Showing 78001 words to 80926 words out of 80926 words
Abba na rungume da yaro sai kallonsa yake Yana Murmushi , duban ta yayi sannan yace " nifa
haryanzu narasa da wa wannan yaron yake kama , Hajiya Nafeesa jitayi gabanta ya fad'i
Amman sai ta dake tace " haba Alhajina wannan yaron ai kana ganin sa anganka , Murmushi
kawai yayi Dan bai ga ta inda suke kama da yaron ba , duk yadda yataho Yana d'okin yaron
Yana ganin sa yaji bai kwanta Masa Rai ba sab'anin sauran yaran sa , Hajiya Harira ce ta sauko
daga sama tana fad'in" kaga iyayen yaro kunsa shi agaba tamkar za'a k'wace muku shi , zama
tayi kusa da Hajiya Nafeesa tana fad'in " sonake nazo na wuce gida tunda na kammala Miki
komai , Hajiya Nafeesa ta dubi Hajiya Harira tana yi Mata alama da ido ya sukayi da su Goga ?
Ta bud'e baki zatayi magana sai ga su Sanam da Mummyn ta da Hajiya Babba da Diyana sun
shigo , Bayan su kuma Maryam ce da Bahijja da kuma Mahaifiyar Bahijjar , a zabure Hajiya
Nafeesa ta mik'e ita da Hajiya Harira suna kallon juna .........
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
ν Ύν΄¦ν ΌνΏ»ββοΈν Ύν΄¦ν ΌνΏ»ββοΈ
*NA*
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*ν ½ν³
( Domin Marubuta Mata )
β¨ (W.W.A) β¨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Alhamdulillah ! Alhamdulillah !! Alhamdulillah !!!
Chapter 50.
Da sauri Bahijja ta nufi wajen da Alhaji Abba ke zaune rik'e da jariri a hannu , tana
zuwa tace " bani d'ana mugaye azzalumai , Alhaji Abba cike da mamaki ya dubi Bahijja
sannan ya Kai duban sa ga Hajiya Nafeesa wacce zufa ke tsatstsafo Mata , duk irin yadda
na'urar ac. Ke aiki Amman Hajiya Nafeesa gumi take, kafin yayi magana 'yar sanda mace ta
shigo tare da nufo Hajiya Nafeesa da ankwa tana fad'in your onder arrest , sai a lokacin bakin
Alhaji Abba ya bud'e yafara magana " Wai meye yake faruwa zaku shigo min cikin gida batare
da izini na ba kuma kuna neman tafiya da iyalina , 'yar sanda ta dubi Alhaji Abba tace "
kabiyomu office duk sai kasamu wannan amsar tambayoyin naka , take suka ingiza Hajiya
Nafeesa a gaba zuka nufi fita da ita , Hajiya Harira na k'ok'arin guduwa Huneed ya rik'eta tare
da mik'awa 'Yan sanda ita yace itama suje da ita , ...
Koda Hajiya Nafeesa tazo wucewa ta gefen da Maryam da sauri Maryam ta tare ta tace "
Allah ya tsareni daga sharrin ki tun lokacin da kika shirya kasheni nake harkance dake , duk
wani motsin ki akan idanuwa na kike shiyasa Nima na shirya Miki nawa Shirin , inaso kuma inyi
Miki albishir akan duk wani Shirin ki da kikeyi akan Sanam tasan komai , zare idanu Hajiya
Nafeesa tayi Maryam tayi wani murmushin takaici sannan tace " ki k'arewa gidan Nan kallo Dan
da alama ba lallai ki dawo ba , tuni akayi gaba da Hajiya Nafeesa wacce tuni tafara zubar da
hawaye.....
Alhaji Abba har yanzu ganin abin yake kamar al 'amara , Nan su Huneed suka zaunar
dashi sannan Huneed ya umarci Maryam data fad'i duk irin Shirin Hajiya Nafeesa da yadda ta
kawo ta gidan , Nan Maryam tashiga karantawa Alhaji Abba komai da dukkan irin makircin da
Hajiya Nafeesa ta shirya Masa , Banda kalmar Innalillahi Babu abinda Alhaji Abba ke Mai
maitawa , Nan aka Kira Fahad a waya akan anasan ganin , dayake baisan komai ba haka ya
nufo gidan kansa tsaye...
Sai da ya shigo sannan yaga abinda yake faruwa agidan , Nan Alhaji Abba yasa shi agaba
akan shima yanaso yaji komai daga bakinsa , Fahad ba yadda ya iya tunda akan kamasu da
laifi dumu dumu haka ya gayawa Alhaji komai da Yayar tashi take k'ullawa , wani abun da
Maryam d'in ma Bata fad'a ba shi Fahad sai daya fad'awa Alhaji Abba , wani jiri Alhaji Abba
yaji Yana d'ibarsa daga zaune , da sauri Sanam ta k'arasa tana rik'eshi da sauri , duban ta yayi
cike da so da k'auna ya rungumeta Yana kuka , cikin zuciyar sa Yana tirr da halin Hajiya
Nafeesa wacce yaji yanzu a duniya ba wanda ya tsana sama da ita , ....
Kukan Maryam ne yadawo dasu daga shurun da akayi , rok'on Alhaji Abba gafara tashiga yi
tare da Sanam da kuma Huneed shima ,. Jaririn ta na hannun ta tana rik'e dashi , Alhaji Abba
yace " ta tashi taje ya yafe Mata , Nan ta mik'e ta fice Fahad shima yabi bayanta , ....
Suna fita Fahad yadubi Maryam yace " yanzu shikenan haka zamu tafi Babu komai da
muka samu ? Maryam ta kallesa cike da tsana tace " Dan kaga ka Sha shine kake wannan
maganar , wallahi nayi danasanin had'uwar mu dakai , gakuma d'anka Nan kasan yadda zakayi
dashi , Fahad ya kalleta shek'e k'e yace " wannan shegen d'an zan karb'a Abu mummuna dashi
, Maryam tace " koma dai meye ai jinin kane kuma dole ka anshe shi , wani mari ya sakar Mata
tare da Fara zaginta , Huneed Wanda tun fitowar su ya biyo bayan su Yana jin komai da suke
fad'a take ya kama Fahad , dama Yana so ya hukuntashi shima akan abinda sukayi Masa
shida Sanam , take yasa aka tafi da Fahad Dan shima abashi horo me tsanani .....
Maryam kuma ta nufi gidan su tare da jaririn ta a hannu.....
*Bayan kwana biyu*
Alhaji Abba yanzu ya d'an samu sauk'in abinda Hajiya Nafeesa tayi Masa , ya tattara komai
nata da yasani yayi sadarsu , komai na cikin gidan tuni yasa aka kwashe su dan ko kad'an baya
k'aunar abinda zai sa yasake tunawa da Hajiya Nafeesa a rayuwar sa , tuni ya rubuta Mata
takardar sakin ta kawai so yake yaje police station yakai Mata ,. ...
Tuni anbawa Bahijja d'an ta tare da tsare Hajiya Nafeesa da Hajiya Harira a gurin 'yan
sanda , nurse d'in da suka had'a baki da ita aka canza Yaron itama ankamota tare da tufe
Asibitin gaba d'ayanshi , ...
A can b'angaren su Sanam ransu fess sun rabu da annoba , Mummyn Twins sai k'ara
kwantar wa da Alhaji Abba hankali take , ranar da zai kaiwa Hajiya Nafeesa takardar sakin ta
Sanam tace zata bishi , aikuwa tare suka taho dashi da Sanam da Twins wad'an da sukayi
wayo , suna zuwa aka fito da Hajiya Nafeesa wacce saboda dukan datasha har ta canza
kamanni , Alhaji Yana ganin ta ya kauda kansa cike da wata iriyar tsanar ta , Hajiya Nafeesa
tana k'arasowa ta zube kan gwuiwo winta tana fad'in " Alhaji dan Allah ka yafemin wallahi na
tuba nadaina komai , Alhaji Abba ya mik'o Mata takardar ta Yana rungume da da Twins , kasa
ansa tayi jikinta sai rawa yake tana fad'uwar gaba , tana dubawa kuwa taga dakinta yayi saki
kuma har uku Babu batun komowa , rushewa tayi da kuka tana fad'in kayimin Rai Alhaji natuba
, ta juya wajen Sanam tana fad'in " Dan Allah kisa baki Daddyn ki ya yafemin , Sanam tayi
Murmushi sannan tace " Nafeesa kenan , ke aganin ki Yana da kyau a zauna da wacce zuciyar
ta Babu Allah acikin ta ? Har kisan Kai fa kikasa ayi Allah yasa asirin ki ya tonu , duk irin
abinda kikayi Daddyna ya yafe Miki sai dai bamason ki k'ara dawowa cikin rayuwar mu ,
mik'ewa sukayi Alhaji ya dubeta yace " Ina son in Gaya Miki daga yau ko me kama dake bana
son k'ara gani acikin rayuwar mu nida iyalina , nagode wa Allah da baisa na had'a zuri'a dake
ba , Yana fad'in haka yashige ya tafi shida 'Yayan sa suka bar Hajiya Nafeesa da tarin Dana
sani..........
Tuni Aka tura su Hajiya Nafeesa da Hajiya Harira da Nurse virson zaman shekara uku da
horo me tsanani ,.....
*Bayan shekara d'aya*
Tuni an saka ranar Huneed da Sanam wata Uku masu zuwa , Diyana itama lokacin aka
saka Ranar ta da wani saurayin ta Umar , Soyayya ake zabgawa tsakanin Huneed da Sanam
tamkar sukai junan d'aki , lokacin saura wata biyu da sati biyu su Sanam su kammala digree d'in
su , kuma a lokacin Huneed yasamu k'arin girma yazama Babban Major ,
Mummyn Twins sai aikin gyara 'yar ta take da kayan Mata , duk wata kunya yanzu ta cire ta
janyo 'yar ta jikinta tamkar k'awaye.....
Mummyn Twins yanzu ta ko'inah kulawa take bawa mijinta , dan Bata son Koda minty d'aya
tabada k'ofar dazai yi tunanin wata mace bare kuma ya Kai ga aurowa , ...
Alhaji Abba kuwa kwata kwata baya tunanin k'ara wani aure ma , Dan duk wata kula Yana
samu a wajen Hajiya Maimunar sa , ....
Koda Sanam tabawa Maryam kud'in da tayi Mata alk'awari k'in karb'a Maryam d'in tayi ,
sai da Sanam ta takurawa Maryam sannan ta nuna Mata ai ba komai ko jari taja dan ta rik'e
kanta , Dan tunda Maryam ta haihu tasamu lalura saboda irin wuyar da taci , tuni Maryam ta
tuba tasamu waje d'aya ta zauna tana kula da yaron ta ....
Akwana atashi yau saura kwana biyar bikin Sanam da Huneed Diyana da Umar , tun ranar
talata aka fara biki domin biki ne na 'yar gata gaba da baya , Sosai kayi b'arin kud'i Amarya
Sanam tasha kyau tamkar ita ta tsara kanta.
Duk Wanda ya d'ora idanuwa akan Sanam bazai so ya d'auke ba , gyara iya gyara tasha shi
duk inda ta gifta sai dai kaji k'amshi na tashi ,. Haka sukasha Dinner kala kala da Reception ,
nera tayi kuka Dan tsayawa fad'in irin kud'in da aka kashe da kuma kyan Ango da Amarya sukai
b'ata baki ne , ....
An d'aura auren aranar lahadi a masallaci dake cikin unguwar Asokoro Abuja , daga Nan
Sojoji suka shiryawa Ango da Amarya Babban Reception , anci ansha sannan Sojoji sukayi
wasa da bindiga tare da gwangwajewa , ....
Diyana ma a Nan gidan su Sanam akayi komai nata kuma komai tare suke , yamma nayi
aka kawo motocin d'aukar Amare , Nan Aka Kai Sanam da Diyana wajen Alhaji Abba yashiga
yi musu nasiha me ratsa zuciya , Mummy itama shigowa tayi Nan itama tayi musu nata fad'an
tare dayi musu fatan Zaman lafiya da mazajen su , Alhaji Abba ya d'auki mukullayen mota
kowacce yabata kyauta , Nan aka fito dasu kowacce aka nufi gidan ta da ita.......
Gidan Sanam dake Unguwar Maitama yagaji da had'uwa , ga Uwar dukiya da ka narka
Mata tamkar basa son kud'in ,
Bayan kowa ya watse sai Sanam a bakin gado tana kukan rabuwa da gida , Ango Huneed
ne ya shigo cikin d'akin d'auke da Manyan ledoji a hannun sa , Yana zuwa ya bud'e fuskar
Sanam Yana fad'in "My wifey wannan kukan ya isa haka Kar ki janyomin ciwon Kai , shagwab'e
Masa tayi sannan tace " My Sojana nifah gaskiya komawa gida zanyi dan Ina missing d'in Twins
, rungumota yayi jikinsa Yana fad'in " indai Twins ne Nima Ina missing d'insu Amman Wanda
Zaki haifomin a wannan cikin naki , shafo cikin yayi Yana Murmushi Sanam ta ture hannunsa
tana mejin kunya......
Wanka Huneed ya shiga bayan ya fito itama tashiga tare da d'auro arwala , Bayan sunyi
sallah ya gabatar Mata da tambayoyi akan karatun addini tabashi amsar abinda tasani , ledojin
da yashigo dasu ya bud'e musu suka Fara cin kajin da yashigo dasu , da k'yar Sanam taci Dan
kawai iya su Madarorin kwali ta dunga Sha , suna kammalawa ya d'ebe sauran ya nufi cikin
frize da su ....
Brush Sanam tayo sannan tasa wata rigar bacci tare da feshe jiki da turaruka masu
k'amshi tabi lafiyar gado , Huneed shima dashi sai boxer da singlet ya nufo gadon ya kwanta ,
Nan zance ya canza salo Dan tuni Su Ango Huneed aka Lula duniyar da ba'atab'a zuwanta ba
, sosai Huneed yayi mamakin samun Sanam a virgin d'inta , Dan ganin irin yadda ta taso
idanuwa a bud'e ga tsantsar wayewa da rashin ji sayake tuni ta bayar da jikinta , sai yasamu
sab'anin hakan , Dan haka ya shiga Samata albarka tamkar ya had'iyeta ......
*Bayan shekara d'aya*
Tuni su Sanam anzama Manyan Mata , wata irin soyayya suke itada mijin ta Huneed
tamkar Laila da Majnun , kullum suna tare ko dama tuni yadaina zuwa ko Ina saboda yanzu
yaxam Babba , Koda yaushe Yana tare da Matar sa musamman yanzu da take laulayin ciki .....
A can b'angaren Hajiya Nafeesa kuwa ansako su duk ta rame ta lalace saboda bak'ar wuyar
da suka Sha , tun a cikin virson suka rabu da Hajiya Harira baram baram , Dan haka suna
fitowa kowacce ta kama gabanta , Hajiya Nafeesa da k'yar tasamu kud'in motar da ta koma can
garinsu meduguri , Koda ta koma tuni sun samu labarin komai akanta a wajen Fahad Wanda
ya dad'e da komowa gida ,.
Tunda ta koma take fama da cutar tari , daga k'arshe aka gane ta kamu da tarin tv Dan
haka 'yan uwa kowa ya gujeta , dama data na gidan Alhaji Abba bawani zumunci take ba ko
ganin su ba zuwa takeyi ba bare ta tallafa ,shiyasa kowa ya gujeta da k'yar take samun abinci
so d'aya a Rana ,........
Cikin Sanam Yana isa haihuwa ta haifi Santalelen yaron ta me kama da Babansa , ranar
suna yaci sunanan Mahaifin Huneed suke Kiran da da Abeeh , sosai aka Sha hidima lokacin
itama Diyana ta haifi yarinyar ta data saka Mata sunan Besty ta Sanam , suke ce Mata Uktee ,
Hajiya Maimuna tuni suka koma can k'asar Paris ita da Alhaji Abba da Twins , lokacin tana
mak'ale da cikin ta k'arami Wanda keta tsokanar ta da cewa " 'Ya na haihuwa uwa nayi , ....
Zaman lafiya da kwanciyar Hankali tsakanin Sanam da Mijin ta Huneed sai abinda ya k'aru
, Koda yaushe in suna zaune sai Huneed ya tsokani Sanam farkon Had'uwar su shida ita data
fesa Masa ruwan tab'o , Nan zasuyi dariya yace " aini ruwan tab'o Yayimin Rana tunda ya
mallakamin wacce ba kowanne namiji ne zai sameta ba sai me sa'a , Nan Sanam tayi Murmushi
tace " Nima Ina godiya da samun gwarzon Namiji jajurtacce Wanda ko wacce mace take burun
samu , Alhamdulillah Allah ya kuma tsaremin Kai mijina Abin k'auna ta Uban 'Yayana kuma My
Sojana,.......
*Alhamdulillah*
*Anan nakawo k'arshen wannan littafin ina rok'on Allah kuskuren danayi a cikin sa ya
yafeminν ½νΉν ΌνΏ»ν ½νΉν ΌνΏ»ν ½νΉν ΌνΏ»ν ½νΉν ΌνΏ» Allah yasa ya amfani al'umma baki d'aya*
_Nagode sosai Masoyana da yadda kuka dunga bibiyataν Ύν΅°ν Ύν΅°ν Ύν΅° har nakawo k'arshen
wannan labari_
βν ΌνΏ»βν ΌνΏ»βν ΌνΏ»βν ΌνΏ» *Kubiyoni a sabon Book Dina me suna*
_Bazawara CE_