Showing 39001 words to 42000 words out of 80926 words

Chapter 14 - YAR KISHIYA Book Complete BY Zee MD.pdf

Zee MD   

10 Jul 2025

4188


kiran Huneed wajen goma tare da test d'in sa , dafe kai tayi tana fad'in ohh my god na manta
kwata kwata da wayar ma , Test d'in dayayi mata ta karanta wanda fad'a yayi mata akan gudun
data fita d'azu tanayi , murmushi Sanam tayi sannan a hankali ta furta " shauk'in soyayyarka
itace tamin yawa har nake wannan gudun , amman daga yau nadaina dan banaso mu kuma
wani fad'an , kiran wayar tashi tashiga yi har ta katse wayar bai d'aga ba , Sanam ta furta
wato fushi kayi kaima bazaka d'aga ba kenan , haka ta dudduba sauran kiran wanda duk
number d'aya ce kuma batasan number ba , tsaki taja ta ajiye wayar tare da hayewa gado ta
kwanta , ..

Jaydeen da Hajiyar sa tunda suka taho daga gidan su Sanam suke hirar ta , Hajiya
Halima tace " gaskiya yarinyar tahad'u sosai dole tasace zuciyar Jarumin d'ana , murmushi
Jaydeen yayi sannan yace " Mumy yarinyar fa ta had'u sosai ba inda bazan shiga da ita ba ,
daman Abokaina na cewa saga irin yarinyar da zan aura , aikuwa zasu ganta wacce zatafi duk
nasu matan cewar Hajiya Halima , dan tana son duk abinda zai kankarowa Tilon d'anta mutunci
, kuma ta shirya tsaf dan bin duk wata hanya da Jaydeen zai samu Sanam , Abinda ya tsaya
mata arai shine ganin kwata kwata Sanam bata kama da Hajiya Nafeesa , Sanam Farace Sol
har wani jaja takeyi tsabar farinta , gata da wani sirtaccen kyau mara misaltuwa , ga gashi

tamkar 'Yar india ga dirin jiki tamkar dai ita tazab'i halittar ta , ita kuma Hajiya Nafeesa ba fara
bace kuma ba bak'a bace , kawai dai tana da kyau itama ga kuma dirin jiki , kawar da zancen
tayi daga zuciyar ta tana fad'in " inajin ita ko da Mahaifin ta take kama.....


Bayan Huneed yagama ganawa da Ogan sa ya fito yaga kiran Sanam , zama yayi cikin
motar sannan yashiga kiran number ta ta , sai da ta kusa yankewa sannan Sanam ta d'aga ,
Huneed yace " barka da wannan lokacin My wifey , Sanam wani lumshe ido tayi tare da janyo
filo tana k'ank'amewa dan jin dad'in sunan daya kira ta dashi , murya k'asa k'asa tace " Barka
kadai dafatan kayini lafiya , Kashe murya yayi yana fad'in " ban yini cikin sukuni ba tunda banji
muryar wacce zata sakani inyini cikin sukuni ba , Murmushi Sanam tayi sannan tace " ayya
sorry yau busy nayi dayawa ban samu d'aukar waya ba , Huneed yace " shiyasa naga kinfita da
wannan gudun naki da kikamin alk'awari kindaina , Sanam batasan sanda tasa dariya ba tana
fad'in " sorry Sojana nadaina daga yau , wani dad'ine ya rufe Huneed dajin sunan da Sanam ta
kirashi dashi , a hankali ya furta My Wifey d'an mai maita sunan da kika kirani dashi plss , sai
sannan Sanam taji kunya ta rufeta da sauri ta kashe wayar , Huneed murmushi yashiga yi
nasamun Nasarar mallakar zuciyar Sanam d'in , wani nishad'i yajishi aciki nan da nan ya tada
motar ya nufi gida dan bazai iya jurewa ba dole yaje yaga sanyin idaniyar sa , .......

Tuni Fahad yakira Maryam a waya ya sheda mata yana son ganin ta , Maryam dayake
Allah yasa mata k'aunar Fahad jitayi tamkar tayi tsalle saboda murna , nan ya kwatanta mata
gidan Hajiya Nafeesa sukayi sallama , ........
[9/27, 10:00] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA
_Rik'on Me Hak'uri_
‍♀️‍♀️


*NA*
*Zee* *MD*



*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/





*Bisimillahir Rahamanir Rahim*

Chapter 27.


Tuni Maryam ta shirya tsaf ta nufo gidan Hajiya Nafeesa , dan cike take da
d'okin sanin dalilin kiran nata da Fahad yayi , tana zuwa k'ofar gate ta kira Fahad ta sheda masa
gata nan a k'ofar gate d'in gidan ......

ba ad'auki lokaci ba Fahad yak'araso suka shigo gidan tare , tunda Maryam ke shige shige
bata tab'a shiga gidan daya had'u kamar wannan ba , tuni tasaki baki sai kallon ko'inah take na
gidan tamkar 'Yar k'auye , Fahad yajanyo ta jikin sa yana fad'in " wannan irin kallon gida tamkar
wacce tazo daga Ruga ? Murmushi Maryam tayi sannan tace " ai gidan ne yayi mugun had'uwa
tamkar a turai , gaskiya banga laifinka ba Dear daka dawo wannan gidan da zama , dan ko nice
Yaya ta take irin wannan gidan wallahi da gudu zan had'o kayana nadawo , dariya Fahad ya
shiga yiwa Maryam yana fad'in " ai yanzu ma zaki dunga shigowa duk sanda kike so idan har
kin amincewa me gidan da buk'atar ta , Maryam ta dubi Fahad alamar tambaya ? ya d'aga
mata kai yace " muje daga ciki sai muyi magana ,.....

Tana shigowa cikin Palor gidan sai kawai taga ashe harabar gidan ba komai bace duba da
irin had'uwar da palor yayi , sakin baki tayi tana kallon palor wanda yagaji da had'uwa tamkar a
turai , ba kowa a palor shiyasa Maryam tasaki jiki tana k'arewa palor kallo , Fahad ya mik'e
yana ce mata " bari naje nayiwa Hajiya Magana kinji , Maryam tace " to batare da ta dube saba ,
sama ya haye abin sa ya nufi d'akin Hajiya Nafeesa.......

Sanam tunda tagama waya da Huneed takejin wani dad'i na ratsa duk ilahirin jikin ta ,
mik'ewa tayi tafad'a toilet dan yace mata gashinan zuwa , samun kan ta tayi da murnar son
ganin sa dan haka dole tayi masa kwalliya ta musamman ......

Hajiya Nafeesa na zaune suna waya da Hajiya Harira Fahad yashigo d'akin , sallama tayi
wa Hajiya Harira tana fad'in " sai mun sake waya ta katse wayar , duban Fahad tayi sannan
tace " lafiya kuwa ? Fahad ya zauna a hannun kujerar dake bedroom d'in nata yace " Yarinyar
nan da zamu sa aikin itace ta k'araso , Hajiya Nafeesa tace " har tazo kenan , kaje kufara
magana ganinan zuwa ka gaya mata komai da muke so tayi kafin nazo , Fahad ya mik'e yana
fad'in " to shikenan sai kin sakko , har yaje bakin k'ofah zai fita Hajiya Nafeesa tace " Fahad
inaso kaduba ko 'inah na palor nan ka tabbatar ba kowa dan banaso muyi magana wani yaji ,
Fahad yace " angama Hajjaju yasa kai yafice daga palor......


Koda Sanam ta fito daga wanka zama tayi a gaban Mirror tayi kwalliya ta musamman ,
bayan tagama tabi jikin ta da wata had'add'iyar Khumra , bud'e dirowar kayan ta tayi tafara
duba wanda zata saka , idanun tane suka sauka kan wata atamfar ta sabuwa d'inkin riga da

siket strike gown , tsagar dake bayan siket d'in abud'e take ko kad'an ba'arufe taba , sosai
kayan suka kama jikin ta , hips d'in ta tamkar an dasa mata shi haka yayi , d'an kwalin ta ta
d'aura dan Sanam sosai ta iya d'aurikan d'an kwali kala kala , fesa turatuka daya kawo mata
tayi sai mur mushi take , mayafi kalar atamfar ta d'auko k'arami tare da wani hill d'in takalmi tasa
, kana ganin ta sai kazata wani gagarumin biki zataje irin had'uwar datayi , tana cikin saka
takalmi kiran wayar Huneed ya shigo wayar ta , sai da takusa yankewa sannan ta d'aga yace
mata ya iso , nan tace masa ya k'arasa d'akin saukar bak'i gatan zuwa , dama tuni tasa
angyara d'akin tare da turareshi da turaruka masu k'amshi , sai da tabari minty 10 tayi sannan
ta fito daga d'akin nata tanufo k'asa ...

Fahad tuni ya wassafawa Maryam abubuwan da suke so zatayi , duk shaid'an cin
Maryam sai da ta girgiza da batun su , amman yadda Fahad ya shiga kwad'ai ta mata yadda
zata samu kud'i da irin yadda zata huta tuni taji ai abun ma bakomai bane , ita da tasaba yin ciki
ta zubar so d'aya ne ma ta haihu ta yarda jaririn tun randa yazo duniyar , bare wannan da gata
zai samu itama ta samu ai ta warke zata amince da wannan abun ko dan son datakewa Fahad
d'in , tana cikin zancen zuci suka hango sakkowar Sanam daga sama cikin takun ta na isa da
izzah , tuni Maryam tasaki baki tana kallon Sanam cikin ranta fad'i take " tsarki ya tabbata ga
Mahaliccin wannan sura me kyau , tabbas wannan yarinyar ta had'u tamkar ita tayi kanta , lallai
'Yayan masu kud'in nan suna hutawa ga kyau ga kud'i kamar su sukafi kowa a gun Allah , da
sauri tace " Astagafirlah Allah muma kabamu kud'in nan muhuta , Sanam nagama sakkowa ko
kallon wajen da suke batayi ba bare tasan Allah yayi ruwan su agun , haka ta fice daga palor
tabarsu da shak'ar k'amshin ta , Fahad har wani lumshe ido yake yana bin Mazaunan ta da kallo
har ta fice , cikin ransa yake kissima yadda zai sarrafa Sanam duk randa ya damk'eta a hannun
sa , Maryam ta dubesa tace " Dear wannan kyakkyawar Babyn fa Yarinyar Auntyn naka ce ?
Fahad yace "ea yarinyar tace Maryam tace " gaskiya ta had'u sosai tamkar ita tayi kanta , zata
sake magana tahango Hajiya Nafeesa tana sakkowa itama , Acikin second biyu Maryam ta
k'arewa Hajiya Nafeesa kallo taga yadda suke kama da Fahad , cikin ranta tace "inajin ita
yarinyar da Babanta take kama dan ta nunka Hajiya Nafeesa kyau sosai , ....


Tunda Sanam tayi sallama palor bak'i Huneed ya shak'i k'amshin ta , tana shigowa yayi
mutuwar zaune saboda tsabar had'uwad dayaga tayi masa , tasbihi yashiga yiwa Allah tare da
addu'ar Allah ya mallaka masa Sanam a matsayin mata yasan yagama dacewa , haka ta
k'araso har kusa dashi tana murmushi tashiga gaidashi , yaji dad'in yadda Sanam ta gaidashi
tare da nuna masa ashe itama tana da tarbiya ba laifi , duk yadda yake tunanin Sanam sai yake
ganin ashe tana da dad'in zama , yasan da sannu zata dawo yadda yake buk'ata insha Allah ,
nan Huneed yashiga tambayar ta ya Mumy da Daddy , tace" Mumy lfylau take Daddy kuma
yana d'aya gidan bangan saba amman nasan lfylau yake , Huneed ya d'an dubeta da mamaki a
fuskarsa yace " dama Daddy matan sa biyu kenan ? Sanam tace ea su biyune amman nidai
guda d'aya nasani Mumyna bansan wata ba bayan ita , Murmushi Huneed yayi yana duban
Sanam yace " wato kishi kike taya Mumyn ki ko ? canza fuska Sanam tayi tana fad'in " plss
Sojana mubar wannan maganar muyi hirar mu kaji , ganin batason maganar yasa Huneed yayi
shuru tare da d'auko wata hirar daban.......

Hajiya Nafeesa tana zuwa Maryam ta gaida ta cike da girmamawa , Hajiya Nafeesa ta
kalleta cike da kulawa ta amsa , tambayar Fahad tayi akan yafad'awa Maryam komai da suke
buk'ata tayi ? Fahad ya amsa da nafada mata kuma ta amince , Hajiya Nafeesa tadubi Maryam
tace " kinji komai ina fatan bazamu samu matsala ba ? kuma inason wannan Abun yazamo sirri
tsakanin mu , daga ke sai Fahad saini banason surutu dan kinsan koni wace duk abinda naga
zai ban matsala zan kaudashi , Maryam tayi kasa da kai tana fad'in " Insha Allah bazan gayawa
kowa ba komai kikeso nayi Alk'awarin yi miki shi , Hajiya Nafeesa tace " yauwa kiturawa Fahad
account Number dinki zaisa miki kud'i sai najiki , tana kaiwa nan ta mik'e ta ta haye sama
abinta..........



*Tabbas in banga Comment ba bazan cigaba da Typing ba*���
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
‍♀️‍♀️


*NA*
*Zee* *MD*



*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/





*Bisimillahir Rahamanir Rahim*





Chapter 28.

Maryam bin Bayan Hajiya Nafeesa tayi da kallo tana k'issima ina ma itace a
wannan matsayin , Fahad ne ya katse mata tunanin ta yace " to My Baby kinji komai kuma ina

fatan zaki bamu had'in kai ? Murmushi Maryam tayi sannan tace " angama Oga na ai farin cikin
ka kai da Auntyn mu nima shine nawa , Fahad ya dubeta yace " kizo mushiga daga cikin d'akina
tun yau nafara aikin samo Baby Boy , Maryam tawani kashe masa ido tana mik'o hannu alamar
ya d'auketa , murmushi Fahad yayi sannan yace " Baby ai kinyi nauyi dayawa kawai ki mik'e
mutafi , turo baki Maryam tayi har sai da Fahad ya d'auke ta ya nufi bed room d'in sa da ita......

Sosai Sanam tasaki jikinta da Huneed suka sha hirar su , sai wajen goma da rabi yayi
mata sallama ta rakoshi har jikin motar sa yatafi , juyowa tayi d'auke farin ciki akan fuskar ta ,
batasan meyasa in suna tare da Huneed kwata kwata bataso yayi nesa da ita ba , dai dai da
zata shiga k'ofar palor Fahad da Maryam suka fito suma hannu cikin hannu , tsayawa Maryam
tayi cak tana kafe Sanam da idanu , Sanam mamakine ya kamata naganin Fahad tare da mace
sun jero daga cikin gidan hannu cikin hannu , koda yake bazatayi mamakin ganin hakan ba
tunda tasan waye Fahad farin sani , kallo d'aya tayiwa Maryam ta d'auke kai tare da bi ta gefen
su ta shige abinta......

Maryam ta dubi Fahad tace " gaskiya wannan yarinyar Auntyn naka ta had'u sosai , duk
da naga kamar zatayi rashin Mutunci amman tashiga raina sosai tayimin , dama zaka had'amu
k'awance wallahi dana ji dad'i , Fahad ya dubi Maryam yace " mutuk'ar kina son zaman lafiya
koda kinzo gidan nan to karki shiga shirgin Sanam , bata da mutunci ko kad'an batak'i ta
tsinkaki a cikin taron mutane ba , Maryam tace "wow My Dear sunan nata ma wallahi ya had'u
gaskiya tahad'u shiyasa sunan ta ma yake had'add'e , Fahad ya rik'o hannun ta yana muje kar
Sanam ta zautaki tun d'azu sai yaba kyanta kike , Maryam tayi murmushi tana fad'in " ai dole
na yabi kyanta amman da alama ita da Mahaifinta take kama ko ? Fahad kawai ea yace tare da
d'auko wata hirar , dan shi yafara gajiya da tambayoyin Maryam d'in tamkar 'Yar jarida......

Jaydeen tunda suka koma gida da Hajiyar sa yake faman kiran wayar Sanam , sai dai ko
sau d'aya bata tab'a d'agawa ba , har a whaspp yayi mata magana nan ma bata dawo masa da
reply ba , gashi kullum soyayyar ta k'ara ninkuwa take cikin ransa , tunyana hak'uri har yagaji
Hajiyar sa tasan halin dayake ciki , d'aukar waya tayi ta kira Number Hajiya Nafeesa , bayan
sun gaisa takeyi mata bayani akan k'in d'aga wayar Jaydeen da Sanam keyi , sannan ta k'ara
da cewa shine dalilin kiran nata taji ko lafiya kuwa ? Hajiya Nafeesa tasan halin Sanam sarai
bata da mutunci , musamman indai batason Abu to bataso ko kad'an ya rab'e ta , cikin iya
siyasa da kissa tace " kinsan Halin yaran yanzu tunda ga ranar da kukazo na gaya mata muka
shiga wasan b'uya da ita , kuma inajin ba lallai in tana da number tasa ba , amman insha Allah
zan mata magana zata d'aga , sannan A bawa My Son d'ina hak'uri Sanam tamkar tazama
tashi angama , Hajiya Halima akayi dariyar jin dad'i ta shiga godiya tare da addu'ar Allah ya
daidai tasu , Nan suka tab'a hira kafin suyi sallama da juna......

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login