Showing 12001 words to 15000 words out of 80926 words
ya kama Sanam wato ita yagama horata shikuma gashi nan sai wani farin ciki
yake abinsa , wani murmushi yasaki yana fad'in " kinsan Allah na matsu sosai na ganki ,
gaskiya kiyi ki tattaro ki dawo Nageria , ko mai akace masa daga can b'angaren yace " habawa
ai ba wacce ta isa ta kwace miki ni , kinsan matan Abujan yawancin su duk garorine , gasu da
rashin tarbiya uwa uba kuma akwai su da iya bin saurayi , Sanam ji tayi tamkar ta rufesa da
duka dan tasan wannan magan ganun da ita yake , haka ta k'yalesa tanaji yana ta zubawa
Budurwar sa luv , har wata shagwab'a yake yi mata tamkar k'aramin yaro , a haka har suka
k'araso cikin Estate d'in su , lokacin har ankira sallar magriba haka ya ajiye Sanam tare da cewa
" daga yau nake so naga kinfara aiki da abinda nace miki , rashin hakan zai tabbatar min da
cewa bakiji magana ta ba , rashin jin magana ta kuma tamkar kin k'ara ansar hukunci na ne ,
kuma inaso kisani in ma kin fad'awa Iyayenki babu abinda aka isa ai min sai dai ma ki saka
kanki a wata babbar matsalar , in kunne yaji to jiki ya tsira zaki iya fita sai wani lokacin , A
hankali Sanam ta bud'e motar ta fice batare da tayi magana ba , tana fita ya ja motar sa da
gudu ya nufi gidan su dan sauri yake yaje yayi sallah tunda ankira........
Lokacin da Sanam ta zo k'ofar gate bugawa tayi da hannun ta , megadi yana sallah lokacin
haka ta ci gaba da bugu har ya idar yazo ya bud'e mata , yana ganinta ya zube yana fad'in "
kiyimin rai hajjaju wallahi sallah nake shiyasa banzo na bud'e ba , kuma banji k'arar motar ki ba
shiyasa tuba nake , wuce wa tayi batare da tace masa kanzil ba har ta shige k'ofar falor su ,
binta yayi da kallo yana mamakin yanayin ta , cikin ransa yana addu'ar Allah yasa dai lafiya .......
Sanam na shiga cikin falor sukayi ido biyu da Fahad , da sauri ya mik'e yana fad'in " Oyoyo
my Special ina kikaje haka ? tunda nazo nake cigiyar ki banji kiba , daurewa kawai Sanam take
dan kanta ne yake ciwo sosai , murmushi tayi sannan a hankali ta furta " na d'an je gidan su
k'awata ne dafatan kazo lafiya , Fahad ya rik'o hannun ta yana fad'in " lafiya lau nazo My
Special me yasa me kine naganki haka ? Sanam ta zame hannun ta a hankali tana fad'in kaina
namin ciwo bari na hau sama , bata jira amsar da zai bata ba ta haye sama abinta......
Da ido Fahad yabi bayan ta ana had'iyar wani mugun miyau , cikin ransa yake yaba tsarin
halittar da Allah yayi wa Sanam , dan duk iya yawon dayayi k'asa she baiga mace me dirin jikin
Sanam ba , dan haka ko tak'i ko taso dole yasha romonta .......
Huneed yana shiga gida ya fad'a toilet yayi wanka tare da d'auro arwala , yana fitowa ya
nufi masallaci lokacin har sun tada sallah , bayan an idar yayi lazimin sa da yasa ba sannan ya
taso ya shigo cikin gida abinsa , samun Hajiyar su yayi ita da Hisham suna hira abinsu cike da
so da k'auna , shima zama yayi suka ci gaba da hirar abinsu , sai bayan sallar isha'i sannan
suka ci abinci ya fito , Hisham ne ya biyosa yana cewa " wai Ya Huneed yaya ta kasance kai da
Sanam ? murmushi Huneed yayi sannan yace " nakuma saka mata doka ta biyu inaso naga
yadda zata kuma karya ta , murmushi Hisham yayi yana fad'in " Wannan yarinyar kuwa zata iya
bin doka ? amman bari dai mugani nan da gobe ko zata iya , Huneed yace " inaso ka d'auki
motar ta ka kaimata gidan su ga wayar ta nan ka had'a mata da ita , Hisham yace " to shikenan
bari na kai mata na dawo , Huneed ya shiga motar ya fice dan akwai wasu aiki da xaije
dubawa........
Koda Hisham yakai motar gidan me gadi yabawa yace ya shigar mata dasu , me gadi ya
ansa da mukullin da wayar ya nufi cikin gidan dasu .......
Tunda Sanam ta hau sama wanka taje tayi ko sallah batayi ba ta haye gado ta kwanta ,
sai dai me tana rufe idon ta hoton Huneed ne ke yawa a cikin idanun ta lokacin da ya ke fincikar
ta yana shiga da ita cikin gidan , hawaye ne taji yana bin kuncin ta tabbas Huneed ya karya
mata record d'in ta , itace harda yin fitsari itace har dayin wanki , ga uwa uba kukan data sha
tamkar ranta zai fita , tabbas batason dame zata rama abinda Huneed yayi mata ba , tunani
tatafi akan yadda zata rama abinda yayi mata har bacci yayi gaba da ita......
Fahad ne ya hawo sama dan kawo mata wayar ta da mukullin motar , yana shigowa d'akin
nata yaganta tana bacci duk ilahirin cinyoyin ta a waje , gashi saman k'irjin ta ya bayyana duk
da gashin kanta ya rufe wani wajen , wani miyau ya had'iya tare da nufo gadon yana jin D
d'insa na mik'ewa , Hawowa yayi cikin sand'a tare da nufar ta dan yadda yakejin kansa bazai
iya rik'e sha'awar saba , turo k'ofaf da akayi shine ya dakatar dashi yana wai wayen yaga waye
wanda yashigo..........
*Bana ganin Comment fa*
*'Yar Mutan Kanawa* _Ce_
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 10.
Hajiya Nafeesa yagani tsaye a bakin k'ofa , sauko wa yayi daga gadon yana sosa
k'eya , duban sa tayi tace " me zakayi mata ? k'asa yayi da kansa yana fad'in " sorry My Aunty
babu komai kawai yarinyar ce tahad'u sosai , Hajiya Nafeesa tace " amman karka manta yau fa
kazo kabari aikin da zamuyi yafara tafiya , yanzu in ka haike mata sai ka b'ata komai na shirin
namu , Fahad yace Shikenan za'a kiyaye hakan insha Allah , fitowa sukayi daga d'akin tare da
janyo mata k'ofah suka sakko.....
Washe gari .
Sai wajen k'arfe sha d'aya Sanam ta sauko cikin kwalliya tare da trolly ta matafiya , lokacin
Hajiya Nafeesa da Fahad suna zaune a falor suna hira , suna ganin ta suka tsaya suna kallon ta
, dan iya had'uwa Sanam ta had'u tamkar itace ta tsara kanta , sai da ta k'araso sannan suka
d'auke kansu da ga kallon ta , Sanam ta k'araso jikin Hajiya Nafeesa ta rungume ta sannan tace
" Mumy yau zanbar k'asar nan inaso tafiya Turkey saboda zuwa na da wuri yana da amfani ,
Hajiya Nafeesa jitayi kamar ta shak'e Sanam d'in kowa ya huta , a fili kuma tace " haba My
Dauther kibari mana bikin yataho basai ki tafi ba , kodai wani abun akayi miki da kikeson
guduwa kibar mu ? Sanam a cikin ranta take fad'in " tabbas ina buk'atar yin tafiyar kwana biyu
ko dan wannan azzalumin mutumin , mutuk'ar tana gari to tabbas zata biya ko nawa ne aje a
kashe mata shi , tunda take a rayuwa ba'a tab'a yi mata abinda yayi mata ba , shurun da tayi ne
yasa Hajiya Nafeesa fad'uwar gaba , cikin ranta take ayyana kodai Sanam tajisu jiya da
daddare ne ? da sauri ta dubi Fahad tayi masa wata inkiya da idanu , shima hakan yayi mata
sannan Hajiya Nafeesar ta katse shurun da cewa " Haba My Dauther na d'auka ina da
muhimman cin da zansan dukkan damuwar ki ? ashe ba haka bane ! idan wani ne ya shigar
miki rayuwa yana da kyau ki fad'amin mud'au mataki akansa , Sanam tace " babu komai fa
Mumy kawai inaso in tafi da wuri dan Rauda tace sainaje zatayi komai , wata a jiyar zuciya tayi
sannan tace " to shikenan hakan ma yayi kyau , yanzu yadda za'ayi ki kira Daddyn ki ki sheda
masa kin janyo tafiyar yau kikeso , in kina buk'atar rakiya ga Uncle d'in kinan sai yaraka ki ,
Murmushi Sanam tayi sannan tace " munyi waya da Daddy tunda asuba kuma ya amince intafi
yau , Fahad yace " to bari na had'o kayana mutafi tare nima naga gari , murmushi Sanam tayi
sannan tace " Uncle ai dama kayi zamanka tunda nima ba wani dad'ewa zanyi ba , kuma kai
daka zo hutawa ai baka kuma shan tafiya ba , Sanam kwata kwata jininta bai had'u da Fahad
ba , tun tana k'arama in yazo gidan bashi da aiki sai rungumar ta da yi mata wasanni wad'an da
bata so , dan haka bata shiri dashi ko yaushe ta gansa sai ta tsiri fita kullum.....
Ganin Sanam bata son tafiya da Fahad yasa Hajiya Nafeesa tace " to shikenan amman
yana da kyau kije gidan Hajiya Maimuna kiyi mata sallama , Sanam tace " sauri nake Mumy
kuma yanxu haka saura minty sha biyar jirgin mu yatashi , tana fad'ar hakan ta mik'e daga jikin
Hajiya Nafeesa tana fad'in " Miss u so much my Mumyna , bye sai munyi waya ki kula min da
kanki Mumyna , Hajiya Nafeesa cike da kissa tace " Miss u so much my luvly Allah yatsare min
ke , Fahad ya mik'e yana fad'in " kawo trolly d'in naki na rakaki airpot d'in tunda ba'ason nayi
rakiyar can d'in , murmushi Sanam tayi sannan tace " haba Uncle kana Abbana zan baka rik'on
Trolly ? kabar shi kawai ai ina fita zansa a bayan mota , haka suka fito dukan su har jikin mota
sannan Fahad ya shiga wajen direba ya zauna tare da cewa ta shigo ya kaita airpot d'in , sake
rungume ta Hajiya Nafeesa tayi sanna tayi mata adawo lafiya ta shiga motar Fahad yaja suka
tafi.......
Huneed koda yaje bacci kasa bacci yayi saboda tunanin Sanam , tabbas yarinyar tafara
shiga ransa , sai dai gaskiya yanayin tarbiyar ta baya burgesa ko kad'an , inda zai ga iyayen ta
tabbas sai yayi musu gyara sosai a cikin rayuwar su , dan yakamata ace sun bata tarbiyar da
za'ayi alfahari da ita a matsayin ta na 'Ya mace , a haka bacci yayi awon gaba da shi me cike
da mafarkin Sanam kala kala......
Washe gari wajen sha d'aya na safe ya fito waje yana zaga Estete d'in nasu , can ya
hango motar Sanam tataho a hankali batare da wannan gudun na hauka ba , mamaki ne ya
kamashi na ganin tabbas ta fara d'aukar horonsa , bai gama tunani ba motar tazo giftawa ta
kusa dashi , anan ya hangi wanda yake tuk'in ashe ba Sanam d'in bace , sai dai itama ya
hango ta tana cikin motar tana danna wayar ta , cikin ransa yake fad'in " wannan d'in shikuma
waye ? take wani kishi ya ziyarce shi wanda bai tab'a jinsa ba ko akan Fateema wacce zai aura
, da sauri ya nufi cikin gidan su dan d'auko motar yabi bayan su dan kwata kwata bai yadda da
guy d'in ba .......
Fahad suna tafe yanajin music ya dubi Sanam yace " Baby yanzu kuma sai yau she zaki
dawo ? Batare da ta dube sa ba tace " inason inyi 2 weeks kawai , in kuma na zarta to babu laifi
dan can ma gidane , Fahad yace " gaskiya bazan iya jure rashinki har 2 weeks ba , ki taimaka
min kiyi 1 weeks kidawo kinji Baby , murmushi Sanam tayi tare da mamakin maganar Fahad
d'in , a cikin ranta tace kaji mun Uncle sai kace wata budurwar sa wai zai yi missing d'ina , a fili
kuma tace " kamar yaune ai Uncle kuma ai zamuyi waya , Fahad yawani shagwab'e baki
tamkar yaro yana fad'in " My BBy ki kulamin da kanki karki kula kowa kinji , Sanam tace " zan
kula . Daga haka tayi shuru bata sake magana ba har suka k'araso air pot......
suna zuwa dai lokacin aka fara kiran sunayen matafiya , Daddyn ta ta hango yana
murmushi ya nufo ta bayan sa body quart suna biye dashi , da sauri ta nufi wajen daya ke
itama tana murmushi , tana zuwa ta fad'a jikin sa ya rungume ta sanna yace " bazan iya zama
banzo munyi sallama da My One and Only d'ina ba , Murmushi Sanam tayi tana fad'in " nasan
hakan Daddyna Abin k'auna ta , jin ankira sunan ta yasa ta saki Daddy tana fad'in " Miss u my
Daddy so much , ta sumbace shi a kunci sannan ta nufi hanyar wajen hawa jirgin , tanayi tana
wai wayen su tana d'aga musu hannu har ta k'ule......
Duk abinda akeyi Huneed na tsaye yana kallon Sanam har ta k'ule , cikin ransa ya furta "
wato zaki bar k'asar kenan kije ki k'ara koyo wasu banzayen halayyar , duban wajen dasu
Daddyn nata suke yayi suna tsaye har lokacin suna magana da Fahad , takawa Huneed yayi
har wajen da suke yayi musu sallama tare da gaisar da Daddy , amsawa yayi cike da kulawa
yana fad'in " kamar Canal Huneed Abdallah ko ? Huneed yayi murmushi sannan yace " nine ,
Daddy yace " masha Allah ya fama da gwagwar maya ? kuna k'ok'ari sosai Allah yabiya ku ,
Huneed yace " Ameen ya Allah nagode da addu'a , nan suka wuce shikuma ya tsaya yana
dube dube , Huneed ya tsaya ne yana son sanin wacce k'asa Sanam tatafi ? yanaso yasan
k'asar da zataje da kuma dalilin ta na tafiya , cikin wajen ya shiga ya nufi office d'in ma'aikatan
jirgin , yana zuwa dayake dayawa sun san shi bai sha wata wahala ba suka sanar dashi garin
da jirgin ya nufa , take Huneed yasamu kansa da biyan kud'in visar k'asar Turkey shima
zaije......
*Tofah Sanam kinsamu cingum*
Tunda Sanam ta isa garin Turkey takejin wani nishad'i na ratsa ta , ba komai take tunawa
ba sai rayuwar datayi a garin , tuni Rauda sunzo airpot d'aukar Sanam dan ta sanar mata da
zuwan ta , ai suna ganin juna Sanam suka fara murna tare da tahowa da gudu suka rungumi
junan su ......
*Comment plss*
*'Yar Mutan Kanawa* _Ce_
[9/27, 09:42] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association*
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
Chapter 11.
Rauda ta dubi Sanam tace " kinga yadda kika koma kuwa ? murmushi Sanam tayi
sannan tace " haba my R ke bakiga yadda kika koma ba saini , Rauda ta rik'e mata hannu tana
fad'in " aini dole na canza tunda nasha gyara haryanzu ina shan gyaran , haka suka k'arasa
wajen motar cike da so da k'auna suna tafe suna hirar yaushe gamo .......
Rauda k'awar Sanam ce tare sukayi karatu tun datazo turkey , sun shak'u sosai har takai
iyayen su sun san da wannan shak'uwa tasu , Iyayen Rauda 'yan asalin Nageria ne amman
suna zaune a Turkey anan suke aikin su , da