Showing 6001 words to 9000 words out of 80926 words
Number Diyana , bugu d'aya tayi ta d'aga tare da fara yiwa Sanam kirari " Babbar Yarinya gidan
kud'i sarauniyar kyauta , duk wanda yaga kiranki to yafara washe baki dan yasan Alkairine ,
Sanam cike da jin kai da wata Izza tace " Diyana kina inah yanzu ? Diyana tace " ina gida a
zaune inah zaman banza ko da aikine inzo ? Sanam tace " tabbas akwai Aiki akan wani Mutum
dayake neman zama matsala arayuwa ta , Diyana tace " waye shi dazai shiga sabgar Uwar
d'akina baya goya marayu ? Sanam tace " shine nakeso kizo yanzu kiyimin bincike cikin Estate
d'in nan namu akan labarin sa kaf , Diyana tace " karki damu *Rik'on Me Hak'uri* ganina zuwa
kibani minty 10 kacal , Sanam ta kashe wayar tare dayin jifa da ita kan gado tana rik'e kai .......
Minty Goma na cika sai ga Diyana a gidan su Sanam tamkar Aljana , tana zuwa Sanam
tafara bata labarin tun daga farkon Abinda Huneed yayi mata har izuwa yau d'in nan daya kafa
mata wannan sharud'an , Diyana tace " inason sanin sunansa dakuma Number gidan su ,
Sanam tace " Sunansa Wai Huneed Abdallah number gidan su kuma wallahi bansan taba , sai
dai inaganin in kika rik'e iya sunan ma yayi zaki samo min komai nasa , Diyana tace kibani 50
min. Zanfita induba miki cikin Estate d'in nan naku harda wajen sa , Sanam tace " hakan yayi
dan sonake nayi shiri sosai akansa dan bazan k'yalesa ba tunda ya tab'oni , Diyana tuni ta
mik'e dan fita nemo labari akan Huneed.......
Diyana na fitowa tafara duba cikin Estate d'in , duk k'ofar gidan dataga da megadi sai taje ta
tambayesa ko yasan Wani Huneed Abdallah , sai da taje gidaje wajen guda hud'u kowanne
yana baisan shiba , tana shirin buga gida na biyar sukayi karo da Hisham yafito daga k'ofar gate
d'in gidansu , yana ganinta suka dubi juna Diyana tasakar masa wani shu'umin murmushi ,
k'arasowa tayi tana wani yauk'i sannan ta dubesa tace " dan Allah tambaya nakeyi ko Allah
zaisa nadace ? Hisham yace " yi tambayarki ko Allah zaisa nasani , Diyana tace " ina neman
wani Guy ne me suna Huneed Abdallah , dubanta Hisham yayi sosai sannan yace " Saurayin
kine Kenan ? murmushi Diyana tayi sannan tace " ko d'aya wlh saurayin k'awatane shine ta
aikoni gunsa kuma ni bansan gidan suba , nadai san a cikin Estate d'in yake shiyasa nake
cigitashi ko Allah zaisa nagansa , Hisham yayi murmushi yace " ni ma bak'one a nan Unguwar
sai dai kibari anjima zansamu me gadin gate d'in Estate d'in gaba d'aya na tambayesa ko zai
san shi , Diyan cike dajin dad'i tace " yauwa nagode sosai kaga ka hutar dani , yanzu bari
nabaka Number na inkasamu Labarin inda yake saika kirani , tuni Diyana tabawa Hisham
number ta , dan ita kam tana ganinsa taji ya burgeta dan guy d'in yahad'u sosai , nan sukayi
salama ta wuce tatafi Abinta , Hisham na tsaye har saida yaga b'acewar ta sannan ya juya
yashiga gida.......
Diyana na dawowa tabawa Sanam labari duk yadda sukayi da Hisham , sai dai kwata kwata
ta manata bata amshi number sa ba itace tabashi tata , gashi ko Sunan sa bata sani ba , dan
haka suka zauna suna jiran kiran wayar Hisham ........
Koda Hisham ya shigo cikin gida tuni yakira Huneed , yana d'agawa ya sheda masa anzo
nemansa kuma budurwa ce wai k'awar tace ta turota , Huneed yayi murmushi yace " kai me
kake tunani akan haka ? Hisham yace " nidai bankawo komai ba nayi tunanin kodai ita wacce
tazo nemanka d'in itace take sonka ? Murmushi Huneed yakumayi sannan yace " aikota akayi
amman ba itace ba , kuma Bera ce ta saka ta tayi bincike akaina dan haka kabasu duk Abinda
suke buk'ata indai basu wuce gona da iri ba , sai munsake waya kit yakashe wayar yabar
Hisham rik'e da waya baki asake , yana bala'in mamakin Huneed da wannan halin nasa ,
tabbas zai iya cewa Huneed d'in d'an baiwane sosai acikin mutane.......
*Bana ganin Comment*
*Zantafi yajin aiki*
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on_ _Me_ _Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
Chapter 5.
Har aka kira Magriba Sanam da Diyana basu ga kiran Hisham ba , k'arshe dai
Diyana tayiwa Sanam sallama akan gobe zata dawo lallai sai ta nemo mata labarinsa......
Sanam sosai takeson sake ganin Huneed , dan ita komai nasa ya tsaya mata aranta ,
tabbas bata tab'a ganin mutum da bashi da tsoro ko kad'an ba irinsa , dan haka tanaso ko sau
d'ayane ta bashi tsoro ta kuma nuna masa wacece ita......
Duk wani motsi na Sanam tuni Huneed yasa asaka masa ido akanta , dan haka ma yasan
shirin su akan sanin waye shi ita da Diyana..
Washe gari Hisham ya kira wayar Diyana yace mata inta shirya a inah zasu had'u yabata
labarin Huneed d'in , aikuwa tamkar anyi mata albishir da gidan Aljannah haka takira Sanam ta
sheda mata , Sanam tace " kawai ki kawosa gidan mu cikin Garden sai muzauna anan yagaya
mana , da wannan shawarar Diyana ta kira Hisham ta fad'a masa inda takeso su had'u , nan
suka tsaida lokaci sannan sukayi sallama.......
Tuni Diyana ta iso gidan su Sanam dan bataso yazo bai sameta ba , suna zaune suna
hira saiga kiran wayar Hisham akan ya k'araso , sawa sukayi aka shigo dashi tare da kai masa
kayan motsa baki , yafi minty 10 dazama sannan yagansu sunjero sun taho suna hira abinsu ,
suna zuwa suka gaisa da Diyana , ita kuwa gogar sai wani shan k'amshi take ita ala dole tanajin
kanta , Hisham ya dubeta yace " barka da hutawa Hajjaju dafatan kina lafiya , ata k'aice ta amsa
masa da cewa lafiya , daga haka taja kujera ta zauna tare d fara danna wayar ta tamkar
batasan damutane a wajen ba , murmushi Hisham yayi cikin zuciyar sa yana fad'in " tabbas
wannan yarinyar bamai saita ki sai Yaya Huneed shine zai iya saita ki , a fili kuwa yace " to
Malama Diyana nasamo miki labarin Wannan guy d'in da kika sani , Diyana tace " ina godiya
sosai dan haka ina sauraren ka ......
Da farko dai Sunan sa Huneed Abdallah Ma'aji , Haifaffen garin Borno state ne acan yayi
karatunsa tunda ga matakin primary har yakai ga kammala Digree d'insa , Mahaifinsa ya
kasance Babban Soja a Barrack d'in Borno , su biyu iyayensu suka haifa dagashi sai d'an
uwansa , Mahaifinsa Canal Abdallah Ma'aji yarasu a wajen wani yak'i da akayi lokacin a garin
Barno , tunda nan Huneed yayi shirin maye gurbin Mahaifinsa , tashi farko dayatafi training
yadawo da babban resure akan and'aukesa aikin soja , kuma yafito da babban matsayi yanzu
haka Shima babban Canal ne , aiki ne yadawo dasu Abuja shiyasa yataho da Mahaifiyar sa
dakuma d'an uwan sa , Huneed mutum ne me rik'o da Addini gashi da son zumumci , sai dai
Akwai abubuwan da baya shiri dasu sune baya shiri da mutum me girman kai , baya shiri da
mutum me wulak'anta Al'uma , sannan bayason mutumin da girmama na gaba dashi , miskili ne
sosai inkinga dariyar sa to yana cikin 'yan uwansa ko kuma yana tare da mahaifiyar sa ,
bayason yawan tambaya ko kuma a dunga yi masa dariya , hakan na harzuk'asa sosai kuma
yana son wasa da k'ananan yara , a b'angaren cima kuma mutum ne me son tuwon biski miyar
taushe , yana son saka kaya k'ananu sannan duk Juma'a yana saka jallabiya , yanason
k'amshi sosai yana shiri da dukkan mutum me tsafta da kuma k'amshi , wannan shine cikakken
labarin Huneed Abdallah Ma'aji , sai dai kuma abinda ba'a rasa ba wanda bansani ba .....
Ajiyar Zuciya Diyana tayi tare da cewa " mungode sosai Hisham , Sanam tuni ta mik'e tabar
wajen tamkar batasan da wasu mutane ba abinta , binta Hisham yayi da kallo yana fad'in
tabbas akwai babban aiki atare da Yaya Huneed , Diyana ta dubesa tace " magana kakeyine ?
yayi sauri ya mik'e yace " ni zan zo na wuce dan nasan lokacin da Hajiyar mu zata sha magani
yayi , nan sukayi sallama da Diyana ya wuce yatafi abinsa ........
*Kuyi maneji*
*'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_
[9/27, 09:37] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on_ _Me_ _Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}* ✨✨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
Chapter 6.
Diyana na shiga cikin gida tasamu Sanam a falor tana zagaye , tana ganin Diyana
tace " tabbas dole asameshi da wannan halin ashe soja ne , to tabbas saina janyo masa
ansallameshi daga wajen aikin dayake tak'ama dashi , tunda harya shigo rayuwata sai yagane
bashi da wayo , nagode Diyana nasa miki dubu d'ari biyar a account d'inki kasha ice cream ,
tana gama fad'ar haka ta haye sama abinta , Diyana cike da murna ta fice abinta tana murnar
samun kud'i........
Tundaga nan Sanam tayi sercing d'in Huneed a Social media , duk wani posting d'in dayayi
sai data bi ta duba , tab'e baki tayi cikin Zuciyar ta tana yaba kyan halittar Huneed , samun
kanta tayi da kafe shi da ido tana kallo saita ke ganin tamkar murmushi yakeyi mata , Wurgi tayi
da wayar sannan a hankali ta furta Huneed zakasan nice nashiga rayuwar ka bakaine kashiga
tawa ba....
Washe gari tuni motar Sanam data canza ta iso , nan tasha wanka tashiga tafara zagaya
gari , ranar gudun datakeyi ya wuce ko wanne irin gudu datake , duk inda tayi saikaga kowa na
neman hanyar tsira da ransa , a haka ta k'araso gidan su Diyana dan nuna mata motar ta ,
tana shigowa lokacin Diyana na fitowa daga cikin gidan su , sakin baki Diyana tayi tana kallon
had'uwar motar da Sanam ke ciki , cikin ranta tace " arzik'i yayi arayuwa , Allah yabamu rabon
mu mu inba dan muna shiri da Sanam ba banga dalilin da zai hanani auran Daddyn taba , dai
dai lokacin Sanam ta fito cikin wasu d'amammun riga da wando tana sanye da glass a idonta ,
mukullin motar ta na hannunta sai karka d'ashi take tana taunar cingum , da gudu Diyana ta
k'araso tana fad'in " wow congrat my k'awa kice motar ta iso , Sanam tayi murmushi tana duban
Diyana tace " Zahra meyin gasa dani to wlh wannan motar ko Babanta baitab'a hawan irinta ba ,
Diyana tace " wace ita taja da me *'Yar kishiya rik'on me hak'uri* ai duk kud'in Baban ta bai isa
ya siyamata irin wannan ba , Sanam tace "kinshirya hawan ta ko ba yau ba ? da Sauri Diyana ta
zagaya tana fad'in " wanne ba yauba yanzu ma haka dama ice cream zani sha , nan Sanam ta
shiga taja motar dawani mugun gudu.......
Alhaji Abba yana zaune a falor sa yana cike wasu takaddu , Hajiya Maimuna ta sakko daga
sama tana zabga k'amshi tamkar sabuwar Amarya , tana k'arasowa tace " sannu da aiki My
Husbee , murmushi Alhaji Abba yayi yana duban Hajiya Maimuna yace " yauwa tauraruwar
mata , samun waje tayi ta zauna tana duban sa sannan tace " inason magana dakai amman
ina fatan kayimin kyakkyawar fahimta , Alhaji Abba yace " ina sauraranki ki fad'i duk abinda
kikeson fad'a , Hajiya Maimuna tace " inaso dan Allah ka nemawa Sanam makarantar islamiyya
kasata a ciki , yadda take tafiyar da rayuwar ta yakamata ace tana da ilimin addini ko Allah
zaisa ta rage wasu abubuwan , Alhaji Abba yayi shuru yana nazarin maganganun Hajiya
Maimuna , can ya nisa yace " kinsan a yanzu My Baby ta girmi zuwa makarantar islamiya , sai
dai zanyi magana da ita muji yadda zatace , inta amince sai asamar mata akaita , dan kinsan
tunda tadawo daga k'asar turkey tace hutu take buk'ata , amman zanyi mata magana duk
yadda tace haka za'ayi , dubansa Hajiya Maimuna tayi sannan tace " Haba Husbee taya zakace
sai yadda tace haka zakayi wai kaine ka haifi Sanam ko kuma itace ta haifeka ? Murmushi
Alhaji Abba yayi sannan yace " bazaki gane irin son danakeyi wa Sanam ba , karki manta itace
kad'ai 'Yar danake da ita a duk duniya sai kuma abinda yake cikinki , kinga kuwa wanda yake
ciki bani da tabbacin samunsa ita kuwa tana doron duniya dole insota fiye da komai , Hajiya
Maimuna tace " ban hanaka kaso Sanam ba amman inaso kasani yakamata kasan cewa ita fa
mace ce kuma gidan wani zataje , mutuk'ar tana tafiyar da halayyar ta yadda takeso to tabbas
bazata iya zaman aure ba , da sauri Alhaji Abba yadubi Hajiya Maimuna yace " dole saitayi
auren ? inaso kisani mutuk'ar mijin da Sanam zata aura bazai k'yaleta tayi yadda takeso ba to
wallahi sai dai ta zauna haka dan bana son ace antakurawa Rayuwa ta , wallahi Maimuna
badan kece kika tsugunna kika haifi Sanam ba to wallahi zance kinq kishi da ita , kuma da
yanzu kindad'e da barmin gida , wani tsaki yaja tare da d'ebe takardunsa dukansu ya nufi
sama......
Hajiya Maimuna binsa tayi da kallo tana mamakin irin halin Alhajin , kwata kwata indai
akan Sanam ne bashi da mutunci , zai iya rabuwa da kowa akanta ita kanta tasheda , saboda
Sanam yarabu da ' Yan uwansa da dama a hankali ta furta Allah kasa sugane shi da 'yar
tasa.......
Sanam da Diyana sunshiga gari sai faman wasa suke da motar , duk inda suka wuce sai
anyi Allah wadai dasu , gidan su Zahra suka nufo dan nuna mata motar , lokacin Zahra na
zance da saurayin ta Najeeb , ji sukayi anayin wani shegen hon. Me gigita mutane , da gudu
megadi ya bud'e gate d'in aikuwa Sanam ta figo motar a guje tashigo cikin gidan , Zahra da
Najeeb tuni suka mik'e tsaye ganin yadda aka shigo da motar da gudu tamkar za'a yo kansu ,
bin motar Zahra tayi da kallo dan tasan bata tab'a ganinta ba , kuma sannan Daddyn ta yana
gida bare tace shine yayi sabuwar motar , kid'an dataji yana tashi tamkar anje club yasa tagane
Sanam ce aciki , tuni taji ranta yayi mugun b'aci , bata gama tunani ba taga anbud'e murfin
motar Sanam ce ta fito tana taunar cingum tamkar wata karuwa , d'aya gefe kuma Diyana nace
tafito itama , dukansu bawacce tayi shigar mutunci ko wacce surar ta a bayyane take , wani
kishine ya ziyarci Zahra dan tasan halin Najeeb sarai da son mata , musamman had'add'un
mata irin su Sanam , Diyana ce tace " barka da hutawa Zahra dafatan munsameku lafiya ,
daman zuwa mukai mu nuna miki sabuwar motar da Sanam tayi , itama idan kinga zakisa
Daddyn ki yasai miki to mukuma zamu kuma canza wata , dan kinsan *'Yar kishiya* anriga da
antara mata ba Albashi suke d'auka ba , Zahra sosai taji zafin maganganun Diyana amman sai
ta dake tace " *'Yar* *Kishiya* ina tayaki murna Allah yasanya Alkairi , ke kuma Diyana ai
wanda ni ansan muna dashi kefa dakike binta kike maula , murmushi Diyana tayi sannan tace "
dad'in abin nice nake maular ba Ubana ba , kuma inayin maular ne a inda nasan akwai