Showing 57001 words to 60000 words out of 80926 words
da nafara ganin farin ciki d'auke a fuskar Mummy , Abinda yaban
mamaki ko fad'an data saba yimin yau naga bayayi ba , lallai naji dad'in wannan yanayin kuma
indai hakane daga yau zan dunga kawo mata ziyara kodan inga K'annena , Huneed cike da jin
dad'i yace " ai dama Mummy Twins bata da laifin komai Bby , kece bakya zuwa ki gaida ta
shiyasa takejin rashin dad'i , suna tafe suna hira wacce duk akan maganar zuwa gidan Hajiya
Maimuna ce har suka k'araso gida......
Suna shigowa harabar gidan basu dad'e ba Huneed yayi mata sallama yatafi......
Sanam sai da taga fitar sa daga cikin gidan sannan ta juya ta nufi ciki , tana shigowa cikin
palor tasamu Fahad da Maryam suna ta wasan banza , had'e fuskar ta tayi dan ta tsani
wannan k'azamar rayuwar da sukeyi , zata wuce kenan Maryam ta mik'e da gudu tana kakarin
Amai a karo na biyu , aikuwa Sanam ranta ya kuma b'aci dama d'azu da zata fita tayi mata
haka wato shine yanzu ma zata kuma yi mata , to wallahi ko waye uban ta yau saita bar musu
gida , a fusace Sanam tabi bayan Maryam har wajen k'ofar toilet , Maryam na fitowa tayi karo
da Sanam ba wata wata Sanam ta shak'i wuyan Maryam d'in , cikin tsananin b'acin rai Sanam
tace " meye a jikina da kike rainawa kan ki hankali in kika ganni ? d'azu da zan fita kinyi min
haka yanzu ma kuma da nadawo sai ki kuma yimin , Maryam sosai taji shak'ar da tayi mata dan
ko magana ta kasayi , gashi turaren sai kuma dukan hancin nata yake wani Aman na sake taso
mata , Fahad ne ya k'araso da gudu dan ya kwaci Maryam , sai dai koda yazo Sanam bata cika
ta ba sai marin fuskar ta take tana fad'in " wallahi sai kin fad'amin abinda kikewa Amai a jikina ,
Fahad yacewa Sanam " dallah cikata dan kinga tazo gidan ku shine kikeson tozar ta ta ,
Sanam da wani mugun kallo ta bishi sannan taci gaba da tambayar Maryam akan lallai sai
tafad'a mata me tagani ajikin ta da take amai , hayaniya tayi yawa har Hajiya Nafeesa taji ta
sauko , koda tazo da k'yar ta kwaci Maryam daga hannun Sanam , Maryam ana kwatar ta
takuma shiga toilet da gudu tana shara amai , Hajiya Nafeesa ta kalli Fahad tace " meye ya
had'asu haka ? Sanam ta ja tsaki tare da barin gurin dan bata da abin fad'awa Mummy ........
Fahad yabita da harara tare da kallon Hajiya Nafeesa yace " a gaskiya wannan yarinyar
bata da mutunci , kawai dan Marry ta nufi toilet tana amai shine ta nufo ta tahau duka wai da ita
take , Hajiya Nafeesa ta dubesa tace " tabbas akwai abinda Sanam take shirin yi , dan nima
yanzu tagama bani mamaki wai itace yau harda zuwa gidan Uwar ta , yanzu nake shirin
sakkowa na fad'a maka har status tayi ita da Twins d'in su , Fahad yace " tabb lallai kina Ruwa
Aunty kina nufin kicemin Yanzu Sanam tafara son Mahaifiyarta kenan ? Hajiya Nafeesa tace "
ga alama nafara gani kuwa , ba wanda yake had'a wannan muna funcin kamar shegen yaron
nan , Fahad yace" kawai kibamu aiki akan sa wallahi zamu rabasu nida Maryam , fitowar
Maryam daga Toilet yasa dukan su suka fara duban ta , Hajiya Nafeesa tace mata " sannu kinji
kiyi hak'uri da abinda tayi miki , Maryam tace " babu komai Hajiya koni ce abinda zanyi kenan ,
kuma wallahi turaren data sane bayamin dad'i , inajin sa sai naji Amai yatahomin shiyasa ,
Hajiya Nafeesa tace " cikin jikin kine bayaso tunda kinga masu ciki sunajin irin hakan , abinda
nakeso dake kawai kidaina zama a palor gudun irin haka , kuma indai kina yin haka to lallai
shirin mu zai lalace , dan Sanam tana da hankali dole zata gano akwai wani abu a k'asa ,
Maryam tace " zankiya ye dama ba sosai muke had'uwa da ita ba , Dawowa cikin palor suka
zauna sannan Hajiya Nafeesa ta dubesu tace " Maryam inaso kiyimin wani aiki , Maryam ta
dube ta sannan tace " fad'i ko wanne irin aiki kikeso zanyi miki , Hajiya Nafeesa tace " tunda
kinsan wannan k'awar Sanam d'in inaso kiyi min aiki akansu , zan samo number Huneed da ita
Diyana a wayar Sanam zaki had'amun su , Maryam ta dubi Hajiya Nafeesa tace " ki fahimtar
dani ban gane me kike nufi ba ? Hajiya Nafeesa tace " inaso Kisan yadda za'ayi Huneed yaje
k'ofar gidan su Diyana , sannan itama Diyana ta fito wajen sa ayi musu hotuna a turawa Sanam
yadda zamu saka mata tsanar su , nasan wace ce Sanam akan kishi mutuk'ar taga wannan pic
d'in zata d'auka gaske ne , Maryam tayi wani shu'umin Murmushi tace " ki kwantar da hankalin
ki wannan aikin ai me sauk'ine kisa aranki kamar anyi angama , murmushi Hajiya Nafeesa tayi
sannan tace " yau Jarumata shiyasa nake yinki saboda kaifin basirar ki , Fahad yace " shiyasa
kika ga na zab'o ta akan tayi mana wannan aiki dan ita kad'ai ce zata iya , nan wayar Hajiya
Nafeesa tashiga k'ara ta mik'e tana barin gurin dan tayi waya da Alhaji Abba , .......
Sanam tana hawa sama toilet ta fad'a tayi wanka sannan b'acin ran nata yaragu , amman
cikin ranta ta shirya ciwa Maryam mutuncin da har sai tabar musu gida , kayan baccin ta tasa ta
haye gado tana me d'aukar wayar ta ,......
Hajiya Nafeesa tana d'aga waya tafara yiwa Alhaji Abba shagwab'a , tuni ya rud'e yana
fad'in " kodai nadawo muyi rainon cikin tare ? murmushi tayi cike da kissa sannan tace " basai
kadawo ba yallabai na , nafiso kadawo kaga bby boy kawai an haifosa , Alhaji Abba yace "
haba Mummyn Sanam ayimin afuwa dai nadawo naganki da ciki , dan inaso naga yadda ciki
zaiyi a jikin ki nasan zakiyi kyau sosai , Hajiya Nafeesa tuni tsoro ya cika mata ciki , cikin
zuciyat ta tashiga fad'in "ina zanso kadawo ai asirina ne zai tonu mutuk'ar kadawo , maganar
sace ta katse mata tunanin datakeyi " yanaji kinyi shuru ko da matsala ne ? da sauri tace " babu
matsalar komai Dear kayi zaman ka indai cikine zanyi maka video sa da kuma hotuna in turo
maka , murmushi Alhaji Abba yayi sannan yace " shikenan ai daman cikin bayaso nagansa
tunda saida ya koreni sannan yazo , haka suka ci gaba da hirar su kafin daga k'arshe suyi
sallama.......
*Bayan kwana biyu*
Maryam bata k'ara yadda sun had'u da Sanam ba , itama kuma Sanam d'in bata bin takan su
saboda karatun dayasha mata kai , kuma a wannan lokacin Hajiya Nafeesa tayi nasarar samo
number Huneed da ta Diyana a wayar Sanam , tana samowa tasamu Maryam ta tura mata
tare da ce mata tana jiran ta da kyakkywan result , .... Maryam tuni ta shiya yadda zatayi aikin batare da tasamu matsala , unguwar su ta nufa
sanye da nik'af tana zuwa tasamu wani me shago dake kallon gidan su Diyana , tana zuwa ta
d'age nikaf d'in tana duban sa , Deeni yana ganin ta ya washe baki yana fad'in " Hajjaju Maryam
ashe kina nan kwana biyu bakya lek'omu , murmushi Maryam tayi sannan tace " Ina nan Malam
Deeni yagari ya yan gari inason muyi wata magana in badamuwa , Deeni ya washe baki yana
fad'in " ina sauraron ki hajjaju , Maryam ta kalli gefe da gefen Unguwar tasu taga babu kowa
sannan tace masa " Diyana tana siyayya agurin kane ? Deeni yayi d'an dum sannan yace "
Diyana kullum tana siyayyan Fresh yo guda biyu , wani lokacin ma in bata zo ba da kaina
nakan aika mata , wani murmushi Maryam tayi sannan tace " dan Allah inaso kamin wani aiki
kafad'i nawa zan biyaka , Deeni yace " wanne irin aiki kenan Hajjaju ? nan Maryam ta d'auko
wata k'waya ta bawa Deeni tace " wannan kawai nakeso ka sawa Diyana a cikin lemon datake
siya , Deeni ya zare ido kad'a yana fad'in " kinaso nayi kisan kai fa kenan ? Maryam tace "
bawani kisan kai da zakayi kawai dai zata d'an bugu na wani lokacin kai kuma zan baka dubu
hamsin , Deeni mayen kud'ine shiyasa Maryam tazo wajen sa , dan tasha wucewa tagansa shi
da Diyana suna hira ko kuma taga Diyana ta siyo lemo a wajen sa , da wannan tayi amfani da
kuma son kud'in Deeni , take ta curo Dubu Hamsin tabawa Deeni sannan sukayi sallama akan
anjima zata dawo inyayi mata aikin , .......
Acan gidan su Sanam itama ansa mata k'wayar bacci a cikin lemon ta , kuma tana dawo
wa daga sch taci abinci tasha lemon ba 'ajima ba bacci yayi awon gaba da ita , tuni Hajiya
Nafeesa tazo ta kashe wayar Sanam d'in tare da ajiye ta a k'asan filow......
Diyana kamar kullum ta nufo wajen Deeni domin ansar Fresh Yo d'in ta , tana zuwa sukayi
wasa da dariya sannan ya d'auko ya mik'a mata , nan tace masa " yanzu kud'in ka sun kai nawa
kenan ? yayi murmushi yana fad'in " zan duba list hajjaju ai baki ansa dayawa ba , daga haka
Diyana ta ansa ta nufi cikin gida.....
Nan Deeni ya kira Maryam a waya ya sheda mata aiki ya kammalu , Maryam tayi
murmushi sannan ta d'au waya takira Hajiya Nafeesa tace " ina fatan Sanam taui baccin da
mukeso tayi yanzu ? Hajiya Nafeesa tace " tuni tayi bacci kawai ke nake jira kifara aiwatar
danaki aikin , nan Maryam takashe waya tashiga neman number Huneed , sai da ta kira kusan
sau uku sannan ta ya d'aga yana fad'in waye ? Maryam ta gyara murya tamkar me kuka tace "
K'awar Sanam ce dama Sanam ce tazo gidan mu kuma naganta bata cikin hayyacin ta , sai
wani sambatu take dan Allah kataimaka kazo ka maida ta gida , cike da tashin hankali Huneed
yace " wacce unguwa gidan naku yake ? nan tashiga yi masa kwatance tiryan tiryan , ...
Yana kashe waya Maryam ta fito daga gidan su ta nufi motar da suka zo da ita , take ta
shedawa Fahad abinda ake ciki nan ya shedawa me d'aukar hoto ya fito dan yafara aikin sa ,
bayan kamar minty 13 sai ga Motar Huneed ta shigo cikin unguwar su Diyana , take Maryam ta
lab'e tana kiran number Diyana , tana d'agawa Maryam tagane kwayar da tasha tafara aiki dan
wata iriyar magana ta shiga yi , Maryam tace " kifito k'ofar gidan ku Sanam ce inaso muyi
magana yanzu , Diyana tana cikin maye tace ganinan zuwa shegiyar Besty ta ashe kina gari ,
Maryam tuni ta kashe shikuma Huneed yashiga kiran wayar Maryam d'in dan ya sheda mata ya
iso.........
[9/27, 10:08] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 38.
'Dagawa Maryam tayi tana fad'in ganinan fitowa , Huneed ya fito daga motar yana
gyara tsayuwar sa a jikin motar , baifi minty 2 da tsayuwa ba sai ga Diyana ta fito rik'e da gyale
a hannu ta tana had'a hanya , kana ganin ta kasan ba a hayyacin ta take ba saboda yanayin
yadda take , Huneed ya tsallako batare da ya kula da yanayin da Diyana take ba , tambayar ta
yashiga yi yana cewa "ina Sanam d'in take plss ? tuni su Fahad sunfara aikin d'aukar hoto
batare da Huneed ya lura ba , Maryam wayar ta ta d'auko tashiga yin video tana murmushi ,
Diyana kallon Huneed take tana dafe kanta tare da nazarin tambayar da yayi mata akan ina
Sanam , duban sa tayi sannan tace " wace Sanam kuma kaima waye ? mamakine ya cika
Huneed to ba itace takirasa tagaya masa cewa Sanam na cikin wani hali ba yazo , gashi yanzu
kuma tana ce masa wace ce Sanam , kafin Huneed ya dawo daga tunanin dayake yaji Diyana
a jikin sa ta fad'o , da sauri ya rik'e ta tare da fad'in " subhanallah yana dube dube ko zai ga
wani a shigar da ita gida , hango su Fahad yayi a tsaye duk da Fahad d'in yasa face mark ya
rufe fuskar sa , sannan yasa Glass suna ganin ya kallesu suka yi saurin waske wa suna juyar
da fuskokin su d'aya gefen , Huneed jiyayi kawai gaban sa ya fad'i kawai yaji yana zargin
wad'an da yagani , Da sauri su Fahad suka shige motar suka gudu dan yadda suka fahimta
Huneed yaganesu , Maryam ta maida Nikaf d'in ta tare da nufar wajen da Huneed yake rike da
Diyana , da saurin ta take fad'in " Subhanallah meyafaru haka Malam ? Huneed yace " yauwa
dan Allah shigar da ita cikin gidan nan wlh bansan meyafaru da itaba take hakan , Maryam na
rik'e Diyana tana fad'in " wayyo Allah sannu Diyana muje ciki , Huneed tuni ya tsallaka ya shiga
motar sa dan so yake ya gano meyasa mutanan nan suka gudu da suka gansa ? sosai yake
gudu amman yarasa hanyar da sukayi , tuni zuciyar sa ta yanke masa akan yaje gidan su
Sanam dan ya tabbatar da lafiyar ta , .
Maryam tana ganin tafiyar Huneed tayi saurin kiran Fahad a waya , yana d'agawa tace " ku
canza hanya wallahi daga ganin Guy d'in nan ku ya biyo , kuma tabbas yakama ku to shirin mu
zai lalace nima yanzu zantaho , tana kashe wayar ta shigar da Diyana cikin gidan su tare dace
musu ganin ta tayi zata fad'i a waje , Maryam ba b'oyayyiya bace a gidan su Diyana nan suka
mata godiya tafito tabarsu........
Huneed yana zuwa gidan su Sanam me gadi ya bud'e masa ya shigo , tambayar me gadin
yayi Sanam na cikin gidan kuwa ? me gadi yace " tabbas Hajjaju tunda ta shiga gida haryanzu
bata sake fitowa ba , Huneed yace " taje Sch ne yau ? Me gadi yace " taje shine tunda tadawo
bata sake fita ba , nan Huneed ya shige tare da yin parking d'in motar sa ya fito , kiran wayar
ta yashiga yi sai dai haryanzu a kashe yake jin ta , yana tsaye yana ta kai kawo tare da tunanin
meyasa Sanam ta kashe waya yasan dai ba rashin caji ne yasa wayar taje a kashe ba , me yi
musu aiki yagani ta fito da alamar aiken ta akayi , kiran ta yayi ya ce mata ta kira masa Sanam ,
jim tayi sannan tace " Bacci take tund'azu , yanzu ma haka daga d'akin ta nake naje shigar
mata da kaya , Huneed yayi hamdala jin Sanam na gida tana bacci ya tabbatar da lafiya take ,
nan ya shiga motar sa yafara nazarin lallai akwai wata a k'asa , tabbas wani abu ake shirya
masa wanda akeso a saka shi a rud'ani , amman dole zai bibiyi number da aka kirasa dan gano
ko wacece tayi masa hakan ........
Tuni su Maryam da Fahad sun dawo gidan sun samu Hajiya Nafeesa tare da hotunan da
Video , wata shewa suka shigayi suna dariyar mugunta, Hajiya Nafeesa tace " yau zanyi bacci
harda minshari dan nasan k'arshen Halak'ar su tazo , babban burina shine naga shegu biyun
nan basa tare da Sanam , wannan kad'ai zaisa komai mukayi mata yakama ta , yanzu wannan
sabon sim d'in zaki d'auko ki saita whaspp dashi ki turawa Sanam Videon nan da hotunan ,
tana ganin su komai zai rikice dan nasan Sanam farin sani tana da kishin masifa , musamman
aka abinda takeso dan tasha cemin zata iya rabuwa da kowa akan abinda takeso , dariya
sukayi su dukan su suna fad'in kice muna da ganin game , Hajiya Nafeesa tace "