , sai Hajiya Nafeesa ce tace " waye yakeson ganin nata ? risinawa yakumayi yace "
wani mutum ne a waje ban waye shi ba , Hajiya Nafeesa tace " kaje kace " yashigo ka kaishi
d'akin saukar bak'i gatana zuwa , Sanam da sauri ta kalli Hajiya Nafeesa tana fad'in " Mumy
taya zakimin haka ? murmushi tayi cike da kissa tace " haba my Luv kinsan dai yakamat ace
kinfara sauraren samari dan kin isa kuma kin kai , nan tashiga lallab'a ta har tasamu ta amince
zataje , Alhaji Abba yana jinsu ko tari baiyiba yada saka aransa zai fita dan ganin waye yazo
gun 'yar tasa , dan yanson ace kowaye yazo to yaasance d'an mutunci ne wanda yasan mutucin
ta , wanda zai iya rik'e masa yar sa batare da ta nemi komai ta rasa ba , mik'ewa Sanam tayi ta
fita ahaka dan tace babu abinda zata canza ko kuma ta gyara , .....


tana zuwa K'ofar d'akin saukar bak'i taji wani k'amshi yana fitowa , lumshe idanun ta tayi
tana son tuna inda tasan k'amshin turaren , ta dad'e a tsaye tana tunanin sannan ta tura k'ofar a
hankali tare da yin sallama , Huneed na zaune yana dannan waya yanajin shigowar ta ya d'ago
yana amsa sallamar tare da duban ta , Sanam naganin Huneed k'irjinta ya buga take taji wani
abu ya tsaya mata a k'irji wanda tarasa ko na farin cikine ko akasin hakan , kafesa tayi da ido
tamkar taje tafad'a jikin sa wani kyau dataga yayi mata , tayi nisa a tunani taji yana hure mata
ido yana fad'in " irin wannan kallo sai kace baki tab'a ganina ba , da sauri ta rufe fuska tana
murmushi tare dajin kunya , shima murmushin yayi yace " barka da fitowa shugabar 'yan rigima
, rigimar ki tana da yawa kinsa na rud'e har naga bazan iya jira ba sai nazo , Sanam wata
kunya takumaji tamkar ta nitse cikin ranta tace " kardai ace ya fahimci ina kishinsa ? kuma
mutuk'ar ya fahimta to tabbas yasan tana sonsa kenan ? a hankali ta furta " wayyo shikenan na
rusa ajina a idon sa , Huneed kamar yasan abinda take tunani yace " Sanam dan mace taso
Namiji ba laifi tayi ba fa , hasalima hakan yayi duk da baki furta min kina sona ba , amman iya
hakan ya bayyana min cewa yadda nakamu da sonki nima haka kike sona , sai dai a zahirin

gaskiya nafi sonki dan tunda ga randa nafara ganinki nakamu da sonki sosai , duk wannan
takurar da nayi miki da kuma yadda na dunga bibiyar ki wallahi sonki ne yasa hakan ,
durk'usawa yayi da gwuiwar sa k'asa yace " Sanam yau ga Huneed a gabanki ina me rok'on
soyayyarki , inason kizama uwa awajen 'Yayana sannan ki zama wacce zata zame min bangon
jingina duk lokacin da nazo gareki ......


Sanam tamkar zata saka ihu saboda murna , wani dad'i takeji har ranta sai dai kuma ai
yace mata yana da mata , to taya zata rayu da wanda yake da mata , dan ita fa ko a sittira
batason kishiya balle a rayuwar gidan mijin ta , dan ta tsara rayuwar da zatayi da mijinta
mutuk'ar tayi aure , to taya zataso wata takasance tare da mijin nata , ganin shurun da tayi
yasa Huneed karaya yana mik'ewa yana duban ta , idanun sune suka had'u waje guda take
kowa yaji wani abu tunda ga tsakiyar kansu har ilahirin gangar jikinsu............
[9/27, 09:55] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
‍♀️‍♀️


*NA*
*Zee* *MD*



*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/


*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*




Chapter 23.


Sunfi Minty biyar ahaka kafin Sanam tayi k'arfin halin janye nata idon , Ajiyar zuciya
suka saki lokaci d'aya kafin kuma shuru yasa ke biyo baya , k'wan k'wasa k'ofar d'akin ce ta
katsesu su dukan su suka dubi hanyar shigowar , Me gadin gidan ne ya shigo d'auke da
sallama a bakin sa sannan yace " ranki ya dad'e Alhaji yace kuje keda bak'on naki ku samesa a
palor sa , Sanam ta d'aga masa kai alamar to batare da ta furta komai ba , Bayan fitar megadi
da kamar minty biyar Sanam tadubi Huneed tace " Bisimillah katashi muje gun Daddy yana

kiran mu , Huneed batare da fad'uwar gaba ba ya mik'e suka jera suka nufi cikin gidan ....

Tunda Jaydeen ya isa gida ya ke maganar Sanam , Mumyn sa ta dube sa tace " My Son.
Kodai gamo kayi a hanya ne ? tunda ka dawo kake zancen yarinyar nan , ko abinci kaki
tsayawa ka nutsu kaci , murmushi Jaydeen yayi sannan yace " Mumy dan dai baki ganta ba ne
shiyasa zaki ce haka , Yarinyar ta had'u sosai Mumy ga ta irin macen da nakeso ce , Hajiya
Halima tayi murmushi sannan tace " wacce irin mace ce kake so My son . ? kafad'i ko wacce
irin mace ce a duniyar nan , mutuk'ar kud'i zai iya siyo maka soyayyar ta to tabbas kasame ta ka
gama , yanzu abinda nakeso dakai shine " ka tsaya kaci abinci kayi wanka sai ka nutsu ka
fad'amin yar gidan waye a garin nan na Abuja , Murmushi Jaydeen yayi najin dad'in abinda
Mumyn nasa tace , fara cin Abincin yayi yana fad'in " nasan komai nakeso a duniyar nan kuna
samar min shi Mumy , dan haka inaso a wannan lokacin a nemomin auren wannan yarinyar dan
shine kawai cikar burina a yanzu , nan yaci gaba da bata labarin irin had'uwar da Sanam d'in
tayi , har kwatan ta mata yadda take magana yake cike da sauk'i , Jaydeen kenan 'Da d'aya
tilo a gurin Ambasador da kuma Hajiya Halima......


Sallama su Sanam sukayi a palor cikin gidan inda Daddyn nata yake zaune shi da Hajiya
Nafeesa , amsawa Hajiya Nafeesa tayi d'auke da murmushi a bakin ta , sai dai tana had'a ido
da Huneed taji k'irjin ta ya buga , kwata kwata taji tana tsoron sake kallon sa batare da tasan
me hakan ke nufi ba , A b'angaren Alhaji Abba kuwa yana kallon Huneed yaji ya masa kwarjini
gashi ingarman Namiji wanda kowacce mace zatayi burin kasan cewa tare dashi , take ya fara
fara'a tare da cewa " sannu da zuwa sirikina , kunya ce ta kama Huneed ya durk'usa yana gaida
Alhaji Abban , da sauri Alhaji Abba yace " mik'e ka zauna a kujera kaji kasaki jikin ka tamkar ba
yau kafara zuwa cikin gidan nan ba , Huneed ya mik'e ya zauna a kujera yana murmushin jin
dad'in karamcin da Alhajin yayi masa , Sanam zama tayi kusa da Daddyn nata tana murmushi
najin dad'in yadda taga mahaifin nata ya karb'i Huneed , gaisawa sukayi cike da mutuntawa
sannan Huneed ya juya yana gaida Hajiya Nafeesa , amsawa tayi tana k'ak'alo murmushin dole
tare da yi masa sannu da zuwa , mik'ewa tayi sannan ta dubi Sanam tace " My Angel zo muje
ki kawo masa kayan motsa baki , haka ake tarar bak'o maza muje kinji , Sanam ta mik'e tana
turo bakin shagwab'a tana fad'in " kai Mumy nifa kinsan bansan yadda akeyi ba , da ido
Huneed yabi Sanam da kallo a zuciyar sa yana fad'in " ashe a cikin gidan ma haka kike

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login