Showing 81001 words to 84000 words out of 99112 words

Chapter 28 - Mijin Marigayiyya Part Complete Hausa Novels.docx

17 Sep 2025

88

dawo daga asibiti? Allah ya gani babu abinda ta sha, cikin nan ma bata taba kawo masa zubewa ba kuma ko da wasa bata so hakan ba. Kawai dai Allah yayi ikonsa ne kamar yanda yayi a wancan karon, kuma ta san shine zai fitar da ita daga duk wani zargi da zai iya tasowa. Kujerar Makka ma idan dai Mustapha ne zai bata kam bata so ta san Allah zai hore mata taje tunda ita ma tana kan neman kudinta.

…….

Can da yamma su Hajia suka shigo ita da Yaya Jidda da ‘yan matanta. Bata san da Hajia suka shigo ba don haka ta yi banza da su tunda ta jiyo su a wajen Naja. Jimawa kadan suka hawo saman gaba daya; ta saukesu a nan parlor dinta ta kawo musu ruwa da lemo, suka zauna suka yi mata dubiya da jaje. Suna cikin hirarrakinsu Mustaphan shima ya shigo ya zauna aka cigaba da hirar yana sa musu baki lokaci zuwa lokaci.

Yaya Jidda ta dubeta tace ‘Alhazai dai sun kusa tashi balle ma ace za a canza a baki kujera tunda cikin da ya hana ya fice, ko ka canza ne Mustapha?’

Ya kalleta sannan ya kalli Khadeejan yace ‘A’a ai an gama wannan maganar, ita zata zauna da yara idan Allah ya kai mu shekara mai zuwa sai aje da ita.’

PAGE 205

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Hajia tace ‘E ai an gama wannan maganar. Allah ya baki lafiya ya kawo wasu yaran masu albarka. Ita Najan sai suje kamar yanda aka tsara.’

Ita dai tana zaune a tsakiyarsu amma bata iya ce musu komai ba; to kenan suma zarginta sukeyi da zubar da cikin ko me? To me Mustaphan ya gaya musu har suke mata wannan zargin?

Sai da suka gama hirarrakinsu sannan suka yi mata sallama suka tashi suka fice.

Bayan sallar Magriba Mustaphan ya sameta a dakinta tana zaune a gegen gado, bayan ta amsa sallamarsa ya karasa ya zauna a gefenta. Tayi masa sannu da zuwa ya amsa suka zauna suka dan yi shiru, jimawa kadan ya kirawo sunanta. Bayan ta amsa ya kakkafeta da ido sannan yace ‘Wai ni me kika yi ne cikin nan ya zube, ko wani abun kika sha saboda ya zube mu tafi dake aikin Hajji.’

Tayi ‘yar dariyar takaici sannan tace ‘Mustapha ban zubar da ciki ba, domin kujerarka ta maka bata isa ta saka ni na zubar da ciki ba. Kamar yanda Allah ya kawo wancan cikin ya zube ba tare da nayi wani abu ba wannan dinma hakan ce ta kasance.’

Yace ‘To ai kin ce wancan wahala ce da aiyuka suka yi miki yawa ya sa ya zube, ko ba haka kika ce ba? Wanna kuma na ga babu wannan ko?’

Ta gyara zama itama ta kakkafeshi da ido tace cikin zafin rai tace ‘Mustapha wai baka ji me nace ba; ban zubar da ciki ba kuma kujerar Makka bata isa ta sani na aikata hakan ba. Na riga na san baka yi niyyar zuwa dani Hajj ba domin lokacin da kake cewa ina da ciki ba zaka je da ni ba itama Najan cikin ne da ita. Ka dai zabi matarka wadda kake so ka tafi da ita ni kuma ‘yar aikin gidanka ka barni na kular maka da gida da yara kamar yanda ka saba. Idan ma kai ne ka gayawa ‘yan uwanka wannan maganar har suke yar min da magana to ka koma ka gaya musu karya ne.’

Ya mike a fusace ‘Daga an tambayeki kuma shine zaki yi min rashi kunya kamar yanda kika saba saboda ke ba a gaya miki gaskiya ko?’

‘Wannene rashin kunyar a ciki; ganewa da nayi cewa kayi rashin adalci wajen zabar matar da zaka je da ita hajji ko kuwa gaskiyar da na gaya maka?’

‘Mtsewwwww!’ Ya ja dogon tsaki ya mike a fusace ya fice daga dakin.

PAGE 206

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta zuba fuskarta a tafukan hannayenta, so take hawayenta ya fita ko zata samu taji sanyi a ranta amma hawayen ya bushe kyamas. Kirjinta har zafi yake saboda yanda zuciyarta take turiri; Mommy ce ta fara yi mata wannan zargin gashi yanzu Mustaphan ma da shi da ‘yanuwansa suna zargin ta zubar da cikin ne don yaje da ita Hajji. Tabbas Allah sai ya bi mata hakkinta.

Haka ta kwanta zuciyarta na mata zafi saboda takaici; ta so ta kirawo Mommy ta gaya mata ko zata sami salama a ranta, to amma hakan ba zai yi mata wani amfani ba. Tunda Mommy din ce ta fara yi mata wannan zargin. Ta sake fashewa da kukan takaici ta gyara kwanciyarta; yau itace da kwana amma ta san yanda Mustapha ya fice daga dakin nan watakila sai dai idan ya dawo daga aikin hajji sannan ya waiwayeta.

………

Ranar laraba aka kirawo su Mustapha, jirginsu zai tashi karfe biyar na yamma don haka aka basu shawara su kasance a cikin airport din tun kafin azahar. Sun gama hada kayansu shi da Najan kuma ya riga ya sanar da Khadeeja, ya danka mata duk wani abu da take bukata don kula da gidan.

Wajen karfe sha daya yana zaune a parlor dinsa shi da yara Khadeeja ta fito daga dakinta ta shige kitcen don dora abincin rana. Ya tsallake yaran ya bi bayanta ya tsaya daga kofar kitchen din ya rungume hannuwansa a kirji sannan yace ‘Kada fa ki dafa abincin da ni yanzu zamu wuce airport, ki dafa ke da yara kawai.’

‘To.’ Ta amsa murya kasa-kasa.

Ya kula tunda sukayi maganar zubewar cikinta take son tada masa fitna shi kuma ba zai saurareta ba, fata yake kawai Naja ta gama hada kayanta su fice su bar mata gidan kafin ta takalo rigima. Don haka ya juya ya koma cikin yara ya zauna.

PAGE 207

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Har ta dauko tukunya zata dora shinkafa sai kuma ta fasa, ta ajiye tukunyar ta fito daga kitchen din ta koma dakinta. Tana shiga ta wuce gaban mudubi ta ja kujerar ta zauna; bata san me ya sa ta fasa dora girkin ta zo ta zauna ba. Kamar dai tana bukara wani wanda zasu yi magana ne amma ta rasa wanda zata gayawa damuwarta ya fahimceta. Ta daga fuskarta ta kalli kanta a cikin mudubin, at yiwa kanta murmushi sannan ta sake sunkuyar da idanuwanta. Yanzu haka zata cigaba da rayuwa a gidan nan a matsayin ‘yar aiki? Tunda matsayinta bai wuce hakan ba, duk wasu alamu sun nuna. Mustapha ya tabbatar mata ba zai taba iya yi mata adalci ba tun ma tana ita kadai matarsa balle yanzu da ya hadata da wadda yake kauna. Ta sake daga ido ta kalli kanta a mudubin; to wai zaman me take a gidan Mustapha ne? Shi dai ya gama nuna mata ba zai taba canzawa ba; duk wani abu da yake yi mata a halin yanzu zata iya yiwa kanta. Bukatar aure ce kawai wadda dama sai ya gama dama yake zuwa wajenta tunda ta daina binshi dakinsa. Ta yanke kauna daga samun adalci a wajen Mustapha komai yawan kaunar da zata nuna masa da kulawarta ga ‘yayansa. Ta tabbatar shi ba zai iya nuna mata kauna da kulawa ba; watakila sai dai idan ana kwatan soyayya ta kwata ta karfin tsiya daga wajen Mustapha; to idan sai an kwata kuma ya koma ba so ba. Ta ja gwauron numfashi, ta zuba fuskarta a tafukan hannayenta, dumin hawayenta ne ya sa ta daga fuskar tata ta kalli hawayen da ya diga a hannuwanta. Ta jijjiga kai tana murmushi a lokacin da hawaye yake gangarewa a kumatunta; ta gaji, ba zata iya ba, ta gaji da wannan kokawar, ta gaji da kokawar kwatowa kanta mutunci da so a wajen Mustapha, ta gaji ba zata iya cigaba ba.

Ta mike kamar wadda aka tsikara ta nufi gaban wardrobe, ta sauke akwati ta fara zuba kayanta. Ba zata iya cigaba da wannan rayuwar ba, gara kawai ayi ta ta kare.

A hankali ya turo kofar dakin ya shigo da sallama, fuskarta fayau kamar ma farinciki take. Ta dubeshi ta amsa sallamarsa ta cigaba da jera kayanta a cikin akwatin. Ya dubeta da mamaki yace ‘Ya naga kina hada kaya, ko wardrobe din kike gyarawa?’

PAGE 208

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta dan tsaya da zuba kayan ta kalleshi tace ‘No ba gyarawa zan yi ba, gidan mu zan tafi.’

Mamakinsa ya karu, ya karsa matsawa kusa da ita ‘Ban gane gidanku zaki tafi ba bayan yanzu zamu tafi, shigowa ma nayi na gaya miki ki fito kuyi sallam da Naja zamu wuce.’

Ta rufe akwatin ta zuge sannan ta juya cikin wardrobe din ta dauko jakarta ta sake ajiyewa a kan gadon. Ta kalleshi tace ‘Ka bani minti biyar na karasa hada kayana na fita sai ka rufe gidan gaba daya don nima gidanmu zan tafi.’

Ya dan fara fusata ya matsa ya sha gabanta yana cewa ‘Bana son wulakanci Khadeeja, wai ke me yasa ne duk lokacin da mutum yake cikin uzuri yake so kiyi masa wani abu sai kin yi fitna ne? an gama magana dake amma yanzu saboda kina so ki sa muyi missing flight zaki fara maganar zaki tafi gida.’

Tayi murmushi ta daga kai ta kalleshi tana cewa ‘In sha Allahu wannan itace fitna ta karshe da zan yi maka Mustapha, daga ita ba zan sake ba. Gidanmu zan tafi Mustapha saboda na gaji da aurenka, kuma na gama aurenka daga yau. Zaka iya sakina yanzu ko kuma duk lokacin da ka sami natsuwa ka rubuta min takardar sakin ka aiko gida; amma ba zan sake zama a matsayin matarka ba.’

Gaba daya yawun bakinsa kafewa yayi saboda bai taba zaton Khadeeja zata iya fada masa haka ba, ya saketa! Kuma a wannan lokacin; ya kalleta ya sunkuyar da kai, jimawa kadan ya sake kallonta sannan yace ‘Saboda kujerar Makka kike so ki kashe aurenki Khadeeja? Kujerar da na gaya miki next year dake za a tafi. Tukunna ma kin san hukuncin matar da ta nemi saki a wajen maigidanta ba tare da wani dalili ba?’

Ta jijjiga kai tana murmushi a daidai lokacin da kwalla ta fado daga idonta, ta share kwallar sannan tace ‘Ko daya, kujerarka ba ta kai ta daga min hankali ba tunda dai kasar Makka ta Alla ce ba taka ba. Alhamdulillahi ma kace wadda ta nemi saki ba tare da dalili ba; don ni ina da dalili kuma Allan da ya halicceni ya fi ni sanin dalilin. Amma tabbas yau zan bar gidanka da aurenka Mustapha.’

Ya ja baya ya sake kare mata kallo, yace ‘Kin san me kike fada kuwa Khadeeja? Please idan wasa kike ki bari kada ki saka muyi missing flight.’

PAGE 209

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Tayi yar dariya yayinda ta ware hijabinta ta saka tana cewa ‘Ba wasa nake ba, amma dai kana da zabi. Ka sakeni yanzu ko kuma ka tafi idan ka dawo ka rubuta min takardar ka aiko min gida.’

Ta kwayeshi ta bude dauko jakarta daga kan gadon ta nufi gaban mudubi.

Yana tsaye mamaki ya hanashi magana. Yana daga kai idonsa ya sauka a kan agogon bangon yake kafe a saman dakin; 12:52pm agogon ya nuna; shi da aka cewa su zama suna cikin airport kafin azahar.

‘Mteww!’ ya ja dan gajeran tsaki sannan ya fesar da iska daga bakinsa. ‘Khadeeja yanzu ya kike so nayi da yaran bayan mun gama magana dake? Kuma me nayi miki da har zaki rike a matsayin hujjar da ta saka zaki ce na sake ki?’

‘Yara kam ai yanzu ba matsalata bane, duk yanda kayi da su daidai ne. Ni dai zan tafi, yanzu in sah Allah.’

Ta sauke akwatinta ta fara ja tana nufin koafr dakin.

Ya bi bayanta da kallo; to me yayi mata da har zata ce ya saketa a wannan lokacin? Anya kuwa ta san menene zawarci? Kawai saboda bakin cikin ba da ita zai fara tafiya aikin Hajji ba? Ko ma me take nufi ya kamata ya cika mata burinta, watakila kafin ya dawo ta dawo hayyacinta kuma ta gane mahimmancin aure a rayuwarta. In ya so idan ya dawo da ita sai ta hakura ta zauna tunda dai shi bai ga wani abu da yayi mata ba.

Tana daf da karasawa bakin kofar yace ‘Khadeeja.’

Ta juyo ta dan tsaya ‘Ki je na sakeki saki daya.’

Ta yi sauri ta juya fuskarta saboda kaucewa hada ido da shi; duk da ita nema kuma da yakinin zai aikata haka amma sai da fitar kalmar tayi mata ciwo. Ta sake juyowa cikin murya kasa-kasa tace ‘Nagode.’

‘Zaki yi nadamar rabuwa da ni Khadeeja.’ Ya fada a gajarce.

Ta kalleshi tayi murmushi sannan ta kawar da kanta ta faki idonsa ta goge kwallar da ta taru a kwarmin idonta.

Bugun kofa ne ya klatsesu da Shukra tana cewa ‘Abba Anti tace zaku makara fa.’

‘Um, gani nan zuwa.’ Ya amsa daga cikin dakin.

Ya wuce Khadeejan ya bude kofar ya fice. Ta bi bayansa janye da akwatinta. Shukra ta tsaya a gefenta tace ‘Anti kema harda ke za a tafi?’

Ta kama hannunta tace ‘A’a ni gidanmu zan tafi ba da ni za a tafi ba.’

PAGE 210

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

‘Gidan Mommy? To damu zaki tafi?’ ta tambaya da mamaki.

‘Eh, gidan Mommy zan tafi amma ba daku zan tafi ba. Abbanku zai gaya muku wadda zata zauna da ku.’

Gaba daya yaran suka zuba mata ido suna kokarin gani me take fada. Ta kwalawa Hafsa kira ta bata umarni ta hada kayanta su tafi gida. Ba tare da bata lokaci ba ta juya.

Ta dubi Naja wadda take zaune tana binsu da kallon mamaki tace ‘Maman Rukayya sai kun dawo, Alah ya amsa ibada Alah ya maimaita mana.’

‘Amin.’ Ta amsa a gajarce sannan ta dubi Mustapha tace ‘Ban fa gane ba, me yake faruwa ne?’

Kafin ya bata amsa tuni Khadeeja ta ja akwatinta ta fice daga parlor din. Shukra wadda ta karasa ta fada jikin Abbanta ta rushe da kuka; saboda ta kasa fahimtar me yake faruwa su da aka ce za ayi tafiya har Abbansu a barsu da Anti kuma Antin ta fara tafiya.

Ya dubi naja yace ‘Cewa tayi na saketa kuma na saketa, tunda ita ta nema.’

Ta dan firgita ta dafe kirji, bata san lokacin da yawun da yake bakinta ya wuce ba tace ‘Saboda me? Kai kuma ka biye mata?’

‘Saboda bakin cikin zan tafi dake Hajji ban tafi da ita ba.’ Ya fada cike da adcin rai.

Ya karasa ya zauna a kan kujera a jigace kamar wanda aka tura.

Sukayi cirko cirko suna kallonshi.

Habib ya shigo a guje ko sallama bai yi ba, yana cewa ‘Abba na ga Anti tafi. Me yake faruwa ne? waye zai zauna damu?’

Ya mike a jigace yana cewa ‘Maza kowa ya debo kaya ko kala daya ne mu wuce, sai na ajiyeku gidan Hajia. In ya so ko gobe sai ku dawo da Yaya Jidda ku debi kaya. Antin ta tafi.’

Ya fice batare da ya sauraresu ba Naja ta rufa masa baya.

Nasreen ta kalli Habibi ta kare gefeb bakinta kamar me rada tace ‘Ya saketa.’

Ya zaro ido zai yi magana suka jiyo muryar babansu daga kafar bene yana cewa ‘Maza fa ku sauko.’

Suka mike gaba daya suka shirya suka fice.

PAGE 211

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ba karamin mamaki Hajia da Alhaji suka yi ba da Mustapha ya gaya musu ya saki Khadeeja.

Shi kadai ya shiga da yaran don ita Naja ma cewa yayi ta zauna a mota saboda kada ta bata musu lokaci. Suna shiga yaran suka wuce cikin gida shi da Hajia da Alhaji suka tsaya a parlor yana musu bayanin abinda ya faru.

Alhaji yace ‘To kai wane irin rashin hankali ne wannan? Ai don mace tace a saketa ba a sakin nata. Zuciya ce ta kwasheta kuma sai daga baya zata zo tana nadama. Da ka sani ka barta da aurenta idan ma tafiyar zata yi ta tafi idan ka dawo kalau zaka ga ta dawo.’

A fusace yace ‘Alhaji yarinyar ce ta kureni, ita kullum sai dai ay mata yanda take so amma ita ba zata yi yanda ake so ba? Taje idan mutuwar aure dadi ne ai ta samu sai ta dana ta fi shiga hankalinta.’

Hajiya tace ‘Ai shikenan tunda haka ta zaba. To yanzu in Hammad din da Rukayya? Ban gansu tare da ‘yan uwansu ba.’

‘Shi Hammad dama yana gidansu, ita kuma Rukayya gidansu ta kaita.’

‘Ai shikenan, Allah ya sauwake. Idan ka dawo a san yanda za ayi domin dai aure bai kamata ya mutu saboda kujerar hajji ba.’ Alhaji ya fada cike da nadama.

Mustapha ya dubi Hajia yace ‘Mukullin gida yana hannun Habib in an jima Baba Sani abokina zai zo ya kaisu shi da Afaf su debo kayansu su rufo gidan. Idan sun dawo sai ya bawa Alhaji mukullin gidan ya ajiye min. akwai ATM card din a hannun Afaf idan ana bukatar wani abu na kudi sai taje ta ciro ta bayar.’

Yayi musu sallama ya fice zuciyarsa cike da damuwa.

……….

Zuciyarta fayau ta fito daga gidan tana addu’ar Allah ya sa iyakar zamanta kenan da Mustapha tunda ta san saki daya yayi mata. Sun tsaye a bakin titi ita da Hafsa suna jiran mota ya zo ya wucesu a guje a tashi motar. Ta bi bayan motar da kallo tana murmushi; ta tuna lokutan da yake zuwa ya wuceta a titi zata tafi makaranta amma ba zai iya rage mata hanya ba. Tayi murmushi ta kawar da kai. Jimawa kadan da wucewarsu ta sami mota, suka hau suka nufi gidan Mommy.

Tana tura gate din gidan Baffa ne a tsaye yake rufe motarsa, da alama dawowarsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login