Showing 45001 words to 48000 words out of 99112 words

Chapter 16 - Mijin Marigayiyya Part Complete Hausa Novels.docx

17 Sep 2025

92

ma tun tuni na daina tambayarsa.’

Suka dan yi shiru na dan lokaci Mustapha yana ta kokarin hada ido da ita yayinda ita kuma take ta kokarin kauce masa don ko gefen da yake bata kalla ba.

Baffa yace ‘Shikenan abinda ya saka ki fushin ko akwai wani abun?’ kana jin muryarsa kuma ka kalli fuskarsa zaka san ransa ya sosu matuka, domin karsashi da rahar da ya fara wannan tattaunawar da su duka babu.

Har ta gyada kai Mommy ta zungureta da kafa, ta dago suka hada ido. Ta sunkuyar da kanta tace ‘Baffa ita sakatariyar tasa kuma na tambayeshi menene a tsakaninsu; idan ma aurenta zai yi ai sai ya gaya min ba wai kawai na dinga ganinta a motarsa ba tana yawo a gari ni ina yawo a tasi. Saboda ni dai yanda naga ta nuna alakarsu ta fi karfin ta office kawai, don yaran ma duk sun santa ni kadai ce a gida na fara ganinta ranar.’

Baffa ya mayar da idonsa kan Mustapha wanda yayi sauri ya sunkuyar da kansa kasa, ji yake kamar ya zura da gudu don bai taba zata Khadeeja zata kawo wadannan maganganun a gaban Baffa ba.

Suka yi shiru na dan lokaci kowa yana sauraron abinda Mustaphan zai ce, shi kuma ya sunkuyar da kai yayi shiru kamar wanda ruwa ya ci. Mommy ce ta gaji da shirun tayi gyaran murya tace ‘Uhm, ai gara ka gaya mata idan auren sakatariyar zaka yi ka ga tunda dai na san cewa ta san ka kai ka kara auren.’

Ya gyara zama yana shafa kewa yace ‘A’a ba ma shi bane, kawai dai da na aiketan ne to kuma ana dan wahalar mota shien nace taje a motata tunda ta iya tuki.’

Jimawa kadan Baffa yace ‘Allah ya sauwake.’

Mommy tace ‘Amin dai.

PAGE 114

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Suka sake yin shiru na dan lokaci, sannan Baffa ya kirawo sunan Khadeeja, ta amsa ta dubeshi suka hada ido sannan yace ‘Kiyi hakuri Dije, kin ji.’

Ta gyada kai shi kuma ya dan numfasa sannan ya cigaba ‘Kiyi hakuri ki bi mijinki, kin ji bayanin da yayi. Kuma idan ma yace zai auri waccan yarinyar wannan bai kamata ya zama matsala ba tunda dai kin san duka wani namiji mijin mace hudu ne. kiyi hakuri ki cigaba da hidimarki kamar yanda kika saba, kin ji. Batun kaiwa makaranta kuma kinga shi ‘yayansa yake zubawa a mota yake kaisu a makaranta kuma tabbas haka ya kamata uba nagari ya kasance, don haka idan kika gama shirya masa nashi yaran kema ki shirya kiyi min waya sai na zo na kaiki tunda dai kema ‘yata ce; kai ki makaranta kuma ba bakon abu bane a wajena.’

Ya gyara zama ya dago kai a razane ‘A’a Baffa ayi hakuri ai ba sai an yi haka ba, in sha Allahu zamu dinga tafiya ma. Dama ai bata gaya min ne shiryawa kawai take tace ta tafi.’

‘Kada ka damu, zan dinga zuwa ina kaita wannan aikina ne.’ Baffa ya bashi amsa rai a bace.

‘Ayi hakuri Baffa, in sha Allahu ba za sake ba, ni din ma zan dinga kaita. Ayi hakuri.’

Mommy tace ‘Ke kuma kiyi hakuri da yaranki tunda su ba suyi miki komai ba, ki kula da su ku zauna lafiya. Shima kuma kin ji bayaninsa, kije kuyi zamanku lafiya kamar yanda kuka saba saboda Allah. Ita rayuwar aure hakuri ce, ku dinga hakuri da juna. Kuma nan gaba ko wata matsala ta taso muku kuyi kokari ku kasheta a tsakaninku.’

‘Toh.’ Ta amsa cikin sanyin murya.

Jimawa kadan suka yiwa Baffa da Mommy sallama suka fice; Khadeeja ta so shiga cikin gidan wajen Nabeela amma Mommy tace kada ta shiga ta barshi yana jira idan ta shirya ta dawo suyi hirar.

……..

Tunda suka shiga motar bai ce komai ba sai muzurai kawai yake, don haka itama zuciyarta wasai take. Ta ji dadin yanda Baffa ya nunawa Mustapha cewa itama da gatanta; duk da dai har yanzu tana jin cewa ba zata dorawa kanta jiransa ya kaita makaranta ba balle ta dorawa kanta damuwa.

PAGE 115

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Suna shiga gidan ta wuce dakinta shima ya wuce nashi dakin. Sai da tayi sallah sannan ta fito wajen yaran; zuwa lokacin Shukra har ta riga tayi bacci. Bayan ta tabbatar sun ci abinci ta wuce kitchen, ta kirawo Rashida tana tambayarta me suka dafa da daddare. Ta gaya mata indomie suka dafa saboda haka Afaf tace, ta nuna mata indomie din da ta saka a flask ta ajiyewa Abbansu.

Ta riga ta san baya son indomie, musamman idan ta fara sanyi kuma itama yunwa take ji bata son cin indomie mai sanyi. Don haka Rashida ta tayata ta gyara busasshen kufi ta dafa musu jollof sphageti mai rai da lafiya. Nan da nan gidan ya dauki kamshi; zuwa loakcin yaran duk sun kwanta. Ta jera abincin a dining table sannan ta hada masa shayi mai kayan kamshi irin wanda yake so sanna ta wuce dakinsa ta tura kofa ta shiga. Saura kadan tayi dariya saboda ganin yanda dakin yayi kaca-kaca; ga kura ga kaya da tarkacensa ko ina. A ranta tace mutum sai kace kuturu, ya sa hannu ya gyara makwancinsa kawai ya gagareshi.

Ta danyi gyaran murya tace ‘Ga abinci can na saka a dining,’

Dama tunanin abincin yake don yunwa yake ji sosai; ya riga ya san indomie suka dafa tunda jiya ma ita suka dafa don haka ya riga ya fara tunanin yanda zai yi sai kuma tace masa ga abinci.

Ya dubeta ya dan sassuauta fuskarsa yace ‘Yanzu zan fito.’

Ba tare da ta bashi amsa ba ta juya ta fice, ya bi bayanta da kallo yana murmushin yake. Ya rasa dadi zai ji ta bashi abinci wanda hakan yake nuna zata cigaba da hidimarta; ko kuwa haushinta zai ji saboda yanda ta yaga shi a gaban Baffanta. Haka dai ya taso ya fito, babu kowa a parlor din don haka ya zauma ya ci abincinsa ya koshi; irin koshin da ya kwana biyu bai yi ba.

Sai da ya gama cin abincinsa ya huta sannan daga baya yaje ya kullo gidan ya shiga dakinsa; har ya kwanta kuma ya tashi ya bi bayan Khadeeja. Ya kula idan ya biye mata ba zata nemeshi ba, ko ba komai kuma yana so suyi magana ya kara kwantar mata da hankali game da maganar Naja don ba yanzu yake so ta sani ba. Sannan kuma yana so ya nuna mata rashin jin dadinsa game da yanda taje ta kunyata shi a gaban Baffa.

PAGE 116

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Duk yanda yaso ta taso su koma dakinsa su kwana kamar yanda ya saba bai samu, daga haka ya gane idan ya fiye takura mata zata sake dauke musu wuta; don haka sai ya hakura ya zubar da duk maganganun da ya taho da niyyar gaya mata. Ya hakura suka kwana a nan dakin nata tunda tace ta fara bacci bata son canza daki.

……….

Tun asuba ta tashi kamar yanda ta saba, nan da nan ta shiga hidima da yara da taimakon Rashida. Ba karamin dadi ya ji ba da ya dawo daga masallaci sallar asuba ya jiyota a kitchen, don haka cike da walwala ya wuce daki ya koma bacci kamar yanda ya saba. Karfe bakwai na safe yana fitowa kowa ya shirya yayinda Khadeeja take kaiwa da kawowa tana jera masa nasa abincin a dininga table.

Bayan ya amsa gaisuwar yaran yace ‘To kowa ya dauki kayansa mu wuce ko?’

Nan da nan suka mike suka fara ficewa.

Ya dubi Khadeeja wadda take fitowa daga kitchen yace ‘Baki shirya ba ke, ko sai an jima zaki tafi.’

Da murmushi tace ‘No, yau bamu da lecture ba zan je ba.’

‘Ok.’

Tayi musu a dawo lafiya suka wuce.

Bayan ya dawo haka yayi ta tambayarta idan ta san zata je makaranta ta gaya masa ya jirata ya tafi da ita ya kaita; sai da ta tabbatar masa ba zata fita ba sannan ya fita ya tafi office.

…….

Washegari ranar Juma’a ce; kamar yanda ya saba yana kwance a daki bayan ya dawo daga masallaci yana rage bacci kafin a gama shirya yara ya kaisu makaranta. Wayar Khadeeja ce take ta faman ringing a dakin tana katse masa bacci, baya saon tashi don haka yayi tsaki ya gyara kwanciyarsa. Sai dai wayar da ta tsinke sai a sake bugowa; to waye ma yake kiranta da wannan safiyar bayan ko wayewa garin bai gama yi ba? Wayar tana fara ringinga a karo na uku ya mirgina ya mika hannu ya dauko wayar daga kan durowar gefen gado. Ya kallin screen din inda sunan wanda yake kiran ya bayyana “Baffa” ya karanta a fili yana watssakewa. To me yasa Baffan Khadeeja yake kiranta yanzu? Allah ya sa dai ba wani abun ne ya faru a gidan nasu ba.

Nan da nan ya sauko daga kan gadon dauke da wayar ya nufo kitchen inda Khadeejan take faman zubawa yara abinci suna tsaye kowa yana karbar nasa.

PAGE 117

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ya mika mata wayar wadda take ringing yana cewa ‘Ki amsa Baffa ne yake ta kiranki kin baro wayar a daki.’

Tana karba ta amsa ta kara a kunnenta; yana tsaye yana kallonta yana tsoron kada ace wani abu ne ya faru a gidan nasu.

Bayan sun gama gaisawa da Baffan tace ‘A’a Baffa, ina nan ne muna shirin makaranta ni da yara.’

Daga daya bangaren Baffa yace ‘Karfe nawa ne lecture din naki Dije?’

Tace ‘Karfe takwas.’

‘Idan nazo 7:30am ai kin gama shiryawa ko?’

‘Eh Baffa.’

‘To ki shirya idan na karaso zan yi miki waya ki fito na kaiki makarantar sai na wuce office.’

Cike da girmamawa kamar wadda zata tsuguna a wajen tace ‘To Baffa na gode, Allah ya kara lafiya.’

Ta ajiye wayar bayan ya amsa, kafin tayi wani abu Mustapha yace ‘Lafiya kalau dai naga Baffa yana kiranki da safe.’

Ta mikawa Habib shayinsa da ta hada masa tana cewa ‘Uhm zai zo ya kaini school ne shine yake tambayata karfe nawa zai zo.’

Habib ya karbi shayinsa ya fice yayinda Mustaphan ya matsa kusa da ita cike da kulawa da damuwa yana cewa ‘Makaranta kuma? Ba nace zan dinga kai ki ba? Yanzu ke saboda rashin tausayi sai ki taso shi da wannan safiyar kawai don ya kai ki makaranta? Ke abu ba zai wuce a wajenki ba?’

Ta juya cikin halin ko in kula tana cewa ‘Shine ya karbi timetable dina yace zai dinga zuwa yana kaini ko? Ai a gabanka ya fada.’

‘Kuma a gabanki na bashi hakuri ai; wannan wanne kalar abin kunya ne ina nan kuma ina da abin hawa amma zaki taso Baffa ya zo ya kai ki makarnta don Allah?’

Daryace take son ta kwace mata saboda yanda duk ya muzanta kamar ma Baffa yana tsaye yana kallonsa. Kafin ta bashi amsa ya dauki wayar tata ya dannawa Baffa kira ya mika mata waya yana cewa ‘ki gaya masa zan kai ki ba sai kin yi min wulkanci ba.’

Kafin tayi magana har Baffan ya dauka, don haka ta kara a kunnenta tace ‘Um Baffa ka bari ma Abban Afaf zai kai ni makarantar.’

Yace ‘Ah, kin tabbata dai ko?’

‘Eh Baffa, gasu ma tare zamu fita gaba daya shiryawa muke.’

Ya zare wayar daga hannunta kafin ta sake magana ya kara a kunnensa cike da girmamawa yace ‘Baffa zamu tafi tare in sha Allahu, zan dinga kaita. A yi hakuri.’

PAGE 118

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid

Yace ‘To, to babu laifi. Allah yayi muku albarka.’

Ya ajiye wayar yana harararta yana cewa ‘Yanzu zan je na shirya, kema ki shirya sai mu fita gaba daya ko kuma idan na kaisu sai na dawo kafin nan kin karasa sai mu wuce.’

Tace ‘Um, ka ga babu komai fa, zaku iya tafiya ma sai na wuce kawai ba sai na gayawa Baffan ba.’

Ya kakkafeta da ido yana harararta har sai da ta sunkuyar da nata idanun, ya juya yana cewa ‘Ki shirya nace.’

Ya fice ya barta a nan.

Tayi dariya ta cigaba da aikinta.

Bata da zabi haka ta shirya suka fita tare, kuma daga wannan lokacin ya zama ko da wanne lokaci zata makaranta haka yake barin abinda yakeyi ya zo ya kaita. Sai dai idan ta gama abinda takeyi kawai sai ta hawo motar haya ta dawo.

.......

A zaune yake a parlor din Ahaji, yayinda Hajia take zaune a kusa da Alhajin. Zuwa yayi musu da labrin auren yana son ya kara don har ma yana gaya musu sati me zuwa yake so aje a kai kudin aure.

Cikin walwala Alhaji yace ‘Ai kwanaki da mukayi magana da kai da na jika shiru na zata ka fasa.’

Yayi ‘yar dariya ‘Ba fasawa nayi ba Alhaji, na dai dan tsaya ne na kara shiryawa, na gaya maka zan sayi gida ai. To dama tsayawa nayi a samo gidan, kuma yanzu an samo, cinikin ne ma bai fada ba saboda ina so su dan yi min ragi. Amma in sha Allahu ina sa ran zamu daidaita shi yasa nake son yanzu a kai kudin auren.’

Murmushin Alhaji ya kara fadi, ya dubi Hajia sannan ya dubi Mustapha yace ‘To ma sha Allahu. Wannan ai sai dai mu sa albarka kawai. Kaje ka sami babanka Safiyanu kayi masa bayanin ita yarinyar idan ya gama bincikensa ya tabbatar gidan mutunci ne ai sai suje su kai kudin. Allah ya sa albarka, Allah ya kara budi.’

Suka hada baki shi da Hajia suka ce ‘Amin.’

Hajia tace ‘To ka gayawa Khadeejan ko? Me tace?’

Ya shafa kai yana murmushi ‘Ban gaya mata ba tukunna, amma in sha Allahu zan gaya mata. So nake sai an gama magana tukunna idan ya zama saura kamar sati uku ko hudu sai na gaya mata ko don saboda gudun fitina. Kafin nan na siya gidan mun koma.’

Alhaji yace ‘Eh, to hakan ma yayi. Sai dai kuma Allah ya sa kada mata su rigaka gaya mata.’

PAGE 119

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Hajia tace ‘A’a babu wanda zai gaya mata, kayi abinka a hankali idan ka shirya ka gaya mata.’

Nan suka kare hirarrakinsu daga baya yayi musu sallama ya kama hanya.

……….

Abu daya ne yake ciwa Khadeeja tuwo a kwarya rashin haihuwa, domin har yanzu tun bayan cikin da ta samu ya bare bata sake ko da batan wata ba. Gashi yanzu har sun shiga final year amma babu wani labari. Duk lokacin da tayi yunkurin zuwa asibiti Mustapha sai ya nuna halim ko in kula ko kuma yace lafiyarta kalau zata je ta fara neman fitna, don haka ta tattara ta hakura. Sai dai ta yanke kanta hukuncin cewa da zarar ta gama final exam zata je asibiti a dubata a tabbatar mata da abinda ya hanata samun ciki; ko babu komai itama tana so taga ta haifi dan cikinta. Tunda idan ta gama karatu bata san lokacin da zata sami aiki ba.

Haka ta hakura ta mayar da hankali a kan karatunta tana addu’a.

Zamanta da yaran Mustapha kadai ya isa ya sa ta ji tana son haihuwa; domin yanzu yaran sun girma tunda Shukra auta ma tana primary 1 yayinda Afaf take SS. Kusan gaba daya yaran yanzu ba dadinsu take ji ba, domin abinda suka ga dama sukeyi. Habib ne ma kawai wanda ya damu da rayuwarta kuma yake neman shawara a wajenta kamar uwa, amma Afaf da Nasreen ma bata san wanene yake basu shawara ba. Ta dai san duk wani abu na wulakanci da sukeyi mata da sa hannun Yaya Jidda. Ga wani mahimmanci da Musttapha yake bawa Afafa ta yanda ko da sun gama magana da Khadeejan Afaf tana iya saka shi ya canza. Duk abinda ya shafi yaran kuma ko da Khadeeja ce ta gaya masa to a karshe da Afafa din zai yi shawara. Hatta kitchen din gidan ya zama kamar na mata biyu; domin a lokuta da damam sai ta gama girka abinda kowa zai ci ta fita daga kitchen din sai Afaf ta shiga itama ta dafa abinda ta ga dama tace bata cin wanda Khadeejan ta dafa. Tayi magana har ta gaji, tunda Mustaphan ya fara nuna tana so ta takurawa Afaf ne saboda ba ita ta haifeta ba.

………

Tana kwance a dakinta tana jiyo hayaniyar yaran a parlor; Afaf ta shigo ta sameta ta mika mata waya tana cewa ‘Anti Abba ne yake waya yace yana kiran wayarki bata shiga.’

PAGE 120

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta tashi zaune ta karba ta dan kalli wayar taga whatsapp call ne, sannan ta kara a kunnenta.

Yace ‘Ina kika shiga ne anke kiran wayarki ana ta cewa not reachable?’

Tayi yar dariya tace ‘Sai dai ko idan network ne don ga wayar ma a hannuna.’

‘Kin san Ali Ahmed ko? Abokina da muke zuwa zance tare.’

‘Eh na san shi mana.’

‘Yauwa da Allah shine ya shigo gari nan da kamar awa daya zamu zo gidan, me zaki iya dafa masa sai muyi dinner tare. Yana dai son tuwo’

‘Ok, to sai ayi tuwon ai. Amma dai ka bari na duba freezer tukunna naga yawan kazarmu yada za samu kuma ayi muku peppersoup ko?’

‘Eh, kwarai kuwa da zobo ma please. Duba idan babu kazar sai na bayar a kawo miki yanzu, rike wayar ki duba ki bani amsa.’

Ta mike ta dubi Afaf da take tsaye tana jiran wayarta ta nufi kitchen. Suna fitowa parlor Afaf din taga Nasreen ta canza channel ta mayar Disney Junior, da sauri tayi kanta tana cewa ‘Wane mara kunyan ne ya canza min channel ban gama kallo. Anti idan kin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login