Showing 36001 words to 39000 words out of 80926 words
, izini ta bashi akan yabarsu su shigo....
Hajiya Halima suna shigowa ciki ta k'ara tabbatar da irin gidan da take so d'an ta ya nemo
aure , murmushi tayi tana kallon Jaydeen wanda shima ita yake kallo yana murmushin , K'ofar
palor suka tura dai dai lokacin Sanam ta mik'e zata koma sama dan wayar tasu da Huneed ta
yawaita , taga kuma kamar Hajiya bak'i tayi ita kuma batason duk abinda zai shigar musu
rayuwa , karo taci da Jaydeen tatafi zata fad'i k'asa yayi saurin taro ta jikin sa , a hankali ta
bud'e ido suka had'a idanuwa da Jaydeen , wata fad'uwar gaba ce ta ziyarci Sanam cikin
ranta ta furta wannan lokacin ma , to meya shigo dashi gidan mu har muka kuma karo haka ?
suntafi tunani su dukan su sun manta a inah ma suke sukaji gyaran muryar Hajiya Halima , Da
sauri Sanam ta turesa tana mejin kunya , sannan tayi saurin hayewa sama abinta...........
[9/27, 09:59] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*WOMEN* *WRITERS* *ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir* *Rahim*
Chapter 25.
Jaydeen yayi murmushi tare da binta da kallo har ta haye saman , juyowa yayi ya
kalli Mumyn sa sukayi murmushi tare , dai dai lokacin Hajiya Nafeesa ta sauko daga sama cikin
shiga ta Alfarma sai zabga k'amshi take , tana ganin Hajiya Halima tasaki murmushi tana fad'in
" lale marhabun da manya manya , Hajiya Halima itama tagane Hajiya Nafeesa dan sun tab'a
had'uwa so biyu , d'aya a wajen Wankin kai d'aya kuma a Dinner bikin 'yar gidan Hajiya Turai ,
dan har sunyi musayar contac kafin asace phone din Hajiya Halimar , nan suka gaisa cike da
sakin fuska tare da tambayar bayan saduwa , nan danan Hajiya Nafeesa tasa aka kawo musu
abin motsa baki , hira suka shigayi sosai shikuwa Jaydeen duk hankalin sa na wajen Sanam ,
Allah Allah yake yaga takuma fitowa dan yanason yasake ganin ta da wannan shigar , Hajiya
Halima ta dubi Hajiya Nafeesa tace " to mufa da magana mukazo akan yaron naki , murmushi
Hajiya Nafeesa tayi sannan tace " to meke tafe daku dan tunda kuka shigo naga yakasa sakin
jiki , Hajiya Halima tace " dama yarinyar wajen ki yagani sunhad'u a jirgi tun daga Turkey ,
tunda yadawo bashi da zance sai nata yau dai nasashi a gaba muka fito neman ta , to Allah
yasa muka samu gidan ashe ma yar wajen kice , Hajiya Nafeesa tayi murmushi sannan tace "
tabbas Sanam ce dan itace taje Turkey , lallai abu yayi kyau to Allah ya tabbatar mana da
Alkairi , cike da fara'a Hajiya Halima ta amsa da Ameen , sannan tace " amman ina fatan ba'ayi
mata mijiba dan karmuyi nema cikin nema , dariya Hajiya Nafeesa tayi sannan tace " bakuyi ba
dan bata kula kowa saboda karatu takeyi , wani dad'i Jaydeen yaji aransa jin ance bata kula
kowa nan ya k'udurta aransa zaiyi yadda zaiyi ganin tazama tashi shi kad'ai , sakkowar Sanam
daga sama yasa Jaydeen katse tunanin sa yq zuba mata sex eyes d'in sa , wasu kayan yakuma
gganin ta dasu wanda sukaci uwar na d'azu kyau da tsaruwa , gashi sun kama mata jikin ta
komai nata ya baiyana , jiyayi tamkar yatashi yatafi da gudu ya d'auketa cak yadunga zagayawa
da ita , ko kallon inda suke Sanam batayi ba tanufi hanyar fita daga falor , da sauri Hajiya
Nafeesa tace " My luv zo mana , Sanam ta tsaya cak tamkar baza ta zo ba sai kuma ta jiyo ta
tako a hankali , tana k'arasowa ta tsaya tana turo baki tare da cewa " Gani Mumy sauri nake
zamu fita nida Diyana , Hajiya Nafeesa tace " baki ga munyi bak'i bane zaki fita ko gaisawa
bakuyi ba , Sanam ta d'an turo baki tare da kallon b'angaren da Hajiya Halima suke tace "
sannu n ku anyini lafiya , Hajiya Halima cike da sakin fuska tace " lafiya lau My Dauther ,
Sanam bata sake bi takan su ba tayi sauri juyawa ta fice Abinta , Jaydeen tuni yatashi yabi
bayan ta dan yana son suyi magana.....
Hajiya Halima da Hajiya Nafeesa sukayi murmushi ganin yabita , Hajiya Halima taja ajiyar
zuciya tace " Allah ya dai dai tasu dai , Hajiya Nafeesa ta amsa da Ameen , suka ci gaba da
hirar su irin tasu ta manyan mata......
Sanam na fitowa tuni dama tasa an wanke mata motar , tana fitowa ta nufi wajen motar
zata shiga , da sauri Jaydeen yasha gaban ta yana fad'in " haba sarauniyar mata abin kuma
'yar haka ce ? Sanam ta ya mutsa fuska batare da tace dashi kanzil ba , gyara tsayuwar sa
yayi sannan yace " wajenki fa nazo amman naga kina neman fita batare da munyi magana ba ,
Sanam tadube sa a wani shek'ek'e sannan tace " wajena kamar yaya ? dan Allah Malam inason
kabarni ina sauri zanfita ne , Jaydeen sosai yaji rashin dad'i abinda Sanam d'in tayi , amman sai
ya shanye tare da k'ak'alo murmushi yace " haba Gimbiyata , amman kinsan yadda nadamu
dake kuwa ? dan Allah kibani aron minty 5 zamuyi magana plss , dafe kai Sanam tayi sannan
tace " Inajinka fad'i abinda zaka fad'a dan sauri nake , Jaydeen yace " Ina Sonki Sanam kuma
ina son muyi aure dan Allah kisoni , zanbaki duk wata kulawa plss kisoni My Sanam , Samun
kanta tayi da kallon sa kafin tayi murmushi tace " inaso nan da sati biyu kadawo zanfad'a ma
duk abinda na yanke , bata jira cewar sa ba ta shige motar ta taja tana zuba hon.Da sauri me
gadi ya bud'e mata gate ta fice da mugun gudun nata data saba.......
Jaydeen binta yayi da kallo har ta fice daga gidan , cikin zuciyar sa yake tunanin " meyasa
komai takeyi burgesa take , duk irin yadda ta raina masa hankali amman ko kad'an baiji yana jin
haushin taba sai ma k'ara shiga ransa datayi , tunowa yayi da yadda 'yan mata ke binsa suna
mutuk'ar son sa , har da masu bashi jikin su saboda yayi amfani dasu , tabbas Sanam ta
dabance ita kuma tashiga zuciyar sa kuma bayajin zai iya rqbuwa da ita , juyawa yayi yashiga
cikin gidan dan yanaso yasamu Number ta wajen Mumyn ta .......
Huneed shida Hisham suna zaune a k'ofar gate d'in gidan su , wannan al'adar Huneed ce
indai yana gari , koda yaushe zaka samesa a k'ofar gida shida d'an uwansa suna hira , Sanam
ce tazo ta wuce da mugun gudun nan nata da tasabayi , Hisham ya d'ago yana kallon motar
wacce har ta k'ule yace " gaskiya wannan yarinyar bataji wato haryanzu bata daina gudun ba
kenan , Huneed sosai yaji ransa ya b'aci wato Sanam zata dawo da halinta kenan , wayar sa
ya lalubo ya danna kiran ta , har ta katse bata d'aga ba haka ya jera mata kira sau uku amman
bata d'agawa, test ya tura mata sannan ya ajiye wayar tasa.....
Tana zuwa unguwar su Diyana tasamu Diyana a tsaye a k'ofar gida tana jiran ta , shigowa
motar tayi sannan suka nufi Garden na cikin Asokoro .......
Hajiya Halima tuni sukayi sallama da Hajiya Nafeesa , nan suka kuma musayar contac
tare da alk'awarin zuwan da Hajiya Nafeesar tace zatayi , Jaydeen yadubi Hajiya Nafeesa yace
" Mumy dan Allah kibani Number Sanam dan inaso muyi waya , Hajiya Nafeesa cike da fara'a
tabashi phone d'in ta tare da gaya masa sunan da zaigani akan number Sanam d'in , Bayan ya
d'auka sukayi mata sallama tare da fitowa harabar cikin gidan , siyayyar da Hajiya Halima
tayiwa Sanam tabawa megadi ya shigar mata da ita sannan suka tafi......
Sanam da Diyana zaune akan wani had'add'en cafet suna hira , Duk rabin hirar akan
Zuwan Huneed ne sannan kuma tashiga bata labarin Jaydeen , Diyana tayi murmushi sannan
tace " besty kawai haka zakice min kinyi samari jarumai , zan so ingansu dukan su dan jinjina
musu ta yadda suka tunkareki , Sanam tayi murmushi tace " kefa Diya akwai ki da iskanci ,
nifa kwata kwata ban shirya soyayya yanzu ba dan kinsan yadda nakeson in koma inyi degree
dina , in nace zan had'a karatu da soyayya bazan nutsu yadda nakeso ba , sannan shifa
Huneed Soja ne kuma kinsan yadda natsani soja da d'an sanda , dariya Diyana ta tuntsire da ita
har da rik'e ciki , Sanam ranta yafara b'aci saboda iskancin Diyana , duban ta tayi rai a b'ace
tace " meye hakan kuma wannan dariya saikace mahaukaciya , Diyana ta dubeta kuma har
lokacin dariya take tace " wallahi dariya kika ban wai bakyason Soja da 'Dan sanda , to dan
Allah besty meye aibun su ? ni wallahi inason auren Soja kodan inzai tafi yak'i inrakoshi ina
kuka , sannan kuma wallahi sojojin nan akwai iya soyayya sosai , Sanam ta tab'e baki sannan
tace " wasu kuma akwai iya duka kuma ina ganin tamkar yanayin sa me dukan ne shi , Diyana
tace " taya zai doki wacce yake so ? dan Allah kidaina wannan tunanin kawai ki zab'i wanda
zuciyarki ta kwanta dashi , kinsan dai dole zakiyi aure tunda baza asakaki agaba ana kallo ba ,
Diyana tace " ke kanki kinsan ina da samari 'Yayan manya wadan da suka amsa sunan su ,
amman ban tab'a jin inason wani ba sai akan wannan Sojan , dan gaskiya tun ina turkey nafara
sonsa , kuma a kullum son sa k'aruwa yake a cikin raina , Diyana tace " to ai tunda kina sonsa
komai yazo da sauk'i , kawai ki anshi soyayyar sa nasan bazakiyi dana sani ba , nan suka ci
gaba da hirar su tsakanin su na kawaye kuma aminan juna...........
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
♀️♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 26.
Sai yamma lik'is su Sanam suka baro cikin Garden , gidan su Diyana tafara zuwa
ta sauke ta sannan ta jiyo da motar ta tayo gida.....
Huneed sau kusan takwas yana kiran Sanam amman bata d'agawa , tunani ya shiga yi
anya lafiya kuwa ? tun sanda ta fita da gudun nan daga Estate d'in yake dakon dawowar ta ,
yana zaune a wajen har ogan sa ya kira sa akan yana son ganin sa , haka ya shiga gida ya
shirya sannan ya fito da motar ya nufi kiran Ogan nasa.....
Koda Sanam ta dawo gida tana shigowa palor tasamu Hajiya Nafeesa da Fahad zaune
suna hira , sallama tayi k'asa k'asa sannan ta nufi hawa sama , da sauri Hajiya Nafeesa tace "
Sanam zonan mana , kwata kwata Sanam batasan ganin Fahad shiyasa ta canza fuska da
tashigo , k'arasawa tayi kusa da Hajiya Nafeesa tace " gani Mumy , Duban ta Hajiya Nafeesa
tayi sannan tace " waye ya tab'amin ke naga fuskar ki haka babu walwala ? Sanam ta d'an saki
fuska kad'an tace " babu komai Mumy kawai nagaji sosai ina buk'atar hutawa , Hajiya Nafeesa
tace " kuma gashi inason yin magana dake amman in kin huta sai ki sauko kici abinci sai muyi
magana , Sanam tace " to Mumy tana fad'in haka ta juya dan dama a k'age take ....
Da ido Fahad ya bita kafin yace " gaskiya hak'uri na yana k'ok'arin k'arewa , wannan sura
me kyau kana tare da ita amman ace har yanzu bakayi test d'in ta kaji yadda take ba , Hajiya
Nafeesa ta galla masa harara tana fad'in "kaifa baka da kunya Fahad har yanzu halin nan naka
yana nan nabin matan banza , sosa kai yayi yana fad'in " to ai Aunty kinsan abun ne sai da
dabaru yanzu , kinsan dai bani da kud'in da zan yi aure yanzu kuma ke kin ki min auren , Hajiya
Nafeesa ta kallesa tace " wai dama nice zanyi maka aure Fahad ? wai aikin da kace kanayi a
libiya dama k'arya kake , Fahad yace " haba Aunty nawa ne duka kud'in da nake samu da zan
yi aure , nifa nafiso nayi kud'i tamkar mijinki in gina gida me kyau wanda yafi nakin nan , dan
Allah Aunty ki taimaka kisa baki Sanam ta soni nasan Mahaifinta zai mallakamin kud'ad'e ,
Hajiya Nafeesa taja Numfashi tace " Sanam bazata Amince da kai ba Fahad , dan ko idanuwan
ta ka duba zakaga tsanar ka a ciki , inajin ka gwada mata halin naka shiyasa , amman tabbas
naso ace kuna shiri da ita da ko ta b'angaren ta masamu kud'in da mukeso mu samu , Fahad
yace " nifah bawani hali dana nuna mata , kinsan halin shegiyar yarinyar da girman kai tare da
wulak'anci , kuma fa duk lefin kine Aunty yarinya k'arama ta dunga wahalar dake , kawai sawa
zakiyi a kashe ta sannan akashe uban nata ki mallaki kud'a d'enki mukama gaban mu , duban
sa Hajiya Nafeesa tayi sannan tace " baka da hankali Fahad inason mijina fa kawai dai Sanam
d'in ce na tsaneta , kuma inajin rashin dadi yadda Alhaji yake fifita ta akan komai , duk wasu
Companoni da Alhaji ya mallaka gida da waje sunan Sanam ne akai , cewa yake ya mallaka
mata komai to yanzu ko mutuwa Alhaji yayi me zan tsira dashi tunda banice na haifeta ba ,
maganar da nake maka yanzun haka Uwar ta wani cikin gareta itama , Fahad da sauri ya furta
" kutt kawai kice ke zaman banza kike a gidan nan , Hajiya Nafeesa tace " zaman asara dai
dan wannan yafi zaman banza , Fahad yace " in zaki yadda tunda kince Alhajin yakusa yin
tafiya ta wata goma me zai hana inyatafi kice masa kina da ciki , da sauri Hajiya Nafeesa ta
dubi k'anin nata , d'aga mata kai yayi alamar ae cike da rashin fahimta tace " kamin bayani
yadda zan fahimta , Fahad ya gyara zama yace " akwai wata budurwa ta da muke chat kuma
anan garin take , to yarinyar iyayen ta talakawa ne shiyasa take fita yawon ta , gata da kula
kulen maza kuma tana da saurin d'aukar ciki , zan d'auko ta in kawota gidan nan muyi tarayya
da ni da ita har tasamu ciki , kinga da wannan cikin nata zamuyi amfani muce kece me cikin har
Allah yasa ta haifesa , ke kuma zaki samu wani likitan da zai miki alllurar da zaki kumbura
kidinga canzawa a yadda da cewar kina da cikin , sosai Hajiya tashiga nazarin magangun
k'anin nata , tabbas indai hakane Fahad yana da basira sosai kuma ta jinjina masa da irin
wannan aider tasa , nan yashiga bata labarin irin hajiyoyin da yake kulawa suma sunsha aikata
hakan in suka ga basu haihu ba , take Hajiya Nafeesa tayi na'am da shawarar Fahad sannan
tace yakawo mata yarinyar tagani , ......
Sanam na shiga d'akin ta wanka tashiga tayi sannan ta fito , sai a lokacin ta d'auko wayar
ta dan ta duba tagani , Miss call 20 tagani ga kuma test kala kala anyi mata , dubawa tayi taga