Showing 66001 words to 69000 words out of 80926 words

Chapter 23 - YAR KISHIYA Book Complete BY Zee MD.pdf

Zee MD   

10 Jul 2025

4199

, shuru sukayi aka rasa me magana daga ciki ,
Mummy tace " to shikenan tunda bawanda zaiyi magana Bari intashi in baku guri , yunk'urawa
tayi zata mik'e da sauri Huneed yace " Mummy karki tafi zanyi magana , komowa tayi ta zauna
batare da tace komai ba ,
Huneed yace " Mummy nidai haryanzu bansan laifin danayiwa Sanam ba , tun Randa nataka
naje k'ofar gidan k'awar ta wannan abun yafaru , Nan Huneed ya laburtawa Mummy komai
Sanam na zaune tanaji , Mummy tace " tabbas wannan shirine aka shirya muku , kuma gashi
anyi nassara akan Sanam d'in sosai , Mummy Nan ta kunnawa Huneed videon da aka turowa
Sanam a waya tabashi tace yagani ,....

Huneed Yana Fara kallah ya zabura Yana fad'in " tabbas wannan shirine aka shirya Mana ,
wallahi Mummy yadda nafad'a muku haka abin yafaru , Mummy tace " basai ka rantse ba
Huneed wallahi duk me hankali yaga wannan abun yasan shirine , kuma kowaye yayi muku
hakan to tabbas na cikin gidane ,. Sanam shuru tayi tana nazari meyasa zasuce shirine
wannan ? Wata zuciyar tace Mata " tabbas shirine ki yarda Sanam taya Huneed da Diyana zasu
miki haka ? Kinajin duk abinda Huneed yace ankirasa anfad'a Masa a waya , sai kuma tashiga
tunanin tabbas da ta tashi daga bacci tayi mamakin ganin wayar ta a kashe , kenan hakan na

nufin ankashe Mata wayar ne saboda Kar Huneed ya kirata , tabbas itama ta yadda shirine to
waye yake Shirin ganin sun rabu ? Huneed ne ya katse mata tunani da cewa " Mummy zanyi
bincike sosai akan wannan al'amarin kubani kwana daya rak , Mummy tace " kayi komai a
nutse Dan kasan shi mak'iyi Koda yaushe shima cikin shiri yake , sannan inaso kununawa
mak'iyan sunci galaba akan ku , Kar ku yadda ku nuna musu kunshirya kuci gaba da takun
sak'a , gefe d'aya kuma kuci gaba da soyayyar ku , Nan taci gaba dayi musu nasiha me ratsa
zuciya har kowannen su ya gamsu da lallai shirine akai musu Dan anaso arabasu, Sanam sosai
tayi Nadama akan abinda taje gidan su Diyana tayi , .....
Mummy tunda taga Sanam tasaki jiki ta mik'e tabasu waje Dan su zanta....

Huneed tamkar me jiran tashin Mummyn yayi saurin dawowa kusa da Sanam , jikin sa har
Yana gugar nata yace " Haba Bbyna kin wahalar Dani dayawa fa , kinsa naje yak'i Amman
nakasa tab'uka komai saboda tunaninki , Sanam ta d'ago da idanuwan ta da suka sha kuka
tana hararar sa , Huneed ya kama kunnen sa Yana fad'in "ayimin afuwa Dan bazan iya jurewa
fushin My Wifey na ba ,. Sanam ta turo baki tana cewa " bawani Matarka meyasa ka saka
Diyana a jikin da Ni kad'ai nakeson mallakar sa ? Huneed yace " taimakonta nayi ganin tana
neman fad'uwa , Amman da nasan hakan zai ruguzamin farin cikin mata ta Dana barta tafad'i ,
sosai Sanam ta yadda da Huneed Dan dama sharrin zuciyane yasa ta yadda da abinda tagani
batare da tayi bincike ba, Nan Huneed yaci gaba da lallab'a Sanam tare da yi Mata kalaman
soyayya masu kwantar da hankali ,

Sai wajen sha d'aya na dare sannan Huneed yace " zanzo natafi gida Naga dare yafarayi ,
kuma kiksan yau nadawo kuma inaso gobe tunda safe nafara binciken masu son shiga
tsakanina da My Wifey d'ina ,. Sanam tace " Yana da kyau Dan Nima zanso sanin suwaye suka
saka ayi Mana hakan , Mummy ce ta sakko Dan haka Huneed ya mik'e Yana cewa Sanam "
zantafi Amman Dan Allah karki koma can gidan yanzu kibari sai bayan kwana biyu , Sanam
tace " band'auko kayana ba da sauran abubuwan buk'ata ta , sai dai ko gobe naje nad'auko
inyaso sai nadawo , Nima kaina Ina bukatar yin nesa da gidan na kwana biyu , sosai Mummy
taji dad'in kalaman Yarinyar tata , a zuciyar ta tayi Mata addu'a akan Allah yakuma tsareta yasa
daga haka yarinyar ta tadawo gareta,......

Bayan tafiyar Huneed Sanam da Mummy suka ci gaba da tattauna maganar akan abinda
yafaru , Kiran wayar Hajiya Nafeesa ne yashigo wayar Sanam , sai da ta kalli Mummyn ta kafin
ta d'aga Kiran , Hajiya Nafeesa tace " My luvly Wai Ina kika shigane yau ? Tund'azu nake
nemanki a waya Bata shigowa , kuma na Kira wayar k'awarki itama Bata shiga Daddyn ki ma
yakiraki yace min Bata shigowa Anya lafiya kuwa ? Sanam tace " lafiyalau Mummy Ina gidan
Mummyna shiyasa , kuma wayata akashe take shiyasa Bata shigowa sai yanzu na bud'e ,
Hajiya Nafeesa cike da son jin abinda Sanam d'in tace tace " wacce Mummyn naki kenan ?
Sanam tace "Mummyn Twins Aman zan kwana , yanzu zankira Daddyn sai muyi magana
dashi sai da safe Mummy , Bata jira me Hajiya Nafeesar zatace Mata ba takatse wayar ,. Hajiya
Nafeesa rik'e da waya a hannu tayi saroro tana mamakin canzawar Sanam d'in haka........

*Comment* plss

*'Yar Mutan Kanawa*
_Ce_✍
[9/27, 14:27] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
‍♀️‍♀️



*NA*
*Zee MD*



*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/





*Bisimillahir Rahamanir Rahim*




Chapter 43.


Hajiya Nafeesa rik'e da waya a hannu sai mamakin irin canzawar da Sanam tayi ,
tabbas akwai wata a k'asa lallai Hajiya Maimuna ta tashi tsaye , gashi lokaci d'aya Sanam na
neman komawa wajen mahaifiyarta , Hajiya Nafeesa ji tayi wani Abu ya tsaya Mata aranta
Wanda tarasa gane meye , shin murna zatayi da komawar Sanam haka ko kuma bak'in ciki ?
Duk irin yadda ta tsani Sanam da kuma yadda takeson rabata da Mahaifin ta sai data samu
kanta da jin kewar Sanam d'in , .....


*Washe gari*

Tun asuba Mummyn Twins ta tashi Sanam tayi sallah , bayan sun idar da sallah Mummy
ta d'auko Hisnun Muslum tafara koyawa Sanam yadda zata dunga yin azkar ,. Sannan ta Gaya
Mata fa'idar yin Azkar saboda neman kariya daga sharrin Mutum da Aljan , bayan sun kammala
Sanam takoma bacci saboda ba saba tashi tayi a wannan lokacin ba.,.....

Huneed bayan ya idar da sallar asuba Yana fitowa daga masallaci ya nufi unguwar su
Diyana Dan Fara bincike ,.
Yana zuwa yasamu wajen me saida Drinks ya zauna akan banci , Yana zaune har gari ya
k'arasa wayewa mutane suka Fara wucewa , sai wajen takwas me shagon yazo ya bud'e ,
sallama yayiwa Huneed sannan ya shiga Yana aikin gyare gyare , Huneed wayar sa ya d'auko
yafara danne danne a haka har yagama gyara shagon ya fito ya zauna kan Bencin da Huneed
yake ,. Tunda Huneed ya k'arewa Isma'il kallo yasan lallai Yana da mugun son kud'i , Dan haka
yayi amfani da wannan Yanayin nasa yace " Malam inason kamin aiki kuma kafad'i ko nawa
kakeso zanbaka ,.
Isma'il ya kalli Huneed da sauri sannan yace " Oga wanne irin aiki kenan ? Sannan taya
zanyi maka aiki bansan kaba kawai daga ganinka yau sai inyi maka aiki , Huneed yace " sanina
bashida amfani kawai aiki nakeso kamin na Rana d'aya , Amman in bazakayi ba zantafi innemi
wani , Huneed na Gama magana ya mik'e Yana shirin barin wajen ,. Da sauri Isma'il yace " Oga
kadawo muyi magana zanyi maka kafad'amin wanne irin aiki zanyi ?
Huneed yayi wani murmushi Wanda shi kad'ai yasan ma'anar yinsa yadawo ya zauna ,.
Duban Isma'il yayi yace " inaso kafad'amin ranar Asabar d'in data wuce wasu masu motar
k'irar Vibe fantia sunzo wajen nan suntsaya, kalar motar Blue ce misalin k'arfe hud'u da minty
40 na yamma me suka zo yi unguwar Nan ? Isma'il take yagano su Maryam mutumin Nan yake
nufi , Nan Isma'il yace " Oga gaskiya bangane me kake Nufi ba ,kuma Ni ranar ma banbud'e
shagona ba ,. Huneed yayi murmushi yasa hannunsa cikin aljihi ya zato bandir d'in 'yan dubu
dubu guda biyu dubu d'ari biyu kenan , da sauri Isma'il ya Kai dubansa kan kud'in Yana wani
lashe harshe tamkar yaga abinci ,. Huneed Yana lura dashi sai yayi kamar baigansa ba yace "
Bari natafi wajen wani tunda naga Kai baka buk'ata , dasauri Isma'il yace " Wallahi inaso Oga
sai dai gaskiya inajin tsoron abinda zaije yadawo , Dan komai dayafaru a ranar da saka hannu
na Amman bansan abinda akayi Mata ba , Huneed ya gyara zama Yana duban Isma'il yace "
inaso kafad'amin gaskiyar komai da yafaru Babu abinda zaayi maka , Nan
Isma'il yabawa Huneed labarin yadda Maryam tazo tasamesa akan yasawa Diyana k'wayar
bacci a lemo da kuma yadda yaga Maryam d'in tazo da wasu maza guda biyu , komai da Isma'il
ke fad'i tuni Huneed ya nad'eshi a waya , daga Nan Huneed ya mik'e Masa sallama tare da ce
Masa yabashi number Maryam d'in , Bayan yabashi Huneed ya gargad'i Isma'il akan karya
kuskura ya shedawa Maryam zuwan sa , in kuma har yayi hakan to lallai zai hukuntashi , Isma'il
yace " hakan ma bazata faruba Oga Nan yabashi kud'in da yayi masa alk'awari tare da barin
gurin......


Sai wajen sha biyu sannan Sanam ta tashi tashiga wanka , Mummy nashiga d'akin taji
alamar wanka take Nan ta bud'e wordrup ta d'auko mata d'aya daga cikin dogayen rigunan ta

sababbi Wanda ko sawa Bata tab'ayi ba , ajiye Mata tayi akan gadon sannan ta had'a Mata da
sabon Pant da breazia ta fita daga d'akin , Koda Sanam ta fito taga wannnan kayan abakin
gado tasan Mummy ce ta ajiye Mata , Nan ta nufi kan mudubi Wanda ya cika da kayan shafa
kala kala da kuma turaruka masu tsadar gaske ,. Nan tashafa Mai tasa kwalli sannan ta shafa
kulacca da had'add'un Humra , rigar ta d'auko tasaka tamkar Dan ita aka siyo tayi Mata cif ajiki
, gashi tayi Mata kyau sosai ta fesa turare sannan ta yafa d'ankwalin rigar ta fito daga cikin
d'akin....

A falor k'asa tasamu Mummy da Twins sai wasan su suke , Tunda ta taho Mummy ta
kafeta da ido lallai jininka jininka ne komai na Sanam irin natane lokacin data na budurwa ,.
Sanam na k'arasowa tace " Mummy barka da Rana , Mummy Twins tace " sannu da fitowa ,
lallai kina Shan bacci da yawa. Haka kikeyi kenan a gidan naku bakya taya Auntyn naki aiki ?
Sanam tayi Murmushi tana cewa " Mummy to mezanyi akwai 'yan aiki fa , Mummy tayi
Murmushi itama sannan tace "duk da haka Yana da kyau kidunga shiga kitchen kina ganin
yadda akeyin aikin girki , inkinje gidan ki ai dole kiyiwa Mijinki girki da kanki , Sanam tace "
Mummy shi ma sai yaci na 'yan aikin kawai , Daddy ma girkin 'yan aiki yake ci Dan Mummy
Bata shiga kitchen sosai ,.
Murmushi Hajiya Maimuna tayi cikin zuciyar ta tana tuno yadda Alhaji Abba keyi " duk ranar
girkin Hajiya Nafeesa saiya ci ya k'oshi a gidan ta sannan yake tafiya , Dan akan hakan sunsha
fad'a dashi tace Masa yatafi gidan sa yaje yaci abinci tunda ba girkin ta bane , yakance Mata
shi bayajin dad'in girkin kowa indai bana taba , ko tafiya yayi yabar k'asar kullum saiya Mata
k'orafin baya iya cin abinci sai su cheefs da coffe ,. Tabbas dole ta tashi tsaye wajen koyawa
Sanam girke girke , mutuk'ar mace ta iya girki to ta hau mataki casa'in da tara a cikin matakan
zama lafiya da miji ,
Kiran wayar ta da akayi yasa tadawo daga tunani data tafi , d'agawa tayi suka gaisa sa
Huneed , Nan yake sanar Mata yasamu nasarar Fara gano Wanda suka musu wannan abun ,
gashinan Yana hanyar zuwa gidan yanzu haka , Mummy tace " to Alhamdulullah sai kazo ,
kashe wayar tayi sannan ta dubi Sanam tace " ga Huneed Nan yataho Yana hanya kishiga
kitchen keda murja kuyi Masa jallof rice akwai komai a Frizer , Sanam tace " to sannan ta mik'e
ta nufi cikin kitchen d'in.....

Hajiya Nafeesa ta dubi Fahad sannan tace " nagaji da halinka na d'aukarmin Motar kufita
yawo kaida wannan shegiyar mara galihu , duk inda kukabi indai mutanena sunga motar sai
sunkira sunce yanzu na wuce , Fahad yace " Aunty Dan na d'auki motar ki na fita shine abin
magana ? to kisa Mijinki ya canza Miki wata sai kibarmin wannan Kinga shikenan , Hajiya
Nafeesa ta kalleshi da wani mugun kallo tace " lallai Fahad to ko canzamin motar Alhaji yayi
kana ganin zanbar maka wannan ne ? Duk maganganun da sukeyi Maryam na lab'e tana jinsu
tunda ga farko , k'ara kasa kunne tayi tanaji Fahad yace " ashe akwai abinda zaki iya hanani
Aunty ? Hajiya Nafeesa cike da k'osawa da maganar Fahad tace " Dan Allah kafita Ina buk'atar
hutu , tana cewa haka tashige can cikin d'akin ta tabar Fahad tsaye bashi da tacewa , ...

Shima fitowa yayi daga d'akin Yana meyin k'wafa , karo sukaci da Maryam ta kafeshi da
idanuwa tana kallon sa , shima ita yake kallo da yimata alamar taji duk abinda suke cewa ? Nan

Maryam tayi Murmushi mugunta sannan tace " naji komai kawai ka k'yaleta zamuyi maganinta
kabari na haihu , Fahad yace " haba Merry har saikin haihu ma za'ayi maganin ta kawai ki nemo
Mana mafita ,.

Maryam tace " kabani Nan da kwan biyu zan tsara Mana yadda zamuyi Mata .......


Huneed Yana zuwa bayan sun gaisa da Mummy ya kunna Mata Muryar Isma'il wacce
yayi record a waya , komai sai da Mummy taji Nan tashiga salati tare da jinjina lamarin , tabbas
mak'iyi abin gudune , kuma d'an Adam butulune yanzu ita Diyana da Wanda ta amincewa dashi
aka had'a baki aka sa Mata k'waya a lemo tayi bacci , Sanam ce ta fito daga cikin kitchen tana
turo baki , Huneed ya zuba Mata muyin idanun sa ko k'iftawa Babu , Mummy ta kalli Sanam d'in
sannan tace "lafiya ke kuma kike turo baki haka ? Mummy Wallahi girki akwai wuya nidai kawai
kicewa Murja ta k'arasa nagaji dayawa , Huneed ji yayi kamar yatashi ya rungumo ta yadunga
juyata a cikin palorn , wani kyau yagani tayi na musamman lallai inyasamu Sanam yagama cika
burinsa na duniya ,. Kwata kwata ya manta a inda yake ya kafeta da idanuwa sai kallo yake ita
kuma tamkar wacce Bata gansa ba sai wani narkewa take tana zabga wa Mummy shagwab'a ,
sai da Mummy tayi gyara murya sannan Huneed yadawo sai dai Yana sosa k'eya , Mummy tace
" wannan budurwar taka zaka sha fama sosai batason aiki ko kad'an yadda na Fahimceta ,
Murmushi Huneed yayi sannan yace " Mummy sai anemo Mana masu aiki Dan Nima bana so
tasha wuya , Nan Sanam ta zauna kusa da Mummy suka shiga gaya Mata abinda yafaru , take
Sanam taji jikinta ya kumayin sanyi akan abinda tayiwa Diyana , Nan suka shiga tattaunawa
har number Maaryam da ya anso sai daya Gaya musu , take suka yanke cewar yasa sabon layi
yakira number Dan asan yadda za'ayi su kamata , ....

Take Huneed yasa sabon layi a wayar sa ya dannan Number Maryam , sai data kashe ya
kuma Kira sannan ta d'aga , Babu sallama Babu komai tace " waye ne yake neman damuna da
tsakar ranar Nan haka ? Huneed a hands free yasa wayar Nan ya dubi Sanam da Mummy suka
Masa alama da yayi magana ,. A hankali ya furta aminci agareki barka da hutawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login