Showing 51001 words to 54000 words out of 80926 words
" nace inzakije
gidan Mumyn Twins kifad'an amman naji ki shuru , Sanam tace " bantashi zuwa bare in fad'a
mikin amman kijira sai randa zani zan miki magana , tana kaiwa nan ta katse wayar tayi jifa da
ita tana me fad'awa kan gadon ta .......
Da Alhaji Abba cewa yayi dole sai dai Hajiya Nafeesa ta shirya su tafi tare saboda ya
dunga kulawa da ita , amman sam tak'i yarda ta lallab'ashi aka ai nan da wata biyu zata ware
taji sauk'i , sannan ta k'ara da cewa zata kira waya can Gidan su a turo mata wata k'anwar ta ,
da haka ya barta tare da cewa ba lallai yayi wad'an nan watannin ba , nan yatafi yana kewar
iyalin sa su duka suma suna kewar sa , musamman Sanam wacce itace ta rakashi air pot har
kuka tayi lokacin da jirgin nasu zai tashi ....
Bayan kwana biyu tuni Sanam tafara zuwa Universaty ta abuja dan kammala digree d'in ta
, duk kwana uku kuma Malamin Islamiyya nazuwa yana koya mata karatun alkur'ani , sosai
tana maida hankalin ta a karatun duka , lokacin Huneed yayi tafiya zuwa Lagos wani aiki , sai
dai ko yaushe suna manne da junan su a waya tamkar su janyo junan su , ......
Tuni Hajiya Nafeesa ta ware tadawo yadda take abinta , Maryam ma tuni ta dawo gidan
da zama dan haka jin kanta da k'aryar ta sai suka k'aru , tana so ta shigewa Sanam amman ko
kad'an ba fuskar daza ta tunkare ta , Koda Sanam taga Maryam a gidan sai Hajiya Nafeesa ta
shara mata k'aryar wai 'yar gidan k'anin Mahaifin ta ce , Sanam da yake bata da damuwa da
sabgar su shiyasa ko ajikinta.....
Yau takama asabar Su Sanam suna hutu dan haka tana gida abinta tana shan barci ,
wayar tace tashiga ruri cikin barci ta janyo ta ta danna ta kara a kunne , jin muryar Muradyn ta
yasa ta wartsake tafara rikitashi da shagwab'ar ta , aikuwa Huneed ya kuma narkewa harji yake
kamar ya bud'e ido yagan sa a gaban Sanam d'in sa , nan ya sheda mata gobe Sunday yana
hanyar dawowa dan shima yakasa komai yanzu in ba zuwa yayi yaganta ba murna sosai
Sanam ta shiga yi tana fad'a masa yadda tayi missing d'in sa , haka sukaita misayar kalamai
har suka yi sallama da juna zuwa anjima .....
Tana kashewa ta kira Diyana tace mata lallai ta shiryo yanzu zata raka shopping , dan
turarikanta sun kusa k'arewa gashi My Husbee d'in ta zai dawo , Diyana tace gatan dan tasan
itama zata d'ibi abin datake so .....
Ba'afi minty Goma ba sai ga Diyana lokacin itama Sanam ta shirya cikin shigar ta me kyau
sai k'amshi take , tana zuwa suka fito tare suna hira abinsu , dai dai wajen da zasu shiga mota
Maryam da Fahad suka taho hannu cikin hannu , turus Diyana tayi tana kallon su tare da cewa
" wanake gani Kamar Maryam Harka ? Sanam ta kalli Diyana tare da kallon su Maryam d'in ,
itama Maryam Diyana take kallo duk jikinta na rawa kada asirin su ya tonu...........
[9/27, 10:05] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 34.
Ganin za'a ranfota yasa Fahad yayi saurin zungurar ta , da sauri ta saita kanta tana
duban Diyana tare da cewa " Baiwar Allah banganeki ba ni sunana Maryam amman bansan
d'aya sunan da kika kira ba , Diyana ta dube ta sosai sannan tayi murmushi tace " Haba Harka
ko bacci nake naga me kama dake ai saina ganeta bare kuma ido biyu , Fahad a k'ufule ya kalli
Diyana yana fad'in " ke dallah Malama ki iya bakin ki , wanne irin sunan banza ne haka kike
kiranta dashi tunda tace bata sonki ba ana dole ne ? aikin banza kawai sai wani shishshigi kike
da cusa kai , sosai maganar ta tab'a zuciyar Sanam , tsawa ta dakawa Fahad d'in tana cewa "
to kai ina ruwanka tunda ba kai take tambaya ba , juyawa tayi ta kalli Diyana tace "kema
gashinan kinjawa kanki ai , koda yaushe ina gaya miki ki rage cusa kai a irin wannan wajen ,
tsaki taja sannan ta wuce motar tabar su Fahad baki bud'e , Diyana itama motar ta nufa tana
mamakin yadda Maryam Harka ke neman raina mata wayo...
Sai da suka fita daga harabar gidan sannan ta dubi Sanam wacce har lokacin ranta yake
had'e , a hankali ta furta " Besty wannan Maryam d'in kodai 'yar uwar kuce ? nifah abin
mamaki yake bani ganin yadda ta raina min wayo , Sanam tana tuk'in Motar ta kalli Diyana tace
" to ke a inah kika santa ? Diyana tace " wallahi A k'asan Unguwar mu take , duk cikin fad'in
Unguwar nan bawanda bai san Maryam Harka ba , amman k'iri k'iri tana neman ta maidani wata
bugun shaho , Murmushi Sanam tayi sannan tace " Maganin ki ai tunda kin iya saka ido ai dole
ayi miki haka , dama basu rufeki da duka ba kuma kinsan ba kwatar ki zanyi ba , Diyana tace
hmm " nifah dole sai nabi duddugin abinda yakawo Harka gidan ku , dan duk inda taje to tabbas
ba Alkairi akwai wani k'ullin ak'asa , Murmushi Sanam tayi sannan tace " aiki ne yasameki
wallahi , Ni Mumy cemin tayi 'yar kanin Baban tace , kinsan bawani sanin Family d'in ta nayi ba
, tunda duk rabin su suna can Borno state acan suke da zama , tunda tazo gidan naga take
taken ta tanaso tasamu fuska a gurina nikuma tuni ba fara had'e girar sama da k'asa , dan
kwata kwata banji ko kad'an zan bata fuska ba , Diyana ci gaba tayi da Maimaita kalmar 'Yar
K'anin Baban ta , to itadai tun tasowar ta a layin su bata tab'ajin su Maryam harka suna da 'Yan
uwa masu kud'i ba ,
Asalima Baban ta harya mutu sana'ar sa Baduku ne , ko zaman makoki ba'ayi masa ba
saboda basu da halin yin abincin masu zaman makoki , itace take fita yawonta tasamo musu
abinda zasuci ita da Maman ta da k'annen ta , Sanam jin Diyana tayi shuru yasa ta kalleta tace
" ko kinfara bin diddigin ne tun yanzu ? murmushi tayi suka ci gaba da hirar su , sai dai Diyana
ta k'udurta aranta tabbas sai tagano me Maryam tazo yi gidan su Sanam......
Bayan fitar su Sanam Maryam ta dubi Fahad tace " akwai matsala sosai fa , Fahad yace
wacce irin matsala kenan ? wallahi wannan k'awar Sanam d'in da kagani unguwar mu d'aya da
ita , tasanni farin sani gata da iya saka ido tamkar 'yar jarida , Fahad yace " karki damu bari
muje muyi magana da Aunty intaka ma a hanata shigowa gidan nan sai a hanata , sai sannan
Maryam tasaki ajiyar zuciya suka shige cikin gidan.......
Huneed tunda sukaje gidan Mumyn Twins wato Mahaifiyar Sanam , sai da ya koma sau
biyu gidan gar number ta garesa , har waya suke da Mumyn yana kwantar mata da hankalin ta ,
anan ya kuma jin halin Hajiya Nafeesa da yadda ta lalata Sanam tuntana k'arama bata ganin
Mutuncin kowa sai nata , kuma itace ta rok'eshi Alfarma akan tanason Sanam tasamu ilimin
addini ko yaya ne , dan har da rashin ilimi yana d'awainiya da ita , haka Huneed ya shiga
kyautatawa Mumyn Sanam duk da yasan babu abinda suka nema suka rasa , amman duk
k'arfin mutum kuma duk kud'in sa yana mutuk'ar son yaga ana kyauta ta masa , kuma koda
wasa bai tab'a gayawa Sanam ba bare ya nuna mata a fuska.......
Babban wajen Shopping Sanam sukaje ita da Diyana , sosai ta d'ibi kaya da turaruka
manya tare da sabulai masu tsada , Diyana itama Sanam tace mata ta d'auki duk abinda
takeso , haka ta zage ta d'ibi kayan kwalliya da turaruka itama , sai dogayen riguna had'add'u
wanda ta d'aukar musu kala biyu ita da Sanam iri d'aya , suna cikin zagaye a wajen suka ci
karo da Jaydeen yana tsaye yana duban su , wani tsaki Sanam tayi tare da k'ok'arin canza
hanya , da sauri Jaydeen yasha gaban ta yana fad'in " plss ko Minty 5 kibani inason magana
dake , Sanam ta galla masa harara tana fad'in " Malam dan Allah kabani waje ina da abubuwan
yi , Jaydeen yayi murmushi yace mata " Sanam inasonki sosai araina kuma tunda nake ban
tab'a son Abu ban samu ba , kamar yadda Mumyn ki tace mun in kwantar da hankalina tamkar
nasameki ne , to kisani kafin Daddyn ki yabar k'asar nan sai da Daddyna yaje sukayi magana
dashi , kuma shima Daddyn ki ya tabbatar wa da Daddyna cewar yana dawowa zai d'auramin
aure dake , wani kallo Sanam tayi masa wanda yake nuni da baka da hankali , magana yaci
gaba dayi yana fad'in " inaso inja kunnen ki akan wannan matsiyacin saurayin naki , daga yau
sai yau karki k'ara binsa ko inah dan bazan jure ganin yanamin yawo da Mata a titi ba , wani
takaicine ya kama Sanam takasa magana , tsaki tayi kawai ta wuce batare da ta kuma bi takan
sa ba ,....
Suna k'arasawa gun biyan kud'i akace musu anbiya musu , Sanam cike da fad'a ta kalli
wanda yace anbiya musun tace " to ce muku akayi bani da kud'in da zanbiya ne ? Malam inaso
kubashi kud'in sa kufad'amin nawa zanbiya , wani daga ciki yace " haba Hajiya ai ba'a maida
hannun kyauta baya , wata harara ta watsa masa sannan tace " to ni na maida sai ayimin
hukunci , Diyana ce takamo hannun ta suka fito daga wajen dan inba haka ba yanzu zasuyi
b'atacciya ,.......
Fahad shida Maryam tuni suka shedawa Hajiya Nafeesa maganar Diyana , Hajiya
Nafeesa tashiga zage zage " nifah wallahi tuntuni na tsani yarinyar nan dama , kowanne aiki
intayiwa Sanam ita take rusashi , lallai lokaci yayi da zatayi maganin ta dan wannan karon a
shirye take da tayi komai dan burin ta ya cika , take ta shiga shirya yadda zata yi maganin
Diyana ta shirin Had'ata fad'a da Sanam.....
Har suka baro wajen Shopping Sanam na ruwan jaraba , babu abinda yafi tsaya mata arai
sama da maganar da yace Daddyn ta da nasa sunyi , yaushe wannan abun yafaru batasani ba
? dama taga take taken Mumy bason Huneed take ba , tasan tunda Jaydeen ya kasance d'an
gidan k'awar ta dole zata bi duk yadda za'ayi ta cusa mata shi , itakuma wallahi ko ba'abata
Huneed ba babu abinda zatayi da Jaydeen , ko maza sun k'are a duniya da ta xauna dashi
wanda ta mutu babu aure , Diyana dai babu bakin magana , dan tamkar Sanam zatayi aljanu
haka tashiga yi tana zage zage , addu'a Diyana tashiga yi akan Allah yakaisu gida lafiya dan
yadda take tuk'in motar ma tashin hankaline , a haka Allah yakawosu gida lafiya tashiga
dannan Hon. me rikitar wa , me gadi tamkar zai kifa haka yayi sauri ya nufi gate d'in yana
bud'ewa , yana gama bud'ewa motar tana danno kai da mugun gudu cikin gidan , wani uban
tsalle me gadi yayi dan karta take masa k'afa , bin motar yayi da kallo ya tabbatar da lallai yau
antab'o 'Yar gwal , tana fita daga motar ta nufi cikin gida kai tsaye tana k'walawa Hajiya
Nafeesa kira " Mumy Mumy kina ina inason magana dake , da Hajiya Nafeesa da Fahad da
Maryam duk mik'ewa sukayi jikin su na rawa jin irin kiran da Sanam kewa Hajiya Nafeesar ,
tuni suka shiga jin tsoron kodai Diyana ta je ta nemo labarin abinda yakawo Maryam cikin gidan
? In kuwa hakane to tabbas sai tayi magani Diyana a yau basai gobe ba , Sanam tana
shigowa palor tabi su da kallo sannan tace " Mumy inaso kijawa wannan 'Dan gidan k'awartaki
kunne wallahi yafita daga sabga ta tunkafin insa ayimin maganin sa , wata ajiyar zuciya Hajiya
Nafeesa tasaki tare da hamdala a zuci , Cike da kissa da nuna kulawa tace " wanne d'an
k'awar tawa kenan ? Sanam tace " wannan kalar 'Yan daudun dan banason sa ko kad'an ya fita
daga sabga ta , tana gama fad'ar haka ta haye sama tabarsu baki bud'e , Hajiya Nafeesa taja
tsaki sannan tace" aikin banza kalar d'an daudun kuma shine mijin ki , dan duk yadda zanyi
yazama mijinki sainayi banza wawiya , Fahad yasa murmushi yana kallon Hajiya Nafeesar
sannan yace "Aunty ai batasan kinayiba dama binta kikayi kika fad'a mata , wata harara ta galla
masa sannan sukasa dariya su dukan su , dai dai lokacin Diyana tashigo cikin palor idanun ta
akan su , aikuwa su duka suka canza fuska tamkar basu suke wannan dariyar ba , Diyana ta
kalli Mumy ta rissina tana fad'in " barka da yamma Mumy , Hajiya Nafeesa tayi tsaki sannan
tace " barka shugabar munafukai , Diyana tamkar bataji ba tashige abinta batare da tabi
takansu ba , ....
Hajiya Nafeesa tace " inaso asan yadda za'ayi a had'a Sanam fad'a da wannan shegiyar
yarinyar , Maryam tace " wannan shirin kibarmin shi a hannuna dan nafi kowa son naga sunyi
fad'an da baza ta kuma takowa gidan nan ba , kawai inason inga saurayin da Sanam tafi so
dan ta dalilinsa zamu saka su yin fad'a , nan suka saka wata shewar murna dan shima shegen
dama so suke yadaina zuwa , dan tun sanda yakawo mata malamin dazai dunga koya mata
karatun Hajiya Nafeesa takuma tsanar sa , kuma sosai taga canji yanzu a tare da Sanam ,
komai inzatayi yanzu tadaina gaya mata sab'anin da , tabbas zataso ace sun rabu dan komai
zai fi mata sauk'i........
*Kumin Afuwa Zazzab'i nadamuna*
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 35.
Koda Diyana ta hau sama ta samu Sanam cike da nutsuwa tace " dan Allah Besty
kirage saurin zuciya , wannan halayyar bata dace dake ba , Sai sannan Sanam ta sai ta kanta
tafara magana "Diyana inason Huneed fiye da tunanin ki banason duk abinda zai zame mana
barazana a cikin soyayyar mu , kinajin abinda Guy d'in nan yafad'a wai Daddyna danasa sunyi
magana , duk da nasan Daddyna bazai tab'amin auren dole ba , amman naga kamar Mummy
tafison wannan Jaydeen d'in akan Huneed , Diyana ta mik'e ta k'arasa kusa da Sanam sosai
tace " ki kwantar da Hankalin ki Besty tunda har kinsan Daddyn ki bazai aura miki wanda
bakyaso ba , kawai dai shawarar da zan baki shine kiyi magana da Huneed akan yasami
Daddyn ki da maganar auren ki , Sosai Sanam taji dad'in abinda Diyana tace mata , dama
Huneed tuntuni yake damun ta da Maganar yanaso yaturo , itace take ce masa yabari tayi nisa
a karatu sai ya