Showing 72001 words to 75000 words out of 80926 words

Chapter 25 - YAR KISHIYA Book Complete BY Zee MD.pdf

Zee MD   

10 Jul 2025

4189

21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
‍♀️‍♀️



*NA*
*Zee MD*



*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ ( W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/




*Bisimillahir Rahamanir Rahim*




Chapter 46.


Diyana tasakar Mata jakar tana k'ok'arin wuceta tabar gun , Sanam tayi saurin k'ara
Shan gaban Diyana tana cewa " plss My bestyna kitsaya ki saurareni , Nan Diyana ta tsaya cak

tana duban Sanam , Sanam batace komai ba kawai videon dake wayar ta ta kunnawa Diyana
tana cewa " Dan Allah ki kalli wannan video sai ki fahimcine , Diyana ta rik'e wayar tana kallon
video take idanun ta sukayo waje , a hankali tashiga furta "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un , da
sauri ta kalli wajen da Huneed yake tsaye sannan ta kalli Sanam tace " wallahi bansan sanda
wannan Abun yafaru ba besty , Nan Huneed yadubi Diyana yashiga bata labarin duk abinda
yafaru , Diyana a mugun fusace ta nufi wajen Isma'il me kanti , Huneed ya dakatar da ita yace "
ki k'yalesa Nan da kwana biyu zansa azo akamasa , yanzu in kika Masa maganar zai iya
guduwa Dan Kar muka Masa , Diyana sosai ranta ya b'aci da irin abinda Isma'il yayi Mata ,
wato mutum dai ba abin yarda bane , duk yadda take mutunci da Isma'il Ashe za a iya had'a
baki da shi Dan acutar da ita , Nan Sanam ta dafa kafad'ar ta tace " Besty Kinga abinda nagani
idanuwana suka rufe har nakasa jurewa sai Dana zo gareki nayi Miki wannan Abun , inaso
kiyimin afuwa da abinda nayi Miki Dan nasan ko kece kika ga irin hakan matakin da Zaki d'auka
kenan , Diyana ta juyo tana kallon Sanam cike da so da k'auna irin na K'awayen asali , take ta
rungumeta tana saka kuka tare da cewa " wallahi ko d'aya banrik'e kiba kawai dama nasan
had'amu akeson ayi , Sosai suka burge Huneed dan kana ganin su kasan suna k'aunar junan
su da gaskiya , ....

Dukansu suka shiga motar suka nufi gidan da Huneed ya ajiye Maryam ,..

Tunda Huneed ya kaita gidan na yabaro ta Bata sake jin motsin kowa ba , ga uban sauro
dake cizonta sai kuka take tana yiwa Huneed Allah ya isa , tunda take bata tab'a kwana a
k'ask'ancen cen waje ba sai yau , tana zaune tana kuka tare da tarin tsoro da ya mamaye Mata
zuciyar ta har bacci yayi gaba da ita , ....

Acan b'angaren Hajiya Nafeesa kuwa tun jiya suke Kiran wayar Maryam Amman akashe ,
Fahad yadubi Hajiya Nafeesa yace " Wai bata fad'amiki inda zataje bane ? Hajiya Nafeesa tace
" Ina tafad'amin kuwa ni bansan ma bata gidan ba inbanda kagayamin ,. Fahad yace " to kodai
gidan su ta tafi ? Kuma indai Maryam zataje gida ai tana sanar min , Hajiya Nafeesa ta tab'e
baki sannan tace " wayasani ko zuwa tayi ta kwana da wani gardin , kasan halin ta dan wallahi
wannan yarinyar kwata kwata batayi ba , kana ganin ta kasan tana da mugun son abin duniya ,
Fahad ya dubi Hajiya Nafeesa sannan ya tab'e baki yace " kema ai kina da son kud'i Aunty ,
tunda yarinyar nan tazo gidan nan baki tab'a Bata kud'in kashewa sai dai inzata Miki wani aikin ,
Kinga kuwa Dan taje ta kula maza a waje ai ba laifi tayi ba , Hajiya Nafeesa ta gallawa Fahad
harara sannan tace " to angaya maka banki ce ni da zan dunga bata kud'i , duk irin hutawar
datakeyi a gidan Nan bai yi Mata ba , taci abinci me kyau tasha lemuka masu tsada ta kwanta
a waje me kyau to metake buk'ata sama da hakan ? Fahad ya kalleta shima cike da takaici yace
" duk wannan abubuwan da kika lissafo ai kud'i Yana gaba dasu , Hajiya Nafeesa a fusace
tacewa Fahad "bazan Bata kud'in ba kuyi yadda zakuyi dani , ta haye sama tana sababi tamkar
zata kifa ....
Fahad haushine ya kamasa ya furta " kiyi kigama wallahi duk kud'in da kika tara saina
k'wacesu ko ta halin k'ak'a , mace bata da aiki sai mugunta tana da kud'i Amman bazata Bari
aciba , tsaki yaja yafice daga cikin gidan baki d'aya......

Maryam tana kwance kan tayes duk ta takure saboda sanyin da takeji , jitayi an bud'e
k'ofar gidan alamar za'ashigo , dasauri ta mik'e tana kallon hanya aikuwa ido biyu tayi da
Diyana da Sanam ,. Jitayi tamkar ta nutse dan shikenan tasan asirin ta ya tonu itakam , Diyana
ta tab'e baki tace " banyi mamakin irin abinda kikayi ba dan komai akace zakiyi nasan Zaki
aikata , Amman ba laifin kiba ne laifina ne Dana d'auki yadda nabawa Isma'il shikuma yasamu
damar cin amanata , Sanam tana k'arasowa ta dubi Maryama kuma a dai dai lokacin Huneed
yashigo , durk'usowa yayi Yana cewa Malama Maryam ga abin Kari nakawo Miki kici ki k'oshi
sai kibamu bayani akan shirye shiryen da kukeyi keda uwar d'akin naki , take away ya ajiye
Mata indomi'e ce aciki tare da ruwan shayi a leda , Maryam tabbas tana jin yunwa Dan da
badan haka ba bazata iya cin komai ba a halin datake , Amman itama zataso tafad'awa Huneed
duk shirin da Hajiya Nafeesa keyi akan Mahaifin Sanam , tunda itama Hajiya Nafeesar ai ba
Amana gareta ba , Nan ta janyo take away tafara cin Abinci hannu baka hannu k'warya , ...

Tana kammalawa tasha ruwan tea sannan ta ajiye sauran data rage , Huneed ya dubeta
yace " muna sauraranki kuma mutuk'ar kika b'oyemin gaskiya to tabbas zaki ji ajikin ki ,
Maryam cike da rawar Murya tace " Dan Allah in nafad'a muku gaskiya Dan Allah kasakeni intafi
gida , Huneed yace " in har hakan zai yuwu mazai Hana muna jinki , Nan Maryam ta fara bawa
su Sanam labari tundaga farkon had'uwar ta da Fahad har ya zo garin Abuja tare da kuma Kiran
ta akan aikin da zatayiwa Hajiya Nafeesa , Maryam duk wani Shirin na Hajiya Nafeesa akan
Sanam da Mahaifin ta sai data Gaya musu , sannan ta kuma Gaya musu k'udirin Hajiya
Nafeesa nasan raba Sanam da Mahaifin ta har maganar da Marayam taji Hajiya Nafeesa nayi
ita da k'awar ta akan kashe ita Maryam d'in sai data Gaya musu , Sanam tuni taji wata iriyar
zufa na tsatstsafowa ta jikinta baki d'aya , dukan su bawanda bai girgiza dajin irin Shirin Hajiya
Nafeesa ba , .......





*NI KO ITA* _littafine daya Sha bambam da sauran. Kudai kuyi saurin mallakar
naku dan kashe k'wark'watar idanuwan ku ,. Anan zakuji yadda Uwa take tarayya da 'Danta na
cikinta tamkar Miji da Mata , kudai Kar kubari yabarku kuyi saurin Mallakar naku akan Farashi
200 kacal_✍ *Domin mallakar naku ku tuntub'i Marubuciyar akan wannan Number : 09137064556 sai
najiku*


_Taku a ko yaushe_
*Zeee MD*
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_

‍♀️‍♀️


*NA*
*Zee MD*



*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/





*Bisimillahir Rahamanir Rahim*




Chapter 47.


Sanam Hawaye ne yashiga zubowa a kuncin ta , Ashe duk irin yadda Mummy
Nafeesa ke nuna Mata k'auna ba gaskiya bane ? Duk tana yin hakane Dan kawai ta shiga
tsakanin ta da Daddyn ta , shiyasa kwana biyun Nan in takira Daddy a waya baya d'agawa ,
yanzu inta kirashi ma akashe ake cemata , kuma tanajin yauma da safe ya Kira Mummy twins ,
Diyana ce ta dafa kafad'ar Sanam tana cewa " Sorry Bestyna nasan da ciwo ace wacce ka
d'auka a matsayin uwa itace zata maka hakan , Amman ki godewa Allah da yasa asirin ta ya
tonu tunkafin ta kammala Shirin ta , Sanam cikin muryar kuka tace " me nayi Mata haka
takeson shiga tsakanina da Mahaifina ? Duk wata soyayya na nuna wa Mummy Nafeesa , zan
iya cewa nafison Mummy Nafeesa akan Mummyna data Haifeni , Daddy ba gatan da baya
nuna Mata , kafin yayiwa Mummyn Twins Abu sau d'aya yayiwa Mummyn Nafeesa sau goma ,
Amman kiduba kiji irin abinda takeson aikata Masa , ta d'auki d'an shege a matsayin d'an da
zata ce shine jininsa , lallai duniyar Nan abin tsoro ce , Huneed ya mik'e tare da cewa " ki
share hawayen ki duk abinda ta shuka a yanzu zaizo k'arshe , Sanam tayi wani shu'umin
Murmushi tare da mik'ewa tsaye itama tana fad'in " banason Shirin ta ya rushe a yanzu , kamar
yadda ta shirya hakan ne zai tafi Amman inaso daga k'arshe wasan ya canza salo ,. .
Huneed ya dubi Sanam da mamakin abinda tace , Sanam itama tana duban sa sannan taci
gaba da magana " Maryam inaso kifad'amin nawa ta biyaki kike Mata aiki ? Maryam datayi
tsuru tana kallon su duk jiki na Mata ciwo tace " lokacin da zanyi mata aiki munyi da ita zata

bani " 2 million Amman Bata bani ba kawai dubu d'ari biyu tabani shima dan kawai zan Mata
aikin rabaku da juna , Sanam tace " inaso kituromin account number ki zansa Miki 3 million kiyi
min nawa aikin , Maryam sosai ta girgiza dajin hakan to itakuma wane aiki zatayi Mata hakan?
Huneed da Diyana su kansu kallon Sanam suke suna son jin wane aiki zata saka Maryam ,
Sanam tace " inaso kici gaba da zama a gidan mu , sannan karki kuskura ki nunawa Hajiya
Nafeesa nasan komai data ke shiryawa , Abu na k'arshe kuma kiyi yadda zakiyi kishiga jikinta
sosai Dan ki jiyomin duk wani shiri da take akaina , kuma ban yadda ko Fahad yasan da
wannan maganar ba , yanzu za'a sakeki kitafi sai ki nuna musu accident kikayi tunjiya shiyasa
baki kwana a gidan ba ,
Diyana ta kalli Sanam sannan tace " Besty meyasa kikeson yin hakan ? Sanam tayi
Murmushi sannan tace " inaso Daddy yazo yakamata da hannun sa , tunda yanzu Daddy ta
had'ani dashi komai zance bazai yadda ba , kuma yanzu bamu da hujjar tunkarar ta da wannan
maganar , zata iya k'arya tawa tare da sake sabon shiri Wanda ba lallai musan irin Shirin da
zatayi Nan gaba ba , dukansu sukayi Na'am da maganar da Sanam tayi , Huneed ya kalli
Maryam sannan yace " kinji abinda tace Miki ko ? Maryam da sauri ta d'aga kai Dan tana
mugun tsoron Huneed , Huneed ya durk'uso wajen fuskar Maryam yace " inaso kisani mutuk'ar
kika sake wannan Shirin namu ya lalace to tabbas saina kashe ki da hannuna kafin ita Uwar
d'akin naki takashe ki , Maryam cike da tsoro tace " bazan karya alk'awariba , Nan Huneed ya
fito suma dukan su suka fito har Maryam datake d'ingishi ,


A jikin motar suka samu Huneed Yana jiransu , kullo gidan yaje yayi sannan yazo ya
bud'ewa Sanam murfin motar , shiga tayi itama Diyana tashiga sai Maryam a tsaye sai muzurai
take , wata tsawa Huneed ya daka Mata Yana cewa" ko bazaki tafi ba ne in maidake cikin
gidan ? Da sauri tashige motar Dan Bata fatan sake taka k'afarta a k'ofar gidan ......

Huneed sai da suka Kai Diyana har cikin makaranta sannan suka taho , tsayawa sukayi
nesa da gidan Hajiya Nafeesa suka sauke Maryam tare dayi Mata Manyan worning akan
maganar da sukayi , jikinta na rawa ta amsa da to tayi saurin barin gurin......

Huneed da Sanam tunda suka sauke Maryam kowanne yayi shuru , a haka har suka
k'araso gidan Mummy twins , suna shiga suka sameta a palor tana kallo twins duk sunyi bacci ,
sallama sukayi Mata ta amsa tana cewa " sannun ku da dawowa , Huneed yace " sannu da gida
Mummy , yauwa sannu Huneed kungaji da yawa daga ganin ku , Sanam tana k'arasowa ta
durk'usa wajen k'afar Mummyn Twins tasaka wani kuka me tsuma zuciya .........

Mummyn Twins Bata hanata ba illah zuba Mata idanuwa datayi tana kallonta , cikin
muryar kuka Sanam tace " Mummyna Dan Allah kiyafemin duk iri Abubuwan da nayi Miki ,
tabbas na aikata kuskure Wanda bansan illar hakan ba sai yanzu , na d'auka duk duniya Hajiya
Nafeesa tafi kowa Sona saboda yadda take nuna min gata da kuma yadda take barina inayin
yadda nakeso , Ashe duk ba haka bane duk duniya ba Wanda yakaiki Sona Mummyna kece
kikasan ciwona kece kika fi kowa k'aunata , nayi nadama akan duk abinda na aikata Miki Dan

Allah ki yafemin Mummy ko nasamu sauk'i a zuciyata ,Hajiya Maimuna cike da so da k'auna ta
rungumo 'Yar ta jikinta tana bubbuga Mata baya tare da cewa " kiyi shuru kidaina kuka Ni
bantab'a rik'eki araina ba , a Koda yaushe Ina Miki addu'a akan Allah yashirya minke , kuma
Koda yaushe kina cikin raina bantab'a ganin laifin kiba akan abinda kikeyimin , nasan komai da
kikeyi bayin kanki bane irin tarbiyar da aka baki ce tunfarko ,yanzu Alhmdllh tunda Allah ya
amshi addu'ata ya shiryamin ke kindawo hanyar danake son kihau , Allah yayi Miki albarka
Sanam Allah yakuma tsaremun ke daga sharrin dukkan abin k'i , Huneed ya amsa da Ameen
cike da so da k'aunar Mummyn Sanam , cikin zuciyar sa Yana hamdalar samun sirika ta gari
abar alfahari , ......

Nan Huneed ya kwashe komai da Maryam tafad'a musu yagayawa Mummyn Twins ,. Sosai
ta girgiza dajin maganar Bata tab'a zatar abin Nafeesar zaikai hakaba , lallai Allah yanason su
tunda gashi ba'aje ko'inah ba Allah yatoni asirin ta........
[9/27, 14:29] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
‍♀️‍♀️


*NA*
*Zee MD*



*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/






*Bisimillahir Rahamanir Rahim*





Chapter 48.


Har irin Shirin da Hajiya Nafeesar take akan raba Sanam da Daddyn ta sai da

Huneed ya gaya Mata , Mummyn Twins tace " insha Allah bazatayi nasarar hakan ba , inaso ki
kwantar da hankalin ki k'arshen makircin tane yazo shiyasa tashirya muku wannan Shirin nata ,
gashi kuma ta dalilin hakan nata Shirin duk zai wargaje , Nan sukaita tattauna akan irin
abubuwan da Hajiya Nafeesar ta ke k'ullawa , Sai bayan sallar la'asar sannan Huneed ya yiwa su Mummy sallama tare da sheda musu
gobe da Asuba zai koma kan aikinsa , Nan Mummy tayi Masa addu'a tare dayi Masa godiya
akan yadda ya jajurce akan lamarin Sanam ,. ..

Sanam har jikin Motar ta rako Huneed Nan suka tsaya , duban ta yayi yace " My wifey zan
koma kan aikina Ina buk'atar addu'ar ki , Sanam ta dubesa tana kashe idanu cike da kissa tace
" My Soja shigowar ka cikin rayuwata Babban Alkairine , Kai d'in agareni Babban jigone Dan
haka addu'ata a Koda yaushe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login