Showing 45001 words to 48000 words out of 80926 words
Sanam tafad'a soyayyar sa ko daga ganin yadda take rawar k'afa dashi ,
cike da kissa tace " yauwa nagode wa Huneed da ya miki hakan , in ba haka ba nasan ba zuwa
zakiyi ba lallai yayi min maganinki , turo baki Sanam tayi cike da Shagwab'a tana cewa " au
Mumy haka zaki ce ma kenan ? kawai dai zanje ne shima badan shi ba sai dan ra'ayin kaina
sannan kuma inason inga yaran da Daddy yace sunfini kyau , Murmushi Hajiya Nafeesa tayi
tana nufar d'akin ta tana fad'in " baki da dama Baby kedai akwai rigima , cikin ranta kuma
tashiga tunanin yadda zata raba Sanam da wannan shegen Huneed d'in .....
*Washe gari*
Tuni Sanam tabawa Diyana labarin Mumyn Asokoro ta haihu , Diyana tashiga murna tare da
cewa Besty yaushe zamuje barka inga 'yan biyu ? nasan yaran sun had'u sosai koda bangan
su ba , kinsan Allah Sanam inason Mumyn Asokoro saboda tana da mutunci gata me kyau har
ta fiki kyau , Sanam cike da jin haushin Diyana tace " sai ki koma gidan ta da zama ki ta kallon
ta , tunda kinason ta saboda tana da kyau ko to madallah sai anjima , kit ta kashe wayar batare
da Diyana tayi magana ba , Diyana rik'e da waya a hannu tana mamakin irin tsanar da Sanam
tayiwa Mahaifiyar ta ta , wannan wacce irin rayuwa ce ace mutum da uwar sa amman ko zan
cen ta bayaso anayi masa , ina ma itace tasamu uwa irin Hajiya Maimuna wallahi da duniya sai
tasan wace Uwar ta , mata gata me mutunci ga kyau tamkar ita tayi kanta , duk kyan Sanam
inta tsaya gaban Hajiya Maimuna wallahi sai ta dusashe , tab'e baki Diyana tayi sannan ta furta
" duk wannan makirar matar itace tasa kika tsani Mumyn ki Sanam , amman insha Allah watara
na zaki so ta kuma zaki k'aunace ta , ......
Huneed tunda sukayi waya da Sanam yace " ta shirya k'arfe biyar na yamma zai zo suje
barkar , tana sama tunda garin Allah ya waye bata sakko ba , ko kayan break a kitchen d'in ta
na cikin d'aki ta had'a komai ta karya , Hajiya Nafeesa ce ta turo k'ofar d'auke da sallama a
bakin ta , Sanam ta amsa mata tare da cewa "Sorry Mumy yau banzo na gaidaki ba keda
Daddy ko ? Hajiya Nafeesa tayi murmushi tare da cewa " nasan baki tashi da wuri bane Daddyn
ki kuma ya tafi gidan masu jego tun k'arfe goman safe , Sanam taji rashin dad'i yanzu har
Daddyn ta yafara fita batare da yagan ta ba ? wani haushin jariran taji ya kama ta , duk yanayin
data shiga Hajiya Nafeesa na kallon ta , kuma dama abinda takeso kenan ace Sanam tafara jin
haushin Mahaifin nata , shima kuma zata san yadda zata fara tura masa tsanar Sanam d'in
shikenan tayi musu farraqu , lokacin da Alhaji Abba zai fita sai da ya shigo d'akin Sanam
yasamu tana bacci , har shafa mata kai yayi yana fad'in " Rigimammiya ta haryanzu bata motsa
ba , Hajiya Nafeesar ce cike da kissa tace masa yabar mata 'yar ta tana bacci karya tashe ta ,
murmushi yayi yafice yana nima bazan so ta tashi yanzu ba kar tashiga yimin rigima , amman
yanzu sai ta nunawa Sanam cewa wai d'okin Yaran sa sababbi yake dan haka ya manta da ita ,
aikuwa tayi nasarar zuga Sanam dan sosai tashiga jin zafin Mahaifin nata tare da Twins d'in da
Hajiya Maimuna ta haifa ........
Wajen K'arfe hud'u da rabi Huneed yakira wayar Sanam , d'agawa tayi lokacin tana
zaune akan gadon ta tana shan chocolate , dan Sanam akwai shan zak'i tamkar sha zuma ma ,
d'aga wayar tayi a hankali ta furta Sojana , har cikin jikin sa yaji muryar ta ta tare da jinsa a
wani yanayi da yakasa bam ban cewa , cikin kasalalliyar Murya yace " Babyna ina fatan kin
shirya dan banajin zan kai har k'arfe biyar d'in nan batare da nayi tozali da idanun ki ba ,
Sanam cikin murya me sanyi tace " ni dai bazani ba gaskiya dan banason inje inga sunfini kyau
, gashi a saboda su yau Daddy ko damuwa baiyi dani ba harya fice baiga lafiya ta ba , kuma
haryan zu Daddy bai kirani ba dan haka naji banason ganin su kawai mubarshi , Huneed ji yayi
Dariya ta kamasa a hankali ya furta " haba Babyna taya zasu fiki kyau kinsan yadda kike da
kyau kuwa ? kwantar da hankalin ki kizo muje mugansu kinga sai kiga kaman nin su , ni ajikina
naji basu da wani kyau Babyna tafi su komai da komai , ked'in fa sarauniya ce acikin matan
duniya kinga kuwa taya za'afiki kyau , nan Huneed ya shiga lallab'a Sanam da kalamai masu
ratsa zuciya , aikuwa yayi nasarar shawo kanta tace zataje bari ta shirya yabata Minty 20 .......
Huneed sosai yayi dariya bayan ya kashe wayar , tabbas ya lura da Sanam k'uriciya
nadamun ta , daga haifar yara tafara takun sak'a dasu tabbas yasan akwai me zuga Sanam ,
wannan kishin datakeyi da Maman yaran gaskiya yayi yawa , murmushi yayi tare da cewa " Zan
yi k'ok'arin yadda zanyi naga nasa miki soyayyar k'annen ki koda ba uwa d'aya ce ta haifeku ba
.....
Bayan minty 20 tuni Sanam ta shirya cikin wani had'adden less , d'inkin riga da siket ya
kamata sosai d'in ki , less d'in kalar pink yaji duwatsu a jiki sosai , ta d'auki blue d'in gyale
k'arami ta yafa tare da saka wani blue d'in takalmi me tsini , fesa turarukan ta tashiga yi masu
k'amshi da tsadar gaske , tana gamawa ta kira wayar Huneed tana fad'in " Sojana na shirya
kai nake jira kawai , Huneed yayi murmushi yace " My angel kifito harabar gidan ku tun d'azu
nake jiran sarauniya ta , murmushi tayi tare da kashe wayar sannan ta fito , koda tazo palor
bata samu kowa ba haka tafice abinta ....
Tunda ta fito idanun da yake kanta yana yaba tsaruwar datayi , cikin ransa sai kuma
hamdala yake ga Allah da samun Sanam cikin Rayuwar sa , tana k'arasowa ta shigo cikin motar
tana wani kashe masa ido , shima kashe matan yayi yana fad'in " kinyi kyau sosai My Wifey
tamkar kar mufita kinsan banaso ana gane min ke , murmushi tayi cike da shagwab'a tace " to
muko ma kawai mu zauna dama nima bason fitar nake ba , dariya yasa yana fad'in " ank'i
wayon sai munje munga Twins d'in Daddy , tuni yatashi motar me gadi ya bud'e musu gate
suka fice.......
Sai da suka biya wani kataferen store Huneed yayiwa jarirai siyayya , duk inda suka
gilma sai ankallesu saboda had'uwar da sukayi , suna gama siyayyar suka fito Huneed ya
mik'awa Sanam key d'in motar yace " ungo kiyi driving d'in mu nagaji dayawa , batare da musu
ba Sanam ta karb'i mukullin tashiga b'angaren wajen driving , taja suka tafi.....
Tafiyar minty 10 ita takawosu Anguwar Asokoro , duk wanda ya kwana ya tashi a garin
Abuja yasan Anguwar Asokoro unguwa ce ta masu dashi , unguwa ce data amsa sunan ta ta
zallar masu kud'i da 'yan siyasa , gidaje ne had'add'u da suka tsaru tamkar a turai , Sanam ta
shiga Hon. A k'ofar wani katafaren gida , dasauri aka wangale mata k'ofar gate d'in gidan me
gadi yana musu sannu da zuwa , wajen parking space taje ta paka motar tana duban Huneed ,
murmushi yayi mata sannan yace " yayi kyau babbar direba , ashe haka kika iya motar sai kace
wata enginer , dariya tayi har dimple dinta ya motsa sannan tace " ai kafini iyawa tunda kai kana
jan motar yak'i , Huneed yayi murmushi yace " kema zan koya miki dai kishirya , ganin Sanam
sai jan shi da hira take tak'i bari su fita daga motar yasa shi cewa " My Wifey yakama ta mu
shiga daga ciki ko , batace masa komai ba ta bud'e murfin k'ofar motar ta fice abinta , shima
fitowa yayi tare da saka me gadi ya d'ebo kayan cikin but d'in motar ya biyosu dashi ......
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 31.
Jerawa Sukayi suka shiga cikin Palor gidan , kana ganin su tamkar miji da mata dan
iya dacewa da juna sungama yi , Huneed tunda suka shigo cikin gidan ya raina kansa sosai ,
duk tsaruwar gidan su Sanam sai yaga ashe bakomai bane wannan shine k'arshen had'uwa ,
suna saka kansu cikin palor gidan wani k'amshi tare da wani dadda d'an k'amshi ya bugi hancin
su , Sanam gawanar son k'amshi tuni ta lumshe ido tana kuma bud'e hanci tana shak'ar
k'amshin turaren wutar , tunda takejin turaren wuta masu k'amshi bata tab'a karo da wannan me
dad'in k'amshin haka ba..
Sallama sukayi su dukan su dan Huneed k'in yarda yayi ya tsaya a harabar gidan , shi
burun sa bai wuce yaga Twins da suka kasance k'annen Bbyn tasa , palor cike yake da 'Yan
uwan Hajiya Maimuna suna ta hira abinsu hankali kwance , sallamar da Su Sanam sukayi itace
duk ta dakatar dasu daga hirar da sukeyi , tuni kallo ya dawo gun Sanam da Huneed wanda
suka tsaya daga bakin k'ofa sukayi turus , Hajiya Maimuna idanu ta zubawa Sanam tana
mamakin zuwan ta , dan rabon data ga Sanam a gidan nan har ta manta ma , d'aya daga cikin
'Yan uwan Hajiya Maimuna ce tace musu " sannun ku da zuwa bisimillah ku shigo , Sanam
tamkar wacce batason tafiya haka ta taka ta zauna a d'aya daga cikin kujerun palor , Huneed
ya durk'usa har k'asa yana gaidasu su duka , amsa masa sukayi cike da sakin fuska sannan ya
mik'e shima ya zauna , Mamaki ne ya kama zuciyar Huneed ganin duk matan dasuke cikin
palor kusan kamar su d'aya da Sanam , Wacce ya ke kallo kuma yaji ajikin sa itace me jegon
tafi kowacce kama da Sanam , dan wallahi badan tana da shekaru ba kuma gata da jiki wallahi
si yace Sanam ce , dan kamar tasu ta b'aci sosai . cikin zuciyar sa yake tunanin tabbas akwai
abinda Sanam ke b'oye masa , amman wannan kana Ganin ta basai anfad'a maka ba kasan
itace wacce ta haifi Sanam , wata ce daga cikin Matan tace " Sanam baki gan mu bane kikayi
shuru batare da kin gaida mu ba ? sai sannan Huneed ya tuna da abinda Sanam tayi wato
rashin gaida mutanen da tagani , shuru tayi tamkar wacce batasan ana magana ba , Huneed
ya dube ta itama shi take kallo yashiga yi mata alama da ido akan ta gaidasu mana , d'auke kai
tayi tana turo baki kafin tace " ina yinin ku , amsawa sukayi da lafiya sannan kowacce ta mik'e
tana barin palor , Hajiya Maimuna ya rage a ciki itama kuma mik'ewar tayi zata bar palor , da
sauri Huneed yace " Mumy ina Twins d'in suke plss , cak ta tsaya tana juyowa ta kallesa tabbas
wannan ko waye yana da matsayi me girma a wajen Sanam , kuma ita kanta tunda suka shigo
tare ta yaba da nutsuwar sa da kuma kwarjinin sa , a hankali Hajiya Maimun ta furta zan turo
akawo maka su yanzu , sai dai dan Allah inaso kar kabawa wannan yarinyar ta kusa da kai
yarana , dan shi mak'iyi duk lokacin da zai kusan ce ka to dole akwai mugun abu acikin ransa ,
tana gama magana ta juya ta bar palor abin ta itama...
sosai maganar Hajiya Maimuna ta ratsa zuciyar Sanam , mik'ewa tayi da sauri tayi hanyar
barin palor idanun ta cike da hawaye , da sauri Huneed ya sha gaban ta yana fad'in " ina zakije
Sanam ? inaso kidawo ki zauna dan akwai abinda nakeso ki sanar dani game da Mumyn Twins
, meye ya had'a da ita kuke irin wannan rayuwar haka ? sannan jikina yabani Mumyn Twins
itace wacce ta haifeki Sanam duba da yadda kuke kama sosai , dan Allah ki taimaka ki cireni
acikin duhu wallahi kaina yafara d'aukar zafi , daga Bayana su yaji ana cewa " tabbas Maimuna
itace Mahaifiyar Sanam , Itace wacce ta ta raineta tuntana ciki har Allah ya fito da ita duniya , ta
shayar da ita na tsawon shekara biyu bata re da ta k'osa ko gajiyawa ba , da sauri Huneed ya
jiyo da ganin wacece take magana wata dattijuwa ce fara sol tamkar ita tayi kanta saboda kyau
, kamar su d'aya da Sanam har tafi kama da Sanam d'in akan Mumyn Twins , Hannun ta rik'e
da kyawawan jariran wad'an da suka sha kayan sanyi ajikin su , Sanam k'urawa Hajiya Babba
idanuwa tayi dan tunda take bata tab'a ganin taba , gashi komai nasu iri d'aya dan har tafi kama
da ita fiye da Mumyn nata , tabbas wannan ko tantama babu itace ta haifi Mumyn ta , take taji
soyayyar dattijuwar me cike da kwarjini da kamala ya kama ta , ido ta zuba mata ko k'iftawa
babu tana kallon ta , Hajiya Babba taci gaba da magana " tunda ga randa aka yaye Sanam bata
k'ara zama tare da Maimuna ba , Mahaifinta ya d'auke ta yayi wa Matar sa kyautar ta wacce
itace sanadiyyar raba Uwa da 'Yar ta , Sanam jin ance Hajiya Nafeesa itace sanadin rabata da
Mumyn ta yasa taji haushin Hajiya Babbar ya kamata , take ta bud'e k'ofar palor ta fice abinta
rai a b'ace , dan duk duniya batason atab'a Mumyn ta Hajiya Nafeesa wacce takejin ta duk
duniya bata da kamar ta , ....
Huneed duban Hajiya Babba yayi cike da girma mawa ya gaida ta , amsawa tayi cike da
sakin fuska dan tayaba sosai da hankalin sa , kuma tanaji ajikin ta shine zai kawo wa jikar tata
Alkairi a cikin Rayuwar ta , ansar yaran yayi tare dayi musu addu'a ya d'auko wayar sa yayi
musu pic , tabbas Daddy yayi gaskiya daya cewa Sanam sunfita kyau sosai gaskiya yaran sun
gaji da had'uwa , k'aunar suce tashiga ratsa shi ta ko 'ina yana kallon su , tunowa da Sanam
yasa yabawa Hajiya Babba su tare da mik'ewa yana fad'in zai tafi , Hajiya Babba ta dubesa
tace " Yaro mungode sosai Allah yayi maka albarka , nasan wannan zuwan da kukayi kai ne ka
saka Sanam tazo , hakan ya nuna mana tana sonka kuma kaima kana sonta , dan Allah inaso
kayi amfani da soyayar ka da ita ka dai daita tsakanin ta da Mahaifiyar ta , ka kuma dunga nuna
mata muhimman cin Mahaifiyar ta dan duk duniya bata da kamar ta , duk da munsan komai
datakeyi yasamu nasaba ne daga irin hannun data taso , ilimin addinima ba lallai tana dashi ba
dan Maimuna tasha gayamin ita kanta marik'iyar ta ta bata damu da ibada ba , dan Allah yaro
ka taimaka ka ceto rayuwar ta daga cikin duhu ka dawo da ita haske , dan ajikina nakejin
had'uwar ku da ita alkairine kuma tunda naganka naji kashiga raina , Huneed yace " insha
Allah zanyi iya k'ok'arina naga Sanam ta canza halayen ta marasa kyau , kuma kiyiwa Mumy
Albishir insha Allah ni Huneed nayi mata Alk'awari Sanam sai tadawo gare ta cike da so da
k'auna , wani dad'i Hajiya Babba taji nan danan tashiga saka masa albarka yayi mata sallama
yatafi.....
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata