Showing 3001 words to 6000 words out of 80926 words
tamkar zata tashi sama , kowa yasanta
kaima dan dai baka dad'e da dawowa ba shiyasa bakasanta ba , Huneed ya dubi Hisham yace
" wai kana nufin kace wannan gudun da akeyi da motar mace ce haka ? murmushi Hisham
yakumayi yana cewa " Allah ya taimakeka ma daba ta taka kaba , dan kusan duk Estate d'in
wallahi kowa yasan wannan mugun halin nata , shiyasa duk lokacin dazata wuce kowa yake
killace kansa saboda sanin halinta , Huneed jiyayi ransa yakuma b'aci tabbas saiya yi
maganinta kuwa , dan tunda tashiga gonarsa wallahi saita raina kanta , mik'ewa yayi yace "
inaso kafad'amin da wanne lokacin take wucewa dan tabbas saina saita mata hankalinta ,
Hisham yace " anjima ma zaka iya jinta sannan wajen sha biyun dare ma tana zuwa wucewa ,
amman inaso kabar wannan maganar ka shareta , dan wallahi bata da mutunci ko kad'an gashi
Daddynta ko k'ararta bayaso ana kai masa , Huneed yace " wallahi daga ita har Daddyn nata
dai dai nake dasu kuma tunda har ta tsokanoni wallahi saina koya mata hankali , yatasa tsaki
yasa kai yafice daga d'akin nasu .......
Gudu Sanam take tamkar zata tashi sama har ta k'araso gidan gonar Daddyn su Zahra ,
tunda Diyana tagaya mata anan take Partyn nata , tana shigowa aka fara ihu ana fad'in "
Oyoyo *'Yar kishiya rik'on me hak'uri* wannan sunan Sanam tana mugun sonshi , dan haka
kawai hannu tasaka cikin jakar ta tafara zuba musu ruwan dollars , dan kwata kwata bata
amfani da kud'in Nigeria mutuk'ar zasuyi wani party da k'awayenta , take gayu suka saka wawa
suna ihun murna tare da zuba mata kirari , kanta ne yake k'ara fashewa tanajinta bakamar ta ,
Zahra tuni ranta yafara b'aci da abida gayun sukeyiwa Sanam , taya ita data shirya Party
amman koda tazo basuyi mata kirari haka ba , daman tsakanin Sanam da Zahra akwai dabi
sosai , kuma kowacce jitake da kanta tare da tak'ama da kud'i , sai dai duk kud'in Daddyn
Zahra bai kai Daddyn Sanam ba , tuni Zahra ta d'auki speaker tayi wata tsawa tana fad'in "ya
isheku haka malamai , in itace ta taraku zan iya tafiya inbaku guri , nan suka shiga bata hak'uri
suna mata nata kirarin , Sanam ta tab'e baki tare da hawa step d'in da Zahra take , tana zuwa
ta mik'awa Zahra hannu tana fad'in " Congrat k'awata rai yakashe , bandir d'in Dollars ta saka
mata a hannu tare da cewa " gashi kyasha mai , tana gama fad'in hakan tayi sauri ta sauko tare
da watsa kud'i sama sannan ta bar gun.....
Huneed tunda akayi sallar isha'i yaja ya zauna a k'ofar gate d'in Estate , dan yace yau bazai
shiga gidaba har sai Yarinyar nan tazo tasamesa , kulle k'ofar gate d'in yayi yacewa megadi
yaje ya huta zuwa anjima zai jire masa , wajen k'arfe goma na dare saiga Sanam ta nufo Estate
da mugun gudunta data saba , koda Huneed yaji tahowar ta sai ya mik'e tare da nufar k'ofar
gate d'in , aikuwa tuni Sanam tafara mahaukacin Hon d'in ta , cikin ransa yace zakiyi bayani
wallahi nan ba k'ofar gate d'in gidan ku bane da kika saba iko , ganin ba'azo an bud'e mata ba
yasa tafito a fusace , k'ofar ta nufo tana fad'in " wane mara mutuncinne wajen daya ruf'e gate
d'in kuma yanaji ana hon bazai zo yabud'e ba ? buga k'ofar tafarayi amman taji shuru ba
wanda yayi magana , ranta tuni ya k'ara b'aci sosai lallai masu gadin nan basu san ta bane
shiyasa , tuni Huneed ya nemo ruwan sanyin s bokiti guda harda k'ank'ara sannan ya nufo
k'ofar gate d'in , dama gashi anyi ruwan sama garin ya d'au wani sanyi me ratsa jiki , sakatun
dayasa yashiga zarewa yana murmushin mugunta , lokacin Sanam ta kira wayar Mumy amman
ba'ad'agaba , ranta yagama b'aci mutuk'a , tanajin anfara zare sakata ta dubi k'ofar tana
k'issima irin rashin mutuncin dazatayiwa wanda ya bud'e .....
Bata ankara ba sai saukar ruwan sanyi taji ajikinta , tuni ta tsorata tana ja da baya jikinta
yana tsuma , gashi ko kad'an Sanam bata shiri da ruwan sanyi , Huneed ya hasketa da
touthlith yana fad'in " jiki wata k'azama dake sai rashin kunya da iya shege , inaso kisani
ba'ayimin batare da na rama ba , kuma daga yau mun k'ullah nida ke , dan saina gyaraki a
wannan Estate d'in namu , maza kizo ki wuce kibawa mutane guri mara kunyar banza , Sanam
data daskare tamkar gunki a wajen ko motsi batayi saboda tsabar takaici.........
*Comment* plss
*'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_
[9/27, 09:37] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on_ _Me_ _Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
Chapter 3.
Tanaji tana gani Huneed ya juya yashige cikin Estate d'in , da kallo Sanam tabi
bayan sa tare da mamakin irin Zarrarsa dayayi mata wannan wulak'ancin , komawa tayi cikin
motar ta taja ta da gudu tashiga Estate d'in itama........
Sanam tana zuwa tayi wani mahaukacin Hon. Da gudu megadinsu yatafi tamkar zai kifa ya
bud'e gate d'in , da gudu ta shigo tayi parking ta fita kana ganinta kasan a fusace take , tana
shiga cikin Falor ko kallon kowa batayi ba tahaye sama da gudu.....
Hajiya Nafeesa lokacin suna zaune ita da Alhaji Abba suna hira , yana ganin wucewar
Sanam a haka ya mik'e yana cewa " Anya lafiya kuwa naga My luv tashigo gida a haka ? Hajiya
Nafeesa cike da kissa tace " nima naga kamar ranta a b'ace inajin dai akwai abinda akayi mata ,
da sauri Alhaji Abba ya nufi sama d'akin Sanam , Hajiya Nafeesa tabishi da wata uwar Harara
tana fad'in " aikin banza yarinya ta dunga garaka kamar wani k'wallo , wannan soyayya taku
gab nake da datseta , tsaki taja tare da nufar saman itama ........
Sanam tana shiga d'akinta tanufi toilet tasakarwa kanta ruwan d'umi , tanayin wanka tana
tunanin irin rashin mutuncin da guy d'innan yayi mata , tabbas tunda aka haifeta batajin akwai
wanda yatab'a yimata irin wannan wulak'ancin ba ,
Shigowar Daddyn ta taji cikin d'akin nata yana kiran sunan ta , dasauri tayi maza ta fito daga
toilet d'in d'aure da tawul, Daddyn ta yace " meyafaru dake kika shigo a wani yanayi ? murmushi
tayi sannan tace " babu komai Daddy wlh gajiya nayi kuma gashi inajin fitsari shiyasa , wata
ajiyar zuciya yayi tare da cewa " kin tsoratani My luvly Dauther , dai dai nan Hajiya Nafeesa
tashigo tana fad'in " meye yafaru my Happiness duk kin tsorata mu , murmushi tayi tace " babu
komai fa Mumy kawai fitsari nakeji shiyasa , nan Hajiya Nafeesa ta rik'e mata kunne cikin wasa
tana fad'in " zanyi maganinki agidan nan , naga kullum sabuwar rigima kike k'arayi , dariya suka
saka dukansu sannan Daddy yace " in kinshirya kifito zamuyi magana , Sanam tace " to Daddy
bari nasa kaya ganinan zuwa.......
Huneed baki har kunne saboda Abinda yayiwa Sanam ko banza zata shiga taitayinta , duk
dayaji da gudu ta wuce amman zai gyara mata zama kwanan nan ,
Tunowa yayi lokacin daya watsa mata ruwan tayi tsamo tsamo da ita , dariya ya tuntsire da
ita yana cewa " ni ko fuskar ta ban tsaya gani ba saboda wulak'ancinta , cikin zuciyar sa yace "
amman gaskiya tana kama da Aljanu , dan yaga farinta har yaso yayi yawa duk da bawani
tsayawa yayi ya k'are mata kallo ba ......
Sanam cikin kayan bacci ta fito Falor tasamu guri kusa da Daddyn ta ta zauna , cike da
Shagwab'a tace " Daddy gani mezaka gayamin ne ? murmushi yayi yadubi Hajiya Nafeesa yace
" ki gaya mata da kanki , murmushi Hajiya Nafeesa tayi tace " kagaya mata da kanka kaidai ,
Sanam tafara turo baki tana cewa " wai Daddy mene dan Allah kugayamin plss , Daddy cike
da murna yace " zaki samu k'anwa ko k'ani kwanan nan , wani tsalle ta daka tana rungume
Hajiya Nafeesa tace " Mumy da gaske cikine dake wayyo dad'i zansamu k'ani , murmushin
yak'e Hajiya Nafeesa tayi tare da cewa " banice nake da cikiba my Baby , Mumy Maimuna itace
take da ciki , tsayawa tayi cak murnar ta ta koma ciki tana fad'in " toni ina ruwana da cikinta
tunda ba Mumyna bace , Daddy ya dubeta yace " haba My luv yakamata kitayani da murna
koda bazakiyi murna saboda itaba , karki manta inaso naga kinsamu k'anne wanda zakina wasa
dasu , shuru tayi nawasu mintyna sanna tace " Daddy kayi addu'ar Allah yabawa Mumyna
sainayi duk yadda nakeso dasu , amman a yanzu bana murna dan nasan soyayyar dakakemin
ce zata ragu , murmushi yayi yace "haba my luv kinsan duk yawan Yaran da zansamu a
duniya babu abinda zai ragu game da soyayyarki , ked'in kece wacce Allah yafara bani a
duniya kinga kuwa dole zansoki tamkar raina , Hajiya Nafeesa dauriya kawai takeyi saboda
wani abu dake tokare da k'irjinta , mik'ewa Sanam tayi sannan tace " saida safe Daddy nagaji
bacci nakejin , to my luv Allah yatashemu lafiya kiyi bacci me dad'i , matsawa tayi ta
sumbaceshi a kunci , shima ya sunbace ta a goshi sannan ta juya wajen Mumy itama hakan tayi
mata Ta juya tahaye sama d'akinta.....
Zahra tunda Sanam tabata wannan kud'in takejin haushi , ita Sanam zatazo har wajen
Party d'in ta ta tozar tata , tabbas saita rama ai lokacin Birthday d'in Sanam yakusa anan zata
rama abinda tayi mata ...
.
Washe gari Sanam sai sha d'aya ta farka tayi wanka ta shirya cikin wata doguwar rigar
atamfa , d'inkin sosai yakamata ko ina najikinta a d'ame , sakkowa k'asa tayi sai faman zabga
k'amshi take tamkar wata sabuwar Amarya , zama tayi kan dinnig tafara had'a break fast ,
Soyayyiyar plantain ta xuba tare da had'a tea , sai da tagama zubawa cikinta sannan ta mik'e
tafita........
Harabar gidan tafito tafara tunani wanne mataki zata d'auka akan wanda yayi mata wanka
da ruwan sanyi , tabbas saita nemosa ta nuna masa da banbanci tsakanin matsiyaci dakuma
me kud'i , dan daga ganinsa talaka fak'iri dan tasan duk cikin estate d'in su babu wanda yakai
Daddyn ta kud'i , ita kuwa duk wanda bai kai Daddynta ba to tabbas ba me kud'i bane a wajenta
, a hankali take tafiya har ta k'araso k'ofar gate , da gudu me gadi yataho yanayi mata kirari tare
da cewa " hajjaju aikene kikawo ayi miki ? bud'emin gate kawai tace tana kuma d'aure fuska ,
da sauri ya bud'e mata tare dayi mata fatan dawowa lafiya.......
*Kuyi hak'uri da wannan*
*Comment plss*
*'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_
[9/27, 09:37] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on_ _Me_ _Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
Chapter 4.
Tunda Sanam ta fito daga cikin gidan su tafara zagaye a Estate d'insu duk akan idon
Huneed , dan shima tunda gari ya waye yafito yake gadin wucewar ta , dan yanaso ya tabbatar
da cewa taji kashedinsa ko kuwa , tana tafe tana duba k'ofofin gidajen dan sotake ta tabbatar
da a wanne gida yake , kamar daga sama taji muryar sa yana fad'in " sokike kiganni ko ? da
sauri taja da baya tana dubansa cikin zuciyar ta take fad'in " anya wannan mutumin mutum ne
kuwa ? zarrarsa da kuma yadda yake nuna wata izza dajin kansa , katseta yayi da cewa "
kind'auka ni Aljanine ko ? k'iris yarage Sanam bata zura da gudu ba , wata zufa ce ta tsatstsafo
daga jikinta duk irin sanyin da akeyi , amman ta dake ta dubesa tace " Hmm nasan kai
mutum ne kamar kowa , sannan ba kowa bane kai face talaka fak'iri wanda bai wuce kazo a
meyimin wankin takalmi ba , Wani Shu'umin murmushi Huneed yayi yana dubanta sannan ya
matso gab da ita Numfashin su na dukan juna yace " inaso kisani duk wani d'agawarki da ji da
kanki da kuma dukiyar dakike tak'ama da ita duk abanza suke a wajena , kuma kamar yadda
kikace ni bakowa bane yes ni bakowa bane kuma ba d'an kowa bane , amman inaso kisani ni
ba k'ask'astance bane bakuma mara zuciya bane , ni d'in da kike gani Namiji acikin mazaje me
zuciyar Nema , kuma mutuk'ar muna numfashi dani dake a duniya to watarana sai kin gogemin
takalmin da zansa , kuma kin wankemin kayan jikina tare da gogemin motar dazan hau , yana
gama gaya mata hakan yajuya zai tafi tuni tayi saurin shan gabansa tare da rik'e k'ugu tace "
wai kai dame kake tak'ama da har kakemin irin wannan maganganu ? Huneed ya dubeta yace "
bana tak'ama da komai sai dai innuna miki Namiji Namijine a ko'inah kuma duk irin girman kan
mace to tabbas Namiji ne gatan ta , nasan duk wanna d'agawar taki da jin kan naki dole
watarana gidan wani zakije kuma dole ya juyaki mutuk'ar ba maza yarako duniya ba , kuma ina
fatan kina sane da sharud'an da na gindaya miki akan gudu da motar , in kunne yaji to jiki ya
tsira yashige yafara tafiya abinsa , a fusace Sanam tace waye kai d'in kuma acikin Estate d'in
inaso isan waye Mahaifinka da har kake kafamin doka haka ? batare da Huneed ya juyoba
yace " Sunana Huneed Abdallah Kiyi tambaya cikin Estate d'in zakiji tarihina in kina buk'ata ,
Nabarki lafiya Bera a cikin Mata.........
Sanam tsayawa tayi tana kallon sa har ya k'ulewa ganinta , Sunan daya kirata dashi tashiga
maimaitawa Bera a cikin Mata , tabbas wannan yaraina mata hankali wato yana nufin ita ba
mace bace ba , lallai zata nuna masa kalar halinta sai yagane lallai ita ba Bera bace mace ce
data amsa sunan ta , a fusace ta juya ta nufi Hanyar gida.......
Huneed yana dawowa yasamu kira a wajen ogan su , tuni aka turasu aiki wani gari a jihar
Calaba dan ko 'Yan ta'adda , had'a kayansa yayi kafin yafito har anzo d'aukar sa , yana fito wa
yaron sa ya fito ya sara masa tare da bud'e masa murfin mota , Hisham yadubi Huneed yace "
Soja wuta soja harbi Soja gatan daji inbaku gari baza ya kwana k'alau ba , inayi maka fatan
samun Nasara a wannan fitar taku Allah yadawo mana dakai lafiya , Murmushi Huneed yayi
tare da duban Hisham yace " Ameen d'an uwa ka kulamin da Hajiyar mu kadunga bata
magungunan ta akan lokaci , sannan inaso kasa idonka akan Berar yarinyar nan kaga zata
gyara halin nata ko saina fito mata a kalar ta , tuni Hisham yasa dariya yace " Anya wannan
yarinyar zata canza kuwa ? amman zandunga saka ido naga yadda wasan naku zai k'are ,
Huneed yayi Murmushi yace " ai haryanzu yarinya ce batasan komai na duniya ba , gata da
kud'i shine tasani amman da sannu saina saita ta tadawo dai dai , tarbiyar da iyayenta sukayi
mata saina gogeta na d'ora mata tawa , Hisham yace " Allah yasa hakan dan gaskiya basu
d'orata adai dai ba , Huneed yace " zata dawo dai dai tunda har ta shiga gonata , juyawa yayi
ya shiga motar tare dacewa Hisham sai sunyi waya....
Koda Sanam tadawo gida Sama tahaye cikin d'akinta , wayar ta ta d'auko tare da kiran