Showing 18001 words to 21000 words out of 80926 words

Chapter 7 - YAR KISHIYA Book Complete BY Zee MD.pdf

Zee MD   

10 Jul 2025

4092

sa sun k'ara mata magana ba suka shige sukayi tafiyar su cikin gida......

Sanam na zaune a samon motar wayar ta ta soma ruri , d'auko wa tayi tana duba screen
d'in wayar dan ganin waye yakira ta , Daddyn tane da sauri ta d'aga wayar tana fad'in " Miss u
my luvly Daddy , shima cike da k'auna yace " My Dauther dafatan kin sauka lafiya ? lafiya lau
Daddyna ina Mumy na take ? Alhaji Abba yace " ina gidan d'aya Mumyn naki gata ku gaisa ,
daman baki mata sallama ba kika taho , dan danan Sanam ta turo baki tamkar tana ganin su
tace " Daddy nifa bance kabata wayar ba kasan ba sona takeyi ba , Hajiya Maimuna da wayar
take a kunnen ta tuntuni ji tayi maganar ta doke ta , cikin ranta tace " duk wanda zai soki a
duniya bayana yake , nice wacce na d'auki cikin ki har na haifeki kika girma kika zama hakan ,
Maganar Sanam d'in ce ta katse ta daga tunanin datake tace " ba Daddyn naki bane nice ,
Sanam cike da jin haushi tace " kinyini lafiya ? Hajiya Maimuna tayi murmushin takaici wai 'Yar
da ta haifa ce keyi mata irin wannan gaisuwar , kashe wayar tayi batare da ta ce uffan ba ta
mik'awa Alhaji Abba wayar sa tamik'e tabar gurin .......

Sanam najin Hajiya Maimuna ta kashe wayar ta tab'e baki tare da fad'in " huta roro ,
saukowa tayi daga kan motar ta nufi cikin gidan Itama ......

Duk abinda Sanam keyi Huneed na tsaye yana kallon ta , har ta shige cikin gidan sannan
yasa me taxi ya maida shi hotel d'in daya sauka , koda ya koma hotel d'in band'aki ya shiga
yayi wanka sannan ya fito ya anso abinda zai iya ci yadawo , yana cin abincin yana tunanin
yadda zai gyara Sanam tunda ya fahimci batajin magana sosai , haka ya gama batare da ya
yanke me zaiyi mata ba ya kwanta dan ya huta......

Washe gari..

Yau akeyin Bridel Shower dan haka tunda suka tashi suka fara shirye shirye , Sanam na

zaune sai faman chat take da Diyana suna labarin k'awayen su , sai wajen k'arfe biyu ta tashi
tayi wanka sannan ta fito ta shirya cikin wata riga wacce suka d'inka duk iri d'aya , sosai kayan
sukayi mata kyau dan dama Sanam akwai kyau na tamkar itace ta k'era kanta , gashin ta
dayake a baje a gadon bayan ta ta kamo tasa masa ribon kalar rigar data saka , sannan ta saka
wani hils d'in takalmi me tsinin gaske , kwalliya bata dami Sanam ba sai dai tana saka kwalli
wanda ke k'ara fito da kyawun idanunta masu kama da madara , fitowa tayi palor tuni mutanen
dake zaune cikin falor suka saki bakin kallon ta , Ammin Rauda tana duban ta tace " wow my
Beautifull queen , murmushi Sanan tayi wanda siririyar wushiryar ta ta fito tare da dimple d'inta
ya lotsa , ai take suka rud'e sai cewa suke " wow so beautifull nice , aikuwa Sanam tasamu
abinda takeso wato a fasa mata kai ace tana da kyau , wani yauk'i tashiga yi har ta fito harabar
gidan , lokacin Abokan Ango sunfara zuwa d'aukar su dan kaisu wajen Party , suna ganin
Sanam kowanne ya kafeta da ido suna k'arewa k'ugunta kallo da k'irjin ta , wanina ciki yace "
wannan Babyn ta had'u sosai dama zata yarda tabani dare d'aya dana mallaka mata duk
abinda takeso , dukan su suka shiga yabon halittar Sanam wacce ta tsaya gefe d'aya tana
danna waya da alamar kiran wani zatayi .......


Huneed tunda gari ya waye ya shirya ya shiga gari , sai wajen biyu da rabi yasamu kansa
da son zuwa gidan da Sanam ta sauka , dai dai lokacin dayazo a dai dai lokacin Sanam ta fito
da wannan shiga , bayan wata bishiya ya lab'e ya saka face mark d'in sa da glass yana lek'owa
, ganin yadda maza ke kallon Sanam hakan ya kuma b'ata masa rai over , cikin ransa yace "
wai wannan yarinyar anya mutum ce kuwa ? sai kace shaid'aniya zatayi irin wannan shigar ,
tamkar ma ba musulma ba dubi jikinta ko d'ankwali bata saka ba , Asuk' ne ya fito daga motar
ya nufo wajen Sanam , tana zuwa yayi hugging d'in ta batare da ta kula dashi ba , tuni mutanen
dake gurin suka fara yin tafi suna jinjina masa yadda yayi hakan , Huneed nadaga bayan
bishiya jiyayi juwa na neman kamashi , wani abu yaji ya tokare masa a k'irjin sa tamkar
numfashin sa zai tsaya haka yaji , Sanam jin yadda Asuk' ya rungume ta yasa ranta yayi
mugun b'aci , k'arfin ta ta had'a guri guda ta hankad'ashi gefe , tana yin hakan tayi saurin
komawa cikin gidan dan yagama b'ata mata rai over , Asuk' sosai yaji haushin abinda tayi
masa dan har bige kansa yayi jikin motar , dan haka shima cikin gidan yabita.......

Huneed take ya yanke shawarar mutuk'ar Sanam tafito to sai ya d'auke ta , dan ya fuskan
ci wannan guy d'in zai iya yimata komai yadda ya fusata , kuma shima bazai so ace ko d'an
yatsan ta wani banza yasake rik'ewa ba , haka ya zauna zaman jiran fitowar ta , yana zaune
motoci suka fara wucewa dan tafiya gurin Kamu , kwata kwata bai ga Sanam ta fito ba har ya
tashi yafara nufar cikin gidan dan ganin me takeyi , lokacin kowa yatafi wajen party har Ammin
su Rauda da k'awayen ta itama , ita kuwa Rauda dama tuni suna can ana shirya ta daga can
za'a wuce sa ita , yana tsaye yana kai kawo a harabar cikin gidan sai ga Sanam da gudu ta fito
tana kuka rigar ta duk ta yage ana ganin jikinta , bayan ta Asuk' ne daga shi sai gaje ran wando
ya biyota da gudu shima , wajen Huneed ta nufo tana fad'in " dan Allah ka taimaka min wallahi
d'an iska ne , wani mari Huneed ya tsinka mata sannan ya janyo hannun ta ya kawo ta wajen
Asuk' dake tsaye yana kallon su yace " gatanan kayi mata duk abinda kakeso kayi , mamaki ne
yaka ma Sanam tafara Nazarin a inah tasan wannan muryar ? Asuk' ya rik'e hannun ta tare da

cewa " Huneed thank u Yana k'ok'arin janta ya shigar da ita cikin gidan , kwata kwata Sanam
bata ceton kanta take ba so take ta tuna muryar waye wannan dan tabbas tasan muryar kuma
taji ta ba sau d'aya ba , juyawa Huneed yayi yana dafe kansa yayin da Asuk' yake jan hannun
Sanam zai shiga da ita cikin gidan , ita kuma tana wai wayen Huneed tana son sanin waye shi ?
gab da zasu shiga k'ofar falor Huneed yace " Stop dawata murya wacce tasa dukan su suka
firgita , tuni Asuk' yasaki Hannun Sanam yana duban Huneed wanda ya nufo su gadan gadan
tamkar zaki , yana zuwa yashiga duka Asuk' yana fad'in " rungumar da kayi mata baiyi ba sai
ka ai ga keta mata haddi , mara tarbiya kawai wawa jaki , sai dukan sa yake tamkar zautacce
haka yakoma , tuni ya sumar da Asuk' sannan ya waiwayo kan Sanam wacce tagama tsurewa
jikin ta sai rawa yake , yana zuwa yajanyo hannun ta batare dayayi magana ba har suka fita
daga gidan suka nufi titi , tunda ya rik'e mata hannu ta tuno da ko waye , Huneed bai saki
hannun Sanam ba har sai da suka isa Hotel d'in dayake suka shiga har cikin d'akin daya kama
...........




*Comment plss*



*'Yar Mutan Kanawa* _Ce_ �
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
‍♀️‍♀️


*NA*
*Zee* *MD*



*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046

✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨


*Bisimillahir Rahamanir Rahim*



Chapter 14.

Sunfi kusan minty goma a haka sannan aka d'auke ruwa , da sauri Sanam ta mik'e
daga jikinsa tana sunkuyar da kanta k'asa dan kunya ce ta kama ta , Huneed shima mik'ewa
yayi tsaye yana dube dube tamkar wanda yake neman wani , motocin da suka hango sun nufo
k'ofar gidan su Rauda ya tabbatar musu da Andawo daga wajen party , Huneed ya juyo ya kalli
Sanam yace " zan iya tafiya yanzu tunda naga sundawo , inaso ki kula da kanki sai wani lokacin
, bai jira amsar ta ba ya wuce yabar wajen......

Da kallo Sanam tabi bayan Huneed tana jin kamar ta tashi ta rungumosa, cikin ranta taji
kamar ta kirashi tace yadawo su dauwa ma a haka, tana kallon bayan sa har ya k'ulewa ganin
ta amman ta kasa d'auke idon ta akansa , tayi nisa cikin tunanin taji andafa mata kafad'a , da
sauri tayi firgigit tadawo daga tunanin data keyi tana duban wanda ya dafa ta , Rauda tagani
tasaha kwalliya cikin shigar amare ba k'aramin kyau tayi ba , Rauda tace " ina kikaje Sanam
kwata kwata banganki a wajen Kamu ba , gashi in ankira wayar ki bakya d'agawa ina fatan dai
lafiya ? murmushi Sanam tayi sannan tace " bansan wajen ba, kuma na hau taxi muka gama
yawo bangane ba har aka fara ruwa , Rauda tace " amman Janifa ta gayamin cewa taga kin
shirya cikin shigar da sukayi , kuma lokacin ankawo motoci amman baki shiga kowacce ba ,
Sanam ta mik'e tace " kawai Allah baiyi zanzo ba amman gobe insha Allah bazanyi missing d'in
Lunch ba , tare suka jera suka shiga cikin gidan suna hira abinsu , koda suka shigo harabar
gidan Sanam tashiga dube dube kozata ga Asuk amman bata gansa ba , haka suka shige cikin
gidan wanda yake acike da mutane 'yan biki........


Sanam kwata kwata takasa rintsawa saboda tunanin Huneed , babu abinda ke mata yawo
a ido sai hoton kwanciyar datayi a jikin Huneed , lumshe idon ta tayi tana wani murmushi tana
k'ara rungume filon dake hannun ta , a hankali ta furta " wannan Guy d'in na musamman ne
yana burgeni , a haka barci yayi gaba da Sanam cike da tarin mafarkan Huneed.......

A b'angaren Huneed tunda yabar wajen Sanam ya taho sukayi waya da ogan su , nan aka
sheda masa kiran gaggawar da ake musu akan rikicin da 'yan ta'adda suke a garin sakkoto ,
Kwata kwata Huneed kiran bai masa dad'i ba kawai dai dan ba yadda zaiyi ne , amman kafin
yatafi ko sau d'ayane sai yakoma yaga Sanam dan yarinyar ta tsaya masa arai , kawai halayen
tane basuyi ba kwata kwata amman da sannu zai gyara ta .......


Washe gari.....

Tunda Sanam ta tashi taji tana k'aunar ta sake ganin Huneed , bayan ta karya tayi wanka
tashirya cikin wata doguwar riga me kyau daga cikin wad'an da ya siya mata , samun kanta tayi
da saka d'aya daga cikin Hijab d'in mahadin rigunan , ba k'aramin kyau tayi ba ita kanta sai sai
k'ara duba mirror take , tana fitowa su Rauda suna zaune suna shirya abubuwan da zasu yi

amfani dasu anjima , suna ganin ta suka tsaya suna kallon ta kowanne sai yaba kyan datayi
suke , Rauda tace " Sanam kowanne kaya kikasa sai kinyi kyau inama ace nice haka ,
murmushi tayi sannan tace " kema haka ai kike My R kowanne dresing kikayi sai yayi miki kyau
, Rauda tayi murmushi tace " ai nasan kinfini nesa ba kusa ba , wai ina ma zakije haka muna
shirye shirye kina ficewa ke kuma ? Sanam tace " sorry my R yanzu zandawo ba dad'ewa zanyi
ba , da sauri ta fice dan batason Ammi taji zata fita ta tsaida ta ma , tana fitowa harabar gidan
suka kuma karo da Asuk , tana ganinsa ta had'e ranta tana yin gefe da fuskar ta , shima
dayake yanajin haushin ta ko kallon ta bai kuma ba ya shige abinsa tamkar bai ganta ba .....

Taxi ta tsaida tagaya masa inda zai kaita , sai da ta shiga ta zauna sannan tafara zancen
zuci " to yanzu innaje mezan ce masa nazo yi ? wata zuciyar tace " kawai kice kin yarda abinki
ne shine kika dawo d'auka , tana wannan tunane tunanen nata har suka zo dai dai k'ofar Hotel
d'in , fitowa tayi sannan tabiya me taxi kud'in sa yayi gaba , ta dad'e a k'ofar wajen tana kaiwa
da komowa , da shawarar da zuciyar ta ta yanke nacewa wani abun ta yardar tashiga ciki......


Tunda gari ya waye Huneed ya had'a kayan sa cikin jakar sa , wajen goma na safe a can
k'asar ya fita yashiga gari zaiyiwa Hajiyar sa siyayya , daga can ya biya airpot yagama komai
jirgin su zai tashi k'arfe uku na rana , yana gama komai ya nufi gidan su Rauda ya tsaya daga
wajen daya saba tsayawa yana lek'en harabar gidan ko Allah zai sa Sanam ta fito , yafi minty
30 amman baiga kowa ba sai yara suna ta wasan su abinsu , ganin yana k'ara b'ata lokaci yasa
ya juya zai tafi , wata zuciyar tace " to inta fito mai zai ce mata ? kawai ya juya ya hau taxi
yakoma Hotel d'in , a lokacin Sanam na zaune a reception dan sun sheda mata me number da
ta tambaya ya fita , tana xaune ta had'a kai da gwiwa taji wani k'amshi ya doki hancin ta , tana
d'agowa taga wucewar Huneed batare da ya kula da ita ba , sai da tabari ya jima da wucewa
sanna ta nufi d'akin nasa......

Tana zuwa ta k'wank'wasa k'ofa daga ciki yace " yes coming , tura k'ofar tayi tashiga cikin
d'akin lokacin dagashi sai tawul zai shiga wanka , tana ganin da haka ta juya da baya zata
koma waje , da sauri yace " karki fita bati nashiga toilet wanka zanyi , da sauri ya fad'a cikin
toilet d'in yanajin wani farin ciki da ganinta dayayi , Sanam kuwa yadda tagansa ba k'aramin
tsoro taji ba , tunda take bata tab'a ganin jikin namiji haka ba sai yau , samun waje tayi ta
zauna tana tunanin meyake shirin faruwa da itane.......




*Comment* plss



*'Yar Mutan Kanawa* _Ce_ �
[9/27, 09:45] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*

_Rik'on Me Hak'uri_
‍♀️‍♀️


*NA*
*Zee* *MD*



*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046

✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨


*Bisimillahir Rahamanir Rahim*



Chapter 14.


Sunfi kusan minty goma a haka sannan aka d'auke ruwa , da sauri Sanam ta mik'e
daga jikinsa tana sunkuyar da kanta k'asa dan kunya ce ta kama ta , Huneed shima mik'ewa
yayi tsaye yana dube dube tamkar wanda yake neman wani , motocin da suka hango sun nufo
k'ofar gidan su Rauda ya tabbatar musu da Andawo daga wajen party , Huneed ya juyo ya kalli
Sanam yace " zan iya tafiya yanzu tunda naga sundawo , inaso ki kula da kanki sai wani lokacin
, bai jira amsar ta ba ya wuce yabar wajen......

Da kallo Sanam tabi bayan Huneed tana jin kamar ta tashi ta rungumosa, cikin ranta taji
kamar ta kirashi tace yadawo su dauwa ma a haka, tana kallon bayan sa har ya k'ulewa ganin
ta amman ta kasa d'auke idon ta akansa , tayi nisa cikin tunanin taji andafa mata kafad'a , da
sauri tayi firgigit tadawo daga tunanin data keyi tana duban wanda ya dafa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login