Showing 60001 words to 63000 words out of 80926 words

Chapter 21 - YAR KISHIYA Book Complete BY Zee MD.pdf

Zee MD   

10 Jul 2025

4197

Babban game
kuwa , dukan su suka tuntsire da dariya sunajin dad'in muguntar da suka k'ullah ........



*Kundaina Comment Ko*😒🤒🤒
_Kushirya amsa tambayoyi a wajen D.P.O_�� *nagaji da halinku🤨🤨*
[9/27, 10:09] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Riƙon Me Haƙuri_
🤦🏻â€â™€ï¸í ¾í´¦í ¼í¿»â€â™€ï¸



*NA*
*Zee MD*



*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
( Domin Marubuta Mata )

✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/





*Bisimillahir Rahamanir Rahim*




Chapter 39.


Sanam sai wajen sallar Magriba ta farka daga baccin datake , wanka ta fad'a sannan
tana fitowa tayi arwala dan yanzu sallah bata wuce ta , tana idar da sallah ta shirya cikin wasu
kaya marasa nauyi sannan ta sauko ƙasa ....

Bawanda da tasu a cikin palor dan haka ta wuce kitchen , tana shiga ta kunna gas ta É—ora
indomie tasa kifin gwangwani sannan ta koma palor ta zauna , tunowa tayi da wayar ta dan
tasan yanzu haka Huneed ya kira ta , da sauri ta hau sama tanufi É—akin ta dan É—auko wayar ,
tana É—aukowa taga wayar akashe take mamaki yaka mata cikin zuciyar ta take tunanin yaushe
ta kashe waya ? ko bacci zatayi bata kashe waya sai dai tasa ta a silet , kawai taɓe baki tayi
sannan ta sauko ta koma kitchen....

tana zuwa tasamu indomie sa ta É—ora ta dahu , sauke wa tayi ta juye a filet sannan ta
kashe gas É—in tafito ,..
zama tayi kan dinning tafara ci tana danna wayar ta , data ta buɗe take saƙonni suka fara
tururuwar shigowa , koda tashiga duba saƙonni rabi duk numbobi ne baƙi da bata san dasu ba ,
wasu maza ne masu nuna suna sonta wasu kuma mata ne Æ´an sch É—in su , wasu tabasu amsa
wasu kuma tayi tsaki abinta , a haka tana tafiya har tazo kan number da su Hajiya Nafeesa
suka turo mata saƙo , da har zata wuce sai taga ai kamar pic aka turo mata da kuma video take
tashiga tafara buÉ—ewa , suna gama buÉ—uwa Sanam tayi tozali da hotunan masoyinta abin
ƙaunar ta wanda take burin yin rayuwa dashi ta har abada tare da ƙawar ta kuma bestyn ta ,
wata iriyar zabura tayi tana miƙewa tare dayin zoom ɗin pic dan ta tabbatar , tabbas sune
Diyana ce rungume a jikin Huneed kuma a ƙofar gidan su , hannun ta har rawa yake wajen
buÉ—e video dan taga me yake ciki shima , nan ma dai sune a rungume da juna , dama da yake
su Fahad sunsa me hoton yayi musu edityn har wata murya yasa musu tamkar sune , Huneed
na cewa " Diyana kinji yadda jikin ki yake da laushi tamkar auduga , ita kuma Diyana tace "
Allah Babyna dani da Sanam wace kafi jin daÉ—in jikin ta ? Huneed yace " ina da haÉ—i ai kinfita
komai Baby , tamkar da gaske suke maganar amman duk sharrin edityn ne , dan lokacin
Huneed salati yake yadda yaga Diyanan nayi , shine suka saka musu murya tamkar sune suke

maganar , Sanam jiri taji yana ɗibar ta take ta zauna daɓas a ƙasan tayel , duk ac. dake aiki a
cikin palor bai hana Sanam yin zufa ba , tuno hawaye suka fara mata zarya akan kuncin ta ,
cikin zuciyar ta tanajin wani irin É—aci meyasa Huneed zai mata haka ? duk san datake masa
wannan shine tukucin da zai bata kenan ? tabbas tayi nadamar da yadda ta saki jiki take nuna
masa soyayya , komai yace da ita batayin musu haka zatayi masa , amman sakamakon da zai
mata shine soyayya da ƙawar ta wacce tafi yarda da ita akan sauran ƙawayen ta , Lallai Diyana
taci amanar ta amman suje dan kansu daga yau babu ita basu har abada , kuka sosai tashiga
yi me ratsa zuciya tamkar zatayi ihu , duk abinda ke faruwa da Sanam su Hajiya Nafeesa suna
laɓe suna kallon ta , wata dariya suke ƙasa ƙasa gudun kar taji , sai da sukayi me isar su
sannan Hajiya Nafeesa ta nufo wajen Sanam É—in tana faÉ—in " Innalillahi My luv meyasa meki
haka kike kuka ? Sanam tamkar an tunzura ta takuma sakin kukan batare da tace komai ba ,
da sauri ta É—auki wayar tana faÉ—in " me aka turomiki yasamin ke kuka , tana ganin wannan
hotunan tafara salati tare da cewa " wannan ba saurayin nan naki bane Huneed shida Diyana ?
kai Sanam kawai ta iya ɗagawa tana sharar ƙwallah , Hajiya Nafeesa tace " wato dama haka
suke shiyasa tun farkon zuwan sa banyi na'am dashi ba , to tunda naga kina sonsa shiyasa
nima nafara son sa dan inason farin cikin ki , amman ko ranar nan sai da Fahad ya gayamin
yagansa a wani hotel shi da Diyana , gudun ɓacin ranki yasa nace yabar maganar banaso kiji ,
to gashinan kingani da idanunki wallahi sunji kunya azzalumai , tuni Sanam ta miƙe ta haye
sama tana kuma fashewa da kuka......

tana hayewa sama su Maryam da Fahad suka fito daga inda suka ɓuya suna dariya , nan
suka shiga murna na nassarar da suka samu na raba Sanam da Huneed , kuma da wannan
damar zasuyi amfani komai suyiwa Sanam tunda me bata kariyar su musu farraƙu , duk
makircin da suke ƙullawa Rabi me musu aiki tanaji , kawai sai dai ta gyaɗa kai tana jimami tare
dayin Allah wadai da halin Hajiya Nafeesa.....

A ɓangaren Huneed tunda yasamu kira akan zasu tafi jihar Katsina domin kamo ƴan
ta'adda , kwata kwata ji yayi bayason zuwa saboda Sanam , tabbas yanason sanin halin da take
ciki , kuma zuciyar sa na gaya masa lallai akwai abinda ake shirya masa shida ita , amman
bashi da yadda zaiyi dole zai tafi tunda aikin sane haka , kiran wayar ta yayi har lokacin bata
buÉ—e ba , sosai yake mamakin rufe wayar ta datayi yauÉ—in , dan ma dai yaje gidan kuma ya
samu tabbacin lafiyar ta ƙalau bacci kawai takeyi....
Haka ya shirya tsaf yayiwa Hajiyar sa sallama tare da Hisham , su duka fatan Alkairi suka yi
masa sannan ya shige ya tafi cike da kewar gida......

Sai Bayan sallar Magriba ya kira wayar Sanam ta shiga , sai dai har tagama ring É—in ta ba'a
É—aga masa ba , sosai hankalin sa ya tashi dan yayi mata miss call shida amman bata É—aga ba ,
tuni zuciyar sa tankarye tabbas akwai abinda ke damun Sanam , jiyayi tamkar ya dawo gida
yafasa aikin saboda fargaba da kuma son sanin halin da Sanam ke ciki , tuni ya kira Hisham
yace masa yaje gidan su Sanam dan yagano masa lafiyar ta , Hisham yashiga tsokanar sa
sannan yace masa yana gama cin abinci zaije yaga lafiyar ta.....

Koda Hisham yaje bai samu ganin Sanam ba saboda ance masa baza ta samu damar fitowa

ba , kiran Huneed yayi ya sheda masa abinda akace masa a gidan su Sanam , sosai hankalin
Huneed ya tashi yakira Mummyn Twins wato Hajiya Maimuna , nan ya gaya mata abinda yake
faruwa tun farkon kiran da akayi masa har yaje gidan su Diyana dakuma zargin da yake akan
akwai shirin da ake yi akan su , nan tayi shuru tana nazari sannan tace " tabbas akwai abinda
za'a ƙulla muku , amman ka kwantar da hankalin ka ka tsaya kayi aikin da kaje insha Allah
komai aka ƙullah to tabbas xai kwance , nan ta shiga kwantar masa da hankali tare da ƙarfa fa
masa gwiuwa da kuma ƙara tunasar dashi akan yayi addu'a , sosai Huneed yaji kaso tara a
cikin goma na daga cikin damuwar dayake yaragu , tabbas Mummyn Twins Uwa ce da
kowanne ÆŠa zaiyi Alfaharin samun ta , sallama sukayi ya kashe wayar ya koma bakin aiki........

Sanam kuka take sosai a haka bacci ya kuma a wan gaba da ita ,
. Washe gari tana farkawa ta tayi wanka wajen shaÉ—aya ta sauko da mukullin mota a hannu ,
lokacin Hajiya Nafeesa tana zaune ita da Maryam suna yin break fast , koda Sanam ta sauko
Hajiya Nafeesa ta shiga yi mata murmushi tana faÉ—in " zonan my luv , Sanam taje Hajiya
Nafeesa ta rungume ta tana faÉ—in ' kicire komai a ranki ki rabu dasu , kinga in kikasa damuwa
a ranki to tabbas zaki wahalar da kanki a banza ne su kuma ba ruwan su , ni da zaki birgeni ma
da kinfara kula Jaydeen kema dan ki nuna musu kema daman da wanda kikeso , nan Hajiya
Nafeesa tashiga turawa Sanam Jaydeen ta ƙarfi da yaji wai dan ta ɗauki fansa , Sanam kwata
kwata Jaydeen ba birgeta yake ba dan baya É—aya daga irin mazan datake so , ganin inbata
amincewa Mummyn nata ba zatai ta damun ta , dan haka tace tabata kwana biyu inta huta zata
yanke yadda zatayi , tana cewa haka ta fice daga palor zuwa harabar gida, ....

Tana fita tahau motar ta ta nufi gidan su Diyana , tabbas zataje tayi mata rashin mutuncin
da bazata manta da itaba a rayuwa........
[9/27, 14:26] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻â€â™€ï¸í ¾í´¦í ¼í¿»â€â™€ï¸


*NA*
*Zee MD*



*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A)✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*Bisimillahir Rahamanir Rahim*

_Alhamdulillah Allah yayi min dawo wa , ina mutuk'ar godiya gareku masoyana ta yadda
kuka nunamin kauna tare da addu'oin ku gareni , naga yadda kukayi kewata sosai😊😊 nima
nayi kewarku dayawa Allah yabarmu tare_ â¤ï¸â¤ï¸í ½í¹í ¼í¿»í ¾í´


Chapter 40.


Hajiya Nafeesa murmushin samun nassarar raba Sanam da mutane biyun data tsana,

Yanzu tasan komai zatace da Sanam zatayi tunda tarabata da masu zugata, burinta guda
d'aya yarage a yanzu shine, taraba Sanam da Mahaifinta Alhaji Abba.....


Sanam na isa k'ofar gidan su Diyana tayi parking din motar ta tafito , tsayawa tayi tana
kallon k'ofar gidan tare da tariyo video da tagani a idanuwanta, wani kishine yakuma taso Mata
tamkar mahaukaciya haka ta nufi cikin gidan su Diyana....

Tana shiga tasamesu suna zaune suna hira su dukansu a cikin palor, Sanam ko sallama
batayi musu ba ta tsaya a bakin k'ofa tanawa Diyana wani mugun kallo, Diyana d'auke da
murmushi a fuskar ta tace " 'Yar halak yanzu nagama maganarki , Sanam cike da takaici tace
"ai dole kiyi maganata maci amana wacce bata gaji arzik'i ba , duk mutanen da suke zaune a
wajen suka shiga kallon Sanam tare da mamakin jin abinda ya fito daga bakinta , Diyana jikinta
har rawa yake tana duban Sanam, a hankali ta furta " Sanam ni kike kira da maci amana wacce
bangaji arzik'i ba? A fusace Sanam tace " nakiraki da hakan kiyi maganin abun , wallahi Diyana
kinban mamaki ashe ked'in fuska biyu gareki , Kirasa Wanda zakiyi soyayya dashi sai Huneed,
kuma kinfi kowa sanin matsayinsa a wajena , to anyi walk'iya naganku keda shi dan haka babu
ni babu Ku munafukai kawai , tana cewa haka ta juya ta fita hawaye cike a idanuwan ta........
Tabbas Sanam ba iya maganar dataje zatayiwa Diyana kenan ba ,sotayi ta gasa mata
maganganu Amman ganin idanun Umman Diyana yasa Sanam takasa, tana fitowa ta koma
cikin motar ta zauna ta d'ora kanta kan sitiyarin tasaki kuka me cin rai , duk duniya bata da wata
k'awa da suka shak'u kamar Diyana , sannan bata da wanda takeso take mafarkin rayuwa dashi
kamar Huneed, Amman meyasa sukayi Mata haka ? ta dad'e tana kuka kafin taja motar ta tabar
Unguwar su Diyana......

Diyana tunda Sanam ta fita take tsaye tana maimaita kalmomin data kirata dasu, Umman
su Diyana ta dubi Diyana wacce kowa ita yake kallo tace " Diyana me kikayiwa Sanam haka
tabbas ba haka take ba dole akwai abinda kikayi Mata , kuma koma meye akan saurayine tunda
gashi tafad'a , Hawayen da Diyana take ta Rik'ewa sune suka gangaro kan kuncinta, cikin

muryar kuka Diyana tace "Umma wallahi kwata kwata bansan laifin da take tuhuma ta dashi ba ,
Umma kinfi kowa sanin halina bazan tab'a cin amanar Sanam., shuru Umman tayi dan tabbas
tasan halin Diyana , bazata tab'a kula saurayin Sanam da sunan soyayya ba , inajin dai so ake
arabasu Dan anga suna son junan su da gaskiya , Diyana d'aki tashige saboda kukan da ya
kufce Mata ....

Sanam tana tafe cikin motar ta kiran Huneed sai shigowa yake amman ko kallon wayar taki
yi , daga k'arshema kashe wayar tayi Dan ko kad'an batason ganinsa, jitayi batason komawa
gida tasamu kanta da son zuwa gidan Mumyn Twins wato Hajiya Maimuna mahaifiyar ta....
Hanyar Estate d'in su ta nufa dan tanason inda zata samu Hutu nawani lokacin.....


A b'angaren Huneed kuwa hankalin sa tuni yagama tashi , Kwata kwata yakasa aikin da
sukaje yi, Gashi kusan shine jigon tafiya Dan shine babba a gurin kowa umarninsa yake bi,
jiyayi yana muradin ganin Sanam a yau basai gobe ba, tuni yafara shirin tahowa birnin tarayya
wato Abuja.......

Sanam tana isowa tayi parking tafito tashiga cikin gidan nasu, tana bud'e k'ofar palor wani
k'amshi ya bugi hancinta ,samun kanta tayi da lumshe idanunta tanajin nauyin da zuciyar ta tayi
yana raguwa, sallama tayi duk da babu kowa a cikin palor, zama tayi a d'aya daga cikin kujerun
da suka k'awata palor , banda k'arar ac babu abinda ke tashi acikin palor , tafi minty biyar a
zaune saiga Hajiya Maimuna suna sakkowa daga step d'in benen cikin palor, ganin Sanam
sukayi zaune tayi tagumi hannu bibbiyu tayi nisa cikin tunani , mamakine yakama Mumyn
Twins. Yaushe Sanam tashigo cikin gidan har take zaune a haka ? Suna gama sakkowa ta
mik'awa murja twins tace mata " kuje wajen motor ganinan , da yake fita zasuyi dubo Hajiyar ta
batajin dad'i , har Murja tafice daga palor Sanam batasan anayi ba, dafa kafad'ar Sanam Hajiya
Maimuna tayi , firgigit Sanam tadawo daga dogon tunanin da tatafi , murmushi ta k'ak'alo kan
fuskar ta tana fad'in "Mumy ina wuni ya gida , cike da kulawa Mumy ta amsa tare da tambayar
ta su Hajiya Nafeesa, Sanam tace lafiya lau suke , shuru sukayi nawani lokacin kafin Mumy
Twins tace "meke damunki haka naga kinyi shuru kina tunani ko akwai wani Abun ne ? Sanam
tayi k'asa da kanta tana wasa da yatsun hannun ta , Mummy tana ganin haka tasan akwai
damuwa a tare da Sanam kuma tana buk'atar a rarrasheta , kallon idanunta kawai tayi tagano
irin Jan da sukayi saboda kuka, sosai Hajiya Maimuna taji tausayin 'yar ta yakamata , cikin sigar
kwantar da hankali Mummy tace " ki hau sama kiyi wanka akwai abinci kid'iba kici sai ki kwanta
ki huta , nima zani duba Hajiyar mu batajin dad'i , Amman bazan dad'e ba zandawo tunda ba a
kwance take sosai ba , Sanam ta amsa da to tare da cewa tayiwa Hajiyar sannu..........
[9/27, 14:27] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻â€â™€ï¸í ¾í´¦í ¼í¿»â€â™€ï¸

*NA*
*Zee MD*



*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*Bisimillahir Rahamanir Rahim*





Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login