Showing 24001 words to 27000 words out of 80926 words
ta , musamman lokacin data gansa d'aure da Tawul da kuma lokacin data fad'a
jikin sa a k'ofar gidan su Rauda , haka tai ta juyi ta kasa bacci tamkar mara lafiya , tashi tayi ta
kuma d'aukar wayar ta tashiga Face book shafin sa , aikuwa tana shiga taga bai dad'e dayin
posting ba da shigar sa ta cikakken Army , zoom d'in pic d'in tayi tana k'are masa kallo ,
murmushi tayi tana shafa fuskar sa tana fad'in " tabbas ka cika cikakken namiji wanda yaka
mata a jinjinawa , babu Namijin da Sanam ta tab'a so a duniya sai kai , har wani lumshe ido
take tana shafa masa fuska tare da tuno yadda yake komai nasa irin na isassun maza , tuni ta
danna kiran number sa dan tana buk'atar jin wanna daddad'ar muryar tasa , addu'a tashiga yi
aka Allah yasa ya d'aga mata kira wanna karan , ring take har ta yanke ba'a d'aga ba , sake
kira tayi karo na biyu sai da takusa yankewa sannan ya d'aga yana fad'in " Assalamu Alaikum ,
cike da tsoro Da rawar Murya Sanam tace " wa'alaikas salam barka da dare , da sauri Huneed
ya watstsake daga baccin da yasoma kamashi , cikin ransa yafara fad'in " tabbas wannan
muryar ta Sanam ce , duba number yayi yaga number ta k'asar waje ce , da sauri yace "
wanakeji kamar K'awata Sanam ? Murmushi Sanam tayi har sautin na fito tace " nice nakira
dafatan ban shiga hak'k'in ka ba kana bacci ? Murmushi Huneed yayi yace " kin shiga hak'k'ina
kuwa dan ina tare da mata ta kika kirani , yanzu haka gashican ta turoni waje ta kulle d'akin ta ,
Sanam jitayi wani abu ya tokare k'irjin ta wata zufa ta karyo mata , cikin ranta tace " dama
mutum nan yana da mata bata sani ba ? kamar yasan abinda take tunani kenan yace " kinsan
mantawa nayi kwata kwata ban sheda miki ina da mata ba har da yara guda biyu , yanzu gashi
kinjawomin kwanan k'ofar waje , cikin murya me sanyi Sanam tace " kayi hak'uri wallahi bansan
kana da mata ba da bazan kira ka a wannan daren ba , kabata hak'uri kaji sai da safe , kafin ta
kashe wayar yayi sauri yace " lah babu komai muci gaba da magana kinji , yakike yana baroku
dafatn komai nrml ? Sanam da kishi yake taso mata kawai tace masa " lafiya nake komai yana
nan yadda kabarshi amman kayi hak'uri sai da safe , bata jira cewar saba ta kashe wayar dukan
ta tana jifa da ita , kafin kuka ya biyo baya tare da jin haushin kanta na kiran datayi masa ,
tabbas da tasan yana da aure da baza ta saka shi a cikin ranta har haka ba , yanzu yazatayi da
Soyayyar sa wacce tashiga zuciyar ta lokaci d'aya ? kuka take sosai tana jin babu dadi , gashi
ita tun tasowar ta batason kishiya koda ta sittira ne bare ya kai ga had'a miji , kuka takeyi tare
da addu'ar cire son Huneed daya kamata batare da ta gama shirya hakan ba.......
Huneed tunda ya fahimci Sanam kishi ne yasa takashe waya , dariya yashiga yi sosai yana
murna yadda ta fad'a son sa , dan tabbas wanna kad'ai zai tabbar masa da ta fad'a soyayyar sa
, kwanciya yayi yana tuno yadda komai nata yake , murmushi yake in ya tuna yadda take gudu
sosai a titi ranar da yaje k'asar Turkey , a hankali ya furta " Iluv u my Baby Sanam I really luv u
more , wani lumshe ido yayi lokacin daya tuna yadda ta fad'o jikin sa da ana ruwan saman nan ,
tunda ga ranar ya tabbatar wa da kansa yana son Sanam d'in , dan haka dole da safe ya
rarrashi Abarsa dan kar yaje wani yayi masa bugun baya abarshi da hamma , duk da yaga
tarkon sa yakama kurciya bazai yi wasa da wannan damar tasa ba , amman dole sai ya jajurce
akan tarbiyar Sanam , dan kwata kwata bata da tarbiya me kyau gashi uwa uba yadda ya
fahimce ta bata da ilimin addini , a shirye yake ya tsaya tsayin daka ya gyara ta dan yasamu
nagartattun 'Yaya............
*Tofa su Huneed har anfara tunanin Yara tun ba ashawo kan Sarauniyar Rigima ba*
*Comment* plss
*'Yar Mutan Kanawa* _Ce
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala Writer's Association*
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
_Ina yiwa d'aukacin Masoyana barka da sallah , dafatan kowa yayi sallah lafiya Allah ya karb'i
ibadun mu , Allah ya mai mai ta mana Ameen_
*Mundawo hutu zamu d'ora Allah yabamu ikon rubuta dai dai wanda za'a amfana
dashi*
Chapter 17.
Sanam kuka take sosai tamkar wacce akace Mahaifanta sun mutu , a haka bacci yayi
gaba da ita mai cike da mafarki iri iri akan Huneed........
Hajiya Nafeesa ce rik'e da waya a hannu ta na neman number wata k'awar ta Hajiya Harira
, bugu d'aya Hajiya Harira ta d'aga wayar tana fad'in " Manya manya maganin k'anana k'anana ,
murmushi Hajiya Nafeesa tayi sannan tace " kune manya ai Hajiya Harira , kwata kwata ba'ajin
ki agari tamkar laya kin b'ace , Hajiya Harira tace " Abubuwa sunyi yawa wlh shiyasa kikajini
shuru , Hajiya Nafeesa tace " inason ganinki dan akwai wani aiki dana keso kimin , murmushi
Hajiya Harira tayi sannan tace " shu'uma kice neman da kikemin badan Allah bane kenan ?
dariya Hajiya Nafeesa tasa sannan tace " sai kinzo zamuyi magana kawai , nan sukayi sallama
da juna kowacce ta katse wayar ta .......
Washe gari..
Sanam jitayi tanason tahowa gida , kwata kwata bata da sukuni saboda tunanin Huneed ,
babu kalmar dake mata yawo sai kalmar *Ina da Mata har da yara biyu,* wato mata garesa
harda yara biyu ita kuma fa ? hawayen da ya cika idanunta tasa hannu ta goge , tabbas so
baisan waje ba taya zai kaita inda bata da mahalli , dan ko zata mutu babu aure bazata auri
namijin dake da mata ba , tayi nisa cikin tunani taji andafa kafad'ar ta , firgigit tayi takai duban
ta ga gefen ta Mumyn su Rauda ce tsaye tana k'are mata kallo , wani murmushi Sanam ta
k'ak'alo tana duban Mumyn , cikin harshen turanci Mumy ta tambayi Sanam meke damun ta
haka take tunani , nan Sanam ta karkace tace babu abinda ke damunta kawai tana son tafiya
gida ne , Mumyn Rauda ta zauna gefen Sanam tace mata " ko akwai abinda akayi mata
takeson tafiya ? Sanam ta gyad'a kai alamun a'a , kawai tanason ta tafi ne saboda Babu Rauda
zaman babu dad'i , Mumy Rauda tashiga lallab'ata akan tabari ta huta sosai sai ta koma k'asar
Nageria d'in , badan Sanam ta so ba ta hak'ura akan zata k'ara sati sannan ta tafi.......
Huneed tuni yafara bincike akan gidan su Sanam , dan yanason sanin waye Mahaifinta da
kuma asalin ta , cikin kwana biyu Huneed yasamu cikakken bayani akan wacece Sanam da
kuma Mahaifinta har ma da sanin ai nahin wacce ta haifeta.....
Sosai Huneed yaji K'aunar Mahaifiyar Sanam na yadda ta sadaukar da 'Yar ta ga kishiyar
ta , gashi yadda yasamu labari babu wanda ya b'ata Sanam face Daddyn ta da kuma kishiyar
Mumynta , nan ya k'udirta aransa sai ya gyara ta tamkar yadda Mumyn ta take .....
Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah ,
Sanam tuni an hallara a airpot d'in k'asar Turkey za'a taho gida , Mumyn Rauda da Rauda
da mijinta sune sukayi mata rakiya zuwa Airpot , suna rungume da juna ita da Rauda sai
hawaye suke har aka fara kiran sunayen fasinja , haka suka rabu suna kewar juna tare da
d'agawa juna hannu har Sanam tashige cikin jirgi.......
*Gida Nageria*
jirgin su Sanam ya sauka a garin Abuja , tuni Fahad yaje d'auko a airpot , tana saukowa
daga jirgi a hankali tamkar wacce batason saukowa , wani matashin saurayi shine ya matso daf
da ita suka jero tamkar tare daman suke tafiyar......
[9/27, 09:49] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
Chapter 18.
Dai dai da zasu sakko daga step din k'arshe na jirgin , Sanam ta zame tayi baya zata
fad'i , da sauri wannan guy d'in ya rik'ota ta fad'a jikin sa tamkar a shirin film , duk wanda ya
dubesu a lokacin sai yayi tunanin mata da miji ne suke tare , da sauri Sanam ta turesa tana
janye jikin ta kafin tayi saurin saukowa daga jirgin , mutanen data gani ne yasa ta jin kunya tare
da saurin nufar wajen ake parking din motoci.....
Tana k'ara sowa Fahad ya fito daga motar yana murmushi tare da nufota tamkar zai
rungume yana fad'in " oyoyo My Angel , ganin yana neman rungume ta yasa tayi saurin dakatar
dashi tana fad'in " thanks tayi saurin yi gefe tana bud'e bayan motar ta shige abin ta .....
Fahad sosai yaji babu dad'i akan abinda Sanam d'in tayi masa , murmushi yayi na
mugunta a zuciyar sa yace " zakizo hannu zaki gane baki da wayo sai na cire miki wannan jin
kan naki , nufar motar yayi zai shige a lokacin shikuma wannan saurayin ya k'araso , sallama
yayiwa Fahad yabashi hannu sukayi musabiha , bayan sun gaisa saurayin nan ya dubi Fahad
yace " dan Allah Yayan mu in babu damuwa zanyi magana da Babyn dake bayan motar , Fahad
ya k'are masa kallo yayi d'an mutmushi yace " bisimillah ka yi mata magana , nan yayi masa
godiya ya k'arasa jikin murfin motar inda Sanam din take , Fahad dariyar mugunta ya shiga yi
masa dan yasan halin Sanam bata son jira mutukar tadawo daga tafiya , koda ya k'arasa jikin
motar bubbuga glass yayi, Sanam tanajin sa kuma tana ganin sa amman ko motsi batayi ba
bare ta bud'e , wayar ta tashiga dubawa tana jin wani haushi na tsayawar da Fahad d'in yayi
bai shigo sun tafi ba , tsaki kawai tashiga yi dan batason b'ata lokaci ko kad'an , ganin Fahad
bashi da niyyar tahowa su tafi kuma shima mutumin nan bashida niyar tafiya yasa ta sauke
glass d'in motar , murmushi yayi yana duban ta kafin yace " kin kai kuma kin isa kiyi komai ,
kallo d'aya nayi miki nasan kin cika cikakkiyar mace wacce ta isa , ina neman Alfarma guda biyu
zuwa uku a wajen ki dafatan zan samu ? Sanam tunda yafara magana tanajin sa amman ko
kallon da batayi ba , cikin ranta tace " kaima ka isa a soka amman ko k'afar Huneed baka kama
ba , nan take taji tanason ganin Huneed da kuma son jin muryar sa , cikin ranta take fad'in "
nadamu da kai amman kwata kwata naga ko sau d'aya baka damu dani ba , Maganar saurayin
dayake tsaye a kanta itace tadawo da ita daga duniyar tunanin Huneed datakeyi , murmushi
tasamu kanta dayi sannan ta dubesa tace " bawan Allah kayi hak'uri sauri nake kazo kasameni
a gida muyi magana , Murmushin jin dad'i yayi sanna ya dubeta yace " nagode sosai kuma
zaki ganni in sha Allah , sunana Jaydeen A Ambasodor nasan kinsan Mahaifina a cikin garin
nan na Abuja ? sarai Sanam tasan waye Jaydeen kuma tasan waye mahaifinsa da irin kud'in
da yake dashi , amman sai cewa tayi " nifah bansan wani me irin wanna sunan ba ma , sosai
Jaydeen yaji rashin dad'in maganar da Sanam tayi , amman saboda yarinyar lokaci d'aya ta tafi
dashi , dan duk yawan duniyar da yayi bai tab'a karo da mace me k'irar Sanam ba , ga kyau ga
diri tamakar itace ta shirya kanta , maganar tace ta katseshi tace " dan Allah yiwa direban can
magana yazo mutafi , mamaki ne ya kama Jaydeen ganin yadda Fahad ya had'u amman take
ce masa direba , shi duk a tunanin sa ma Yayan tane , zuge glass tayi batare da tak'ara
magana ba , shima shigewa yayi yasanar da Fahad tare da tambayar sa inane gidan su , nan
Fahad yabashi address sukayi sallama kowa yashige ya tafi.......
Hajiya Nafeesa tuni sunje wajen wani boka ita da k'awar ta Hajiya Harira , duk ta sanar
dashi yadda takeso araba tsakanin Sanam da Abban ta , nan yabata magun guna kala kala
wanda zatayi amfani dashi ......
Tana dawowa tashiga kitchen da kanta tayi girki kala kala , tana murna yau Sanam zata
dawo taci wannan maganin shikenan Daddyn ta ya tsaneta , dan duk duniya bata da wacce ta
tsana a yanzu tamkar Sanam ......
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 19.
Tunda ga farko gate masu gadin gidan Alhaji Abba suka san 'yar lele tadawo , dan
yanayin yadda akeyin hon. Kad'ai zai tabbatar maka da isowar Sanam gida ......
Tunda tafito daga motar suke zubewa suna mata sannu da zuwa amman ba wanda ta
amsawa , hanyar k'ofar falon su tabi tana danna wayar ta , Tura k'ofar tayi wani k'amshi ya daki
hancin ta , lumshe ido tayi dan tana mutuk'ar k'aunar k'amshin turaren wutar , cikin ranta take
fad'in " Mumy akwai san k'amshi da tsafta shiyasa ko da yaushe intayi tafiya take missing d'in
komai na Mumyn nata , bata gama zancen zucin ta ba taji muryar Mumyn tana fad'in " oyoyo My
luvly dauther your welcome , da sauri Sanam ta fad'a jikin Hajiya Nafeesa tana fad'in " Miss u
my mumyna , ina dawowa naji k'amshin turarenki me dad'i , murmushi Hajiya Nafeesa tayi tana
wani rausayar da kai tace " wannan k'amshin ai na musamman ne , dan ke nasa *Zee MD* ta
had'amin turaren ta me k'amshi da kama gida da jiki da kuma kaya , nasan kina son had'in
turaren ta shiyasa na shirya takanas naje gidan ta harda na wanka da Humra na anso miki ,
murmushi Sanam tayi sannan tace " nagode Mumyna bari nashiga ciki nayi wanka sai na fito ,
da sauri ta nufi sama inda d'akin ta yake ......
Hancin motar Huneed ce ta shigo gate d'in gida su , saukar sa kenan daga taraba sunje
wani aiki , yana fitowa daga motar