Showing 9001 words to 12000 words out of 80926 words

Chapter 4 - YAR KISHIYA Book Complete BY Zee MD.pdf

Zee MD   

10 Jul 2025

4091

abin
bayarwa , Zahra zatayi magana Najeeb yace " sorry Baby ba girmanki bane , kishare kawai
karki biyewa 'yar yaga riga , wani mugun kallo Sanam tayi masa sannan tace " waye 'Yar yaga
rigar ? Najeeb yace " wacce take take miki baya mana , Sanam tace " ka gyara lafazinka
tunkafin mu kunyata ka a gaban budurwar taka , tana gama fad'ar haka tashige cikin motar suka
bata wuta sannan suka fice daga cikin gidan.......



*Zantafi yajin aiki tunda ba'ayin Comment*
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
‍♀️‍♀️


*NA*
*Zee* *MD*


*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046

✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨


*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*



_Nagode sosai Mutanena da tarin addu'oinku , Allah yabar k'auna_



Chapter 7.


Bayan kwana biyu Sanam kwata kwata bata canza ba , gudu a motar sai
abunda yayi gaba dan so uku tana jiwa mutane ciwo , Duk abinda takeyi Huneed nasane da
ita kawai jira yakeyi yagama abinda yakeyi yadawo , dan ya fuskanci lallai saiya koya mata
hankali sannan za'asamu sauk'in ta .......
Yau Alhaji Abba na gidan Hajiya Nafeesa suna zaune suna hira sai ga Sanam , tana

shigowa ta dubesu tace " Hi Daddy Hi Mumy , Alhaji Abba yace " Hy my luv your wel come ,
K'arasowa tayi tana taunar cingum ta zauna sannan ta dubi Daddyn nata tace " Daddy inason
zuwa Turkey za'ayi bikin wata k'awata da mukayi karatu tare kuma acan suke , murmushi Alhaji
Abba yayi sannan yace " bakomai My luv zantura miki kud'i ta Account d'inki saikiyi yadda
kikeso , wani tsalle Sanam tayi tana rungume Daddyn nata sannan tace " thanks my
sweetheart Allah yakare mana kai , Ameen my luv Allah yayi miki albarka , Da sauri Sanam ta
mik'e tayi sama tana murna , dan kwata kwata bata zata Daddyn ta zai barta taje Turkey
ba........

Hajiya Nafeesa wani kishine ya turnik'e ta ko magana ta kasayi , cikin ranta take fad'in "
wannan farin cikin naku da kukeyi duk lokacin da kuka kasance da juna kun kusa dainashi , dan
saina saka muguwar k'iyayya a tsakanin ku ta yadda in d'aya yaga d'aya sai yabar guri , Alhaji
Abba ne ya katse ta da cewa " lafiya kuwa Matar kirki ? murmushi Hajiya Nafeesa tayi sannan
tace " jinayi banason Sanam tayi tafiyar nan , dan kasan banajin dad'in na wayi gari bansata a
idanuna ba , wani dad'i Alhaji Abba yaji murmushi yayi yana janyo Hajiya Nafeesa cikin jikinsa
sannan yace " kiyi hak'uri kibarta taje ai nasan baza ta dad'e ba zata dawo , wannan soyayyar
da kike nunawa My luv itace tasa nake k'ara sonki , ina Alfahari dasamunki a matsayin mata ,
kin d'auki Sanam tamkar kece kika haifeta kin nuna mata gata da soyayya wacce ko wacce ta
haifeta batayi mata ita , nagode sosai matar Kirki kema Allah ya nuna min randa zanga d'anki
a duniya , Hajiya Nafeesa cike da kissa tace " inbanso Jininka ba Alhaji wazanso ? Sanam
kuma 'Yace a guna na raineta tuntana tsumma inbanso ta ba wazan so , inajin kewar ranar da
zatazo wacce Sanam zatayi min nisa , Alhaji Abba yace " ai babu wanna ranar da My luv satayi
miki nisa , Hajiya Nafeesa tace " Akwai mana Alhaji ko kamanta da ranar aurenta , kasan nan
gaba kad'an gidan wani zataje dole zamu rabu , Alhaji Abba yace " duk wanda zai kasance miji
a wajen Sanam tabbas zai kasance a k'arkashina yake , dan nafison ta auri wanda zandunga
bashi umarni yana bi wanda yarinya ta zatayi yadda takeso , wani murmushi Hajiya Nafeesa
tayi cikin ranta tace " lokaci yafara , zansa Fahad yashigo rayuwar Sanam yadda zamu tafiyar
da komai a dai dai , a fili kuwa tace " Allah dai yabata miji nagari wanda zai dunga yi mata duk
abinda takeso , Alhaji Abba yace Ameen......

Huneed yau ya dira garin Abuja da tarin Nasarorin da suka samu , sosai Hajiyar sa tayi
murna da ganinsa ita da Hisham , wanka kawai yayi yaci abinci yafito daga gidan , dan yanaso
yau sai Sanam tashiga tai tayinta , bai mi minty 15 da zama ba saiga motar ta nan ta taho da
mugun gudu , aikuwa shima ya shiga cikin tasa ya take mata baya , kwata kwata Sanam bata
kula dashi ba dan cikin murna take sosai sai faman jin kid'a take abinta , sai da yabari tashiga
wani layi mara yalwar Jama'a yayi sauri yasha gabanta , wani wawan birki taja har tana bige
bakinta a jikin sitiyari , cike da masifa ta fito tana fad'in " wanne mahaukaci ne wannan d'in
haka ? motar Huneed ta nufo sai zage zage takeyi tana fad'in " banza talakan wofi kawai , taya
zaka zo kasa mutane su kusa jin ciwo taja wani tsaki mtsss, Huneed tuni yasa bak'in glass ya
rufe k'wayar idanunsa , sannan yasa face mark ya rufe bakinsa da hancinsa , tuni ya bud'e
murfin motar ya fito , baiyi wata wata ba yajanyota ya wurga ta cikin motar tare da zagaya wa
ya shige wajen tuk'i ya figi motar da mugun gudu , tuni yayi waya da Hisham akan yazo ya
d'auke motar Sanam d'in ya maida mata da ita gidan su.......

Ihu Sanam take tana nan agaji tare da k'ok'arin bud'e motar ta fice , sai dai ko 'inah a rufe
yake gam takasa bud'e komai , shikuwa ko kallonta baiyi ba kawai gudu yakeyi sosai tamkar
zasu tashi sama ........



*Kuyi maneji*



*'Yar Mutan Kanawa* _Ce_ �
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
‍♀️‍♀️


*NA*
*Zee* *MD*


*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046

✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨


*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*



Chapter 8.


Dai dai k'ofar wani gida Huneed ya tsayar da motar sa , fitowa yayi daga ciki yana
huci tamkar zaki , zaga yawa yayi b'an garen da Sanam take ya bud'e ta , janyo ta yayi waje da
k'arfin tsiya tamkar zai b'alla ta , k'ofar gidan ya nufa rik'e da hannun ta , yana zuwa ya saka
mukulli ya bud'e gidan yashiga da ita , sosai Sanam ke ihu amman babu mejin ta saboda
unguwar babu gidaje.......

Huneed maida k'ofar yayi ya rufe kuma har lokacin yana rik'e da hannun Sanam , sai da ya
tura wata k'ofar falor sannan ya tura ta ciki ya janyo k'ofar , Sanam ihu tasaka tana fad'in "
menayi maka ne bawan Allah ? plss dan Allah kazo kafitar dani kabarni natafi gida , Huneed

yana jinta ya fito daga gidan yana huci , cikin motar ya koma ya zauna ya fara tunanin yadda zai
hora Sanam ,......

Hisham tunda Huneed yamasa waya akan yazo ya d'auki motar Sanam , yana zuwa daya
d'auketa gidan su ya nufa yaje ya ajiyeta wajen parking space , yana fitowa ya shiga cikin gida
abinsa yana dariyar koya hankalin da Hauneed zai wa Sanam d'in ......

Diyana ce tashiga kiran wayar Sanam , lokacin Huneed yayi nisa a tunanin yadda zai fara
horata yaji ring d'in waya , dubawa yayi yaga ansa My D katse wayar yayi sannan ya kashe ta
gaba d'aya yayi jifa da ita bayan motar , fitowa yayi daga cikin motar yana nufar cikin gidan......
Yana shiga gidan ya bud'e k'ofar falon yashiga , lokacin ya cire face mark d'in sa da kuma
glass d'in , Sanam ta zauna a k'asan cafet ta had'e kanta da gwiwa lokacin tana shan kukan ta
, a lokacin taji shigowar sa da sauri ta d'ago kanta , aikuwa ido biyu tayi da Huneed ya had'e
girar sama da k'asa yana tsaye yana kallon ta , da sauri ta mik'e tana dubansa kafin ta fara
magana " me na tare maka a cikin rayuwa daka takura min haka ? menayi maka kake shiga
cikin Rayuwa ta , kuka ne ya k'wace mata tana yi tana fad'in " wallahi bazan tab'a k'yaleka ba
azzalumi kawai , wata tsawa Huneed ya daka mata wacce tasa Sanam yin shuru jikinta har
rawa yake , Huneed ya k'araso gaban ta yace " keda kike mara kunya wacce bata san darajar
mutane ba , sau nawa ina fad'a miki kigyara halinki amman kika yi min kunnar uwar shegu ?
saboda kin samu sake har taka mutane kikeyi batare da and'au mataki akan ki ba , to kisani
nine zan d'auki mataki yau akanki dan saina gyaraki tunda iyayenki sun kasa baki tarbiya , wani
tsaki yaja tare da dubanta yace " Komai kikeyi aganinki dai dai ne ko ? shuru tayi batare da
tabashi amsa ba , tsawa ya daka mata sannan yace " ina tambayarki kinyi min shuru wallahi
yanzu jikinki zai gaya miki , kuka take k'asa k'asa yaci gaba da fad'in " meyasa bakyajin magana
? nan ma shuru Sanam tayi ba tare da ta Bashi amsa ba , fusata yayi yayi kanta ya d'agota da
gashin kanta da ya baje a bayanta , wata k'ara ta saki tare da sakin fitsari .......



*Dan Allah kuyi hak'uri an hanani kallon hasken waya zuwa lokacin da zanji sauk'i sosai*
[9/27, 09:40] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
‍♀️‍♀️



*NA*
*Zee* *MD*



*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046

✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨


*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*



Chapter 9.


Huneed ko ajikin sa yace " za kiyi magana ko ba zakiyi ba ? da sauri Sanam tace "
zanyi wallahi zanyi , sakin ta yayi sannan yace " to ina jinki meyasa ba kyajin magana kuma
Alhalin ke ba yarin ya bace ? Sanam tana kuka tana fad'in " kayi hak'uri duk abinda kake so
nayi wallahi zanyi , dan Allah ka maidani gida plss , Huneed ya kalle ta fuskar ta jage jage da
hawaye tamkar ba itace Sanam 'Yar gayun nan ba , jiyayi dariya na neman kamashi amman sai
ya maze yace " daga yau inaso inga shedar kin fara jin magana ta , a ko yaushe ki kasan ce
kina jan Motar cikin Nutsuwa , sannan ki girma ma duk wanda yakasan ce ya girmeki , sannan
inaso ki daina irin wannan shigar mutuk'ar zaki fito yawan ki na gari , kuma inaso duk wad'an
da kika buge su da Motar kije kine mesu ki basu hak'uri , nabaki nan da kwana biyu zanga in
kinji magana ta , sosai Sanam take kuka har Huneed yaga ma magan ganunsa , jiyawa yayi ya
kwaso mata wasu uniform d'in sa na Sojoji yace ta shiga toilet maza ta wanke masa sannan
tazo ya maida ta gida , Sanam ba musu ta anshi kayan ta nufi cikin toilet tana share hawayen ta
, tunda take a duniya bata tab'a wanki ba ko sau d'aya , komai sai dai tasa ayi mata amman
yanzu lokaci d'aya ace wani yasa ta wanki , tana shiga toilet d'in tasa ka wani kukan tare da
zuba kayan a cikin wani bawool na wanki , saka kayan tayi a gaba tana kallo tare da tunanin
taya zata fara , gashi intace masa bata iya ba nan ma zaiyi mata wani rashin mituncinne ,
sabulu tagani a gefe a ajiye nan ta d'auka tafara wankin tana kuka.......

Tuni Hajiya Nafeesa ta kira K'anin ta a waya wato Fahad , suna waye take sheda masa duk
abinda yake yabaro k'asar Cameroon yadawo gidan ta , tanaso tasaka shi aiki akan Sanam ,
tuni Fahad yafara shirin tahowa dan dama babu abinda yake sai bin mata kamar bunsuru ,
kud'i ta tura masa ya hawo jirgi ya sauka a garin Abuja......
Yana isowa ta tareshi da murna tare da nuna masa masaukin da zai dunga kwana , bayan
Fahad yayi wanka ya shirya ya fito dan cin abinci , Hajiya Nafeesa tana zaune ta kame tasha
wanka da kwalliya tamkar zataje gidan biki , zama Fahad yayi yana duban ta yace " gaskiya
Aunty kin samu duniya sosai , dubi yadda kika koma tamkar wata shuwa arab , murmushi
Hajiya Nafeesa tayi sannan ta dubesa tace " zaka fara rashin mutuncin naka ko ? yanzu dai
kaci abinci sai muyi magana , Fahad yace " inacin abinci kina gayamin abinda duk kiso ayi miki
, Hajiya Nafeesa ta gyara zama tace " inaso ka bud'e kunnen ka kaji sosai , kasan dai duk
duniya banida kamarka ko ? to inaso kasan cewa duk wannan daular danake ciki da zarar Alhaji
Abba ya rasu bani da wani kaso me yawa aciki , kasan ba haihuwa nayi dashi ba dan ni likita

ya tabbatar min da bazan haihuba saboda yawan zubar da cikin dana ringa yi ina budurwa ,
duk wannan dukiyar ta Alhaji a yanzu inya mutu duk rabinta ta zama ta Sanam , sai kuma uwar
ta wacce take da wani cikin a yanzu , kaga ni zan tashi a tutar babu kenan , abinda yasa na
kira ka dan ka tainaka min nima insamu kaso na me tsoka acikin dukiyar Alhaji , gashi tun
yanzu babu abinda nake k'aruwa dashi , wannan shegiyar 'Yar tasa itace komai akan dukiyar
yanzu , komai na dukiyar sa sunan tane ajiki kuma duk abinda takeso to tabbas sai ya mallaka
mata shi duk tsadar sa , inaso kashiga jikinta ka k'ullah soyayya da ita yadda zaka dunga kwaso
mana rabon mu , ta wannan hanyar kawai zamu samu kud'i yadda mukeso , wani murmushi
Fahad yayi sannan yace " ina yinki Auntyna tabbas kin yi kyan kai , nikuma bazan baki kunya
ba duk yadda zanyi nashiga rayuwar Sanam sai nayi , daman ina masifar sha'awar yarinyar ,
dan naga tana da Albarkatun ruwa atare da ita , wata harara Hajiya Nafeesa ta watsa masa
tana fad'in " kana nan da halin naka kenan ? sosa k'eya yayi yana fad'in " to mezan fasa Aunty
ai mata duniya ce dole sai dasu rayuwar zata tafi.......

Sanam sosai tasha wuya a wajen wankin sannan ta fito tace ta gama , duban ta Huneed
yayi sannan ya kauda kai yana fad'in " kishiga kiyi wanka sai nazo na maidaki dan bazaki shigar
min motar a haka ba , wani takaici ne ya kuma kama Sanam batare da tace komai ba ta juya
cikin toilet d'in.....

Tana fitowa tasame sa a tsaye yace " taho mu wuce , yana fad'in haka ya juya ya fita daga
cikin falor , binsa tayi a baya har ta fito daga gidan tasame sa a k'ofar gidan yana tsaye jikin
motar , tana zuwa ta bud'e baya zata shiga Huneed yace " ni direban ki ne da zaki zauna min
abayan motar ? maza ki dawo gaba ko ranki ya b'aci , da sauri Sanam ta dawo gidan gaba ta
zauna shikuma ya zagaya yaja su suka tafi....

tunda suka fara tafiya yake waya yana musayar kalmomin soyayya shida budur warsa ,
wani ta kaici ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login