Showing 69001 words to 72000 words out of 80926 words
sarauniyar
Mata ,. Kallon Sanam yayi wacce ta runtse idanu tana kauda kanta gefe , tabbas shima ba
haka yaso ba Dan dai kawai Mummy tace yaje Mata da sigar soyayya wannan ne kawai zaiyi
nasarar sanin inda take ,. Maryam tace " yauwa barka kadai sai dai bangane waye ba , Huneed
cike da jin tsanar ta aransa yace " Masoyine Wanda yake mafarkinki a Koda yaushe , inafata
Zaki amshi tayina dan ba wasa nazo ba , Maryam tace " haba Oga banganka ba bansan ya
kake ba kawai sai na karb'i tayinka , kabari muga juna sai muyi ciniki inka siya da tsada saina
sallama maka , Huneed cike da k'osawa da maganar Maryam yace " ok to a inah zamu had'u
Ni a shirye nake ? Maryam tace " kazo ka d'aukeni a Area 11 Estate d'in gidan Makama gida
me No. 13 anjima bayan sallar Magriba , tuni Sanam ta zabura tana mik'ewa ta dubi Huneed da
Mummy tace " gidan mu fa kenan , anya kuwa wannan tasan me take fad'i kodai mistake
address tafad'a ? Mummy shuru tayi tana mamaki to wannan wace yarinya ce haka take neman
Yarinyar ta da sharri , tabbas wannan address d'in gidan Hajiya Nafeesa ne to wacece wannan
d'in ? Huneed ne yayi magana da cewa " ku kwantar da hankalinku koma wacece yau shirinta
yazo k'arshe Dan tabbas saina kamata kuma zata gayawa aya zak'in ta ,. Ai abun yazo da
sauk'i tunda har tayi saurin amincewa Dani komai yazo k'arshe ,. Nan suka shiga zantawa tare
da yin al'ajabi akan wannan abin.....
Maryam tana kwance kan katifa tana Danna wayar ta. Cikin zuciyar ta tana tunani tagaji
da rashin kud'in Nan da take fama dashi , ta fuskanci Hajiya Nafeesa ba ta Bari aci kud'inta ,
dole tadunga fita tana barikinta Dan tasaba da rik'e kud'ad'e a hannun ta , Fahad d'in ma
bawani kud'i yake samu ba Dan ko sigari in zaisha itace ke siya Masa wani lokacin , haka za'a
ajiyeta ba'a Bata manyan kud'ad'e tabbas baza ta sab'u ba Dole ta fita ta nema , addu'a tashiga
akan Allah yasa wannan da sukayi wayar me kud'ine sosai yadda zai jik'ata da nera , tasowa
tayi tafito palor Dan tasamu abinda zataci , tana fitowa tasamu Hajiya Nafeesa da wata k'awar
ta suna maganar ta , Hajiya Nafeesa tace " Wallahi Hajiya Harira tana haihuwa zansa a
kasheta. , tabbas indai har nabarta a raye to tabbas barazana ce ga rayuwata ,
[9/27, 14:27] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 44.
Maryam dake lab'e tana jinsu take jikinta yashiga rawa , lallai rashin Imanin Hajiya
Nafeesa yayi yawa , tsayawa tayi taci gaba dajin su ...
Hajiya Harira ta nisa sannan tace " hakan kawai zakiyi domin wannan yarinyar mutuk'ar
kika barta to sai ta tona Miki asiri , Hajiya Nafeesa tace " ai shiyasa na fad'a miki barin ta
tamkar tonuwar asirina ne , Nan suka shiga tattaunawa akan yadda zasuyi da Maryam inta
haihu ,...
Maryam tana gama ji ta koma cikin d'akin tana Kai kawo , wato tana haihuwa tagama
musu amfani kashe ta zasuyi , to kafin akai ga hakan itama zata tona asirin Hajiya Nafeesa ,
me take k'aruwa dashi a wajen su Daman kawai kwana cikin ac da kuma cin abincin lafiyayya
Wanda tana gidan suma shi takeci ,. Tana da samari kuma suna Mata duk abinda takeso Dan
haka me zai dameta , gobe zataje a zubar Mata da cikin jikinta Amman kafin lokacin dole sai
tasamo number Alhaji Abba Dan ta Gaya Masa duk irin makircin da Matar sa keyi ,.......
Huneed ya d'auko Sanam ya kawota gida , sai dai bai shiga ciki ba saboda Kar Shirin su
ya b'aci ,. Ajiye ta yayi ta shiga Dan tanason d'ebo kayan sawar ta ta dawo gidan Mummy , a
yanzu haka hankalinta kwata kwata yafita daga gidan Mummy Nafeesa tafison gidan Mummyn
ta , tana shiga masu aikin gidan suka shiga gaidata ta amsa ba yabo ba fallasa .....
Tana shigowa palor tasamu Hajiya Nafeesa ita da Hajiya Harira suna hira ,.Hajiya Nafeesa
tana ganin Sanam cike da kissa tafara cewa " oyoyo my luvly Dauther nayi missing d'inki ,
Sanam tayi Murmushi tana k'arasowa kusa da Hajiya Nafeesa tace " Some 2 U my Mummy ,
Nan ta dubi Hajiya Harira tahad'e ranta , batason ganin Matar Nan a gidan su duk wani Abu
itace ke koyawa Hajiya Nafeesa ,. Hajiya Harira ta yak'e baki tana fad'in " Hajiya Sanam 'Yan
Mata ya kike ya karatu ? Sanam batare da ta dube ta ba tace " lafiya sannan ta nufi Sama tana
cewa " Mummy Bari na fito Bata jira abinda Hajiya Nafeesa zata ce Mata ba ta haye sama
abinta...
Tana hayewa sama Hajiya Harira ta dubi Hajiya Nafeesa tace " wannan yarinyar taki
kwata kwata bata da mutunci , kidubi kiga wani banzan kallo data keyimin , Hajiya Nafeesa
tayi Murmushi sannan tace " a haka ma Wai kura tayi lafiya tunda wannan shegen yaron ya
d'an canza ta , da dane wallahi ko kallo baki ishi Sanam ba ke kinsani , Hajiya Harira tace "
hakane kam to Allah ya kyauta , Nan suka canza hira wacce duka akan yadda zasuyi da
Maryam ne..,...
Sanam rik'e da Trolly d'inta tafara sakkowa daga kan step a hankali tana yin waya ,
k'arasowa tayi tana cewa Hajiya Nafeesa " Mummy inaso zankoma Gidan Mummyn Twins inyi
kwana biyu ,. Hajiya Nafeesa ta kalli Sanam cike da kissa tace " wanne laifin nayi Miki haka
kikeson ki gujeni ? Sanam tayi Murmushi sannan tace " Mummy bakimin komai ba kawai dai
inason zuwa , Hajiya Nafeesa tace " shikenan My luv duk yadda kikeso hakan za'ayi , ki
gaidamin da Mummyn Twins d'in ki kuma ce musu nayi fushi , Sanam ta mik'e tana fad'in "
zasuji Mummy sai munyi waya , Nan ta fice abinta suka ci gaba da waya da Huneed har ta
k'arasa wajen da motar sa take.....
Sanam na fita Hajiya Nafeesa ta d'auki waya tashiga Kiran Alhaji Abba, kukan kissa ta sa
Masa akan Wai Sanam ta had'a kayanta tabar gidan , a halin yanzu ma batasan Ina zataje ba
Dan a buge taganta tashigo , Alhaji Abba hankalinsa tuni yayi mummunan tashi , Me Sanam
takeson ta koma ? Angaya Mata gata wasane da zata zama haka , bai ga laifin taba tunfarko
shine ya sakar Mata da yawa shiyasa take hakan , kashe wayar yayi yafara tunanin wa zai Kira
, indai ya Kira Mummyn Sanam d'in yasan tabbas saita nuna Masa kuskuren sa akan tunfarko
shine me laifi , .
Hajiya Nafeesa tayi Murmushi tana duban Hajiya Harira, itama murmushin tayi tana fad'in
" gaskiya kin iya tuggu Hajiyata , Kinga kuwa wannan had'in da kikayi Mata a wajen uban nata
zaisa ya tsaneta , Hajiya Nafeesa tayi wata dariya sannnan tace " Kinga yanzu baruwana da
fargabar Kar Sanam taganni cikina baya girma , kuma yanzu zamuyi yadda mukeso tunda tayi
gaba , ....
Bayan Sanam da Huneed suntafi ya biya da ita ta shopping , sai da ta zab'i abuwan da
zatayi amfani dasu sannan ya dawo da ita gida.......
Bayan Magriba Huneed ya shirya cikin shigarsa ta babban Captain ya nufi k'ofar gidan su
Sanam , Kiran wayar Maryam ya shiga bugu d'aya tamkar jira take ta d'aga , sallama tayi cike
da kashe murya tace " Alhajina kardai kace min har ka k'araso ? Huneed yace " Kinga laifina ai
ba'a sanya da zuwa wajen irinku , Maryam tayi Murmushi sannan tace " gani Nan fitowa kabani
minty 2 kacal ,. Kashe wayar tayi sannan ta d'auki mayafinta ta fesa turare ta fito , aikuwa tayi
sa'a palor Babu kowa tasa Kai ta fita daga cikin gidan baki d'aya , nesa kad'an ta hango motar
Huneed tana ganin motar tasan tayi kamun Babban Alhaji tuni ta canza tafiya harta k'arasa ta
buga murfin motar , bud'e Mata yayi tashiga tamaida murfi ta rufe tana fad'in " Alhajina gani
naso gareka..... Cak bakinta ya tsaya ganin Wanda yake cikin motar , take hanjin cikinta ya
hautsina wani zawo ya taho Mata babu shiri.......,.....
_Masoyana littafin_ *NI KO ITA* _haryanzu yana jiranku Kar ku Bari abaku labari , kuyi
gaggauwar siyan naku akan farashi k'alilan_, 200
Duk meso yayi magana a wannan Number : 09137064556
[9/27, 14:28] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 45.
Da sauri tafara k'ok'arin bud'e motar ta fice , wata Uwar tsawa Huneed ya daka Mata
tuni Maryam tasaki fitsarin dake matse jikinta , Huneed yaja motar da wani matsiyacin gudu
yabar cikin unguwar , ...
Gidan da Huneed ya tab'a Kai Sanam farkon had'uwar su lokacin da take rashin jin ta Nan
yakai Maryam, Yana zuwa ya kashe motar ya fito tare da zagayawa inda Maryam take ya bud'e
murfin motar tare da fincikota , Maryam sai kuka take tana cewa " kayi hak'uri Dan Allah wallahi
nadaina , Huneed ya bud'e gidan Yana rik'e da Hannun ta ko kallon ta yak'i yi saboda tsanar ta
dayayi , Yana zuwa ya jefar da ita a k'asa sannan ya zare belt d'in jikinsa yafara dukanta ,
Maryam ihu take tana fad'in " kayi min Rai Dan Allah ka yafemin , Huneed ya tsaya da dukanta
ya durk'uso wajen fuskar yace " inaso kifad'amin waye yasa ki shiga tsakanina da Sanam ?
Maryam ganin irin dukan da tasha a Hannun Huneed gashi daga ganin sa har kisa zai iya yi ,
batare da ta wahalar da kanta ba tace " Hajiya Nafeesa itace tasani wallahi , Huneed ya tsaya
Yana kallon Maryam sannan yace " ke meye had'in ki da Hajiya Nafeesar ? Shuru Maryam tayi
batare da tace dashi uffan ba , aikuwa ya d'auko belt ya Fara Shirin zabga Mata dasauri tace "
wallahi bani da had'i da ita kawai dai ni budurwar k'anin tane , Huneed ya mik'e yace " hakan
yayi yanzu zanbarki anan dasafe zanzo dole ki fad'amin irin Shirin da kukeyi akan mu , Yana
Gama fad'a Mata hakan ya fito tare da janyo k'ofar ya rufe , yanajin Maryam na kuka tana bashi
hak'uri Amman ko waiwayen ta bai yiba ,
Yana fitowa ya shiga motar ya kunnah yabar unguwar , ring d'in waya yaji Yana tashi Nan
ya kalli kujerar da Maryam ta zauna , jakarta yagani kuma ring d'in daga ciki yake fitowa ,
tsayawa yayi ya bud'e jakar ya d'auko wayar , lokacin wani Kiran ya kuma shigowa , number da
aka kirata dashi ansa My Fahad , tuni Huneed yagane Fahad ne Dan haka yak'i d'agawa har ta
katse, kashe wayar yayi baki d'aya yayi jifa da ita yahau titi ya nufi gida....
Sanam d'aki guda Mummy ta ware Mata Nan ta zuba kayanta a wordrup d'in d'akin , tana
kwance tana tunanin yadda zata je tabawa Diyana hak'uri sai ga Kiran Huneed , da sauri ta
d'aga tana fad'in " My Sojana barka da wannan lokacin , Huneed ya lumshe idanu tare da cewa
" barka kadai My Wifey ya Daren ya su Mummy da Twins d'ina ?Sanam tace " lafiyar su k'alau
sai dai muna kewar ka nida su Twins ,
Huneed yace " badan dare yayi ba Dana dawo Nima Dan nakuma tozali da kyawawan
'Ya'yan Mummy , Murmushi Sanam tayi sannan tace " ya kukayi da shegiyar yarinyar Nan ?
Huneed yace " da safe ki shirya zanzo na tafi dake wajen da na ajiye ta , a yadda na Fahimta
ba iya wannan ne shirinsu ba akwai wani abun a k'asa. Sanam tace " kamar me kenan ? Huneed yace " a yanzu bazan ce Miki ga Shirin su ba sai
dai a gobe inaso inyi Mata abinda komai sai ta fad'a Mana , Amman ta sheda min cewa ita ba
'yar Uwar su Hajiya Nafeesa bace , Ni a yadda na Fahimta ma a unguwar su Diyana k'awarki
take , take Sanam ta tuno da ranar da zasu fita ita da Diyana sunfito sukayi karo da Maryam ,
Nan Diyana tashiga tambayar Sanam meye had'in su da Maryam , Ashe Ashe maganar da
Diyana tafara Gaya Mata akan Maryam d'in gaskiyane , Huneed ya katse Mata shurun ta da
cewa " Ya kikayi shuru ne ko akwai abinda kike tunani ? Sanam tace " ea akwai Nan tashiga
sheda Masa farkon had'uwar su da Maryam ita da Diyana , Huneed yace " gud dole gobe
mutaho da Diyana Dan itama inason tambayar ta wasu abubuwan , Sanam tace " kana ganin
Diyana zata zo kuwa ? Huneed yace " zatazo Amman sai kinje gareta kin Bata hak'uri sannan ,
Sanam tace " inhar zan Bata hak'uri ta hak'ura me zai Hana zanje kuma itama dole tamin uzuri
, nayi Mata komai ne bisa rashin sani kuma ko itace a irin matakin Dana samu kaina zatayi irin
hakan,. Huneed yace " gaskiyane Matar Soja Ashe dai ana kishin Sojan Nan haka , dariya
Sanam tasa sukayi sallama akan anjima zai Kira inya yi Shirin bacci , Nan sukayi musayar
kalaman soyayya sannan kowanne yakashe waya cike da begen junan su .....
*Washe gari*
Wajen k'arfe goma na safe Huneed ya dira a gidan Mummy twins , tare dashi suka yi break
fast suna hira , anan Huneed ya shedawa Mummy duk yadda sukayi da Maryam , Nan Mummy
ta jinjina lamarin Hajiya Nafeesa , sai dai batayi mamaki abinda Hajiya Nafeesa tayi ba Dan tafi
gaban hakan , Bayan sun kammala Break fast Sanam ta mik'e Dan ta d'auko mayafinta , tana
fitowa suka yiwa Mummy sallama suka fita......
Unguwar su Diyana suka nufa Sanam duk kunya ta kamata, sai tunanin yadda zata shiga
gidan su Diyana ta had'a idanu da Umman Diyana , suna tsayawa a k'ofar gidan Diyana na
fitowa zata tafi sch , Nan Sanam ta tuna itama tana da lucture Amman sai Sha biyu , kwata
kwata Diyana Bata lura da Motar Huneed ba , da sauri Huneed ya fito Yana fad'in " barka da
safiya Diyana , tsayawa tayi cak tana kallon sa cikin zuciyar ta tana tunanin me yakawo shi
wajen ta , ko shima yazo ya ci Mata mutuncin ne kamar yadda budurwar sa tayi Mata , Bata
gama tunani ba sai ga Sanam ta fito itama daga cikin motar , Diyana d'auke kanta tayi tana
k'ok'arin ci gaba da tafiya , da sauri Sanam tasha gaban ta tana me rik'e jakar dake hannun
Diyana .........
*Plss kumin afuwa*
*Wlh yau Ina fama da ciwon kai*
[9/27, 14:28] Muhammad Karim: [9/26,