Showing 36001 words to 39000 words out of 99112 words

Chapter 13 - Mijin Marigayiyya Part Complete Hausa Novels.docx

17 Sep 2025

77

/>
MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

‘Ni dai na gaya miki bana son ki barta a gidan idan ina nan tunda ke bakya nan, ki sami inda zaki ajiyeta idan na fita sai ta dawo gidan.’

‘Uhhm!’ Ta amsa sannan ta shige wankan cike da takaicinsa, har ji take kamar zuciyarta tana turiri. Zuwa makaranta lecture kawai ya zama wata drama.

Nan da nan ta karasa shiryawa ta shirya yaran, ta hada tea ta zauna tana sha. A haka Mustafa ya fito ya samesu lokacin 7:15am. ‘Ku tashi muje.’ Ya fadawa yaran.

Ta mike rike da kofin shayinta tace ‘Bari na dauko hijab dina na saka ku rage min hanya.’

‘A’a zaki makarar damu ne fa, gashi ko shayi baki gama sha ba kuma kin san idan suka makara korosu za ayi.’ Ya juaya ga yaran wadanda sun riga sun mike kowa da kayansa a hannu yace ‘Mu je.’

‘Anti sai mun dawo.’ Suka fada sannan suka juya suka fice ya bi bayansu.

Ta bi bayansa da kallo cike da mamaki; ta kasa gane motarsa ce baya son ta dinga shiga ko kuwa tsabar bakin ciki ne a kan zata fita yake hanashi rage mata hanya. To amma kuma yana kaita unguwa, ko da yake wannan fita ce da shi ya ga dama kuma kusan duk inda zata tunda ta aureshi tare yake kaita da yaran suna biye da ita. To me yasa idan dai makaranta zata tafi sai ya san yanda yayi ya tafi ya barta ba tare da ya ko da rage mata hanya ba?

Haka har ta gama shirinta ba tare da ta samo amsar tambayarta ba; ta fito ta sami Rashida a kitchen tace ‘Idan babansu ya dawo ki koma daki ki zauna in ya fita sai ki fito ki cigaba da aikin; idan Shukra ta zauna a wajensa shikenan idan kuma ta taho wajenki to don Allah kada ki bari tayi kuka yaji.’

Tayi mata sallama ta fice tana sauri saboda 7:20am ta riga tayi kuma bata da tabbas din zata iya kaiwa BUK kafin 8:00am.

Ta kusa isa titi Mustapha ya karyo kwana ya shigo layin, ta dauke kanta daga kallon inda yake; bata sani ba ko ya ganta ko bai ganta ba. Ta karasa titi cikin sanyin jiki ta hau Napep tambayoyi daban daban suna ta yawo a kanta; wai ina babe dinta ne? wanda yake son ta? Wanda kafin aurensu har so yake ya daukota daga makaranta ya kaita unguwa ko ya kaita gida don dai tana hanashi ne saboda ta san Baffa ba zai bari ba a lokacin.

PAGE 92

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

To shikenan soyayya ta kare ko me Mustapha yake nufi da ita? Shekara daya fa kenan da ‘yan watanni da aurensu.

Kwanci tashi cikin wannan rayuwar da Khadeeja take a gidan Mustapha har ta gama level 2 a karatunta ta shiga level 3, kuma shekararsu biyu kenan da Rashida mai aikinta. Zaman dai haka ake yinsa cikin dagewa da dagiya; idan Mustapha yana son bukatarsa a wajenta sai taji kamar ba shi ba saboda yanda yake kwantar da kai ya samu bukatarsa ta biya. Amma kuma da zarar tayi maganar karatunta ko wani abu da zai sa ta fita daga gidan ba tare da ta tafi da yara ba to sai ya nuna bacin ransa. Domin a halin yanzu kowa a danginsu ya santa da ‘yayanta domin tare ake ganinsu ko bikin wa ake yi. Gidan Mommy kuwa sun mayar da shi kamar gidan kakarsu, kuma da yake sun sami karbuwa sai suka sake sakewa.

Karatunta yana tafiya daidai tunda ta saka auduga ta toshe kunnenta daga duk wata mita ta Mustapha, sai dai kawai kullum a gajiye take daga aikin gida da kuma aikin tunanin abinda zata yi Mustapha ya daina nuna mata halin ko in kula. Yaran basu saba bata matsala ba a da, amma zuwa yanzu duk tana neman ta rasa kansu; musamman Afaf da Nasreen. Idan dai aiki ta saka su ba zasu ce ba zasu yi ba amma idan basu ga dama haka za suyi kunnen uwar shegu da ita sai dai ko ta yi aikinta ko kuma ta sa Rashida tayi mata. Sannan kuma yanzu Afaf ta kulla kawance da Samira ‘yar wajen Yaya Jidda, don haka kusan duk wani motsi na Khadeeja Afaf sai ta gaywa Samira wadda take kaiwa uwarta rahoto na kai tsaye; don haka ne ma matsawar da Yaya Jidda takewa Khadeejan ta karu.

Sai dai a yanzu ba wannan ne damuwar Khadeeja ba, babbar damuwarta itace rashin haihuwa. Tun bayan da tayi bari a loakcin corona ko batan wata bata sake yi ba gashi ana neman shekaru biyu. Zaman gidan baya mata dadi, bata jin dadin yanda yaran suke mata, musamman Afaf wadda a da take tunanin sun zama daya. Tana fatan itama Allah ya bata ‘yaya wadanda zasu kalleta a matsayin uwa.

PAGE 93

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta rigashi kwanciya kamar yanda suka saba saboda yanda ta kula idan ta zauna jiransa su kwanta tare ita ake cuta tunda dole ta tashi kafin asuba ta shirya yara. Sai wajen sha biyu saura sanna ya gama abinda yake ya kwanta a kusa da ita, ta juya ta gyara kwanciyarta. Yana kwance amma ya daga waya yana chattinga kamar yanda ‘yan kwanakin nan ta kula kullum kafin ya kwanta sai yayi chatting. Ta mike taje ta yiwo fitsari, ta sha ruwa sannan ta dawo ta kwanta, zuwa lokacin ya gama chatting din ya ajiye wayar yana azkar. Ta kwanta ta gyara kwanciyarta, bayan da ta kula ya gama azkar din ta lalubo hannunsa ta rike cikin sanyin murya tace ‘Abban Afaf.’

‘Umm.’ Ya amsa yana kallonta duka da hasken da yake cikin dakin bai kai ya kawo ba.

‘Uhm, gaskiya ina son zuwa asibiti naga gynae doctor.’ Ta fada tana wasa da hannunsa wanda ta rike.

Ya rike hannunta a cikin nasa ya kara bata hankalinsa yace ‘Baki da lafiya ne?’

‘No ba wani specific issue. Ka san dai kwanaki nace maka ina son naje a duba aga abinda yasa har yanzu ban sake samun ciki ba, kada naje wata matsala ce nayi ta zama gara naje a duba.’

Ya gyara kwanciya ya kara matsowa kusa da ita ‘Kina dai so ki dorawa kanki damuwa, har yanzu fa ba a yi shekaru biyu da barin ba. Iya wannan ya isa ya sa ki san cewa lafiyarki kalau, kawai Allah ne bai kawo ba tunda wancan din ma ba asibiti kika je kika samo ba ko?’

‘Na sani, amma dai gaskiya ina so naje a duba ni din na sami nutsuwa. Tunda ka ga idan naje aka ce min lafiyata kalau ai dawowa zan yi kawai na cigaba da addua’a, idan kuma matsala ce sa na nemi maganinta.’

‘Babu wata matsala kina dai son tonowa kanki matsalar. Ke yanzu ma da kike neman ciki ido rufe ya zaki yi da karatun? Tunda gashi kin shiga level 3 kuma ke da kanki kina cewa ya fi wahala. Ya zaki yi da laulayi ga karatu? Ko har kin mata ne? ai zai fi sauki idan ma dolene sai kin je asibitin ki bari ki gama karatun kafin ki kwantar da kanki.’

Suka yi shiru na dan lokaci, kowa da abinda yake tunani.

PAGE 94

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Jimawa kadan tace ‘Ina son zuwa gaskiya, amma dai ina jin zan bari mu gama examsa din wannan semester in ya so kafin a koma hutu sai na samu naje.’

‘To Allah ya kaimu.’

Tana son ta haihu duk da dai Mommy ma tace mata lafiyarta kalau amma ita gaskiya tana so taje a duba ta. Kuma yanda Mustapha yake gwada mata halin ko in kula idan ana maganar haihuwa ya sa gaba daya ta fara tunanin ko bai damu da ta haihu ba; to ya ma za ayi ya so ta haihu tunda shi masoyiyarsa ta haifar masa yara har uku?

Haka tayi ta sake-sake tana juyi, sai gefin asuba sannan bacci ya dauketa.

______

kamar kullum yana shiga office din yau ma damuwarsa ta yaye; musamman yanda kamshin turarenta ya yiwa kofofin hancinsa maraba bayan da ya shiga office din nasa ya rufo kofar. Wannan ya tabbatar masa da cewa ta riga ta zo office din watakila wani office din taje. Ya ajiye jakarsa a kan table ya karasa ya zauna a kan kujerarsa cike da farin ciki.

Sabuwar sakatariyarsa Naja’atu Musa Bello; watanta uku da fara aiki amma soyayya mai karfi ta kullu a tsakanisu. Duk wata damuwa da Khadeeja zata dora masa da ya shigo office din ya ganta yake mantawa da ita, idan kuma an tashi daga office ko a ranakun da babu aiki ya kan je gidansu zance. Duk da dai manya basu riga sun shiga zancen ba amma dai yana ji a jikinsa Naja’atu tasa ce.

Bai dade da zama ba ta turo kofar ta shigo, daga tsaye ta sakar masa kyakkyawan murmushinta wanda baya gajiya da kalla.

‘Ranka ya dade barka da shigowa.’ Ta fada tana juya kwayar idonta.

‘Good Morning my dear.’ Ya amsa yana ta faman murmushin da yake barazanar karawa bakinsa fadi.

Ta karasa ta zauna a kujerar gabansa, sannan ta dauki file a kan teburin ta mika masa. Nan take ya buda ya fara karantawa yana mata tambayoyi tana yi masa bayani. Bayan sun gama ya ajiye file din a gefe ya dubeta yace ‘To meye labari?’

Tayi dariya ta sunkuyar da kai a kunyace tace ‘Komai normal.’

‘Good. So nayi mana order din lunch ko? Don na san ko ance kizo muje mu ci a waje ba kya son zuwa eateries, sai shopping ko?’

Tayi dariya tace ‘Gara dai ayi order din.’

PAGE 95

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Tayi dariya tace ‘Gara dai ayi order din.’

‘Ba damuwa, kiyi mana order din sai ki turo min account number na tura kudin.’

‘Yes Boss, an gama.’

Suka yi dariya gaba daya.

Tana shirin tashi yace ‘Yauwa, gobe ana open daya a school din su Afaf, please idan kika shigo around 10am sai kije musu, ki jiyo min duk bayanasu da performances din su.’

Ta gyara zama tace ‘Uhm, ok. But Madam ba ta nan ne ko bata jin dadi?’

Ya gyara zama ya fara lilo a kujerar da yake kai yana kallonta sosai sanna yace ‘No, lafiyarta kalau but na dai fi son ke kije ki jiyo min komai.’

Cike da farin ciki ta sake fadada murmushinta tace ‘Yes Sir, Allah ya kai mu. Kuma Allah ya sa kada kasa yayata ta bani query saboda na shiga aikinta duk da dai nima ‘yayana ne.’

Yayi dariya ‘Kada ki damu, baki da matsala da ita.’

Suka sake dan taba hira sannan ta fice ta koma office dinta cike da farin cikin yanda alakarsu take tafiya ita da ogan nata.

Ba zata taba bari Mustapha ya kufce mata ba don ta ga mijin aure. Ta gama degree dinta har tayi masters, saurayinta na karshe har sun zo gaisuwa haka kawai ya daina zuwa sai ji kawai tayi ana bikinsa da ‘yar uwarsa. Duk da ta san ba wasu shekaru ne da ita masu yawa ba domin shekarunta 28 kacal, amma dai ta san an matsu tayi aure a gidansu; musammam ummanta wadda aikin ma so tayi ta hanata sai tayi aure. Sai gashi ahse mijin yana wajen aikin. A hankali suka saba, har suka kai yanzu da take jin zata iya cewa ta fi matarsa sanin halin da yake ciki da inda yake a kowanne lokaci; don haka ma take jin cewa kwaceshi a wajen Khadeeja kamar kwace goruba ne a hannun kuturu, domin tun yanzu tana jin ta fara samun nasara tunda kullum ita yake kawowa karar Khadeejan sai ta bashi hakuri, ta riga ta fahimci irin zaman da suke yi da Khadeejan don haka ta gama shirya musu; lokaci kawai take jira.

____

Karfe sha daya take da lecture don haka sai da ta gama shirya yaran dukansu suka fita makaranta sannan itama ta karasa ayyukanta ta shirya.

PAGE 96

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Karfe goma da minti biyar tana zaune a gaban mudubi tana gayar fuska ta tuna jiya da daddare Shukra ta ce mata Anty tace kowa ya zo da Mommy dinsa open day 9am to 11am sannan sai a zarce da sports, kuma idan dai ba ta manta ba ma Afaf ta gaya mata duk da section din su Afaf din da ban da na su Shukra. Sai dai basu yi maganar da Abbansu ba, bai gaya mata itace zata je ko shine zai je ba gaba daya ta manta bata tambaye shi ba. Ta mike ta dauko wayarta wadda take ajiye a gefen gado ta dannan masa kira; sai da ta kirawo sau uku duka wayar bata shiga ba, don haka ta yanke hukuncin idan ta fita sai ta fara tsayawa a makarantar tasu tukunna kada taje sai ta wuce makaranta ya bugo waya yace itace zata je ya jika mata aiki.

Nan da nan ta karasa shiryawa ta saka jilbab dinta me kalar lilac sanna ta saka bakin sneakers dinta ta sallami Rashida sannan ta wuce.

Tana zuwa makarantar kai tsaye ajinsu Shukra ta wuce, duk malaman nasu sun santa saboda zuwa daukansu don haka ba tare da bata lokaci ba aka bayanan Shukra da kuma results dinta na CA. tana gamawa ta ja hannun Shukra suka wuce ajinsu Nasreen inda nan ma aka hada mata komai, Nasreen tana cikin wadanda zasuyi wasan tsere don haka bata samu ta fita daga aji ba Khadeeja ta ja Shukra suka nufi secondary section don ta karbo sakamakon Afaf da Habib.

Tun kafin su karasa kofar secondary section din ta hango Afaf tare da wata mata sanye da bakar abaya da brown envelops a hannunta, suna tafe suna hira; ga dukkan alamu a dai malama ce a nan makarantar duk da ita Khadeeja bata taba ganinta ba. Da suka kara matsowa kusa Shukra ta zare hannunta daga na Khadeeja tana cewa ‘La, Anti Naja ce gasu nan ita da Yaya Afaf.’ Ta karasa wajensu da gudu.

Da fara’arta ta cimmusu, suna haduwa ta kara fadada murmushinta cike da girmamawa tace ‘Sannu Anti.’

Cike da mamaki itama ta dan yage baki mai kama da murmushi tace ‘Yauwa, sannunmu.’

‘Ya aiki ya yaran?’ ta kula da yanda ta ke magana kamar da kyara don haka kafin ma ta bata amsa ta mayar da hankalinta ga Afaf tace ‘Yaya Afafa muje na karbo muku CA report dinku ke da Habib na wuce don nima school zan je.’

PAGE 97

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta dan daga gira cikin halin ko in kula tace ‘Anti Naja ta karbar mana ai, dama na su Shukra zata je ta karba yanzu.’

Ta kalli Afaf din sannan ta kalli malamar da aka kira Anti Naja tana mamaki tace ‘Me yasa? Anti ai da kin barshi na zo gashi sun saka ki aiki.’

Ta kawar da kai ta daga gira tana cewa ‘No ba wani aiki, ai Abbansu ne yace na karbar musu.’

Itama Khadeeja ta dan zaro ido tace ‘Oh, ya zo kenan ko yaushe yace a karbar musu?’

Afaf ta fahimci Khadeeja bata san Naja ba kuma bata ma san da zamanta ba, sabanin ita da kannenta wadanda a cikinsu zata iya cewa Shukra ce kawai bata san Naja ba ko kuma ta santa amma bata san wacece ita ba. Ta dan yi gyaran murya tace ‘Anti ba fa malamarmu bace, sakatariyar Abba ce kuma shine ya turota daga office ta zo mana open day din.’

Mamakin Khaddeja ya karu, ta sake karewa Naja kallo na dan takaitaccen lokaci sannan ta bude baki zata yi magana sai kuma ta fasa. Ta dan yi murmushi da gefen baki sannan ta kalli kasa ta dago suka hada ido da Najan wadda take mata kallon da ta kasa fassarawa sanna tace ‘Oh, ok, Umm.’

Kafin ta ce wani abu Habib ya karaso wajen yace ‘Yauwa Anti kin karaso? Dama ke nake jira; don Allah zo muje ki cewa uncle ni bana son basket ball team ya barni na shiga football team. Haka kawai wai saboda ni dogo ne sai nayi basketball.’

Kafin Khadeeja tayi magana Najan tace ‘Au shine baka gaya min ba Habib, ai da ka gaya min nayi masa magana.’

‘Dama Anti nake jira.’ Ya fada cikin halin ko in kula ya zari envelop guda daya daga hannun Najan ya mikawa Khadija yana dariya yace ‘Anti guess what?’

Ta dan yi murmushi yayinda suka bar Naja da baki bude, tace ‘What?’

Ya zaro takarda daya ya mika mata yana cewa 38 naci a Hausa yau don haka yau da shawarma zan yi dinner ko?’

Ta karba tana dariya sannan ta bashi hannu suka tafa tace ‘Iyye, ai dole kaci shawarma tunda yau ka wuce gori. Haba ko kai fa, kullum komai kaci A da B amma a Hasua ka dinga cin D da F.’

Ya mikawa Khaddeja envelop din yana cewa ‘To zaki ga Uncle din?’

PAGE 98

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Tace ‘No, tunda yanzu ka ga kun riga kun fara games ina jin ka bari sai gobe sai na zo na ganshi. Kafin nan munyi tattauna a kan football da basketball din kuma mun yi magana da Abbanka ko?’

Ya gyada kai ‘Eh, hakane.’

Naja tayi sauri tace ‘Idan kina sauri ne ai sai naje naga Uncle din.’

Tace ‘No ba sauri nake ba, kamar dai goben zai fi dacewa kawai.’

Habib ya katsesu yana mikawa Khadeeja envelope din yana cewa ‘Anti sai mun dawo, goben kya zo kawai.’ Ya wuce ya barsu a nan.

Naja ta mikawa Khadeeja hannu tana cewa ‘Ki kawo na tafiwa da yallabai takardun tunda office zan koma.’

Ta dan yi murmushi tace ‘No ina ga gara ni na tafi masa dasu tunda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login