Showing 54001 words to 57000 words out of 80926 words
turo ayi magana , amman tunda abun yana neman zame mata tashin hankali
dole tayi masa magana, da haka suka shiga hirar su wacce duk rabi akan soyayyar ta da
Huneed ne......
*Washe gari*
Tunda Sanam ta tashi take shirin tarar Huneed , bawani girki ta iya ba bare tace zata shiga
kitchen da kanta tayi masa , sai dai kawai tasa angyara d'akin saukar bak'i sannan aka turaresa
da turaruka masu dad'in k'amshi , shiga kitchen tayi tasamu me yi musu aiki tace tana so tayi
mata girki na musamman tana da bak'o , Alawiya cike da girmamawa tace " ranki ya dad'e me
da me kike so a dafa masa ? Sanam tayi shuru na wasu Mintyna tana nazarin me Huneed
yafiso , can ta tuna wani lokaci suna hira yake tambayar ta wai ta iya Dambun Shinkafa yaji
gyada da zogale , a lokacin tayi wani murmushi tace masa ta iya indai so yake , nan ta kalli
Alawiyya tace inaso kimin Dambun shinkafa yaji zogale da gyad'a , sannan sai kiyi min farfesun
Kayan ciki , ki d'ebi naman kaji ki soya sai ki yi masa kunun Aya , Alawiya cike da girma mawa
tace " angama ranki ya dad'e Sanam ta fita daga kitchen ta nufi d'akin ta.....
Tunda Huneed ya sauka a Abuja yakejin sa cikin wani farin ciki , Hisham ne ya d'aukosa
a mota sai hira suke abin su , suna k'arasowa gida Hajiyar su ta taresa cike da farin ciki da so
da k'auna , 'Dakin sa ya nufa dan yarage kayan jikin sa yayi wanka , yana fitowa kiran wayar
Sanam na shigowa wayar sa , Murmushi yayi sannn ya d'aga yana fad'in " My Wifey sai yanzu
kika tuna da mijin naki ? Murmushi Sanam tayi sannan tace " dama koda yaushe ina tunanin sa
araina , ina fatan My Husbee na ya dawo lafiya ? Huneed yace " waye yafad'a miki nadawo ?
Murmushi tayi sannan tace " a jikina naji cewar Masoyina yana kusa dani , sannan in nasaita
Nunfashina tasaitin gidan ku inajin bugun zuciya ta yana k'ara yin yawa , hakan ya tabbatar mun
da cewa Sojana yana cikin garin Abuja , Wani dad'ine yakama Huneed yayi murmushi yana
lumshe idanu sannan cikin wata kasalalliyar Murya yace " tabbas Matata batayi k'arya ba ,
yanzu haka ina cikin gidan mu a d'akin ina shirin tahowa inga Matata , Sanam tamkar tayi
tsalle saboda murna kawai murmushi take baki yak'i rufuwa , ahaka wayar ta katse tuni tafad'a
toilet danyin wanka.....
K'arfe biyar dai dai Huneed ya iso gidan su Sanam , tunda yashigo masu aikin gidan suke
girmama shi , indai Huneed yazo to suma ranar sai sunsamu rabon su , dan hannuwan sa a
bud'e yake akwai shi da kyauta , dan haka kowa keson zuwan sa kuma suke girma mashi ......
Sanam tuni ta shirya cikin wani Material me tsadar gaske , d'in riga da siket sun zauna a
jikinta das , sabon takalmi kalar jikin adon less d'in tasa tasa kuma mayafi kalar takalmin , fad'in
irin kyan da Sanam tayi b'ata lokacine , inbanda K'amshi babu abinda ke tashi ajikinta , tuni
Huneed ya sheda mata zuwan sa , nan tace masa ya shiga d'akin saukar bak'i gatanan
zuwa.......
Sai da akayi kusan minty 5 sannan Sanam ta sakko cikin takunta na isa , tana gama
sakkowa tasamu bakowa a palor sai Maryam , Maryam tana ganin Sanam ta zuba mata idanu ,
turaren da Sanam ta fesa Maryam na shak'ar sa taji Amai ya taso mata , da gudu ta nufi toilet
d'in dake cikin palor tana kakarin Amai , Sanam tuni ranta yayi mugun b'aci me wannan 'Yar
iskar take nufi da har zata hau Amai dan taganta ? kamar ta je gurin Maryam amman sai tafasa
ta fita daga cikin palor , sai dai tabbas indai Huneed yatafi dole zata sameta taji dalilin ta nayi
mata hakan , duk b'acin da ranta yayi tana tozali da Huneed taji duk yatafi , murmushi yakar
mata itama ta maida masa da nata Murmushin , Huneed ji yayi kamar yatashi ya rungumeta
amman yasan hakan bazai yuwu yanzu ba , zama tayi kusa dashi tana fad'in " sannu da zuwa
My Sojana, Huneed ya rik'o Hannun ta yana fad'in " Matar Soja itama Sojan ce My Wifey irin
wannan kyau haka ? tamkar an canzamin ke komai naki yakuma k'arayin kyau , nan yashiga
yabon kyan datayi da fad'in dole yasiyi wannan kwalliya , wayar sa ya d'auko yashiga d'aukar
ta pic , duk yadda ta motsa sai yayi mata kuma ko wanne yayi sai tayi kyau , sai da yagama yi
mata sannan ya matso kusa da ita yayi musu tare batare da ta kulaba , tana gani tayi saurin
rufe fuska tana murmushi , nan suka shiga hirar su wacce rabin ta akan yadda sukayi Missing
d'in juna , anan Huneed yashiga shedawa Sanam anyi masa k'arin girma nan da kwana biyu
za'ayi bikin karramashi , Murna Sanam tashiga yi tana godiya ga Allah , tuni ta bud'e masa
Abincin datasa akayi masa tafara seving d'insa.....
Bayan Sallar Magriba Huneed yace ta tashi suje wata Unguwa su dawo , batare da musu
ba ko tambayar inda zasu Sanam ta mik'e suka jera har jikin Motar , suna zuwa suka shiga
sannan suka fice daga cikin gidan.....
Sun shagaltu da hira shiyasa Sanam bata fahimci inda suka nufa ba , sai da suka shiga
cikin Estate d'in sannan tagane Gidan Mummyn Twins zasuje , kallon Huneed tayi yasakar
mata murmushi sannan yace " Mummy tanason ganin kyakkyawar 'Yar ta , Sanam ta turo baki
tana fad'in "Haka tace maka kenan kawai dai kanaso kadatsemin farin cikin danakeyi yau ,
tsayawa yayi dai dai k'ofar gate d'in gidan yana hon. Sannan yace mata " kintab'a ganin Uwar
dazata datsewa 'Yar ta farin ciki ? Sanam ta yi shuru bata bashi amsa ba , kuma dai dai lokacin
Megadin gidan ya bud'e musu gate , Huneed yace "to kidaina cewa haka dan duk wata Uwa da
kike gani tafison Farin cikin 'Yayan ta fiye ma danata farin cikin , haka suka fito daga cikin
Motar ya rik'o mata hannu suka nufi cikin Palor gidan .....
Koda shigar su wani k'amshin turaren wuta ne yadaki Hancin su , Sai kuma sukayi ido biyu
da Hajiya Maimuna tana zaune tana bawa Twins d'in ta nono , sallama sukayi mata a tare
Sanam tamkar wacce k'wai yafashewa a cikin ciki take tafiya har ta isa kan kujera ta zauna ,
shima Huneed xama yayi sannan yashiga gaida Mummyn cikin girmamawa , ga Mamakin
Sanam sai taga Mummyn nata ta amsa masa cike da sakin fuska dakuma nuna so da k'auna ,
harji tayi tana tambayar sa ya Hajiyar sa da kuma Hisham , bayan ya amsa mata da duk lafiya
suke sannan takumaji tace masa " ya hanya dafatan kadawo lafiya , ina tayaka murnar samun
k'arin girman dakayi , Allah yatsareka yakuma kareka a duk inda kake , Sanam tamkar mutum
mutumi tazama agun , dan abun yabata mamaki sosai cikin ranta tashiga tambayar " Yaushe
Huneed da Mummy suka san juna haka ? Duk tayaya tasan yayi tafiya harda k'arin girman da
yasamu ? bamai amsa mata wanannan tambayoyin sai Huneed , wasan da Huneed yake da
Twins d'in shiya dawo da ita daga tunanin datakeyi.........
[9/27, 10:06] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 36.
A hankali Sanam tacewa Hajiya Maimuna " Mummy ina yini , sosai Hajiya Maimuna
taji abun kamar almara yau ita Sanam ta kira da sunan Mummy ? wani dad'i taji har cikin ranta
tare da sakawa Huneed albarka dan tasan shine yabata wannan tarbiyar , amsawa tayi tare
da cewa " lafiya k'alau muke dafatan kuma kuna nan lafiya keda Mummyn taki ? Sanam tace
lafiya lau , Mummyn Twins kallon Huneed tayi tana me jinjina masa ta sigar lumshe idanuwa ,
murmushi Huneed yayi sannan yacewa Sanam " Aunty Sanam ga Twins suna mik'o gaisuwa ,
kunya ce ta kama Sanam ganin ko k'annan nata bata tab'a gani ba , da sauri ta matsa ta anshe
macen wacce suke ce mata Amrah , tsayawa tayi tana kallon ta sai taga kamar su d'aya ita da
Amrah , har dimple d'in da take dashi itama Amrah tana wangale mata baki taga ya lotsa , wata
iriyar k'aunar 'Yar k'anwar ta ta taji ta kama ta , sumbatar ta tashiga yi tare da yi mata wasa ,
cike da so da K'auna Hajiya Maimuna ke duban Sanam d'in , cikin zuciyar ta tana fad'in " dama
ace zasu dauwama a haka batare da Sanam tayi nisa dasu ba , ta shagala da kallon Sanam
d'in wacce ta ware take ta wasa da Amrah har da mata wak'a , shima Huneed d'in kallon ta
yake cike da jin dad'in yadda Sanam ta bashi had'in kai wajen faran ta ran Mummyn nata ,
wayar ta ta d'auko a jaka tashiga d'aukar Amrah video tana mata wasa , Hajiya Maimuna tana
ganin haka ta tashi ta nufi sama dan ta d'an basu waje , bakin ta har kunne sai saka wa Huneed
albarka takeyi ,...
Aikuwa tamkar jira Huneed yake ta tashi ya matso kusa da Sanam shima yafara d'aukar
su a waya , Namijin shi kuma ana kiran sa da Ameeer , tuni Sanam ta ajiye Amrah tana fad'in "
My Sojana bani Ameeer d'in shima , mik'a mata shi yayi tashiga kallon sa shima , sosai yafisu
kyau ita da Amrah dan yaron ya had'u , bai kaisu haske ba amma kyansa abin kallo ne ya had'u
, Sanam ta had'asu duka ta rumgume tana cewa yimana pic in d'ora a social media nima aga
k'anne na , murmushi yayi yana duban ta sannan yace " ai baza a yadda k'annan ki bane ,
duban sa tayi da alamar tambaya ? ea mana ai sai dai ace 'Ya'yanki ne tunda ai kin isa haifar
su , dariya tasa tana duban su Suma tamkar sunji me akace suka fara wangale mata baki , tuni
Huneed ya shagala da kallon su yafara musu video , bayan kamar minty 20 Hajiya Maimuna
tadawo hannun ta d'auke da tire , dambun naman kaji ne aciki tazo ta ajiye musu , ta kalli
Sanam tace " in kuna buk'atar wani abun ki shiga kitchen ki dafa muku , ni yau tuwon semo nayi
miyar yauk'i kuma nasan ba lallai kuci ba , Sanam tace " a k'oshe muke Mummy dambun
naman ma ya isa , dama Mummy tasan Sanam din tana son damun nama , dan wani lokacin
tanaji in suna waya da Daddyn ta zatace ya siyomata dambun nama , duk abinda Sanam ke so
Hajiya Maimuna tagama sanin shi , tuni tafara cin dambun naman hannu baka hannu
k'warya..... Huneed duban ta yayi yana dariya yana fad'in " ci a hankali mana Madam , murmushi tayi
sannan a hankali tace masa " bantab'a cin dambun nama me dad'in wannan ba shiyasa , sai
wajen k'arfe goma suka bar gidan Mummyn Twins , Sanam cike da kewar Twins itama Hajiya
Maimuna cike da kewar Sanam d'in .....
Hajiya Maimuna bayan ta dawo daga raka su Sanan jikin mota tad'au waya tashiga kiran
Hajiyar ta , tana d'agawa tashiga bata labarin zuwan su Sanan d'in da komai da komai daya faru
, Hajiya tashiga hamdala tare da cewa " lallai wannan yaron d'an Albarka ne , kuma shine
wanda ya cancan ta yazama miji agare ta , nidama tun farkon ganina dashi naji ya kwantamin
arai , ashe shine sanadin da zai dawo miki da farin cikin ki har gida , inaso kici gaba da addu'a
tare da janyo yarinyar ki jikin ki a hankali , duk abinda kikasan tanason shi to ki dunga aika mata
da shi da haka zaki jawota jikin ki , sosai Hajiya Maimuna tayi na'am da shawarwarin Hajiyar
tata , nan sukayi sallama tana saka mata albarka.....
Sanam tun da suka taho baki yak'i rufuwa sai murmushi take , duban ta Huneed yayi
sannan yace " Madam gaskiya indai mukayi aure kifara haifo mana Twins masu kama da su
Amrah , Sanam tayi murmushi sannan tace " tamkar in dauwama ina tare dasu nakeji , gaskiya
yaran sun shiga raina mutuk'a My Sojana , wlh da Mummy zata bani su tas zanyi mata rainon
su , Murmushin dad'i Huneed yaji a zuciyar sa yace " anzo gurin , a fili kuma yace " taya
Mummy zata baki su ko kin manta k'ananu ne basu isa abada su ba , in rainon su kikeso me
zai hana bazaki dawo gidan Mummyn Twins d'in da zama ba , Sanam ta kalli Huneed sannan
tayi shuru na wasu lokutan kafin tace " ai Mummy bazata bari nadawo ba , kasan ba shiri take
da Mummyn Twins ba shiyasa , Huneed yace " in dai kinason rainon su kawai ki shirya ki koma
gidan su , in kuma bazaki koma ba to kidunga zuwa kina musu kwana biyu biyu , ahaka zasu
shak'u dake har sudunga ganeki inkinje , Nan Huneed yashiga yiwa Sanam dabara tare da
cusa mata ra'ayin zuwa gidan Mahaifiyar ta ......
Tuni Sanam tasa pic d'in su ita da Twins ta rungumo su tana dariya , wasu tasa a status
sai kuma ta zab'i guda d'aya wanda sukayi da Huneed da Twins d'in duka sunyi kyau ta d'ora a
dp....
Hajiya Nafeesa tana chat da k'awayen ta manyan mata taga Sanam tayi status ,
mamakine ya kamata dan a iya sanin ta Sanam batayin Status , sannan pic d'in dake Dp ta yafi
shekara uku tak'i canza shi , sai gashi yau taga tayi status tare da canza Dp , da sauri tashiga
Status tafara dubawa k'irjin tane ya buga ganin Sanam rungume da k'annen ta a palor gidan su
tana dariya , duk pic d'in data saka bawanda basuyi kyau ba ita da Twins d'in , tana duba dp
nan ma sai da gaban ta ya fad'i , yaushe Sanam tafara son Mahaifiyar ta ? yaushe Sanam
tafara zuwa inda Uwar ta take ? tasan ba wanda ya had'a wannan munafincin sai wannan
shegen Huneed d'in , tabbas lokaci yayi dazatayi gaba da gaba dashi akan ya fita daga sabgar
Sanam ,. Wani huci take tana kuma yin zoom d'in pic din tana gani , wato Hajiya Maimuna tana
k'ok'arin yin nasara akan ta , to wallahi bazata sab'u ba dole takoma wajen bokan ta ayo musu
farraqu me zafi........ [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 37.
Farin cikin dake d'auke a fuskar Sanam tamkar wacce aka yiwa tukuci da Aljannah ,
d'auke da murmushi a fuskar ta tadubi Huneed tace " My Hero bani da kalmar da zan furta
maka wajen godiya , sai dai zanyi maka addu'ar Allah yabiya maka buk'atun ka na Alkairi ,
tabbas zuwana gidan mu yanzu yasa na fahimci lallai akwai Alaqa me k'arfi tsakanin ka da
Mummy Twins , komai naka tasani hakan ya nuna min kazama d'an gida sosai da sosai , tunda
na taso yaune karon farko