Showing 63001 words to 66000 words out of 80926 words

Chapter 22 - YAR KISHIYA Book Complete BY Zee MD.pdf

Zee MD   

10 Jul 2025

4192

Chapter 41.


Mumyn Twins na fita Sanam ta mik'e ta haye sama , tana shiga cikin d'akin taji wani
k'amshi ya daki hancin ta me saka nutsuwa , komai a gyare tsaf tamkar ba mai shiga cikin
d'akin , toilet ta shiga wanda yake agyare tsaf sai k'amshi yake fitarwa , had'a ruwan wanka tayi
tashiga tafarayi tana lumshe idanu ,
Acikin kashi d'ari na damuwar yanzu babu arba'in , tabbas ta yadda Uwa Uwa ce ita kad'ai
tana samarwa da 'Ya'yanta nutsuwa, kawai yanzu abinda ke damunta shine tunanin Huneed
wanda yakasa barin zuciyar ta ta huta , tabbas ko mafarki tayi akace mata Huneed zaici amanar
ta to tabbas zata k'arya ta wannan mafarkin , amman sai gashi a gaske abin yafaru wai Huneed
d'inta wanda take burin rayuwa dashi shine yake bin k'awarta harda rungumo ta jikinsa, runtse
idanu tayi tamkar yanzu take ganin hoton abun.....

Ta dad'e acikin ruwan wanka sannan tayi wankan tafito , kitchen d'in cikin d'akin tashiga dan
ta had'a ko ruwan lipton ne tasha, don batajin zata iya cin abinci acikin nan nata , tana
dubawa taga akwai ruwan tea a flast da kuma Samosa a jiye itama, d'aukowa tayi tafito ta
dawo d'akin ta zauna tafara ci......


Tuni Huneed ya sauka a garin Abuja ko gidan su bai nufa ba ya nufi gidan su Sanam,
yana zuwa me gadi ya sheda masa Sanam tafice bata gida, juyowa yayi gidan su Hajiyar sa na

Palor suna hira da me musu aiki Huneed yayi sallama, kallo d'aya Hajiya tayi masa tasan ba
lafiya ba , gaishe ta yayi sannan suka gaisa da meyi masu aiki, d'akinsa ya nufa batare daya
kuma magana ba ,

Hajiya mik'ewa tayi tabi bayansa dan tasan lallai ba lafiya bace tadawo da Huneed , aikuwa
tana shiga tasamesa ko takalmin k'afarsa bai cira ba 'ya kwanta akan gado yayi rubda ciki....

Hajiya tasamu waje gefen gadon ta zauna tayi gyaran murya kad'an , cikin nuna kulawa irin
ta mahaifiya tace " lokacin dawowar ka baiyiba kuma naga damuwa akan fuskar ka inason
insan meye yake damun Babban Soja , Huneed ya mik'e a Hankali ya zauna yana duban
Hajiyar tasa , tabbas bashida wanda yafita a duk duniya , kuma komai zaiyi saiya nemi
shawarar ta kuma kome yake damunsa itace tafarko a duniya dayake gayawa , nan take ya
sheda mata duk abinda yake faruwa tsakanin sa da Sanam tundaga kiran wayar k'awarta har
izuwa yanzu ,
Tamkar zaiyi kuka yace "Hajiyar mu yanzu haka Sanam bata d'agamin waya , wani lokacin ma
inna kira wayar kashewa take , shuru Hajiya tayi nawani lokacin sannan ta d'ago da kanta tana
duban Huneed , akwana biyu duk yarame ya canza tamkar bashi ba , tabbas tasan Huneed
yanason Sanam sosai , dan haka itama take k'aunar Yarinyar duk da bata tab'a ganin ta azahiri
ba sai a hoto , dafa kafad'ar shi tayi sannan tace " Tabbas wannan shiri ne aka shirya muku
kaida ita , duk wannan abun anyini dan arabaku kuma gashi wad'an da sukayi suna neman yin
nasara akan ku , abinda nakeso dakai a yanzu shine kabi komai a hankali zaka kamo bakin
zaren , kuma ka zama ja jurtacce kar kabawa mak'iyanku k'ofah da zasu samu nasarar rabaku
, yanzu katashi kayi wanka kazo palor kaci abinci sai kakoma gidan nasu ko tadawo yanzu ,
Huneed ya ya mutsa fuska yana cewa " bazan iya cin komai ba Hajiyar mu mutuk'ar ba Sanam
nagani ba , Murmushi Hajiya tayi sannan ta mik'e tana fad'in " lallai Sanam zankamata da laifin
horon mu da Yarona datayi , Soja guda yana neman zama sullutu , maza kayi wanka kasameni
a Palor inyaso ko zancen nema sai naraka ka , sosai Huneed yasamu saukin damuwarsa ,
dama duk wata damuwa yana zuwa da ita gaban Hajiyarsu take masa maganin ta , tabbas
shima ya yadda wannann shirine aka shirya musu shida Sanam dan A rabasu , amman tabbas
zaibi duddugi harya gano wanda yayi musu wannan shirin Sai ya d'an d'ana kud'arsa.....

Mik'ewa yayi yashiga toilet dan shima yanaso yaji sanyi ko yayane ajikinsa,.....


Sanam tana gama shan tea da samosa bacci yayi awon gaba sa ita,..

Mumyn Twins tunda taga jikin Hajiyar ta da sauki sosai take shirye shiryen tahowa gida ,
Hajiyar ta ta kalleta tace " wai Maimunatu naga sai sauri kike ki koma gida ko Alhaji Abba yau
zai dawo ne ? Mumyn Twins jitayi tanajin nauyin cewa Hajiyar ta Sanam ce tazo gidan takeso
takoma , Murja me kula dasu Twins ce tace " Auntyn su Twins ce tazo muka barota agidan
shiyasa , Hajiya ta yi murmushi tace "Sanam ce kenan tazo gidan naku shine kuma kota biyoku
taga jikinan nawa , Murmushi Mumyn Twins tayi sannan tace " da'alama ba zuwan dad'i tayi ba ,
dan yanayinta yanuna akwai abinda ke damunta , Hajiya ta nisa sannan tace " to maza kutashi

kutafi dan kije kiji meyake damunta , tunda har kikaga tataho gidan ki to tabbas tana buk'atar
kulawarki , Hajiya takuma nunawa 'Yar ta yadda zata janyo yarinyar ta jikinta har tadunga nuna
mata dai dai, hala sukayi wa Hajiya sallama suka kama hanyar dawowa gida....


Sai Bayan sallar Magriba sannan Huneed yakama hanyar zuwa gida su Sanam , kafin 'ya
fito sosai Hajiyar sa tayi masa nasiha tare da kuma k'arfa fa masa gwuiwa akan lallai 'ya jajirce
kar asamu nasarar rabasu , dan haka da k'arfin gwuiwar sa ya nufi gidan su Sanam,

Koda yaje megadi yakuma sheda masa har wannan lokacin bata dawo ba , sosai Huneed
yashiga mamakin inda Sanam taje haka har wannan lokacin ace bata dawo ba , yasan dai yau
babu sch bare ace lacca taje kuma ko shopping taje yaci ace tadawo yanzu , tsayawa yayi jikin
motar sa yana danna wayar sa , yafi minty 5 a tsaye ya hangi Fahad da Maryam sun nufo
gidan hannu cikin hannu suna wasan banza ,
Huneed kafesu yayi da idanuwan sa yana nazarin su tamkar yanaso yagano wani Abu atare
dasu , suna hangoshi suma sai da gabansu ya fad'i , dan yadda yake kallon su tamkar yagane
sune suka had'a musu wannan shirin ,
Take suka tsaya suna Diri dirin juyawa su koma , Maryam dabara ta fad'o mata tace " kar
mujuya yin hakan zai sa ayar tambaya akan mu , juyowa sukayi suka kama hanyar shiga gidan
, da sauri Huneed ya dakatar dasu dacewa " dan Allah kutsaya zanyi magana daku , jikin su
har rawa yake suka tsaya cak suna kallon sa , yana k'arasowa yabawa Fahad hannu suka
gaisa sannan yace " dan Allah Sanam ina taje ance bata nan ? Wata ajiyar zuciya suka saki
atare sannan Fahad yace " gaskiya bansan ina taje ba , sai dai koke Maryam kinsan inda taje
ne ? Maryam tace " tun wajen sha biyu tafice na rana kuma bansan ona taje ba , nan Huneed
yayi musu sallama yashige yahau motar sa yatafi.....


tunda Huneed yabaro k'ofar gidan su Sanam yasamu kansa da son zuwa gidan Mumyn
Twins , yanaso suyi magana itama da ita ko zai samu sassauci a zuciyar sa , hanyar gidan ya
nufa duk jikin sa a mace tare da tunanin inda Sanam take , gashi kwata kwata wayar ta bata
shiga inyakira ce masa akeyi akashe take , har test ya tura mata amman bashi da tabbacin ma
yaje tunda wayar akashe take......


Sanam bayan ta tashi daga bacci ta sauko k'asa tazauna tana kallo , bata dad'e da zama
ba su Mumyn Twins suka shigo cikin gidan , sosai Mumyn taji dad'in ganin damuwar fuska
Sanam ta ragu sosai , amsa musu sallamar tasu tayi tana musu sannu da zuwa , zama Mumy
tayi kusa da Sanam tana cewa " ya gidan dafatan kinci abinci , Sanam tana ansar Twins a
hannun Murja tana cewa Mummyn " naci amman yajikin Hajiyar dafatan dai da sauk'i ? Sosai
Mumyn taji dad'in yadda Sanam d'in ta tambayi jikin Hajiyar ta , cike da fara'a tace " jikin ta da
sauk'i sosai tace tana gaidake kuma yaushe zakije kugaisa ? Sanam tace " zanje insha Allah
inkwanar mata biyu , nan Mummy ta mik'e tana fad'in " bari nayi wanka nadawo sai muyi
magana , ta mik'e ta hau sama tabar su Sanam tana wasa da Twins abinta tamkar babu abinda

ke damunta.......
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
‍♀️‍♀️



*NA*
*Zee MD*



*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/





*Bisimillahir Rahamanir Rahim*




Chapter 42.


Mummy wanka tayi sannan ta tada sallar magriba , tana cikin yin addu'a taji wayar
ta nayin ring. Bayan ta shafa ta duba Dan ganin me kiran nata Huneed tagani , lokacin wani
Kiran yakuma shigowa ta d'aga tare da yin sallama , amsawa yayi cike da bata girma tamkar
tana ganin sa , gaisheta tare da tambayar ta twins , Nan tace lafiya lau suke tashiga tambayar
sa aikin da yakaisu katsina , Huneed yace"Mummy nifa nataho gida Dan yanzu haka ma ina
hanyar zuwa wajenki , Mummy bazan iya aikata komai ba mutuk'ar bana sanin halin da Sanam
ke ciki , nakira ta Amman kwata kwata bata d'agamin waya duk nadamu dayawa ,. Hajiya
Maimuna tayi murmushi sannan tace "haba Soja kana Captain guda kana wasa da aikin ka ,
yakamata kacire damuwar Sanam aranka katsaya kabawa k'asar mu tsaro , Huneed yace "
Mummy nidai ganinan zuwa sai muyi magana , Allah yakawo ka lafiya ta furta tare da kashe
wayar......

Saukowa tayi k'asa tasamu Sanam har lokacin tana wasa da twins, zama tayi tana duban
ta sannan tace " kinyi sallah kuwa ? Sanam tace " nayi tunkafin kushigo , Mummy ta gyara

zama sannan ta dubi Sanam tace " inason inji abinda yake damunki dan haryanzu hankalina ya
kasa kwanciya da yadda Naga yanayinki , Sanam tuni idanun ta suka Fara hawaye , batace
komai ba illah kunnawa Mummyn nata videon Huneed da Diyana datayi , tana kunna Mata ta
tashi da sauri ta hau sama jin kuka na niyar k'wace Mata......

A can b'angaren su Hajiya Nafeesa kuwa , duniya tayi musu sabuwa kowanne sai nishad'i
yake , Maryam ta kalli Hajiya Nafeesa tace " Aunty yakamata infara zuwa awo tunda cikin yayi
wata biyu , Hajiya Nafeesa tace " kibari nayi magana da likitana komai yace sai kifara zuwa ,
Maryam ba haka tasoba sotake kawai Hajiya Nafeesa tadunga bata kud'i tana fantamawar ta ,
bata rasa ci ba Bata rasa sha ba sai dai gaskiya Hajiya Nafeesa bata sakin kud'i shine babban
matsalar ta , suna zaune Kiran Alhaji Abba yashigo wayar Hajiya Nafeesa d'agawa tayi tana
wani murmushi , Alhaji Abba yace " uwar biyu yakike ya daren ? Hajiya Nafeesa tawani lumshe
ido tana shafa cikin tamkar me cikin gasken tace " habadai Alhajina guda d'aya ma ai ya isa
tunda Babbar Yaya tayi mana twins , murmushi Alhaji Abba yayi sannan yace " kikasani ko
kema ki haifo Mana Twins d'in , Kinga shikenan nahad'a garke babba , Murmushi Hajiya
Nafeesa tayi sannan tace " to Allah yakawo Mana masu albarka , da Ameen ya amsa sannan
yace " Ina shalelena take kwana biyu bamuyi waya ba saboda bana samun lokaci , kuma yau
nakirata Amman wayar ta akashe take ,. Hajiya Nafeesa ta tab'e baki tamkar Yana ganin ta tace
" Sanam Ni kaina yau kwana d'aya bansata a idanuwana ba , da sauri Alhaji Abba yace "
kwana d'aya kuma to Bata gidan ne ko Yaya ? Cike da k'osawa da maganar Sanam d'in dayake
Mata tace " kasan yanzu kullum sai sunfita yawo da wannan yaron Huneed , Dan nayi Mata
magana shine take fushi Dani , kuma bawanda ya lalata Sanam yanzu inba wannan yaron ba ,
kwata kwata batajin magana duk ta canza halinta ,. Alhaji Abba shiru yayi Yana nazarin
maganganun Hajiya Nafeesar ,. Amman meyasa Huneed zaiyi Masa haka ? Ya d'auki amanar
'yarsa yabashi saboda yaga tana k'aunar sa shine zai lalata Masa ita , A hankali Alhaji Abba
yace " idan Kinga tashigo cikin gidan ki kirani a waya ki had'ani da ita , Hajiya Nafeesa da sauri
tace " karka kuma had'ani da ita kasan in kayi Mata magana zata tsaneni sosai tunda tafara
yimin rashin kunya , kawai idan tashigo zance Mata takiraka kaga daganan sai kasan yadda
zaka b'illo Mata da maganar , sosai ran Alhaji Abba ya b'aci yakashe wayar batare da yakuma
cewa komai ba , ....

Hajiya Nafeesa tayi wani shu'umin murmushi najin dad'in nasarar data Fara samu , take ta
yanke shawarar bama sai ta kashe kud'inta a banza ba gurin malamai , kawai wannan kissar
zatayi batare da ta kashe kud'i ba cikin ruwan sanyi taraba Sanam da Mahaifin nata ,. ....


Mummyn Twins tana cikin kallon videon da Sanam ta kunna Mata taji sallamar Huneed ,
ajiye wayar tayi tana Masa lale da zuwa , ko a fuska bata canza Masa ba ko kuma ta nuna
Masa tasan abinda yake faruwa , Dan zuciyar ta bata gamsu da cewa Huneed zai aikata abinda
tagani ba , durk'usawa Huneed yayi Yana gaidata ta amsa cike da kulawa da sakin fuska ,
bayan sungama gaisawa ya zauna kan kujera Yana d'aukar abokin sa , wasa yashiga yi dasu
Nan Mummy tasa Murja ta had'o Masa abin motsa baki....

Bayan murja ta kawo masa tace Mata ta d'auki su Twins su hau sama gurin Auntyn su ,.
Kwata kwata Huneed bai kawo Sanam bace tunda baiyi tunanin tazo gidan ba ,
Bayan Murja ta bargun Huneed ya kalli Mummy yace "Mummy Dan Allah ki kiramin Sanam
wallahi ni inna kirata Bata amsamin waya ,. Mummy wallahi bazan iya komai ba mutuk'ar Banga
Sanam nasan laifin danayi Mata ba , Mummy tace " inaso ka kwantar da hankalinka indai
Sanam ce tana cikin gidan Nan , wata irin zabura Huneed yayi Yana mik'ewa tare da cewa "
Mummy Ina take plss inason ganin ta ,. Hajiya Maimuna tabbas ta yarda da irin son da Huneed
d'in keyiwa 'Yar ta , kuma batajin zai aikata abinda tagani , kallon sa tayi sannan tace inaso ka
nutsu ka zauna bara naje nataho da ita Dan inaso ku dukan ku naji abinda yake damunku dan
samun mafita , Huneed zama yayi yana maida numfashi tamkar wanda yayi gasar tsere ,
mik'ewa Mummy tayi ta nufi sama Dan tahowa da Sanam....

Sanam na kwance kan gadon Mummyn sai kuka takeyi , da sallama Mummy tashiga ta
zauna bakin gadon , a hankali ta furta " Sanam inaso kitashi kije ki wanko fuskar ki kisameni a
k'asa muyi magana , Bata k'ara magana ba tamik'e tabar cikin d'akin....

Bayan kamar minty 5 da dawowar Mummy sai ga Sanam ta sauko daga sama , kwata
kwata bata kula da Huneed ba saboda kanta na k'asa saboda kukan datasha , tunda ta taho
Huneed yake kallon ta saboda ganin yadda ta koma duk ta rame kana ganin ta kasan tana cikin
damuwa kamar yadda shima yake , .
Tana k'arasowa zata zauna idanun ta suka dira kan Huneed dake zaune ya zuba Mata
idanuwan sa , k'irjin tane ya buga take taji ranta ya b'aci tamkar ta juya ta koma Amman hakan
tasan bazai samu ba , d'auke kanta tayi daga kallon sa tasamu waje ta zauna tafara wasa da
yatsun hannun ta , Mummy tayi gyaran Murya sannan tace " Huneed gaka ga Sanam inaso
kufad'amin abinda ya had'aku ku dukan ku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login