Showing 30001 words to 33000 words out of 99112 words

Chapter 11 - Mijin Marigayiyya Part Complete Hausa Novels.docx

17 Sep 2025

73

ai babu abincin, da an gama shan ruwa Baito take juye duk wani ragowar abinci ta tafi da shi. Kuma Hajia cewa take muje gidan Anti Jidda a dafa mana indomie amma idan mun je ba a dafa bana, bakin shayi ake bamu da ragowar kosai ko kunu.’

Ya dauki shukra ya ja hannun Nasreen yana cewa ‘ku zo muje.’

Bayan sun gaisa da Hajia tace ‘To ka barsu suje gidan Jidda ta dafa musu indomie din su karya sai su dawo ko? Yunwa suke ji gasu nan.’

Nan suka yiwa Hajia bayanin abinda ake basu idan suka je gidan yaya jidda; itama tayi mamaki sosai. Tace ‘To me yasa baku taba fada ba?’

Nasreen ta zumburo baki tace ‘Yaya Meena ce tace duk wanda ya fada sai taci ubansa ta karta masa rashin mutunci don ta san mu da tsinin baki.’

Daga Hajiyan har Mustaphan mamaki ne ya kamasu, Meena itace babbar ‘yar Yaya Jidda. To amma me zai sa tayi haka bayan Jiddan da kanta ta gayawa Hajia ya turo kudin indomie da kayan karin kumallon yaran?

Tace ‘Lallai daga Aminan har Jiddan zasu zo su sameni.’

Saboda tsabar takaici Mustapha kasa magana yayi. A nan ya sake bada kudi Habib ya fita kanti ya siyo musu indomie, yana kawowa Afaf ta dafa musu da kwai tunda dama da akwai kwai a gidan. Haka ya saka su a gaba duka saida suka karya azumin suka ci suka koshi.

Nan ya zauna suka cigaba da hira wajen Hajia tunda shima Alhaji ya fice; sai dai har la’asar ta kawo jiki Yaya Jidda bata zo gidan ba saboda yaronta Abdallah ya shigo gidan lokacin suna cin indomie shima ya zauna aka ci da shi kuma yana gamawa ya koma gida ya gayawa uwarsu Abban Afaf ya zo harma ya saan dafa musu indomie da kwai. Don haka tana sanetaki zuwa saboda rashin gaskiya.

Haka ya wuni a gidan ransa a bace yana tunanin mafita; tabbas duk Khadeeja ce ta janyo masa wannan wulakancin. Tunda da ta dawo babu wanda zai yi wa yaransa wannan wulakancin, Kuma shi ya tabbatar ta sami lafiya ko daga ganinta ma ai an San kalau take

PAGE 77

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

To yanzu ya zai yi da yaran? Idan ya tafi dasu ba zasu barshi ya zauna a nutse ba, kuma ma ya san Hajia ba zata yarda ya tafi dasu gida su zauna tare da shi ba. Sai dai kamar yanda ta riga ta fada yaje ya siyo abubuwan da suke bukata ya kawo ita sai ta dinga dafa musu kafin Baito ta zo; domin itama Baito din mijinta ne bashi da lafiya take jinyarsa shi yasa ba zata iya zuwa da safe ba.

La’asar tana matsowa ranshi ya sake baci, kuma har loakcin Yaya Jidda bata iso ba. Bayan ya idar da sallar la’asar yana zaune a kan dadduma yana tunanin mafita Habib ya shigo ya sameshi. Bai dade da zama ba yace ‘Abba da ma ka kaimu gidan Mama, ka ga dama mun dade bamu je ba tunda muka koma gida.’

‘Um, to ai da sallah zaku je ko? Ko ba kwa son zama a nan din ne? ai ka ga yanzu Hajia da kanta zata dinga baku breakfast din ko?’

‘Um, nan din ma muna son zama amma can din ma muna so, in ya so idan Anti Khadeeja ta dawo sai mu dawo.’

Nan sauran yaran suka shigo suka saka shi a gaba a kan su gidan Mama suke so suje; shi din ma yana so ya kaisu don ya san ba za a barsu da yunwa a can ba tunda ko babu mai aiki akwai ‘yan mata. To amma yanzu hakan yana nufin kenan ba za a iya rike masa yaransa a gidansu ba ko me? Ita kuma Yaya Jidda me take nufi? Gashi taki zuwa, shi kuma ba zai je gidanta ba don ya fi so tazo suyi a gaban Hajia. Haka dai yaran nan suka saka shi a gaba dole ya amsa zai wuce da su. Itama Hajia da ya gaya mata zai kaisu sai da ta nuna bacin ranta don gani take kamar fushi yayi da yanda ya sami yaran, sai da Alhaji ya sa baki kuma suka ga nasreen tana nema ta saka musu kuka sannan suka bari ya kwashi yaran suka wuce gidan Maman su Ma’u.

PAGE 78

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Duk da bai ce mata zai zo yau din ba amma dai haka kawai zuciyarta take gaya mata zai zo tunda an bude gari kuma tun wancan lokacin da aka bude gari basu hadu ba. Ta san dai yana jin haushinta daga yanda yake amsa wayarta amma ta nutsu a zuciyarta cewa zai zo din. Tun wuri ta tashi tayi wanka ta shirya don ya sameta a shirye; sai dai ga mamakinta har azahar tana zaune a parlor tana ta faman duba waya, duk wanda ya buga gate da hanzari take tashi ta bude tana saka rai Mustapha ne amma har la’asar bai zo ba.

Dab da la’asar tana zaune a parlor tana ta faman latsa waya tana duba whatsapp ko ya bude sakon da ta tura masa amma ga mamakinta har zuwa lokacin bai bude ba. Mommy ce ta fito daga dakinta; har ta kama hanyar kitchen sai kuma ta kula da Khadeeja a zaune a parlor din. Ta dawo ta tsaya tace ‘Ya na ganki a nan, ina Nabila PA din taki?’

Tayi dariya tace ‘Tana can tana abinda ta saba wato bacci.’

Ta wuce kitchen ta barta a nan, jimawa kadan ta fito ta dawo parlor din ta zauna a kan three seater daga bangareb da yafi kusa da single seater din ta Khadeeja take zaune. Ta dan yi gyaran murya tace ‘Uhm, ai na zata Mustapha zai zo yau din, ko sai da yamma zai zo?’

Ta dan gyara zama tace ‘Umm! Ina jin dai sai da yamman, watakila gidansu ya wuce tunda shi da yara ne.’

‘Um to bari mu gani. Amma dai kuna waya ko?’

‘Eh, jiya da daddare ma munyi magana.’

‘Ai shikenan bari mu gani.’

Suka yi shiru na dan lokaci; jimawa kadan tace ‘Mommy kina neman Mustaphan ne da naga kamar jiransa kike yi?

Ta jijjiga kai tana murmushi ‘A’a me zai yi min; kawai dai na san ya kamata ace ya zo ya duba ki ko, ai ko gaisawa ne a yi duk da dai da an sallace zaki koma.’

Itama dariyar tayi sannan tace ‘Zai zo Mommy in sha Allahu.’

PAGE 79

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Abu kamar wasa har aka sha ruwa babu Mustapha babu labarinsa’ haka dai ta lallaba ta ci abincin ba tare da tana jin dadinsa ba. Tana kula da yanda Mommy ta saka mata ido sosai tana kula da duk wani motsinta tu dazu da suka yi magana.

Sai da aka tafi sallar isha’i lokacin ‘yan gidan duk sun tafi masallaci sannan Mommy ta kirawota; ta riga ta san kiran don haka cikin sanyi ta tashi ta wuce dakin Mommy din. A zaune a kan dadduma ta sameta don haka ta zauna daga gefenta a kan kafet. Sai da Mommy ta dauki lokaci tana allon fuskarta kamar mai karanta littafi sannan tace ‘Wai ya aka yi Mustaphan bai zo ba? Gashi kin san ba za a sake bude gari ba sai satin sallah. Ko wani abu ne ya tare shi?’

‘Umm! Kin san sai sun je office da zarar an bude gari. Sai da aka fara kiran magariba sannan ya kirawoni yake gaya min a lokacin yake barin office gashi yana so ya isa gida kafin a fara tare hanya.’ Ta sharo karya.

Ta sake kakkafeta da ido na dan loakci sannan tace ‘Umm! Ko dai fushi yake don an ce ba zaki koma sai bayan sallah? Naga fa bai sake zuwa ba tun wancan lokacin da ya zo daukanki baki bi shi ba.’

Ta sunkuyar da kai atana ‘yar dariya tace ‘Umm, ya ma gama fushin ai. Da farko ne ya fara fushin ya zata zan fasa zama har bayan sallar amma daga baya da yaga ba zai sami yanda yake so ba ya hakura.’

‘Umm! To ko shi yasa bai zo ba?’

‘A’a fa Umma, na gaya miki ya je aiki ne shi yasa ya makara bai zo ba. Idan aka sake bude gari ko kuma ranar sallah zai zo.’

‘To Allah ya kai mu. Idan dai da akwai wata matsala gara ki fada tun kafin ki koma a san matakin da za a dauka don na kula kamar akwai abinda kike boyewa.’

Ta dan yi murmushi sannan tace ‘Babu wani abu fa Mommy, aiki ne kawai da raino; kin san harkar yara. Bana samun lokacin kaina kullum cikin hidimarsu nake. Shi yasa tunda Biba ta tafi ban sami natsuwa ba. Kinga yanzu kin ce kafin sallah za a samo min yarinya sai mu koma tare, daga wannan babu wata matsalar.’

PAGE 80

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta kalleta da alamomin tambayoyi domin jikinta yana bata kamar akwai abinda Khadeejan take boye mata, amma babu wani abu da zata iya yi a kai tunda bata ma san menene matsalar ba. Tace ‘To kuma shi Mustaphan baya baki wata matsala?’

Tayi dariya ‘Mommy kema dai kin san da da matsala da tuni na gaya miki fa, babu komai.’

Dole Mommy ta hakura ta kyaleta da tambayoyin nan ba don ta gamsu da amsoshin da ta bayar ba.

………

Sai da tayi da gaske sannan ta hana kanta kiran Mustapha a wannan daren; ta yiwa kanta alkawarin daga yanzu ba zata sake kiranshi ba har zuwa bayan sallah. Idan ya zo su koma, idan kuma bai zo ba ita dai to ba zata nemeshi ba.

Haka ta kwana tana matse kwalla.

.........

Duk yanda ya so ya daure zuciyarsa daga sharewar da Khadeeja tayi masa zuwa yanzu ya gaza; ya riga ya saba tana kiransa tana lallabashi da bashi hakuri amma shiru. Yana kallon kiranta ranar asabar yaki dauka don ya san zata ce ya zo gidansu ne; shi kuma ba zai je ba in dai ba daukanta zai je yi ba. Don haka yaki daukan kiran yana sa ran idan dare yayi ma zata sake kira, a lokacin sai ya bata uzurin dare yayi.

Sai dai har ya kai yaran gidan Mama ya huto gida ya gama duk abinda zai yi bata sake kira ba; lokacin da ya tashi sahur ma wayar ya fara dubawa yaga ko ta kirawo yana bacci amma ga mamakinsa babu kiranta ko daya. Haka yayi sahur ya gama ibadarsa ya kwanta.

Sai da gari ya waye zuwa azahar sanna ya tuna akwai messages dinta na whatsapp da ta turo bai bude ba don haka ya je ya lalubo sakonnin ya bude. Ya bisu daya bayan daya ya tura mata amsa, wanda tambayarsa take yi ko zai zo sannan tana gaya masa kayan da zai dauko mata a dakinta ya taho mata dasu.

Har zuwa la’asar bata amsa sakonninsa ba sai dai sun nuna alamar sunshiga; ya buda whatsapp sau babu iyaka amma har zuwa loakcin bata karabta sakonninsa. Bata taba shareshi haka ba; to ko dai bata da lafiya ne? kada fa yaje wani abune ya sameta don idan dai Khadeeja ce ya san zata nemeshi. Zuciyarsa tana gaya masa wulakanci ne kawai take so tayi masa don haka ya rabu da ita duk da yanda ya kasa cire tunaninta daga ransa.

PAGE 81

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Haka suka zauna basa waya kumaga sakonninsa nan ta gani amma taki ta abshi amsa.

Ranar jajiberin sallah ya kasa jurewa shiru din don haka ya kirawota; wayar tana dab da tsinkewa sannan ta amsa.

Murya kasa-kasa cikin halin ko in kula tace ‘Bana kusa da wayar ne.’

‘Kwana biyu na jiki shiru ne, kuna lafiya?’

‘Lafiya Alhamdulillahi. Ya yarana?’

‘Suna nan kalau, suna gidan Mama.’

“Allah sarki, don Allah in kaje kace ina gaida su maman.’

Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan yace ‘Kin yi zamanki a gida gaba daya kin manta da ni ko?’

Tayi ‘yar dariya tace ‘Ka dai manta da ni.’

‘Ko kayan sallarki ma baki tambaya ba.’

‘Uhm, akwai wasu ma a nan da Mommy ta dinka min.’

‘To ya kike? Lafiya dai kike ko?’

‘Lafiya kalau.’

Suka dan taba hirar haka wadda duk gaba daya kusan shine yake ta daddagewa don itama ta ji haushin abinda yayi mata, daga baya yace ‘Gobe fa Sallah, yaushe zan zo mu taho gida?’

‘Umm, in dai ka cire jibi duk lokacin da ka shirya zaka iya zuwa mu tafi, tunda an riga an samo min mai aiki gata har ta koyi duk wani aiki da nake so.’

‘Uhm, dole dai sai kin sani cin tuwon sallah a gidan hajia ko?’

‘To ina laifi, idan ka ci nima kayi min take away.’

Haka suka cigaba da hirararsu a hankali suna sakewa, daga baya suka yi sallama a kan ranar sallah zai zo yaci tuwo kafin ya wuce gidan Hajia.

PAGE 82

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ranar Sallah yana tashi ruwan shayi kawai ya sha ya shirya ya fice; bayan an idar da sallar idi kai tsaye gidan Mama ya wuce wajen yaransa. Yana gamawa da su ya wuce gidan Mommy wajen Khadeej; ko da dai ya ji haushin yanda tayi zamanta a gidansu ta ki dawowa amma ya san yayi kewarta. Duk wani haushi nata da yake ji ya riga ya huce, abu daya yake so a yanzu shine ta dawo gida ya samu ya daina fama yawo shi da yaransa sai kace wasu wadanda basu da gata. Ya kalli kayan sallarta wadanda ya taho dasu ya kai mata ko zata kara, ya kauda kai ya cigaba da tukinsa. Shi ya ga ma kamar bata damu da kayan sallar ba tunda da ita aka kai dinkin amma da yake ta so tayi sallah a gida ko bi ta kansu bata yi ba sai ma ce masa da tayi Baffa yayi mata kayan sallah.

Haka dai yayi ta tunani kala-kala har ya karasa gidansu Khadeeja.

Lafiya kalau suka gaisa cikin mutunci kamar babu wanda yake jin haushin wani a tsakaninsu; ya shiga ya gaida Mommy sannan ya gaida Baffa. Suka dawo ita da shi suka zauna a parlor din baki inda ba tare da bata lokaci ba ta kawo masa tuwon sallah da lafiyayyen zobo mai sanyi. Suka zauna yana ci tana yi masa hira.

Bayan ya gama ya huta yayiwa Baffa sallama inda Baffan ya sanar da shi jibi ya zo ya dauki matarsa. Suka fito tare da Khadeejan ta rakoshi bakin mota.

Tana tsaye rike da murfin kofar motar yayinda shi kuma yake zaune a kujerar direba ya juya kujerar baya ya dauko ledar da take ajiye a kan kujerar ya mika mata yana cewa ‘Ga kayan sallarki duk da na ga baki damu da su ba.’

Tayi ‘yar dariya tana tura masa ledar tace ‘Ka koma da su ka ajiye min a dakina tunda jibi zan dawo.’

Shima dariyar yayi yana mayar da kayan yana cewa ‘Ko dubawa ma fa baki yi ba.’

‘Haba kayan da na riga na sansu, idan na dawo zan duba sannan nayi kwalliyar sallah ta.’

Cike da farin ciki da walwala suka yi sallama sannan ya wuce gidan Hajia.

Yana shiga gidan ya tara da Hajia a parlor dinta suna hira ita da Yaya Jidda, yaranta kuma suna ta kaiwa da kawowa a tsakar gidan.

PAGE 83

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Bayan ya gaida Hajia yayi mata barka da sallah ya juya suka gaisa da Yaya Jidda wadda take ta faman shan kun tana basarwa saboda kar yayi mata wata magana. Bayan sun gaisa sun dana taba hira da hajia ya dubi Yaya Jiddan yace ‘Yaya bari na baki account number ki turo min 10k din da na tura miki ta tiwa yara sayayyar kayan shayi; tunda sun ce min ba a saya ba ko?’

Ta sake hade girar sama da kasa ta kalli hajia sanna ta kalleshi tace ‘Ban gane ba a siya ba, an saiya mana. Kawai dai ba rabar da ka bayar ba don kafin ka turo kudin masu kantunan sun rufe. Shi yasa ba a samu an saya ba har sai ranar da aka sake bude gari, ranar da ka zo kenan ka kwashesu. Da safen da ka tafi da su ai da sun zo zasu tara da kayan komai an saya don har ciko ma nayi.’

Hajia tace ‘Ai kuwa ka ga babu maganar dawo da kudi tunda an sayi kaya.’

Takaici ya kama shi don ko daya bai yarda da wannan zancen nata ba, ya kawar da kai sannan ya sake dubanta yace ‘Hakane, to shi kenan, sai a dauko min ragowar na tafi da su tunda jibi yaran zasu dawo har Khadeejan kuma ko suga babu a gidan sai na sake siya. Ki aika a dauko min su tunda kusan ma ba ayi amfani da su ba kenan tunda ranar da aka siyo ranar suka tafi.’

Kafin tayi magana Hajia tace ‘To su sauran yaran gidan ba ‘yayanka bane da ba za a basu ba, kayan shayin kawai ba wani abu.’ Ta dubi Jiddan tace ‘Ko da yake bari na barku watakila suna nan ki bashi ya kai gidan nasa.’

Ta sake kicin kicin sannan tace ‘Hajia kema dai kin san yaran nan ba zasu bari ga kayan shayin harda Indomie su bari na ajiye ba tare da na basu ba. Sai dai kawai idan biyansa zan yi na yiwa babansu waya ya biya abinda ‘yayansa suka ci tunda yana kallo suna ci kuma ya san ba shi ya siyo ba.’

Hajia tace ‘A’a ba za ayi haka ba, sai kace a garin matsiyata ake.’ Ta dubi Mustaphan tace ‘Kai Mustapha kayi hakuri, bana son wannan rigimar taka. Wannan ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login