Showing 87001 words to 90000 words out of 99112 words
wata mayunwaciyar kura a yayin da ta hango nama yace ‘Ehhm, babu matsala. Um kin gama idda kenan?’
‘Eh, na gama jini uku a jiya. Idan ma an hada da jinin barin da nayi jini hudu kenan duka da shi kwana biyu yayi ya dauke tun kafin sakin.’
‘Oh hakane, Alah ya kai mu, sai sun zo din.’ Ya amsa.
‘Da yake ranar aiki ce zasu zo da wuri domin su sameka a gidan in sha Allahu.’ Ta fada sannan tayi masa sallama ta ajiye wayarta.
Ya mayar da tashi wayar ya ajiye a inda ya dauka ya mayar da hankalinsa ga hanya.
Naja wadda take ta kallonsa tana jiran ya bata labarin abinda aka fada wayar ta gaji da kallonsa kuma bai yi alamar zai yi magana ba tace ‘Maman Hammad ce?’
A gajarce yace ‘Eh.’
Ba iya wannan amsar take son ni ba don haka tace ‘Wai menene?’
Cikin yanayi na kosawa yace ‘Ta gama idda ne take so gobe da safe za a zo a kwasar mata kayanta.’
Ta gyara zama ta bata rai tana cewa ‘Ai na zata furnitures din naka ne?’
A fusace yace ‘Eh, iya nata za a kwasar mata ai ko akwai naki a ciki ne kuma.’
Ta tabe baki tace ‘A’a, me yayi zafi.’
Daga haka har suka karasa ya sauketa babu wanda ya sake magana.
Duk yanda ya so ya mayar da hankali a kan aikinsa hakan bai samu ba; zai iya cewa baya nadamar rabuwa da Khadeeja amma tabbas yau da ta gaya masa ta gama idda jikinsa yayi sanyi. Zai yi kewarta, kuma yaba ji a jikinsa kamar a gutsure wata tsoka daga jikinsa.
PAGE 220
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Bai ma taba tunanin zai yi kewar Khadeeja haka ba amma gashi kayanta kawai aka ce za a kwasa amma ya ji babu dadi. Bai dade da shiga office din ba ya lalubo wayarsa ya danna mata kira, kamar dazu yanzu ma muryarta cike take da walwala. Sosai ya kasa kunne yana kokarin ko gano wata alama ta damuwa a muryarta amma ji yake kamar ma an karawa muryarta zaki.
Bayan ta amsa sallamarsa tace ‘Um kayi mantuwa ne?’
Kamar wanda aka farkar daga barci yace ‘No. Umm! Hammad fa? Ya kamata ya dawo cikin ‘yan uwanasa ai ko?’
A nutse tace ‘Eh haka ne, amma ka ga bai karasa shekaru hudu ba ma. Ina ganin nan da zuwa ya gama primary in sha Allahu sai ya dawo cikin ‘yan uwansa tunda tabbasa ni na san kula da yaro akwai wahala, musamman da yake ka ga Antinsu ba zama take ba tana aikinta. Ina ganin ka bar min shi duk wani abu da yake bukata in sha Allahu zan sanar maka, idan ya iya kula da kansa sai ya dawo gida.’
So yake ya ce mata hakan ba zai yiwu ba ko don ma ya bata mata rai, amma ya kasa. Tabbas yana son ganin yaronsa a kusa da shi cikin ‘yanuwansa amma kuma idan ya karbeshi baya jin Naja zata iya hadawa da shi ta rike, don yanzun ma kullum cikin korafi take a kan yara suna gajiyar da ita. Gara ma ya bari ta rike shi in Allah yayi da ragowar zaman sa koma tare. ‘Um hakane, to babu damuwa. Sai goben kenan.’
‘Ok, Allah ya kai mu goben.’
……....
Bata taba tsammanin Mustapha zai bar mata Hammad da sauki ba, don haka ma da yayi saurin amincewa da maganarta sai ta ji wani dadi marar misaltuwa; domin ta hango wahalar da zai sha idan ya koma gidan; zama zai yi kamar maraya. Tunda su Shukra su hudu ne, Rukayya kuma uwarta tana gidan sai shi kadai wanda ba shi da uwa bashi da dan uwa a gidan.
A hankali ta mayar da wayar tata ta ajiye a kan teburinta. Ta sunkuyar da kanta ta share kwallar da ta taru a kwarmin idonta sannan ta zuba fuskarta a tafukan hannunta; ta tuno lokacin da suna soyayya da Mustapha kafin suyi aure. Wai ina soyayyar nan ta tafi ne? ya barta ita kadai tana ta dakon soyayyarsa har tsawon shekaru takwas?
PAGE 221
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Tabbas ta sha wahala a gidan Mustapha; ba wai wahalar jiki ba don wahalar jiki ta san abinda ta yi bai wuce abinda matar aure zata yi ba. Sai dai wahalar zuciya da ta sha; kulawa da tausaya tare da kauna da zuciyarta take bukata daga wajen Mustapha sune bata samu ba. Ko su din ma ta hakura da su tana zama haka tunda ko babu komai tana kallonsa a matsayin mijinta kuma suna kwana tare. Amma daga lokacin da ya auro wata kuma ya ke bata kulawa da kauna wanda ita ya kasa bata daga lokacin ta yanke kauna daga zaman gidan Mustapha.
Ba zata ce bata jin zafin rabuwa da shi ba domin tabbas ta san ko babu kauna akwai sabo, amma tabbas ba zata sake komawa gidan Mustapha ba. Domin tayi sujjada ta roki Allah kada ya sake hadata zaman aure da Mustapha. Da farko ta fara jin haushnsa amma daga baya sai taga jin haushin babu wani amfani; ko babu komai dole ta yiwa Hammad kara ta girmama mahaifinsa.
Ta sake share kwallar da ta taru a kwarmin idonta, ta kalli ruwan hawayen da ta lakata a hannun nata; to kukan me take a halin yanzu? Ta zata ta gama kuka a kan Mustapha. Tayi murmushi ta sake goge kwallarta; ta san ba zata iya goge Mustapha daga cikin tarihin rayuwarta ba amma tabbas bata fatan sake rayuwa irin wadda tayi a gidansa. Ta goge fuskarta ta fice ta nufi cikin studio inda zata gabatar da labarai.
......
Ba a fi sati daya da kwashe kayan Khadeeja ba Naja ta saka Mustapha a gaba sai da ya sake fentin saman aka gyara ta kwashe kayanta ta koma. Yaran kuma gaba daya ta tattarosu ta dawo da su kasa tare da masu aikinta guda biyu. Dakinta da parlor dinta nan ta mayar dakinsu Afaf, suna ji suna gani babu yanda suka iya. Shi kanshi Mustapha abun bai yi masa dadi ba amma ya kasa magana; yana matukar mamakin abinda ya sa baya iya hana Naja abinda take so a ‘ya kwanakin nan.
Cikinta yana cika wata tara ta sake haifar ‘yarta mace, haka ta dage ta shirya taron suna fiye ma da wanda ta shirya a haihuwar Rukayya. Aka sakawa yarinyar suna Maryam.
PAGE 222
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Washegarin suna su Anti Wiyya da sauran dangi suka soye naman suna suka gyara koma, sannan suka tafi suka bar Anti Wiyya ita kadai wadda zata kara kwana biyu saboda tayata jego.
Tana zaune a parlor din sama Anti Wiyya ta shigo da sallama, bayan ta amsa ta karasa ta zauna a kusa da ita sannan tace ‘Wannan mai wankin naki gaskiya ya iya wulakanci, sai da ya fuskanci ana taro sannan ya gudu. Ni dai wallahi ko kayan sakawa gobe bani da su duk sun yi datti, ga shi duk jikina ciwo yake balle na zage na wanke kuma ‘yar aikinki ma dai ta fini gajiya.’
‘Ai mai wankin nan yayi wa kansa, in sha Allahu gobe Abban Rukayya zai samo mana wani mai wankin kowa ya huta.’ Ta fada tana gyara zama.
Anti Wiyya tace ‘Don ma dai ‘yayanki basa moruwa ne in banda haka ga Habib can a kasa yana wanki ai da ko kala daya ne ya wanke min.’
Ta gyara zama ‘Au ai ban san ma yana gidan ba kwaso kayan duka bari na kirawoshi zai wanke miki yanzu.’
Ba tare da bata lokaci ba ta juya ta koma kasa inda ta kwaso kayan nata yayinda ita kuma Naja ta kwalawa Afaf kira ta sakata ta turo Habib.
Kusan a lokaci guda suka isa parlor din, shi ya tsaya daga bkin kofa yayinda ita kuma ta karasa ta zube kayan a gaban Naja.
Yana daga tsaye a bakin kofa yace ‘Anti gani.’
Tace ‘Mai wanki ya kwana biyu baya zuwa, ka kwashi kayan nan ka wankewa Anti.’
Ya kalli kayan ya kalleta yanda take muzurai; ba wai bata saba yi masa hakan bane, ta riga ta saba musamman tun bayan da khadeeja ta bar gidan. Kawai dai ya kan yi mata binda zai iya wanda ba zai yi ba kuma ya bar mata kayanta. Ya sake kallon kayan yace ‘Ah ku barshi dai yanzu zan fita sai na samo muku wanda zai wanke ku biya shi.’
Har ya juya ya fara tafiya tace ‘Kana nufin ba zaka wanke ba ko me.’
Ya dan dawo ya kalleta ya kalli kayan, har ya bude baki zai yi magana kuma sai ya fasa, ya fice ya barta nan a zaune da kayan.
A fusace ta mike tana huci, kafin tayi magana Anti Wiyya tace ‘Ai na gaya miki wadannan yaran basa moruwa.’
PAGE 223
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
‘Ni ka tafi ka bari ina magana ko Habib? Saboda ka ga ni ba uwarka bace kuma ba khadeeja bace ko? Saboda ba a isa a saka aiki kayi ba ko? To wallahi bari Abban naku ya dawo, sai dai ko ni ko kai a gidan nan don idan dai ba zan moreka ba sai dai ka bar gidan wallahi.’
Wiyya tace ‘Ah to, yaron da bana jin ya haura sha takwas ya dinga yi miki irin wannan rainin, wannan nan da ‘yan shekaru ai sai ya kai miki duka.’
‘Wallahi bari ubanshi ya dawo, dole ya bar min gidan nan idan ba haka ba ni na bar masa gidan. Idan ma Khadeejan ce take zuga shi ta janyo masa.’
Haka Wiyya ta skaata a gaba ta kara zugeta kafin ya dawo.
PAGE 224
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ana idar da sallar Magriba ya shiga gidan, Habib ne ya bude masa gate tare da Baba maigadi yayi masa sannu da zuwa sai dai bai rakashi har cikin gidan ba. Kamar yanda ya saba a parlor din kasa ya sami yaran suna zaune suna kallon TV, bayan ya amsa sannu da zuwansu ya wuce sama. Da da ne Nasreen da Shukra sai sun rakashi har dakinsa, sai dai yanzu saboda yanda Naja take yawan korarsu tana nuna musu su dinga tsayawa a kasa ya sa sun hakura, haka ya haye shi kadai zuciyarsa babu dadi; saboda shima yana kewar wannan rakiyar.
A dakinsa ya sameta tana ta cika tana batsewa, domin ko sannu da zuwa haka tayi masa tana ta faman zumbura baki. Bayan ya amsa yace ‘Me ya faru ne naga kina ta wani bata rai?’
Ta sake hade rai sannan tace ‘Ya za ayi a gidan nan ace ban isa na saka Habib aiki yayi ba? A gaba kowa zan ce Habib yayi aiki amma kai tsaye ya ce min ba zai yi ba? Ai ba haka yake yiwa Maman Hammad ba, ko da yake na ji suna cewa yana zuwa wajenta ban sani ba ko itace take zugashi ya dinga yi min rashin kunya.’
Ya ajiye jakarsa ya zauna a kan kujerar gaba mudubi ya fara cire takalmansa yana cewa ‘Kada ki saka Khadeeja a cikin wannan maganar, da zata sa wani yayi miki rashin kunya da tun tana nan zata saka su. Habib din me kika ce yayi ya ki yi?’
‘Wankin kayansa yake yi shine na kirawoshi na bashi kayan Anti Wiyya kala daya nace ya taimaka ya wanke mata amma yaron nan ya ki, kuma yana kallo mai wankin namu ya gudu. Itace ta ke ta fama kula da gidan kayanta duk sun yi datti amma a gabanta Habib ya ce ba zai wanke mata kala daya ba don wulakanci don ya nuna mata ban isa ba.’
Ya mike ya cire kayansa yana cewa ‘Ki dauko kayan idan na fito zan bashi ya wanke in ya so zan gayawa Baba Maigadi ya zagaya nan makarantar almajirai ya samo yaro a wajen malaminsu wanda zai dinga zuwa yana wankin.’
PAGE 225
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Kafin tace wani abu ya shige bandaki. Ta zubura baki ta ja tsaki don ba haka ta so ba, so take ayi masifa ta sami damara da za a ce Habib ya bar gidan. In ya so sai ta san yanda zata yi da Afaf, tana gamawa da wadannan biyun ta san gidan ya zama nata, musamman da yake Shukra ita matsoraciya ce duk yanda ma aka juya ta haka takeyi.
Jimawa kadan ya fito ya sake kaya sannan ya wuce ya zauna a dining table ya fara cin abinci. Yana cikin cin abincin ya dauki waya ya kirawo Habib, ba tare da bata lokaci ba ya hawo ya same shi.
‘Abba gani.’ Ya fada yana tsaye daga gefe.
Ya ajiye cokalin da yake hannunsa sannan yace ‘Habib me yasa Antinka ta saka ka wanki ka ki yi?’
Yace ‘Abba ba kin yi nayi ba, wankin ne da yawa kuma nace gobe zan samo musu yaro ya wanke a biya shi.’
‘Kala dayan ne da yawa? Kayan ma da ba nawa bane.’ Ta fada tana wasu muzurai.
Yace ‘Ni dai kayan da aka bani zasu kai kamar kala biyar ko fiye, ban sani ba ko ba su aka nuna miki ba.’
Abbansu yace ‘Ka ga Malam, bana son wani karin bayani. An ce kaya kala daya ne kuma gobe ake so ayi amfani da su. Kace a baka kayan ka wanke yanzu in ba so kake ranka ya baci ba, kuma daga yau bana son a saka ka aiki ka dinga kin yi. Ba zan dauki taurin kai da rashin kunya ba.’
Ya bude baki zai yi magana sai kuma ya fasa, ya juya ya fice.
Ya dubi Najan yace ‘Kije kice mata ta bashi kayan ya wanke.’
Ta tashi ta fice.
Yana zaune a tsakar gida wajen Baba maigadi Shukra taje ta kirawoshi. Yana shigowa ya ci karo da wankin a zube a bakin kofa; tabbas wankin sun fi kala biyar. Yana shiga cikin parlor din kafin yayi magana Naja da take tsaye tace ‘Gasu nan kaje ka wanke, kuma wallahi idan basu fita ba sakewa zaka yi har sai sun fita.’
Ta juya ta haye sama ta barsu a nan shi da kannensa.
Ya juya ya dawo ya tsaya a kan wankin yana kare musu kallo yana tunani; tabbas ba zai yi wankin nan ba, ko da kuwa kala dayan ta bayar kamar yanda tace. Kuma yanda yaga a gaban Abban tace kala daya ne kuma ta dauko kaya da yawa haka ta bashi ya san ta shirya wata makarkashiyar.
PAGE 226
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ya san ba lallai Abbanshi ya saurareshi ba saboda tana gabansa tana tsara masa zance, kuma ya san idan har yayi wannan wankin to ta sami damar da zata mayar da shi dan aikin gida kuma ba zai yi ba. Haka ya kewaye ya fice ya bar wankin a nan inda ta ajiye su.
………
Suna sama ita da maigidan suna ta hirarsu cikin kwanciyar hankali, sai waje karfe tara sannan Anti Wiyya ta fito daga dakin baki ta ga wankin. Tayi matukar mamaki musamman da ta tambayi Afaf ta tabbatar mata Habib din ya fice bai dauki wankin ba. Nan ta koma daki ta kirawo Naja a waya wadda ta sauko, ta nuna mata wankin sannan tayi mata bayanin cewa a nan ya fice ya barsu.
Yaran suna kallo ta tsuguna ta tsince kayan ta bar kala daya da hijab guda daya sannan Anti Wiyyan ta koma daki ita kuma ta haye sama.
Jimawa kadan Mustapha ya sako yana tambayar Afaf ina kaninta.
‘Abba ban ganshi ba, ficewa kawai yayi ba tare da yace komai ba.’ Ta bashi amsa.
A fusace ya murda kofar dakin Habib din ya shiga yana kiransa, sai dai ga mamakinsa Habib din baya cikin dakin. Ya fice wajen Baba Maigadi inda ya tabbatar masa bai san inda Habib yake ba, ya kara da cewa ‘Bana jin ma fita yayi, don tun da aka ce ya zo kana kiransa ban sake ganin gilmawarsa ba. Sai dai ko da ina sallah ne ya fice ban sani ba.’
Ya koma cikin gidan ba tare da yace komai ba.
Yana shiga parlor din ya dubi kayan yace ‘Nasreen zo ki kwashi kayan nan ki mayar mata, yayan naki zai zo ya same ni.’
Ya haye saman inda ya tara da Naja a zaune a parlor ita da Rukayya, ya sami waje ya zauna sannan ya dauki wayarsa ya dannawa Habib kira. Ba karamin mamaki yayi ba da yaji wayar Habib din a kashe, sai dai yayi tunanin kashe wayar Habib din yayi don ya san bashi da gaskiya. Don haka sai kawai ya sauko ya sanar da Baba Maigadi cewa idan Habib ya shigo gidan yayi masa waya.
……..
Tun yana sa ran shigowar Habib har abun ya fara bashi tsoro; yaran duk sun tafi sun kwanta har sha biyun dare ta yi amma Habib bai shigo gidan ba, gashi sai kiran wayarsa ake yi a kashe. Yana son ya kirawo Hajia ko Habib din yaje can amma kuma baya son ya daga musu hankali.
PAGE 227
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid
A karo na babu iyaka motsin shigarsa dakin ne ya farakar da ita daga bacci, ta gyarawa Baby Maryam kwanciyarta sannan ta dubeshi tace ‘Wai bai dawo ba.’
A jigace yace ‘Eh, wallahi har abun ya fara bani tsoro. To ina Habib zai tafi? Ina ma ya sani a garin nan shi da ba wani yawo yake ba?’
Tace ‘Ya zaka ce ina ya sani yaron da yake level 1, kuma yake tafiya makaranta da kansa. Ai yanzu ba kamar da bane, tsaf ya san ko ina.’
‘To ina zai tafi a wannan daren? Gashi Baba Maigadi ma yace ko fitarsa bai gani ba kuma gidan nan babu inda bamu duba ba baya nan.’
Tace ‘To