Showing 75001 words to 78000 words out of 80926 words
na zama mallakin ka , Ina yi maka fatan Alkairi Allah ya tsaremin
Kai a duk inda kake , sannan Allah yarabaka da sharrin Matan zamani , Murmushi yayi ya
amsa da Ameen Mata ta Allah ya dawo Mana da Daddy lafiya in turo iyayena a mallakamin ke ,
rufe idanuwa Sanam tayi tana dariya Nan suka rabu tamkar sutafi tare saboda tsananin k'aunar
juna .......
Haka akaci gaba da tafiya kwanaki na shud'ewa , watanni na wucewa har Cikin Maryam ya
shiga watan haihuwa , duk wani k'ulli da Hajiya Nafeesa take Maryam na Kiran Sanam ta sanar
Mata , har Asirin da tazo gidan Mummyn Twins ta barbad'a da niyar zuwa ganin Sanam , Nan
ma Maryam ta sanar da Sanam Dan haka Hajiya Nafeesa na tafiya akasa masu gadi suka
wanke gidan tass.....
Daddyn Sanam sai turowa Hajiya Nafeesa kud'i yake tana Masa k'aryar siyan kayan barka ,
shi ason sa ma soyake ta taho inda yake ta haihu , Amman tashiga tsarashi akan dole ya
hak'ura , sai dai yace da zarar ta haihu zai taho gida ayi hidimar suna da shi , ....
Wani magani likitan Hajiya Nafeesa yashiga bata duk jikinta yafara kumbura tamkar me cikin
gaske , a cikin satin Maryam tafara nak'uda tamkar batayi , asibiti suka kaita da k'yar aka samu
ta haihu Amman tasha wuya sosai , cikin ikon Allah ta haifi d'anta bak'ir k'irin dashi , tamkar
Hajiya Nafeesa tasa ihu saboda munin d'an data gani , haka suka ja gefe ita da Harira suka
shiga magana , Hajiya Nafeesa tace " yanzu wannan jaririn ta inah yake kama da Fahad ?
Shegiyar yarinyar bin mazan ta yayi yawa wallahi , wannan yaron duk Wanda yagansa yasan
ba d'ana bane , Babu ta inda zance Yana kama dani bare kuma Alhaji , Hajiya Harira tace " a
can d'akin Naga wata mata itama ta haihu Amman kamar naji an cewa Bata motsi , me zai
Hana muje muga wanne kalar d'a ta Haifa sai musan abinyi , kinga inyaso sai ki jik'a likitocin
Asibitin da kud'i suyi Mana musanye , take Hajiya Nafeesa tayi na'am da shawarar Hajiya
Harira suka nufi d'akin da Matar take .....
Sukayi sa'a kuwa d'akin Babu kowa Nan suka ga jaririn ta fari kyakkyawa dashi , Nan suka
rik'e baki suna duban juna kafin su fito da sauri suna Hamdala , wata nurse ce tazo zata shiga
cikin d'akin , da sauri Hajiya Nafeesa ta tare ta tana fad'in " kece wacce kika amshi haihuwar
wannan Matar ? Nurse tace " nice lafiya kuwa Hajiya ? Nan suka ja ta gefe suka shiga kora
Mata bayani akan aikin da suke so su sata , tare dayi Mata tayin kud'ad'e masu tsoka inhar tayi
musu aikin , tanajin irin kud'in da suka fad'a take ta amince Nan Hajiya Nafeesa tayi Mata
transfer na dubu d'ari biyar akan zata ciko Mata sauran , Nan suka koma d'akin Maryam suka
d'auko d'anta batare da sun yi karo da kowa ba suka kawoshi d'akin Matar Nan , sannan suka
d'auki na Matar suka dawo dashi d'akin Maryam , Nan Hajiya Nafeesa ta kwanta a gadon mara
lafiya likitan ta har lokacin bai k'araso ba , Yana zuwa yayi Mata wata allura wacce ta maida jikin
ta tamkar namasu jegon gaske , dayake likitan shima ba Mai kula bane gashi da son kud'in tsiya
shiyasa bai San kalar d'an da Maryam d'in ta Haifa ba ......
Tuni aka shiga gayawa 'yan uwa da abokan arzik'i haihuwar Hajiya Nafeesa , Alhaji Abba
baki har kunne yakira waya tare da cewa Yana Nan akan hanya , ..
Koda su Sanam da Mummyn ta suka samu labari take suka shiga dariya Dan wasan yazo
k'arshe ,. Mummy Twins Koda tayi waya da mijinta tayi Masa murna na samun k'aruwar da
akayi batare da ta nuna komai ba , Nan yake sheda Mata gobe Yana hanya shima dan dole
yadawo gida dan taya Hajiya Nafeesa murnar samun haihuwa ,Mummyn Twins tace " gaskiya
dai yakamata kadawo Dan kuwa wannan abin murna ne sosai yasamu, abinda ake nema
shekara da shekaru Allah bai kawo ba sai yanzu ai dole azo ataya murna , Nan sukayi sallama
tana duban Sanam suna dariya , lokacin tuni Sanam da Mummyn ta sunzama tamkar k'awaye ,
duk dangin Hajiya Maimuna babu inda Sanam yanzu Bata shiga , gidan Hajiya kuwa Kakar ta
kusan kullum tana hanya saboda akwai sa'anin ta a Family d'insu kusan kullum suna tare.,...
Sanam tuni ta shedawa Huneed Maryam fa ta haihu , kuma dole yadawo dan a yanzu
Maryam tana buk'atar kulawarsu sosai , tunda kaga ta haihu nasan a Koda yaushe zata iya
sakawa akasheta , Huneed tuni ya had'o kayansa shima ya nufo Abuja Dan wannan wasan
k'arshen dole yadawo agama wasan dashi ........... [9/27, 14:29] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 49.
Hajiya Nafeesa tuni tabiya kud'i akan a kashe Maryam batare da Fahad yasani ba ,
Maryam tasha wuya sosai shiyasa ake bata kulawa a Asibitin , ita kuwa Hajiya Nafeesa tuni ta
d'auki jaririn da sukayi musanye sunyi gida , Koda Maryam ta farka bataga jaririn data Haifa ba
sannan Babu Hajiya Nafeesa , take maganar Hajiya Nafeesa ta fad'o Mata na cewa tana
haihuwa zasu kashe ta , da sauri tafara yunk'urin tashi sai dai jitayi jikinta duk ciwo yake Mata
takasa motsin kirki ,.
Wani zogi taji a k'asanta Wanda ya tabbatar Mata a wajen haihuwa ta k'aru ,. Nan tashiga
neman wayar ta Dan ta Kira Sanam akan ta taimaka Mata , sai dai wayam Babu wayar sai
sannan ta tuna tunjiya data Fara cin wuya tayi jifa da wayar , a hankali Maryam ta shiga
saukowa daga kan gado tana d'ingisawa , a haka har ta k'araso k'ofar fita wacce tazo bud'e
k'yaure tajishi arufe gam , gaban ta ne yafad'i Kar dai ace sun rufeta ne ? Da sauri ta nufi
window tana k'ok'arin lek'awa , wasu maza tagani masu zubin arnan daji a tsaye jikin window
suna Mata muzurai , da sauri tasaki labule tafara zubar da hawayen ta , tabbas Bata da mafita
anan dan basai anfad'a Mata ba tasan wannan Shirin nasu Hajiya Nafeesa ne , jingina tayi da
jikin gado tafara kuka tana addu'ar Allah yakawo Mata mafita,.....
Huneed tuni ya iso Abuja cikin shigarsa ta babban Captain , Koda ya k'arasa gida wanka
yayi sannan yaci abinci ya fito , Kiran Sanam yayi a waya ya sheda Mata isowar sa sannan
yace tafad'a Masa Asibitin da Hajiya Nafeesa take zuwa , Nan Sanam ta gaya Masa yakashe
waya ya nufi Asibitin ,...
Tuni gidan Hajiya Nafeesa ya cika da 'yan uwa da Abokan arzik'i , kowa Yana zuwa yi Mata
barka da murnar samun haihuwa , Jariri kwata kwata tak'i badashi Wai bayason jagwal gwalo ,
Yana kan gadon sa na jarirai sai dai a lak'a aga fuskar sa kowa sai fad'in " tubarkallah yaro
Yana da kyau , ....
Me jego sai washe baki take tana farin ciki tamkar itace ta haihun , Madara ake bashi saboda
itadai ba ruwan nono gareta ba bare tabashi , kuma Koda aka fad'a Mata magungunan da zata
Sha Dan tasamu ruwan Nono k'i tayi , bataji aranta zata iya shayar da d'an da ba nata ba bare
kuma d'an shege , Kullum cikin bashi Madara take tana fad'awa mutane ruwan nonon har
yanzu baizoba......
Acan asibiti kuwa Wannan Matar da su Hajiya Nafeesa suka musanya d'an Maryam da
nata itace ta farko , tunda ta farko ta had'a ido da jaririn da ke kusa da ita tasan ba jinin ta bane
wannan , da sauri ta mik'e zaune tana k'walawa likita Kira , da sauri Nurse dake kula da ita ta
shigo tana tambayar ta lafiya ? Kallon Nurse d'in tayi sannan tace " Ina Babban likita yake ?
Nurse tace " Yana office kina buk'atar wani abune ? Tuni ta sakko daga kan gadon ta ta fito
daga d'akin , Nurse sai binta take tana fad'in " kiyi a hankali baki Gama jin sauk'i ba fa , Likita
Yana cikin office d'insa Yana Zaune Yana waya ta banko k'ofar da k'arfin gaske , da sauri ya
kalli k'ofar Dan ganin Wanda ya shigo haka , batayi wata wata ba ta shak'o wuyansa tana fad'in
" Ina kukai min yarona ? Wallahi wancan bak'in d'an bashi na Haifa , ko ku fitomin da d'ana
konayi k'arar ku , take kuma tashiga kuka tana fad'in " wallahi bazan yadda ba d'ana ko d'umin
jikina baiji ba ace arrabani dashi , likitan jikinsa tuni yashiga rawa Yana fad'in " waye ya d'auke
miki d'an naki muje aduba cikin Asibitin sai aga ku nawa kuka haihu yau , Fitowa sukayi kuma a
dai dai lokacin mijin Matar da 'yan uwan ta sukazo , dama mijin nata da yakawo ta Asibitin sai
ya manta wayar sa a gida shine ya koma Dan ya d'auko ya Kira 'yan uwan ta ,...
Suna iso ta tare su da maganar musanya Mata d'an ta da akayi , da sauri suka nufi d'akin
da take ciki aikuwa suna tozali da wannan d'a kowanne sai yayi baya Yana salati , tabbas
wannan ba d'an Bahijja bane , wannan ce haihuwar ta ta uku kuma duk yaranta kamar su d'aya
da Babansu , kuma yaranta Fara rene itama kuma Fara ce wannan yaro kuwa bak'ir k'irin haka
yake , take cikin Asibitin ya d'auka akan anyiwa wata Mata musayar Jariri , Nurse d'in da aka
had'a baki da ita sai Uwar zufa take tana faman zare idanuwa , Nan take 'yan jarida suka iso
Asibitin suka Fara neman labarai .....
Huneed ya iso asibiti yasamu wannan labarin na musanyan yaro , wucewa yayi yafara
duba inda yake tunanin samun Maryam ,...
Maryam kuwa taci kuka ta k'oshi tarasa ta yadda zata fita daga cikin d'akin , duk wannan
Abu da akeyi na batun musayar yaro batasan anayi ba, jefe jefe tana d'an lek'awa ta window
Dan ganin wannan mutanen suna Nan. ....
Wasa wasa k'aramar magana tazama gaske , Dan tuni Asibitin ya cika da mutane anata
fad'in " dole likitoci sunsan inda d'an wannan Matar yake , Take Babban likitan ya had'a taro
na gaggawa daga kan likitoci har Nurse a Babban office d'insa .,....
Har dare Huneed baiga d'akin da aka kwantar da Maryam ba , Kiran wayar Sanam yayi
yace " My Wifey nayi neman duniya Amman bansamu Maryam ba , ko Zaki tuntub'a Mana kiji
tana Asibitin ko tana gidan ? Sanam tace " yanzu nazo gidan kuma duk inda na duba Banga
Maryama ba , Amman Dana zagaya baya ta wajen tagar palor naji K'awar Hajiya Nafeesa wato
Hajiya Harira tana waya , Koda na kasa kunne naji tana cewa kusan duk yadda zakuyi ku
d'auketa daga cikin Asibitin sai kutafi da ita , sannan naji tace " in sun kashe ta su jefar da
gawar a wajen gari , tabbas nasan ba kowa za'ayiwa haka ba face Maryam Dan haka tana
Nan cikin Asibitin Nima ganinan zuwa , tana gama cewa haka ta fito daga gidan ta hau motar ta
ta nufi Asibitin......
Alhaji Abba tuni ya taho tare da tarin siyayyar da yayiwa yaro da me jego , farin ciki yake
tamkar ba atab'a Masa haihuwa , tunda yataho ya shedawa Hajiya Nafeesa Nan tashiga gyara
jiki da kuma k'ara maida kanta kalar masu jego ka rantse itace ta haihu , ...
Acan Asibiti Sanam na shiga itama ta tadda wannan hatsaniya ta musanyan yaro da akayi ,
sosai tashiga mamaki tare da ayyanawa a ranta watak'ila ma Hajiya Nafeesa ce suka aikata
hakan , haka tashiga cikin Asibitin sanye da face mark tana dube dube , baya ta zagayo aikuwa
ta hango wannan k'artin masu kama da arnan daji itama , tana ganin su tayi saurin komawa da
baya batare da sun ganta ba , wayar Huneed tashiga Kira tana magana a hankali , Nan ta
sheda Masa tana cikin Asibitin daga baya , yazo taga wasu mutane kuma i tadai Bata yadda
dasu ba , Nan ya tambaye ta daga wajen Ina kenan ? Nan tashiga Gaya Masa tiryan tiryan har
ya k'araso , Yana zuwa shima ya lek'a ya hangosu Nan ya tabbatar da duk yanda akayi sune
wad'an da zasu kashe Maryam , Nan take ya Kira yaransa ya sheda musu maza suzo Asibitin
Royal hospital su same shi yanzu , Nan yashiga kaiwa da komawa Yana jiran zuwan su ,
Sanam tace " My Sojana ina shigo naji wata Hayaniya Wai anyiwa wata Mata musanyan yaron
data Haifa , Huneed yace " Nima naji wannan Asibitin ai komai akace zasuyi Babu musu zasuyi
shi , Sanam tace " wallahi jikina yabani Hajiya Nafeesa ce tayi wannan aikin , Huneed ya
dubeta da sauri ta d'aga Masa Kai alamar ea ,. duban ta yasakeyi Yana nazari sannan yace "
bazan yi Miki musu ba Dan wanda yasa akashe wani babu abinda bazai iya ba , Kiran yaransa
ne ya katseshi suka sheda Masa sun iso , Nan yashiga kwatanta musu ta b'angaren da yake ,
Nan take suka zagawo suna k'amewa tare da Sara Masa , Dan dukansu shine ogan su cike da
girma mawa suke bashi girman sa , Nan Huneed yabasu Umarnin kamo Masa wannan
mutanen da aka saka sukashe Maryam , tare suka nufesu har dashi suka kamasu batare da
sun ankare dasu ba , Sanam ta lek'a window Nan ta hango Maryam zaune sai sharar hawaye
take , Kiran sunan ta tayi da sauri ta jiyo tare da mik'ewa tana jin wani dad'i ya ziyarce ta ,
zagayowa Sanam tayi suka bud'e k'ofar tare da shigowa d'akin da Maryam d'in take , Sanam
ce ta rik'o Hannun Maryam suka fito daga cikin d'akin , Nan taga wannan mugayen mutanen
ansaita su da bindugu kowanne Yana durk'ushe akan gwuiwarsa ,.....
Take cikin Asibitin yakuma d'auka ankama wasu 'yan fashi sun shigo zasu kashe wata ,
nanfa 'Yan jarida suka samu abinda sukeso sukayo caa.. dason jin labari , sai dai kwata kwata
Huneed ya Hana ayi magana dasu dan basaso a haska a social media har Hajiya Nafeesa
tagani , Koda suka zo wucewa ta wajen Matar dake kuka akan canza Mata yaron da akayi
Maryam ta hangi yaron ana ta kallonsa , da sauri ta anshe hannun ta daga na Sanam ta nufi
wajen jaririn , tana zuwa ta anshe shi a hannun wata Mata tana fad'in " wannan ai shine d'ana
Wanda na Haifa , aikuwa kallo yadawo kanta yayin da Uwar waccan yaron ta mik'e tana fad'in "
to Ina kika kaimin yarona ? Sanam tace ki kwantar da hankalin ki yaron ki nanan kizo muje daga
ciki zamuyi magana , take suka shiga wani d'aki suka keb'e Nan Sanam tashiga bawa Matar
labarin komai game da Hajiya Nafeesa , takuma shada Mata yanzu zasu d'auki hanya su nufi
gidan Hajiya Nafeesa Nan zata anso d'anta , ba'ayi wata wata ba Sanam da Huneed da
Maryam tare da wannan Mata suka nufi gidan Hajiya Nafeesa......
Akan Hanyar su ta zuwa suka Kira Mummyn Twins suka sheda Mata komai , Nan itama ta
sheda musu Alhaji yadawo dan tund'azu ya sauka kuma yanzu haka Yana gidan Hajiya
Nafeesa shima , itama gatana zuwa zasu taho da Hajiya Babba wato Mahaifiyar ta. .....
Diyana tuni ta bayyana itama a gidan Hajiya Nafeesa , tunda suka taho daga asibiti 'yan
sandan da mijin Bahijja ya d'auko suma suke biye dasu har suka shigo cikin estate d'in area 11
......
Hajiya Nafeesa ana zaune a palor sai wani yauk'i take ita ala dole ga me jego , Alhaji