Showing 96001 words to 99000 words out of 99112 words

Chapter 33 - Mijin Marigayiyya Part Complete Hausa Novels.docx

17 Sep 2025

85

zan yi ba. Don allah ka daina wannan maganar, ka mayar da hankali wajen kula da iyalinka. Ka ga yanzu ni babu aurenka a kaina, idan taji kana zuwa wajena zaku iya samun matsala. Kazo kai baka sami natsuwa da ta gidan ba kuma ni ba aurenka zan sake yi ba.’

PAGE 243

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ya jijjiga kai don baya son wannan maganar, shi yana ji a jikinsa Khadeeja matarsa ce shi kadai don haka duk tsawon lokacin da zata dauka tana yi masa yanda zai jure. Ya zaro envelope daga aljihunsa ya dora a kan tebur din ya tura mata gabanta yana murmushi yana cewa ‘Wannan na zo kawo miki daman.’

Ta dauko tana dubawa tana cewa ‘Me na samu.’

Ta zaro takardun daga envelop ta fara dubawa; kujerar Hajji Mustapha ya bata. Tana dubawa tana murmushi saboda yanda tunanin zata je Hajji ya faranta mata zuciya. Ta ninke takardu ta fara mayarwa cikin envelop din a daidai lokacin da murmushinta ya ragu. Ta tura masa gabansa tace ‘Na ji dadi Abban Hammad, na gode Allah ya kara arziki da rufin asiri. Amma kayi hakuri ba zan iya karba ba, ba wai don na raina ba ko wani abu. Na gaya maka ba zan sake aurenka ba so kaga babu wani dalili da zai sa na karbar maka kujerar Hajji. Kuma ko na karba ma Baffa ba zai taba barina naje ba sai dai a daura mana aure kafin na tafi; kuma wannan ba zai yiwu ba. Please kayi hakuri! Amma na gode sosai.’

Kafin ta gama bayanin fuskarsa ta canza gaba daya, ba tare da ya dauki takardun ba yace ‘To ki karba mana Khadeeja ki bari a daura mana auren, please ki daina guduna haka.’

Ta sunkuyar da kanta cikin damuwa tace ‘Ba gudunka nake ba, amma dai ba zan iya karaba ba.’

Suka yi shiru na dan lokaci. Jimawa kadan yace ‘To yanzu ya kike so ayi? Ni da sunanki na biya wannan kujera.'

‘Kayi hakuri ba zan iya karba ba.’

PAGE 244

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Suka sake yin shiru na dan lokaci.

Kafin suyi magana aka kwankwasa kofar, ta amsa ta bada izini aka shiga. Wata mace ce abokiyar aikinta ta dan leko tace ‘Anti Khadeeja yallabi yace ke ake jira a studio za a fara.’

‘Yanzu zan shigo.’ Ta fada tana shirin mikewa.

Ta dubu Mustapha tace ‘Bari naje kada ka sa a koreni aiki.’

Yayi dariya shima ya mike, sai dai tana kula dashi bai dauki takardun ba. Ta mika hannu ta dauka sannan ta zagayo ta tsaya a gabanshi, ta mika masa takardun tana murmushi tana cewa ‘Kayi hakuri ka tafi da wannan, wallahi ba zan iya karba ba. Idan na karba ba zan iya da rigimar Baffa ba tunda na san ba zan aureka ba. Kayi hakuri please.’

Ya mika hannu ya karbi takardun yana tsareta da ido kamar mai binciken wani abun a idonta, har sai da ta kawar da nata idon. Ta wuce ya biyota a baya suka fito daga office din, suka jero har zuwa reception sannan tayi masa sallama ya fice ita kuma ta mike ta nufi studio din. Tana fatan Allah ya sa dai kada ta kwafsa saboda yanda Mustapha ya jagula mata lissafi; me zata yi da kujerar makansa? Wato ma shi har yanzu tunani yake saboda kujerar Makka yasa ta ki komawa gidansa? Bai ma san wacece ita ba kenan, zaman da suka yi tare bai sa ya fahimceta ba. Ba ta bukatar kujerarsa kuma ta san tabbas idan ba aurensa ta kuma yi ba ko kashi ta kai gida tace shi ya bata sai sun yi rigima da Baffa, kuma bata shirya karya ba saboda Mustapha wanda take so ya rabuda ita ya daina damun rayuwarta.

……..

Tana tashi daga waje aiki ta wuce gidan Yaya Mama, tayi sa a yaran duk sun tafi islamiyya don haka ta sami Yaya Mama ita kadai. Bayan sun gaisa Yaya Mama tace ‘Bari na samo miki ruwa ko lemo.’

Ta dafe cinyarta tace ‘Barshi kawai sai da na tsaya na ci abinci sannan na karaso.’

Ba tare da bata lokaci ba ta fara bata labarin kujerar Makkan da Mustapha ya kawo mata dazu.

Sai da ta gama bata labarin suka sheke da dariya a lokaci guda sannan tace ‘Wai ni zai saya da kujerar Makka dan rainin hankali.’

PAGE 245

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Yaya Mama tace ‘Ai kuwa dan rainin hankali lamba daya, wato tunda ki ce ya sakeki saboda kujerar Makka bari ya biyaki sai ki yarada ya mayar da aurenku.’

‘Ashe kin gane.’

Suka cigaba da hira suna tuna abubuwan da Mustaphan yayi a baya.

Sai da Magriba ta fara kawo jiki sannan Khadeeja ta fara shirin tafiya.

‘Bari na wuce kada magriba tayi min a nan.’

Yaya Mama ta dafa hannunta tace ‘Khadeeja, idan fa zaki koma gidan Mustapha kin san babu wanda zai hanaki ko? Don ni ina ganin ma gara ki koma can din tunda kin ga ko babu komai ga Hammad. Kuma naga har yanzu baki da wani manemin; duk da ma duk wanda zaki aura mijn wata ne don haka kin ga dole ki zauna da kishiya. Ni ina ga gara gidan Mustaphan tunda dai yayi nadama har yana kokarin ya faranta miki.’

Nan take ta bata rai, ta zare hannunta ta dan matsa daga kusa da ita sannan tace ‘Ba zan taba komawa gidan Mustapha ba, aure kuma baya gabana balle na fara damuwa da rashin manemi. Idan Allah ya saka ina da rabon aure a gaba to duk wanda Allah ya sa shine mijina zan aura amma fa in sha Allahu ba zan sake auren Mustapha ba. Mutumin da ya daukeni ne kawai a matsayin solution to his problem. Ko yanzun ma da yake ta kokarin na koma gani yayi kirikiri matar tasa ta kasa kula masa da gidan da yara kamar yanda nayi. Shi yasa ya lallabo ya mayar da ni cikin wahalar da Allah ya rabani da ita. Ba zan koma na, can su karata.’

Ta mike ta dauki jakarta, don haka itama Yaya Maman ta mike. Ta san idan ta fiya takurawa da maganar yanzu zasu yi fada don haka sai ta kyaleta suka yi sallama ta kama hanya.

_____

Wunin ranar gaba daya bai yi masa dadi ba. Ko da dai bai sa ran Khadeeja zata karbi kujerar ba tare da an kai ruwa rana ba amma kuma bai sa ran zata ki karba haka gaba daya ba ba tare da wata kofa ta sulhu ba. Haka ya wuni a office din babu walwala. Sai da yamma tayi sannan ya kwashi kayansa ya koma gida.

Yana shiga dakinsa ya ajiye takardun hannunsa a kan mudubi; takardar kujerar da ya bawa Khadeeja ce a sama tare da wasu takardun na office.

PAGE 246

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Tunda ya je sallar magriba masallaci ya dawo yayi zamansa a kasa shi da yara. Da farko ta dan zauna a wajensu ana hira gaba daya, daga baya kuma sai ta tashi ta haye sama ta barsu.

Dakinsa ta shiga don ta samu ta huta domin nan ne kawai idan ta rufo kofar Rukayya ba zata so ta buga ta tasheta ba. Har ta wuce mudubin sai kuma ta koma da baya, ta sa hannu ta dauki envelope din da ta ja hankalinta. A bude take don haka sai kawai ta zaro takardun ta fara karantawa.

Nan da nan kanta ya kulle; tabbas wannan sunan Khadeeja ne. To me hakan yake nufi? Suna tare kenan yanzu ta zama bazawararsa ko me? Tunda idan ba wata alaka ce tsakaninsu ba me zai saka har ya biya mata kujerar Makka? Kenan ma ita Mustapha zai rainawa hankali, ya saki matar sannan ya koma yama binta? Gaskiya ba zata yarda ba.’

Ta daga kanta ta hango wayarsa tana chaji a kan bedside durowa; nan da nan ta ajiye takardun ta karasa ta dauki wayar. Ta riga ta san PIN din don haka kai tsaye ta bude ta fara duba whatsapp; sai dai har ta gama dubawa bata ga sunan Khadeeja ba. Tana duba calls taga sunan ‘Sweetheart’ shine sunan da yayi saving lambarta tun yana zuwa zance kuma bai taba canzawa ba. Bayan rabuwarsu Najan ta goge ta saka maman Hammad amma bata san yanda aka yi ya mayar ba. Ta mayar da wayar ta ajiye cike da damuwa da takaici.

Ta tashi ta dawo daya gefen gadon ta zauna ta zuba tagumi; tabbas zasu yi rigima da Mustapha don ba zai yiwu ba ya dinga zagayawa wajen tsohuwar matarsa suna raina mata hankali.

Sai wajen karfe tara na dare ya hawo saman, lokacin ya je sallar isha’i ya dawo kuma sun gama cin abinci da yara. Zuwa lokacin itama ta gama duk abinda take yi ta kwantar da yara tana kwance a kan gadon dakinsa sanye da rigar bacci ta mike kafa tana kallo a waya ya shiga daki. Bayan ta masa sallamarsa ta mayar da hankali kan wayar hannunta. Kai tsaye ya wuce ciki ya canza kayansa sannan ya zauna a kan carpet din dake gaban gadon ya mike kafa ya janyo computer dinsa ya kunna ya kama aiki.

PAGE 247

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Yawanci idan dai har yana da aiki to ya kan kai dare sosai a zaune yana aikin, ita kuma ba zata iya jira ba. Don haka ta mike ta zauna ta ajiye wayar da take hannunta tayi gyaran murya sannan tace ‘Uhm, na ga wata takarda, wai Maman Hammad ka biyawa Makka?’

Bai yi mamakin jin tambayar daga gareta ba duk da bai sa rai da ita ba, amma dai ya san ya manta ya ajiye takardun a kan mudubinsa. Ba tare da ya bar aikinsa ba yace ‘Eh ita na biyawa, akwai matsala ne.’

Cike da neman rigima tace ‘To kuma a yanzu meye tsakaninka da ita tunda naga dai babu aure. Ko kuma kun mayar da auren ne nice ban sani ba.’

Har yanzu hankalinsa yana kan aikin yace ‘Bamu mayar ba muna dai kan hanya.’

‘To shine kuma ka biya mata Hajji.’

Ya dago ya dubeta yace ‘Eh, akwai matsala ne?’

‘Gani dai nayi bai dace ba tunda babu aure a tsakaninku.’

‘Wannan ra’ayinki kenan.’

Ta kula so yake yayi mata wulakanci don haka ta mike ta zauna sosai tace ‘Ina fatan dai ka san yanzu ita din ba muharramarka bace, kuma ina fatan ka san ba zai yiwu ina nan gida ina maka biyayya wai ni matar aureba ka dinga zagayewa wajen tsohuwar matarka wadda ka saka da hannunka, ba zan dauka ba gaskiya.’

Ya dago ya kalleta rai a bace yace ‘Sai ki dau mataki a kai.’

Ta kula kamar haushinta yake ji sai dai bata san dalili ba, don lafiya kalau suka rabu da safe ya ajiyeta a office sannan ya fice; to meye ya harzukoshi hakan daga yin magana?

‘Kada fa ka gaya min magana daga tambaya, na dai gaya maka ba zai yiwu ba ina nan ka kulleni a gidanka a dinga ganinka a gari kana yawo da wata matar banzan.’ Ta fada tana mikewa tsaye.

A fusace yace ‘Khadeejan kike cewa matar banza saboda wulakanci?’

Sai dai kafin ya rufe bakinsa ta fice daga dakin ta rufe masa kofar; wanda wannan dabi’arta ce idan dai ya bata mata rai sai ta gaya masa magana mai zafi sannan take fita daga inda yake.

Yayi tsaki ya cigaba da aikinsa don so yake ya gama aikin kafin ya kwanta.

PAGE 247

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Haka rayuwarsu ta cigaba. Khadeeja taki yarda a mayar da aurensu sannan shi kuma ya kasa tunkarar Baffanta da maganar don ya san ba za a yi mata auren dole ba. Amm kuma ya ki ya daina bibiyarta; har ta kai baya iya sati bai nemeta yaganta ba. Idan ya je gidansu wajen Hammad ta ki fitowa to tabbas zai sameta a office. Waya kuwa daman bata yankewa don idan ma ta ki dauka haka zai yi ta kiranta har sai ta gaji ta dauka. Duk wata kalma da zai yi amfani da ita wajen ganar da ita ta yarda su mayar da aurensu yayi amma ta sanar da shi ba zata iya komawa ba.

Duk lokacin da ta ji kamar zata hakura su koma idan ta tuna yanda yake banzatar da ita a gidan kuma ta tuna yanzun ma sai da ya rasa yanda zai yi da gidan sannan ya fara nemanta sai kawai ta ji ta fasa. Tana sane da duk wata rigima da ta faru a gidan tunda kusan duk asabar a wajenta Habib yake wuni, duk abinda ya dameshi sai ya je ya sameta ya gaya mata.

Lokaci zuwa lokaci tana samun masu nuna sha’awar aurenta sai dai auren gaba daya ya fice mata daga rai; don haka yawancinsu bata ma bari su zo gidansu. Kuma duk inda taje idan dai ba an santa a wajen ba to tana gabatar da kkanta ne a matsayin matar aure don ma kada wani ya zo mata da wata magana; don haka mutanen da suka santa sai suka kasu kashi biyu, wasu suna ganin tana da aure wasu kuma suna ganin bata da aure. Amma kuma yawancin mutane kasa tambayarta sukeyi.

______

EPILOGUE

Bayan shekaru 3.

An yi auren Afaf an kaita gidanta, yaron da ta aura kanin abokin Abbanta ne. da kanta taje ta kaiwa Khadeeja katin bikin nata wanda ta karba cike da girmamawa. Tayi mata magiya a kan taje amma duk da haka ba taje ba, domin bata son abinda zai hadata da Naja da dangin Mustapha a cikin taro. Kuma duk yanda Mustapha ya so ya sakata a cikin shawarar bikin Afaf din da inda zai sayi furniture haka ta zame da wayo da dabara har ya gaji ya rabu da ita.

Yana nan dai yana bibiya da kuma addu’ar ta yarda su mayar da aurensu. Kuma a yanda yake fuskanta tabbas hakansa ya kusa cimma ruwa.

PAGE 248

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Yana zaune a dakinsa a kan dadduma yana hutawa bayan sallar la’asar kwana biyu bayan auren Afaf haka kawai ya dauki waya ya kirawo Khadeeja. Ya gyara zama ya jingina da bangon da kofar dakin take jiki ta yanda idan aka budo kofar aka shigo zai zama yana bayan kofar kenan.

Bayan ta amsa suka gaisa suka shiga hirarrakinsu, tana tambayarsa labarin biki. A haka har yace ‘Kin ga da kin yarda ai da tare da namu za adaura.’

Tayi dariya tace ‘Kai kuwa ka ki ka bar maganar nan.’

‘Ba zan bari ba Khadija, har sai kin amince. Ko na tsufa ma sai na dawo dake ko da takaba ne kya yi min sai mu hadu a aljannah.’

Dariya kawai tayi don bata da amsar da zata bashi. Suka yi shiru na dan lokaci sannan yace ‘Duk wani condition da kike so Khadeeja ki saka nayi miki alkawarin zan cika in dai zaki zama mata ta. Just one more chance Khadeeja, ki daina wahalar da zuciyata haka.’

Tayi murmushi mai sauti ba tare da ta ce masa komai ba; tabbas yana nema ya gamsar da ita ta sake amincewa da aurensa, amma a halin yanzu bata san amsar da zata bashi ba. Ya gaji da shirun kuma yana ji a jikinsa cewa kalamansa sun fara yi mata tasiri. Ya katse shirun yace ‘Gobe da safe zan shigo, ok?’

‘Ok, Allah ya kai mu. Amma ina da programme da safe so ka bari sai bayan azahar.’

‘Ok, I will take you out to lunch then. No execuses.’

Tayi dariya ‘Ka dai san ba zan je ba ko? Kada ma ka fara wata rigimar da ban.’

‘In dai rigima ce ai a wajenki na koya. I will see you tomorrow at lunch.’ Ya ajiye wayar ba tare da ya bari tace wani abu ba.

Ko da ba zata yarda ya fita da ita lunch din ba ya fi so ta barshi ya kwana da murnan zai fita da Khadeeja gobe, in ya so idan yaje office din suyi fadan da suka saba.

Tana tsaye a jikin kofar dakin tana jinsa, duk abinda ya fada tana ji. Sai da ya ajiye wayar sannan ta banka dakin ta shiga a fusace. Firgigit ya juyo ya kalli kofar da aka mako, yace ‘Ya haka kamar zaki fizge kofar? Me ya faru ne? ko wani abun ya biyoki?’

PAGE 249

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta tsaya tana masa kallon raini tana jijjiga, sai da gaji da kallon nasa sannan a fusace tace ‘Mustapha na gaji da wulakancin da kake mina akna matar nan, shekara hudu ana abu daya saboda tsohon naci. Wallahi babu ruwan Allah da kun taba aure alakarku haramtacciya ce. Kuma idan ma zina kuke Allah zai kama ku.’

Fadan nata bai harzukashi don ya saba ji, idan ma bata ji yana waya da Khadeejan ba kulllum cikin duba masa waya take. Basa magana ta whatsapp don haka kullum cikin duna calls take, da zarar ta ga call din Khadeeja to sai tayi wannan masifar. Ya mike ya nade daddumar yana cewa ‘Kada ki kuskura ki jefi khadeeja da wannan kalmar yanzu ranki zai baci, kuma kin sani.’

Ta rike kugu tana dan zare ido tana cewa ‘Ohh! Yanzu kai ka fi son Khadeeja kenan da kanka, kai na jefe ka da koma menene amm kada na jefi Khadeeja ko? To wallahi da kai da ita baku isa ba….’

‘Ke kika sani.’ Ya fada tun kafin ta karasa fadin abinda take fada, ya ajiye daddumar ya kewayeta ya fice daga dakin yana murmushi don yana ji a jiki sa kwanan nan Khadeeja zata dawo

Ta juyo ta bi bayansa da kallo cike da takaici sannan ta wuce ta zauna a gefen gado ta zuba fuskarta a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login