Showing 21001 words to 24000 words out of 80926 words

Chapter 8 - YAR KISHIYA Book Complete BY Zee MD.pdf

Zee MD   

10 Jul 2025

4094

, Rauda tagani
tasaha kwalliya cikin shigar amare ba k'aramin kyau tayi ba , Rauda tace " ina kikaje Sanam
kwata kwata banganki a wajen Kamu ba , gashi in ankira wayar ki bakya d'agawa ina fatan dai
lafiya ? murmushi Sanam tayi sannan tace " bansan wajen ba, kuma na hau taxi muka gama
yawo bangane ba har aka fara ruwa , Rauda tace " amman Janifa ta gayamin cewa taga kin
shirya cikin shigar da sukayi , kuma lokacin ankawo motoci amman baki shiga kowacce ba ,
Sanam ta mik'e tace " kawai Allah baiyi zanzo ba amman gobe insha Allah bazanyi missing d'in
Lunch ba , tare suka jera suka shiga cikin gidan suna hira abinsu , koda suka shigo harabar
gidan Sanam tashiga dube dube kozata ga Asuk amman bata gansa ba , haka suka shige cikin
gidan wanda yake acike da mutane 'yan biki........

Sanam kwata kwata takasa rintsawa saboda tunanin Huneed , babu abinda ke mata yawo
a ido sai hoton kwanciyar datayi a jikin Huneed , lumshe idon ta tayi tana wani murmushi tana
k'ara rungume filon dake hannun ta , a hankali ta furta " wannan Guy d'in na musamman ne
yana burgeni , a haka barci yayi gaba da Sanam cike da tarin mafarkan Huneed.......

A b'angaren Huneed tunda yabar wajen Sanam ya taho sukayi waya da ogan su , nan aka
sheda masa kiran gaggawar da ake musu akan rikicin da 'yan ta'adda suke a garin sakkoto ,
Kwata kwata Huneed kiran bai masa dad'i ba kawai dai dan ba yadda zaiyi ne , amman kafin
yatafi ko sau d'ayane sai yakoma yaga Sanam dan yarinyar ta tsaya masa arai , kawai halayen
tane basuyi ba kwata kwata amman da sannu zai gyara ta .......


Washe gari.....

Tunda Sanam ta tashi taji tana k'aunar ta sake ganin Huneed , bayan ta karya tayi wanka
tashirya cikin wata doguwar riga me kyau daga cikin wad'an da ya siya mata , samun kanta tayi
da saka d'aya daga cikin Hijab d'in mahadin rigunan , ba k'aramin kyau tayi ba ita kanta sai sai
k'ara duba mirror take , tana fitowa su Rauda suna zaune suna shirya abubuwan da zasu yi
amfani dasu anjima , suna ganin ta suka tsaya suna kallon ta kowanne sai yaba kyan datayi
suke , Rauda tace " Sanam kowanne kaya kikasa sai kinyi kyau inama ace nice haka ,
murmushi tayi sannan tace " kema haka ai kike My R kowanne dresing kikayi sai yayi miki kyau
, Rauda tayi murmushi tace " ai nasan kinfini nesa ba kusa ba , wai ina ma zakije haka muna
shirye shirye kina ficewa ke kuma ? Sanam tace " sorry my R yanzu zandawo ba dad'ewa zanyi
ba , da sauri ta fice dan batason Ammi taji zata fita ta tsaida ta ma , tana fitowa harabar gidan
suka kuma karo da Asuk , tana ganinsa ta had'e ranta tana yin gefe da fuskar ta , shima
dayake yanajin haushin ta ko kallon ta bai kuma ba ya shige abinsa tamkar bai ganta ba .....

Taxi ta tsaida tagaya masa inda zai kaita , sai da ta shiga ta zauna sannan tafara zancen
zuci " to yanzu innaje mezan ce masa nazo yi ? wata zuciyar tace " kawai kice kin yarda abinki
ne shine kika dawo d'auka , tana wannan tunane tunanen nata har suka zo dai dai k'ofar Hotel
d'in , fitowa tayi sannan tabiya me taxi kud'in sa yayi gaba , ta dad'e a k'ofar wajen tana kaiwa
da komowa , da shawarar da zuciyar ta ta yanke nacewa wani abun ta yardar tashiga ciki......


Tunda gari ya waye Huneed ya had'a kayan sa cikin jakar sa , wajen goma na safe a can
k'asar ya fita yashiga gari zaiyiwa Hajiyar sa siyayya , daga can ya biya airpot yagama komai
jirgin su zai tashi k'arfe uku na rana , yana gama komai ya nufi gidan su Rauda ya tsaya daga
wajen daya saba tsayawa yana lek'en harabar gidan ko Allah zai sa Sanam ta fito , yafi minty
30 amman baiga kowa ba sai yara suna ta wasan su abinsu , ganin yana k'ara b'ata lokaci yasa
ya juya zai tafi , wata zuciyar tace " to inta fito mai zai ce mata ? kawai ya juya ya hau taxi
yakoma Hotel d'in , a lokacin Sanam na zaune a reception dan sun sheda mata me number da

ta tambaya ya fita , tana xaune ta had'a kai da gwiwa taji wani k'amshi ya doki hancin ta , tana
d'agowa taga wucewar Huneed batare da ya kula da ita ba , sai da tabari ya jima da wucewa
sanna ta nufi d'akin nasa......

Tana zuwa ta k'wank'wasa k'ofa daga ciki yace " yes coming , tura k'ofar tayi tashiga cikin
d'akin lokacin dagashi sai tawul zai shiga wanka , tana ganin da haka ta juya da baya zata
koma waje , da sauri yace " karki fita bati nashiga toilet wanka zanyi , da sauri ya fad'a cikin
toilet d'in yanajin wani farin ciki da ganinta dayayi , Sanam kuwa yadda tagansa ba k'aramin
tsoro taji ba , tunda take bata tab'a ganin jikin namiji haka ba sai yau , samun waje tayi ta
zauna tana tunanin meyake shirin faruwa da itane.......




*Comment* plss



*'Yar Mutan Kanawa* _Ce_ �
[9/27, 09:46] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
‍♀️‍♀️


*NA*
*Zee* *MD*



*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046

✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨


*Bisimillahir* *Rahamanir Rahim*



Chapter 15.


Bayan minty 7. saiga Huneed ya fito sanye da kayansa , har lokacin Sanam tana

duniyar tunani batasan ma ya fito ba sai da yayi mata gyaran murya , da sauri ta dawo daga
tunanin tana d'ago kai a hankali tana dubn sa , wani kyau yayi mata cikin k'anan nun kaya ,
Huneed yana da k'ira me kyau dayake jan hankalin 'Yan mata da ita , kana kallon da kaga
cikakken namiji jarumi wanda baya shayin komai , yana kama da wannan sabon jarumin na
indi'a Allu Arjun , sosai Sanam ta shagala a kallon sa tamkar wacce ta warke daga makanta ,
ganin ta kafeshi da idanu yasa yace mata " Hy 'yan mata wannan kallo haka kuma ? wata
kunya ce ta rufe Sanam tayi saurin yin k'asa da kanta , a hankali ya furta " ya kike ya gajiyar ki
ta dukan ruwa , ina fatan bakiyi zazzab'i ba dai ? Sanam tace " lafiya lau babu abinda nayi ,
kaima dafatan kadawo lafiya ? Huneed yace " yes nrml nake dan yanzu haka ma shirye shiryen
barin k'asar nake , wani abu Sanam taji ya tsaya mata a k'irji wanda ta shiga tambayar ko meye
oho , cikin zuciyar ta dai taji rashin dad'in maganar tasa dayayi , tambaya ta shiga yiwa kanta
meyasa dayace zai tafi taji rashin dad'i haka ? maganar sa ce ta katse ta da yace mata " ko
akwai wani abun da kike buk'ata ne ? da sauri Sanam ta girgiza kai alamar babu abinda takeso
, Huneed ya tab'e baki irin ko ajikinsa ya juya gaban mirror yana gyara kansa , ganin shuru
Sanam tak'i yin magana yasa ya juyo yace " Babbar direba ko dai akwai abinda kika manta ne
shine kika zo d'auka ? Sanam tace " Ae daman ina tunanin ko nabar d'an kunne na anan ne ,
Huneed yayi murmushi sannan yace " baki bar d'an kunne ba sai agogo nagani gashican , nuna
mata inda A gogon ta yake na gold. Sosai Sanam ta shiga mamakin halin Huneed , kwata
kwata ma ita ta manta da Agogon ta d'an kunnen ma ta fad'esa ne kawai , dan tasan bata bar
d'an kunne ba ashe tabar a gogo , Agogon ta yana da mutuk'ar tsada dan Daddyn tane ya siyo
mata shi a America , ba yadda Mumy Nafeesa batayi ba akan ya siyo mata irin sa amman yak'i ,
akan hakan har matsala suka samu da Daddyn lokacin , d'auko Agogon tayi ta saka a hannun
ta tana cewa " nagode sosai bari nazo natafi Allah ya sauke ka lafiya , Huneed yace " Ameen
nagode da addu'a , amman ke sai yaushe zaki koma gida ne ? Sanam tana saka takalmi tana
fad'in " bazan dad'e ba nima zantaho , da kallo Huneed yabi yatsun k'afar ta ta wanda yayi
bala'in had'uwa cikin takalmin filet , a hankali ya furta " komai naki yayu yadda akeso , halinki ne
kawai mara kyau duk da naga kin fara rage wani Abun........

Har Sanam ta bud'e k'ofa zata fita Huneed yace " inaso ki kula da kanki har kidawo gida ,
sannan karki k'ara yin direbin a cikin wannan k'asar saboda nan ba Nageria bace , Banda saka
k'ananun kaya plss ki kula sosai kinji k'anwata , Sanam wani dad'i takeji mutuk'ar Huneed nayin
magana , musamman maganar sa ta k'arshe da yakira ta da sunan k'anwar sa , a hankali tace
" zan kiyaye insha Allah , amman inason card d'inka saboda wani lokacin , murmushi Huneed
yayi sannan yace " ni da ba ma'aikaci ba me yahad'ani da card , kawo phone d'inki insa miki
number ta sai mudunga gaisawa tunda yanzu munzama abokai mundaina fad'a ko ? murmushi
Sanam tayi tana d'aga kai alamar Ae , mik'a masa wayar tayi yasa mata number sa ta Nageria
sannan ya bata wayar ta ta , tana ansa ta dube sa tace " Allah ya sauke ka lafiya ta juya ta fita
bata jira cewar saba , har ta fice daga d'akin kwata kwata ya kasa motsi , wata k'aunar ta ce ta
shige sa lokaci d'aya , sai sannan ya kuma jin dadin yadda ta fara canza halayen ta , wani dad'i
yaji ya kamashi ganin yadda tasa doguwar rigar daya ce ta dunga sawa , haka ya gama shiri
cikin farin ciki tare da kewar Sanam d'in , sosai yakejin k'aunar ta na ratsa cikin duk wasu k'ofofi
na jikin sa .........

Sanam na fitowa ta sauko k'asa tasamu waje guda ta zauna , kuka ta shiga yi tana share
hawayen da ke zubo wa akan kuncin ta , cikin zuciyar ta take fad'in " meyasa nakejin wani iri a
game da kai ? tabbas najin tamkar inbishi mutafi iya jiya kawai nakejin wani abu game dashi ,
wata zuciyar ta ta kuma tace " Son shi kike Sanam wannan shine So , da sauri tace " a'a ba
soyayya bace kawai kulawar da yayi danine lokacin da Asuk yaso ketamin haddi , ta dad'e
tana sak'e sak'e akan Huneed sannan ta mik'e tafita daga cikin Hotel d'in .......


Huneed tuni ya janyo trolly d'insa yafito daga Hotel d'in , yana tafe yana murmushi shi
kad'ai wanda yakejin wani shauk'i , Sanam har lokacin ta kasa barin k'ofar Hotel d'in saboda
son tasake ganin Huneed , tana hangoshi tayi saurin lab'ewa bayan wata bishiya tana lek'oshi ,
wani kyau taga ya kuma yi mata ga glass daya sa tamkar ba indiye , Taxi ya tsaida ya hau suka
tafi sannan Sanam ta fito daga wajen data b'uya , da kallo tabi bayan motar har ta k'ulewa ganin
ta sannan itama ta tsaida Taxi tayi gidan su Rauda........


*Hmm wallahi nagaji da rashin Comment dinku*
[9/27, 09:47] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
‍♀️‍♀️


*NA*
*Zee* *MD*



*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046

✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨


*Bisimillahir Rahamanir Rahim*




Chapter 16.

Har aka gama shagalin bikin Rauda Sanam bata cikin sukuni , tunda Huneed yatafi
tamkar yatafi da duk kan wani sukuni nata , gashi shuru sai jiran kiran wayar sa take amman

bai kira taba , haka suka kai Rauda gidan ta sosai anyi shagali tamkar baza adaina ba , haka
aka mik'a Amarya gidan ta kowa ya kama gabansa...

Sanam tuni tunanin Huneed yafara damunta , tuni tabi shafin sa na Face book tana neman
number sa , akuwa tayi sa'a tasamu ranar murna sosai tamkar tayi tsalle , kiran wayar tasa
tashiga yi har ta katse bai d'aga ba , haka ta kuma bin number tasake kira amman yanzu ma
baid'aga ba , sai da tayi kira biyar ba a d'agawa har tagaji ta ajiye wayar tana jin babu dad'i ,
ring din wayar ne yasa da sauri ta d'auki wayar tana tunani ko shine ya biyo ta , number Hajiya
Nafeesa tagani wanda tasa Mummyna , d'an guntun tsaki taja sannan ta d'aga wayar tana fad'in
" Mummyna barka da wannan lokaci , Hajiya Nafeesa cike da kissa irin ta ta ta manyan mata
tace " Barka kadai My Luv yakike ya Turkey ? Sanam tace " lafiya lau Mummy ya gida ya kowa
da kowa ? lafiya lau Luv kunsha biki nasan kin gaji sosai amman yaushe zaki dawo? Sanam
tace " ban fara shirin taho ba amman inaso intaho gida dan ina da abubuwan da zanyi , Hajiya
Nafeesa cikin ranta tace " nima nafiso kiyi kidawo dan insamu infara gabatar da aikina , a fili
kuma tace " yaka mata kidawo dan ina missing d'inki sosai , gashi Fahad ma kullum cikin zance
ki yake wai gidan babu dad'i tunda bakyanan , Sanam ta tab'e baki tamkar tana ganin Fahad
d'in tace " ina nan tafe Mummyna kice ina gaida Uncle d'in , daga nan tace " Byee Mum zan fita
yanzu sai nadawo mayi waya , kafin Hajiya Nafeesa tace wani abu tuni Sanam ta kashe wayar
.....


Tunda Huneed yadawo Nageria aiki yasa shi gaba , dan yana dawowa aka turasu Zamfara
dan maganin ' Yan ta'addar dasuka dami garin , tunda yatafi baya samun wani lokaci gashi
wajen babu network bare yayi waya , kullum zuciyar sa tana tunanin Sanam dan yasan dole
zatai ta zaman jiran kiran sa , wata zuciyar tace masa " wannan mara kirkin ai farin ciki zatayi
da baro k'asar dakayi , wata zuciyar tace " aikuma alamun ta kamar tadaina komai datakeyi ,
haka yashiga tunani akan Sanam yana lissafo kyan dirinta da kuma uwa uba kyan fuskar ta baki
d'aya .....

Ranar da suka dawo gida da nasarar da suka samu a zamfara , ranar Sanam tayi masa
wanna kiran ya shigo sai dai yana kallo yak'i d'agawa , dan basosai yake d'aga kiran number da
baisani ba , duk da yaga number ba ta k'asar bace amman kwata kwata bai kawo Sanam ce ke
kiran saba ,

Acan b'angaren Sanam kuwa tunda ta fice yawo bata dawo ba sai dare , koda ta dawo
wanka tayi tasa kayan bacci ta kwanta abinta , dan kwata kwata Sanam bata damu da ibada ba
, karatun addinin ma ba damunta yayi ba bare , dan haka tana kwanta tawa ta d'auko wayar ta
tafara chat da k'awayen ta , sai ta duba number Huneed taga yana kan online , da sauri tafara
murna tana shirin yi masa magana , wata zuciyar tace mata " kina mace me Daraja da Aji
amman kiyi masa magana , inajin ma yana ganin kiranki d'azu amman yak'i d'agawa , sannan ai
tunda yana da number ki yakamata ace ko sau d'ayane ya kiraki kun gaisa , haka Sanam tabi
shawarar zuciyar ta ta fasa yiwa Huneed magana , hirar su suka ci gaba dayi ita da Diyana

tana ta basu labari akan k'awayen su na Nageria , sai wajen k'arfe d'aya sannan Sanam ta
sauka daga online tayi kwanciyar ta , sai dai me ? tana kwanciya hoton Huneed yafara yi mata
yawo a idanun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login