Showing 42001 words to 45000 words out of 80926 words
*Bayan kwana biyu*
Tuni Soyayyar Huneed da Sanam tayi k'arfi sosai , koda yaushe suna mak'ale da juna a
waya suna shan luv , saboda Huneed Sanam taji bazata iya fita wata k'asar karatu ba , dan
haka ta zab'i tayi karatun ta a nan , Daddyn Sanam sai shirye shiryen tafiya yake zuwa Jamus ,
sosai yake jin dad'in had'uwar Tilon 'Yar tasa da Huneed , yagama yabawa da hankalinsa da
kuma irin yadda yake ja jurtacce , cikin satin da Alhaji Abba zai tafi Jamus Allah ya sauki Hajiya
Maimuna wato Mahaifiyar Sanam , ansamu Twins mace da Namiji cike da k'oshin lafiya ,
karkiso kiga Murna wajen Alhaji Abba tun A asibiti yake kiran wayar Sanam , sai dai kwata
kwata bata d'aga ba saboda lokacin tana tare da Huneed , itama Hajiya Nafeesa tana wanka
tabar wayar a palor k'asa shiyasa batasan yakira ba , ganin haka yasa Alhaji nufo gidan Bayan
an sallamesu daga asibitin yakawo su gida , yana shigowa gidan yasamu Huneed da Sanam a
farfajiyar gidan suna hirar su cike da nishad'i , tana ganin sa ta mik'e tana murnar ganin sa ,
shima baki bud'e ya nufosu yana murmushi tamkar wanda akayiwa Albishir da gidan Aljannah ,
kafin ya k'araso tuni Huneed shima ya mik'e ya nufesa yana rissinawa yana gaidashi , cike da
sakin fuska ya amsa yana tambayar sa 'yan gidan , Huneed yace " lafiya lau suke Daddy duk
suna gaidaka , ina amsawa sosai nima in ka koma ka gaidamin da Hajiyar taka , ..... Zataji
insha Allah inji Huneed...
Alhaji Abba ya dube su yace " Abin farin cikine yasameni tare daku baki d'aya , Sanam
tayi murmushi tace " ai tunda kataho nagane hakan Daddy meyasamu ? murmushi yayi sannan
yace Mumyn ki ce ta haifa miki k'anne Twins , Suna nan kamar su d'aya dake har sun so ma
sufiki kyau , Nan danan fuskar Sanam ta canza daga murmushi zuwa b'ata fuska , shikuwa
Huneed tuni ya saki murmushi yana fad'in " Masha Allah Allah yarayasu yayi musu albarka ,
Lallai munyi k'anne har naji d'okin nagansu , duban Sanam yayi yaga canzawar datayi lokaci
guda duk wata walwala ta tafi daga fuskar ta , Alhaji Abba inda sabo yasaba da halin Sanam
na rashin jituwar da batayi da Mahaifiyar tata , duk da tunfarko yana da laifi dan ko kad'an
bayaso ayiwa Sanam fad'a , duk rashin kunyar da zatayi wa Hajiya Maimuna baya tsawatar
mata , amman ya d'auka in taji anyi mata k'anne zatayi murna sai yaga sab'anin hakan , duban
ta yayi yace " My luv bazaki tayani murnar samun Yara ba kenan ? kin manta koda yaushe kina
fad'in yaushe za'a haifa miki k'anne wanda zaki dunga wasa dasu kina jin dad'i , amman yau
gashi nazo miki da albishir kinyi shuru ko murna bakyayi da hakan , Sanam ta turo baki tana
fad'in " Daddy nifa nafison ace Mumyna ce tanan gidan ta haifamin k'anne , ni kasan ba zuwa
nake gidan waccan Mumyn ba kaga baruwana da yaran data haifa , kuma Daddy har kafara
cewa sunfini kyau wato zaka koma Sonsu kenan nikuma kadaina sona , Alhaji Abba yayi
murmushi yana duban Sanam wato kishi zata fara dasu kenan , Huneed shima murmushi yayi
duk da cikin zuciyar sa yana tunanin meyasa Sanam kwata kwata batason Matar Daddyn nata ,
tabbas yana ganin tsantsar kiyayyar matar a idon ta duk da baisan me tayi mata ba , haka
Daddy yashige ciki yana fad'in " bari naje nayiwa Hajiya Nafeesa Albishir , ....
Koda Daddy yatafi Huneed ya dubi Sanam yace " Baby meyasa abin farin ciki yasamu
Daddy amman ke bazaki taya shi ba ? karki manta in ita mahaifiyar yaran ta kasance me laifi a
gunki to ai su yaran basuyi miki komai ba , asalima su basusan komai ba a yanzu sai
Mahaifiyar su , dan haka karki k'ullacesu a cikin zuciya kijasu ajikin ki tunda sud'in jininki ne
kuma 'Yan uwanki ne , inaso ki shirya gobe In Allah ya kaimu zaki rakani muje tare mugan su ,
Sanam duk jikin ta yayi sanyi game da maganganun da Huneed yayi mata , kuma ko kad'an
bata yi masa musu indai yace mata Abu , haka ta amsa masa da Allah ya kaimu suka ci gaba
da hirar su...
Lokacin da Alhaji Abba ya shigo palor dai dai lokacin Hajiya Nafeesa ke saukowa daga
sama , yana ganinta yasaki murmushi yana kallon ta , itama martanin murmushin ta maida
masa tare da kashe masa ido , tana k'arasowa tashige cikin jikin sa , shima rungumeta yayi
yana fad'in " d'awisu sarkin ado sannu da fitowa gimbiya ta , Hajiya Nafeesa takuma lafewa a
jikin sa tana fad'in " Alhajina kadawo lafiya ina kewarka sosai , Alhaji Abba yace " ai nayita kiran
Wayar ki keda Babyn ki baku d'aga ba , dama sonake inyi muku Albishir munsamu k'aruwa ,
tuni Hajiya Nafeesa gaban ta ya fad'i ta d'ago tana duban Alhaji Abba sannan tace " waye ya
haihu ? Alhaji Abba cike da murmushi yace " Hajiya Maimuna ce ta haifo mana Twins mace da
namiji , ai jitayi tamkar an soka mata wuk'a wani abu ya tsaya mata a k'irji yakasa wucewa , sai
a hankali ta saita kanta gudun karya gane sannan tace " Alhamdulillah kace munyi yara Masha
Allah , Allah yaraya su yayi musu Albarka , nan tashiga nuna masa murnar ta wacce a iya
bakice batakai zuci ba....
Alhaji Abba sosai yaji dad'in yadda Hajiya Nafeesa ta nuna farin cikinta , har addu'a yake
mata akan Allah yabata itama saboda kyan halinta , baisan nan cikin zuciyar ta cike take da
tsanar gudan jinin nasa ba , dayasan yadda takeji a yanzu da ya gaggauta tashi ya fita dan
tasamu tayi kuka ko abunda ya tsaya mata a zuciya zai wuce........ [9/27, 10:02] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATIN*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Raheem*
Chapter 29.
Sama Alhaji Abba ya haye yana fad'in " yaufa ciki na babu komai ataimako da
ruwan lipto kafin asamar min abinda zanci , Hajiya Nafeesa tabishi da harara amman a fili ta
furta " Angama Angon k'arni , murmushi Alhaji Abba yayi cikin zuciyar sa yana jin dad'in
sunan da takirashi dashi , ..... Hajiya Nafeesa tana shiga cikin kitchen tasa kuka mara sauti , yanzu ta k'ara tabbatar da
cewa Hajiya Maimuna tayi mata zarrah ta ko ina , dana sani tashiga yi na irin abubuwan datayi
a baya , dan danan Abubuwan dasu faru a baya suka shiga dawo mata cikin kwakwalwar
ta.......
*Wacece Hajiya Nafeesa*
Malam Umar shine asalin Mahaifin Hajiya Nafeesa , haifaffiyar garin Maiduguri ce asalin
Bare bari , Mahaifin ta Malam Umar Da Mahaifiyar ta Falmata , su Uku iyayen su suka Haifa
Tahir Nafeesa da Fahad , Mahaifin su bawani me k'arfi bane amman yana da wadatar zuci ,
Mahaifiyar su tana sana'ar ta ta hannu a cikin gida , da haka suke rufawa juna asiri suke zaune
lafiya , tun tasowar Nafeesa take da buri sosai , ko cikin k'awayen ta tana da nuna itad'in me aji
ce da kuma nuna itad'in yar wani ce , Ba laifi Nafeesa kyakkyawa ce sai dai Bak'a ce ita ko
kuma ince chocolate colour , tana da tsayi me tafe da dirin jiki shiyasa take rud'a maza sosai da
wannan surar ta ta , Nafeesa tana da son abin duniya shiyasa duk saurayin da yazo gunta in
taga babu mamora atare dashi take yagashi , hakan yasa duk samarinta suka kasance attajirai
masu kud'i sosai , sai dai duk cikin samarin nata ba wanda ke sonta da aure sai dai su shek'e
ayar su.....
Tuntana b'oye b'oye kar iyayen ta sugane har suka fahimci halin data ke dashi , Nan
Mahaifinta Malam Umar yayi ta fad'a yana cewa sai ta fito da miji yayi mata aure ko kuma ya
bata wanda yayi masa , akwai wani Alhaji da sukafi shek'ewar su tare , sosai takejin dad'in
Mu'amala dashi dan haka tasamesa da maganar itafa agida andame ta akan tayi aure , dan
haka kawai ya turo gidan su suyi aure tunda suna son juna , Alhaji Dauda yanason Nafeesa sai
dai shi ba soyayyar aure yake mata ba , Amman ko dan ya huta da ita dole ya aureta na wucin
gadi tun da tana sonsa , batare da b'ata lokaci ba yaturo akayi bikin su shida ita....
Bayan tarewar ta a gidan sa tagane Matan sa Uku Yayan sa goma sha takwas , haka ya
had'asu gida d'aya tashiga takurar gaske , dan kwata kwata matan sa basu da mutunci haka ma
'Yayan nasa , dan ma itama bata da mutuncin shiyasa suke shakkar ta kad'an.....
Tana shiga tasamu ciki Alhaji Dauda naganin haka yasa ta agaba akan saita zubar , shifa
bai aurota dan tayi ciki yanzu ba kawai yanaso su huta ne shida ita , Nafeesa tace itafa bazata
zubar da ciki har sai ta haifesa , nan Alhaji Dauda yafita sabgar ta ko kallo bata ishe shiba , a
hankali tagane duk matan gidan sune suke d'aukar nauyin yaran su wajen karatu da maka
mancin su , ganin haka yasa taje ta samu Alhajin Akan ta shirya aje a zubar da cikin , dan
itakam bazata iya wahala da yara ba haka kawai wanda azubar ta huta , haka kuwa akayi
Alhaji Dauda baki har kunne ya d'auketa sukaje aka zubar da cikin , tunda ga lokacin Alhaji
Dauda yashiga bawa Nafeesa kwayoyin hana d'aukar ciki , itama batare da damuwa ba ta
dunga d'ibgawa cikin ta dan son faran ta masa rai , ana haka ta wayi gari Mahaifar ta tasamu
matsala ko ciki bazata iya d'auka ba , anan kuma Alhaji Dauda ya fara tsiyacewa ko Abinci
ba'aci A gidan sa , tuni Nafeesa tashiga yi masa iskan ci kala kala har sai da yagaji yasaketa ,
yana sakin ta tadawo ruwa ta goge tamkar batayi aure ba taci gaba da iskancin ta , tun Malam
Umar nayi mata fad'an takuma wani auren har yagaji ya k'yaleta .....
Ana haka suka taho kawo Amarya Abuja wata k'awarta , Anan Allah ya had'ata da Alhaji
Abba ya nuna yana sonta , tuni ta amince duba da yanayin data gansa Alhajin burni ga kud'i ga
kuma Kyau , ya sheda mata yana Mata kuma shekarsu hud'u da aure amman bata haihuba ,
Sosai Nafeesa taji kishi akan matar tasa , dan tasan tabbas matar sa tana hutawa ina ma
bashida mata ita kad'ai zai aura , amman jin dad'in ta guda d'aya jin ance matar tasa bata tab'a
haihuwa ba , tana komawa Alhaji Abba yaje gar Maid neman auren ta , bawani jan lokaci aka
d'aura musu aure Amarya Nafeesa ta tare gidan mijinta dake Abuja.....
Bata dad'e da tarewa ba Allah yabawa Hajiya Maimuna ciki , kar kaso kaga murna wajen
Alhaji Abba , Hajiya Nafeesa tayi bak'in ciki sosai amman saboda kissa sai take nuna tamkar
tafi kowa murnar samun cikin , saboda wannan ciki da Hajiya Maimuna tasamu sai da Alhaji
Abba ya biyawa mutum arba'in Hajji , ciki harda iyayen Hajiya Nafeesa da ita kanta da kuma
Yayan ta Tahir , .....
Ciki na shiga wata tara Alhaji Abba yadaina zuwa ko'inah , kullum yana tare da Hajiya
Maimuna yana bata kulawa , wata ranar Alhamis ta tashi da nak'uda akayi asibiti da ita , cikin
sauk'i batare da tasha wuya sosai ba Allah yabata 'Yar ta kyakkyawa me kama da ita , 'Yan Uwa
da Abokan Arzik'i sosai suka tayasu murnar Samun K'aruwa , Hajiya Nafeesa cike da kissa
tashiga hidima kullum tana gidan Hajiya Maimuna tana rungume da Da Jaririya , kayan barka
akwati set goma ta had'awa Jaririya duk saboda iya kissa , sosai Alhaji Abba yaji dad'i na irin
yadda take nunawa gudan jinin sa Soyayya , itama Hajiya Maimuna sosai taji dad'in irin hidimar
da Hajiya Nafeesar keyi , Ranar suna yarinya taci Suna Hafsat sunan Mahaifiyar Alhaji Abba
suke kiran ta da Sanam , sun sha hidima sosai sannan kowa ya watse aka bar me jego da
Baby Sanam , tundaga nan Hajiya Nafeesa ta shiga yin Magiyar abata Sanam in antashi
Yayeta , lokacin da aka Yayeta Alhaji Abba da kansa yad'aukota batare da Hajiya Maimuna
tace kanzil ba , dan dama ita macece me hak'uri basawa ba fitar wa , tunda ganan rik'on
Sanam yadawo k'ark'ashin Hajiya Nafeesa , kuma tunda ganan tashiga horor da Sanam da tusa
mata ak'idar tsanar Mahaifiyar ta , ....
Wannan shine tarihin Hajiya Nafeesa a tak'aice ...... .......
*kuyi Manegi*✍
[9/27, 10:04] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 30.
Ajiyar Zuciya Hajiya Nafeesa tayi tare da yin wani murmushin mugunta , tabbas
Lokaci yayi da zata fara yak'i da Hajiya Maimuna , a haka ta gama had'a masa ruwan lipton d'in
ta fito daga kitchen ta nufi sama , karo taci da Sanam zata sakko itakuma , Hajiya Nafeesa
cike da kissa tace " Baby ashe munsamu k'aruwa Mumyn ki tacan gidan ta haihu , ya mutsa
fuska Sanam tayi sannan tace " nifa ba ruwana da haihuwar ta , gashi daga haihuwar ta har
Daddy yafara cewa wai yaran sunfini kyau , aikuwa Hajiya Nafeesa cikin zuciyar ta wani dad'i
taji ya ratsa ta , dan tasan Halin Sanam da son yara da kusan kullum sai tasa ta gaba da
tambayar yaushe zata haifo mata Baby , ko kuma ta dunga rigimar itama sai an haifo mata
k'anne tunda taje gidan su k'awayen ta taga suna da k'anne , a haka har ta girma tana k'ulaficin
ganin tana da k'anne , sai gashi k'annen sun samu amman bata murna da samun su , wani
dad'i Hajiya Nafeesa taji sannan ta dubi Sanam tace " kwantar da hankalin ki Babyna , kinsan
Daddyn ki da tsokana amman nasan ko rabinki bazasu kamo a kyau ba , wani murmushin jin
dad'i Sanam tayi sannan tace "shiyasa nake k'aunar ki Mumyna , nasan kece kad'ai bazaki juya
min baya ba , Daddy kuwa nasan yanzu batani yake ba ta sababbin Babys d'in sa yake , Hajiya
Nafeesa tace " Rabu dashi ai da tsohuwar zuma ake magani , kece dai tagaban goshi ko ank'i
ko anso , Sanam tayi murmushin jin dad'i tare juyawa zata sauka daga benen ...... Har ta kusa sauka Hajiya Nafeesa ta d'aga murya da cewa " yaushe zakije kiyi mata barka
tare da gano jariran ? Sanam ta juyo tana fad'in " Mumy nifa wallahi banson zuwa amman
Huneed yace dole na shirya gobe muje tare , wata fad'uwar gaba Hajiya Nafeesa taji dan ko
kad'an ita dai wannan Huneed d'in bai yi mata ba , tunda tafara ganin sa taji ta tsanesa gashi
kuma yadda ta fahimta