Showing 39001 words to 42000 words out of 99112 words
a gidansa zan kwana.’
Ta bata rai tace ‘Um, sai an jima.’
Ta wuce rike da takardun Afaf da suke hannunta Afafa din tana biye da ita suna hira.
Khadeeja ta bi bayansu da kallo tana mamaki; to yaushe yayi sabuwar sakatariya? Tunda da dai ta san sakatarensa namiji ne. kuma har yaushe sakatariyar ta kai matsayin tazowa yara open day har tana wani cewa a bata takardu ta kai masa? Tukunna ma; kamar dai yaran nan sun sa wannan sakatariyar, itace bata santa ba. To kenan har yayi introducing dinta a wajen yaransa a matsayinta na wa? Me yasa suka kwana tare bai ce mata tazo open daya ba kuma bayan ya fita ma ya kasa kiranta? Wanda tunda ta aureshi duk wata harkar makarantar yara itace take zuwa kuma shi yake saka ta ta zo. To me yasa wannan ya sa sakatariya? Naja? Bata son ta yanke hukunci cewa akwai wani abu tsakanin Mustapha da Naja amma dai tabbas tana da tarin tambayin da zai amsa mata.
Sai da ta raka Shukra aji sannan ta nufi fita daga makarantar.
Tun kafin ta gama fitowa daga cikin ginin makarantar zuwa farfajiyar wajen da ake ajiye motoci ta hangosu, tana rike da hannun Afaf suna magana har suka karasa bakin motar gefen direba ta sa mukulli ta buda motar; ta dan ja baya ta labe. Me take gani ne? Motar Mustapha? To shine ya kawota ko me?
Tana nan a labe ta hangosu; Naja ta bude motar ta zauna a kujerar direba sannan ta yiwa Afaf sallama ta ja motar.
PAGE 99
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Sai da ta karanta lambar motar a fili domin kara tabbatarwa motar Mustapha ce; kanta ya daure gaba daya. To me hakan yake nufi? Ya aiko sakatariyarsa ta zo wa yara open day kuma a motarsa. To hada kudi sukayi suka sayi motar a tare? Ko kuwa dai tsabar kauna ce ko rashin hankali ya sa suke sharing motarsa da sakatariya? Me yasa bai aikota a motar haya ba ko a motar office? Wato motar da ita idan dai makaranta zata ko arage mata hanya bata isa yayi ba itace ya bawa sakatariya take yawo a gari.
Kai! Gaskiya Mustapha ya rainata.
Tayi sauri ta fito daga inda ta rabe lokacin da ta hango Afaf ta nufo wajen.
Tayi mata sallama sannan ta wuce ta fice daga harabar makarantar.
A bakin titi ta tsaya, motocin haya sai tsayawa suke ba tare da ta hau ba; gaba daya ma ta manta inda zata saboda yanda zuciyarta take zafi; me Mustapha yake nufi da ita?
Har ta juya zata koma gida saboda yanda take jin ba zata iya zuwa lecture din ba sai kuma ta tuna idan taje gidan me zata yi? Rufe kanta kawai zata yi a daki tayi kukan da ba zai mata maganin komai ba; don haka ta sake juyawa ta koma bakin titi ta hau motar BUK. Ta kalli waje ta tagar motar, tayi murmushi ita kadai; wai itace a motar haya yayinda ga wata can tana yawo a motar mijinta. Takawar da kai ta share kwalla.
Ko da ta karasa makarantar ta san an riga an yi nisa da lecture din kuma ko ta shiga ma ta san babu abinda zata gane, don haka kai tsaye ta wuce hostel dakinsu Rahma inda suka saba zuwa su huta; duk da dai ta san suna wajen lecture amma ta san inda suke ajiye mukullansu.
Tana shiga dakin tayi watsi da kayanta ta fada gadon Rahma ta kwanta ta fashe da kuka.
Sai wajen karfe daya da kwata sanna suka shigo dakin suka sameta a kwance ta ci kuka ta koshi. Suna shiga Farida tace ‘Haba Malama, tun dazu muke kiranki a waya kin ki dagawa ashe kina nan abunki.’
Suka karasa suka fada kanta Asiya tace ‘Ko dai abun ya zo ne a tanadi goro da ledar amai.’
Ta sake fashewa da sabon kuka.
Suka yi tsuru-tsuru. Rahma ta shafa bayanta tace ‘Kawata kina fadar mana da gaba fa, don Allah me ya faru? Ko Babe bashi da lafiya ne?’
PAGE 100
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Haka suka yita jero mata tambayoyi, ita kuwa tayi banza da su har suma suka gaji suka yi shiru, suka zauna kawai suna jiranta. Sai da tayi mai isarta sannan ta basu labarin abinda ya faru.
Rahma tace ‘kada fa nayi ashar kawata, kut! Wannan wanne kalar wulakancine mutumin nan yake miki?
Farida tace ‘Motar da yake kyashin daukanki yaje ya bawa budurwa ko ma karuwa take yawo a titi? Lallai an gaida uban Afaf.’
Rahma tace ‘Gaskiya idan ya dau yau ya kamata yayi miki bayani na ganewa, duk da babu wani explanatin da zai sa na yarda babu wani abu a tsakanishi da ita ba sakatariya ba ko DG ce wallahi. Yayi miki bayani kuma kema ki karanta masa; wannan ai zubar da mutunci ne kina yawi a motar haya wata sidechick tana yawo a motar mijinki? Mijinki na sunna fa, Haba! Gaskiya dai ya kamata ki san yanda zakiyi ki kwaci kanki a hannun mutumin nana tunda shi ga alama bai san mutunci ba.’
Amina tace ‘Don Allah ku barta ta bai abun a hankali.’
Ta kalleta rai a bace ‘A hankali Amina? Shi a hankali kika ga yana yi min? Ni budurwarsa take cewa wai na kawo takardun yara ta kai masa saboda tsabar samun waje? Haba mana!’
Farida tace ‘Toh shi dai na gani, aure ai ba hauka bane. Wallahi ya kamata ki dage ki gaya masa abinda yake ranki tunda dai an dade ana ruwa kasa tana shanyewa, ai ba siyoki yayi a bakin rimi ba da zai mayar dake kamar wata sokuwa.’
Amina tace ‘Don Allah ku bari a bi abun a hankali, miji fa ba kamar saurayi bane haba!’
Rahama ta ja hannun Amina tace ‘Taso ‘yar uwa mu nemo abinci wannan batun na masu aure ne ba namu ba kin ji.’
Haka ta wuni a makarantar nan Amina tana bata baki yainda Farida da Rahma suke kara jaddada mata ya kamata ta dauki mataki idan ba haka ba rainin zai wuce haka.
Sai bayan la’asar sannan ta kwaso kayanta ta dawo gidan.
……….
Wunin ranar haka ta karasashi cikin kunci, saida ta cewa yara bata da lafiya sannan suka kyaleta don kowa yana so ya bata labarin sports day. Rashidace ta karasa duk wata hidimar gida da ta yara, har abincin ma da baya so Rashidan ta girka yau cewa tayi ta girka don a yanda take jin ko ta dafa ba zai yi dadi ba.
PAGE 101
MIJIN MARIGAYIYA
A HAUSA NOVEL BY SAKINA YAZID (INNAR SU AMAL)
Sai bayan sallar magriba sannan ya dawo gidan, bayan ya gama hayaniya da yara ya wuce dakin ya sameta. Tana kwance bata ko juyo ta kalleshi ba don haka ya yi zaton bacci takeyi. Sai kawai ya kintsa ya fice daga dakin.
Bata son yiwa yaro alkawari ta karya don haka tun da ta dawo ta sa Rashida ta hada mata duk wasu kayan da take bukata na hada shawarma sanna ta kwaba mata fulawar, yanda idan ta fito bayan isha’i sai ta hada shawarma kamar yanda ta yiwa Habib alkawari idan yayi passing Hausa.
Suna zaune shi da yaran ta wucesu ta shiga kitchen, nana da nan ta fara koakrin dorawa.
Tana daga kitchen ta jiyo yana amsa waya yana kwatancen gida; ta ja tsaki a fili tana fatan Allah ya sa ba bako zai yi ba don ko me zai yi ba zata gaisa da wani bako ba balle ta bashi ko da ruwa. Sai dai yayi duk abinda zai yi. Kafin ta gama wannan tunanin ta jishi yana cewa yanzu zai fito, inda ba tare da bata lokaci ba ta ji fitarsa.
Jimawa kadan ya shigo da leda ya wuce ya sameta a kitchen tana yayyanka fulawa zata fara gasawa. Ya mika mata ledar yana cewa ‘Ga wannan shawarma ce; sakatariyata ce Naja ta aiko delivery man ya kawo a bawa yara. Sai ki duba ki zubo a tray mu ci don na ji kamar da yawa’
Ta kalleshi da jajayen idanuwanta wadanda suka kode saboda kuka da tsabar mamaki; tayi murmushi mai daci sannan ta kashe wutar abinda ta dora a wuta ta nufoshi yayinda ya mika ledar a zaton zata karba. Ta bigi kafadarsa ta wuce ta shige daki ta barshi a nan tsaye.
Ya bi bayanta da kallo cike da tsananin mamaki saboda Khadeeja bata taba yi masa irin wannan wulakancin ba; kuma a gabn yara don duk biyoshi suka yi da suka ji yana maganar a juye a ci.
Nan take ya ajiye ledar kan sink sanna ya bi bayanta daki; yana shiga ya sameta a tsaye a gaban mudubi tana cika tana batsewa kamar ma jiransa take yi.
‘Wannan wane irin wulakanci ne ina miki magana zaki yi min tsaki a gaban yara saboda raini.’ Ya tambaya cikin jin kai da isa.
Ta kalleshi ta dauke kai tana murmushin takaici tace ‘Ji nayi kamar zagina kayi.
PAGE 102
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Kallon takaicin da yake mata ya koma na mamaki, ya tsareta da ido kuma itama ta ki dauke nata idon. Yace ‘Ni na zageki? Ko kuwa dai ke kika zageni?’
Ba tare da ta bashi amsa ba tace ‘Wacece Naja?’
‘Mtseww!’ ya ja tsaki sannan ya cigaba ‘Sakatariyata ce; shine kike nema ki zageni saboda nace ta kawowa yara abu?’
‘Baka gaya min ka mayar da ita wakiliyarka a makarantar yara ba, har sai da naje musu open day sannan sai na ganta wai kai ka turata. Har tana cewa wai na bata takardun yara ita kace ta karbo.’
‘Eh, ai ni nace ta karbo tunda na fita ban gaya miki ba.’
‘Kuma ka kasa yi mi waya kamar yanda kafin yau duk abinda kake so ayi na yaran kake min waya ko da ina sama jannati ne naje nayi?’
Ya fara hasala saboda yanda take maganar a tsiwace ga wani kallon raini da take masa.
‘Ba fa na son wulakanci khadeeja; ni na turata ta karbo ko ban isa bane? Na zata zaki yi murna tunda kullum cikin korafi kike da mitar hidimar yaran saboda kina gani ba ke kika haifesu ba, ke naki karatun ne a gabanki.
Tayi murmushi tace ‘Ka isa har ka yi yawa, kuma alhamdulillahi tunda an sami mai karbata yanzu kam zan huta da wasu abubuwan. Kuma na gane nice ban isa na shigar maka mota ba shi yasa ita da kake ganin mutuncinta ka koya mata mota har gashi nan ta kai ta dauki motarka ta fita yawo.’
Ta daga kafa zata shige bandaki sai kuma ta tsaya ta kalleshi suka hada ido sannan tace ‘Bayan hidimar yaran sai kuma wacce hidimar take maka? Ko ma dai ka aureta ne nice ban sani ba?’
‘Ba fa na son iskanci Khadeeja! Kina ji nace miki sakatariyata ce kike wannan maganar banzar. Na aiketa don haka na bata mota ta taje ta dawo, shine kike wannan rashin kunyar? Idan da kina hidimar yaran ba tare da kosawa ba ai babu wanda zan nema. Na san idan na gaya miki sai kinyi mita don haka na nemi wadda zata yi cikin walwala na sakata, sai dai duk abinda zaki yi kije kiyi amma idan kika zageni wallahi ba zaki ji da dadi ba.’
Tayi murmushi ‘Hmmm! Ka fi karfin zagi yallabai, amma tabbas kayi yanda kake so don haka nima zan yi yanda nake so.’
Ta juya ta shige bandaki ta turo kofar ta barshi nan tsaye.
PAGE 103
MIJIN MARIGAYIYA
A HAUSA NOVEL by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Haka ya gaji da tsayuwa ya juya ya fice daga dakin; tana jin fitarsa ta fito ta saka mukulli ta kulle dakin ta bar mukullin a jiki ta koma ta kwanta.
………..
Tun a office Naja’atu ta sanar da shi haduwarsu da Khadeeja, kuma ita kanta sai da ta nuna rashin jin dadinta a kan ya san Khadeeja zata je ya tura ta. Sai da yayi ta faman bata hakuri sannan ya samo kanta. Bai taba zaton Khadeeja zata bashi matsala, don ya zata idan yace mata sakatariyarsa ce zata fahimceshi, yanzu gashi itama Khadeejan so take ya lallasheta. Yana da niyyar auren Naja don sun ma yi magana da Alhaji kwanan nan ma za a kai kudin aure; kawai dai bai shirya gayawa Khadija ba saboda bai shirya ba, ya fi so sai magana ta tsaya an kusa biki sai ya sanar da ita. Kafin lokacin ya gama gininsa sai su tashi su koma don a can yake so amarya ta tare.
Yanzun ma kuma da hakan ta faru ba gaya mata zai yi ba, idan ta gama fushin nata ya san me zai gaya mata.
Tun yana saka rai zata bude kofar dakin har dare ya fara yi bata bude ba, yara har sun gaji da tambayarta. Haka ya sa Rashida ta basu abinci sannan ta tayasu suka shirya suka tafi suka kwanta, shima ya shiga dakinsa ya kwanta yana sauraron lokacin da zai ji motsinta.
PAGE 104
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Da asubar fari ya tashi, bayan ya gama alwala ya fito da niyyar tafiya masallaci ya karasa kofar dakinta ya murza hannun kofar ko zai jita a bude amma sai ya jita a rufe, sai dai ya hango fitila ta kasan kofar dakin a kunne. Don haka ya kada kai ya wuce masallaci ya san ta riga ta tashi.
Tun kafin ta tayar da sallah cikinta yake kugi saboda jiya bata ci abincin dare ba ta kwanta, don haka tana idar da sallah ta gama azkar dinta ta bude kofar dakin ta fito ta wuce kitchen; a lokacin Rashida da su Afaf babu wanda ya tashi domin dama itace take tashin Rashida kafin tayi sallah su kuma su Afaf bayan ta idar da sallar. Tana shiga ta dora ruwa kofi daya ta jira ya tafasa, ta hada shayinta mai kauri a babban kofi ta dauki burodi ta gutsura ta dauka ta nufi daki.
A falo ta ci karo da shi ya shigo daga masallaci, ya dubeta yace ‘Shayi zaki sha da sanyin safiya kuma.’
‘Um.’ Ta bashi amsa sannan ta wuce dakin.
Da hanzari ya bita don kada ta rufe kofar, ya cimmata a daidai lokacin da take zama a kan dadduma tana ajiye shayin nata. Ko kallon inda yake bata yi ba balle ta nuna ta san mutum ya shigo. Ya karasa ya zauna a gefen gado yana cewa ‘Sai kin gama zaki taso yaran ne? akwai school fa.’
Ta gutsiri burodi ta tsoma a shayin sannan tace ‘Bani da lecture sai 9am so idan na gama zan dan koma ne na rage bacci zuwa kamar 8am sai na tashi na shirya.’
Ya dan yi dariya a kaikaice don ya san kwanan zancen, yace ‘Haba dai, ai kya daure ki shirya yaran kafin ki koma ki kwanta ko?’
‘Oh, ai kuma ka cire al’amarinsu daga hannuna ka saka a hannun sakatariyark kamar yanda ka sanar da ni a aikace jiya don idan ban manta ba ma itace ta kawo muku dinner. Ko ba komai ma ka huta da mita ta.’
Ta dauki kofin sahyinta ta cigaba da kurba.
Ya dan tsaya yana kare mata kallo saboda yanda ya kasa fassara yanayin fuskarta domin kamar ranta ba a bace yake ba kamar ma dai tana cikin yanayi na nishadi. Yace ‘Common Khadija, na riga fa nagaya miki cewa ban sameki a waya ba shi yasa nace ita taje ko? Ko da wani abu ma ai sai ki shiryasu idan na kaisu makaranta sai mu karasa maganar kinga lokaci yana kurewa.’
PAGE 105
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
‘Babu ma wani abu, na riga na fahimci sakon.’
Ya mike yana cewa ‘To don Allah ki fito ki shiryasu kinga idan suka makara rufe gate za ayi.’
Ta cigaba da shan shayinta kamar ba da ita yake magana ba, ya fara kosawa don haka kamar a hasale yace ‘Kina ji ina miki magana ko?’
Ta kalleshi suka hada ido tace ‘Na ji.’
Ya kalli agogon bangon da yake dakin ya ga karfe shida saura kwata, ya juya ya fice ba tare da yace komai ba. Ya wuce dakin yaran don ya kula so takeyi su makara. Idan ya tasosu in ya so sai suzo da kansu su gaya mata ta taso ta shiryasu.
Yana ficewa ta tashi ta tura kofar a hankali ta mayar ta kulle ta bar mukullin a jiki, domin yau babu wanda zata shirya sai dai ayi duk abinda za ayi. Tana zama a kan daddumar taji Nasreen tana buga mata kofa tana cewa ‘Anti mun tashi.’
Har ta gaji da bugun ta ruga bandaki ba a bude mata ba.
Ya fito daga dakin nasu Rashida tana biye da shi, ya dubeta yace ‘Je ki tayat mana ku shirya yara, kun kusan makara fa.’
Ta wuce kitchen yayinda ya nufi dakin Khadeeja, ya murza hannun kofar yana turawa ya jita a rufe ‘Ya juyo da mamaki yana hango kitchen yana cewa ‘Ko kina kitchen ne?’
Ya wuce ya nufi kitchen din, yana shiga ya dubi Rashida yace ‘Bata fito ba?’
Tace ‘Eh.’
Yayi tsaki ya juya ya fice. Ya koma kofar dakin nata ya kara kwankwasawa, sai sai har ya gaji da kwankwasawa bata bude kofar ba, yana kallo ta kasan kofa ya ga duhu alamr an kashe fitilar dakin. Ya ja tsaki ya wuce dakinsa, yana shiga ya dauki wayarsa ya fara kiran lambarta. Sai dai har ya gaji da kira bata dauka ba. Don haka ya ajiye wayar a kan gadon ya fito daga dakin ya wuce kitchen, yana shiga ya tarar da Rashida tana tattare fulawar da ta kwaba jiya za ayi shawarma wadda Khadijab ta barta a nan a bude ta kwana har ta bushe. Yan shiga ta bar abinda takeyi ta tsaya tana kallonsa. Yace ‘Ya baki