Showing 33001 words to 36000 words out of 99112 words
ai ba wani abu bane da za a daga tunda daga yaranta har nakan duk ‘yayanka ne.’
Muryarsa a makogoro yace ‘Shikenan Hajiya.’ Ya mike tsaye yana cewa ‘Bari naje wajen Alhaji mu ci tuwon tare, ko da yake ma a koshe nake me sanyin kawai zan sha
PAGE 84
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Yana shigewa Jidd a ta kalli Hajia tace ‘Kin gani ko Hajia, a kan kayan shiya zai yaga min rigar mutunci, wallahi yaron nan har yanzu bai yi hankali ba.’
Tace ‘Ya fi ki gaskiya, ya zaki karbi kudinsa kuma ki dinga bar masa yara da yunwa?..’
‘Hajia wallahi na gaya miki karya yaran nan suke yi, kawai don sun san za a biye musu ne suke abinda suka ga dama. Idan banda haka ya za ayi na hanasu abinci na bawa su Nawwara tunda ai duk tare suke wuni suna wasansu; kawai dai suna so su nuna su ubansu mai kudi ne.’
‘Ki dai bi shi a hankali kin ji na gaya miki. Bari ma ya fito naji sai yaushe zai kawo min yaran yawon Sallah ko kuma nima laifin naki ne ya shafe ni ya kai yaran wajen waddad da baya son ya bar mata su?’
……..
Haka yana ji yana gani ya hakura ya kyale Yaya Jidda; daman ya riga ya san Hajia ba zata taba bari a ga laifinta ba.
Kamar yanda aka yi alkawari ranar uku ga sallah tun wajen karfe tara na safe ya tafi daukan Khadeeja; da yake sun riga sun yi waya a shirye ya sameta don haka ba tare da wani bata lokaci ba ya daukota ita da mai aikinta Rashida suka kama hanya. Sai da suka tsaya a gidan Mama suka kwashi yara sannan suka wuce gidan Hajia.
Nan suka zauna a parlor ana ta hira yayinda yara suke ta kaiwa da kawowarsu. Jimawa kadan Yaya Jidda ta dubi Khadeeja tana nuna Rashida tace ‘Wannan yarinyar taki kuwa zata iya wani aikin kirki? Kada fu kuje a kama ku da child abuse?’
Tayi dariya duk da yanda maganar ta bata mata rai tace ‘Ah haba dai, shekarunta fa sha biyar yaya don dai kawai bata da girma ne. Aiki kam ta iya sosai ko a gida ma Mommy ta koya mata.’
‘To amma idan Habi ta dawo sai a mayar da ita ko? Tunda na ji Habi din tace baku da wata matsala da ita kuma tana nan itama tana shirin dawowa.’
‘Uhm, sai a hada biyu ma tunda kin ga ga hidimar gida ga ta yara, kuma ina zuwa makaranta.’
‘Haba wace hidima ce sai an hada ‘yan aiki har biyu a wannan gidan? Hidimar har nawa take?’
Kafin ta bata amsa Mustapha ya shigo yana cewa ‘Ku tashi mu tafi ko, don na san kuna da aiki a gidan nan don duk yayi kura.’
PAGE 85
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Suka fara shirin mikewa yayinda ita kuma Yaya Jidda ta kalli Mustaphan tace ‘Na ga kun samo ‘yar aiki, Baba Habi ma fa tana nan tana shirin dawowa.’
Yace ‘Ah ai kawai sai kice mata tayi zamanta tunda dai gaskiya bamu da inda zamu ajiye ‘yan aiki har biyu.’
‘Da nace ta mayar da wannan din idan Baba Habi ta dawo?’
‘To gata nan kuyi magana idan ta fi son Baba Habi din sai a mayar da wannan din.’
Ba tare da bata lokaci ba Khadeeja tace ‘Uhm ai gara a bar wannan din, in ya so in da wata matsala sai nayi magana a nan din a kawo wata.’
Haka dai dole Yaya Jidda ta barsu suka tafi ba tare da ta iya gamsar da su cewa Baba Habi zata dawo ba.
……….
Kamar yanda ya fada kuwa kaca-kaca suka tarar da gidan, sai dai suna shiga suka fara kokarin gyarawa. Kuma da yake yana ajiyesu ya sake fita harda Afaf da Habib aka yi aikin, don haka cikin kankanin lokaci suka gama.
A haka rayuwa ta cigaba; sai dai a bangaren Mustapha idan dai yana gidan ba a saka masa yara aiki, sai dai su suyi ta gara rashida komai ita zasu aika ko su saka. Khadeeja tana son ta tsawatar musu amma tana tsoron abinda ubans zai ce tunda ta ga sun dan sami natsuwa babu wata hatsaniya, bata so ta ja rigima. Don haka haka ta zuba musu ido; abu kadan sai a kwalawa Rashida kira ko da kuwa aikin Khadeejan take yi dole ta bari taje tayi musu yanda suke so.
……….
Ba a dade da sallacewa ba kuma aka bude gari, a hankali kowa ya koma harkokinsa.
Ranar Lahadi da daddare bayan yara sun yi bacci; suna zaune a parlor shi yana kallon balla a Tv yayinda ita kuma take chatting a waya; ta dago daga kallon wayar ta dubeshi tace ‘Babe gobe fa za a koma makaranta.’
Ba tare da ya dauke kai daga kallon TV din ba yace ‘Kin gaya min fa tun last week, kuma na siyo duk wani abu da ake bukata.’
Ta gyara zama ta ajiye wayar tace ‘Nima zan shiga school din na gano, wata kila an kafe timetable, amma sai wajen goma zan fita.’
‘Ok, to zaki dawo kafin 12:30pm kenan ko? Saboda dauko ‘yan makaranta tunda ni kin ga ina office.’
PAGE 86
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
‘Eh, zan yi kokari na dawo kuma idan ban dawo ba ma kafin na fita zan je da Rashida taga makarantar tasu idan lokaci yayi bandawo ba sai taje ta dauko Nasreen.’
Ya gyara zama ya kalleta kamar a foirgice ‘Wai wannan yarinyar ce zata dinga dauko yaran daga makaranta kuma ta zauna ta zauna dasu a gidan ita kadai?’
Cikin halin ko in kula tace ‘To ya za ayi, ai kaga dai nima dole naje makaranta ko? They will be fine fa, yarinyar tana da hankali sannan kuma ka ga ga Afaf tana nan idan ta dawo. Suma ita da Habib na gaya musu idan an tashi daga makaranta su taho tunda na ga ko nice ma naje daukosu idan muka rasa napep a kasa muke tahowa.’
Ya kare mata kallo sanna yace ‘Wai me kike fada ne? su Afafa din ne kike so su dinga tahowa daga makarantar su kadai kuma a kas, sannan harda Nasreen? Wadda sai an tasheta da minti talatin sannan a tashesu?’
‘To babe ya zamu yi? Ai ka ga dai kamar Afaf bashi da wani amfani ace sai Rashida taje sannan zasu taho tare ko? Ni kuma duk lokacin da ta kama ina gidan zan je na daukosu.’
Suka yi shiru na dan lokaci kowa da abinda yake tunani.
Jimawa kadan yace ‘Ni barin wannan yarinyar taki ma a gidan ita kadai gaskiya bai yi min ba, ya za ayi duk mu fice a barta ita kadai kuma a bar mata mukullin gidan? Ai idan muka dawo sai abinda muka gani kenan, za ma ta iya fara shigo da maza gidan ko ayi mata wayo ayi mana barna idan aka gane ita kadai ake bari a gidan.’
‘To yanzu ya kake so ayi? Ka ga dai da ni da yaran ai dole duk muje makaranta ko?’
‘Ni ma ban sani ba, kece zaki san yanda zaki yi. Zaki maiya fita da ita ki rufe gidan in ya so sai ku dawo tare ki dauko yaran, duk yanda dai kuka yi. Amma dai gaskiya wannan tsarin na barinta a gidan bai yi min ba.’
Ranta ya fara baci; me yake nufi ne? so yake yace ta bar makarantarta kawai saboda ta zauna masa da yara ko kuwa mai aikin yake so ya korar mata? Wannan bayanin da yake yi ma sam ba zai yiwu ba gara dai ya sake lissafi ko kuma shi ya dinga baro office yana zuwa yana daukosu.
PAGE 87
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal
Tace ‘Uhm, to ai ka ga ba ni nake rubutawa kaina timetable ba, wani malamin ma sai 1pm yake fara lecture kuma dole nayi attending idan dai ina son na gama degree din. Sai dai ko ka kawo wata dabarar da kai kake ganin za ayi da daukosu in ya so ita Rashida idan zan fita sai na fita da ita duk lokacin da na gama lecture sai mu dawo tare.’
Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan ya tashi ya jefar da remote din TV din da yake hannunsa ya shige daki.
Ta bi bayansa da kallo tana mamaki; wai me mutumin nana yake nufi ne? shikenan sai ta jingine rayuwarta ta zauna ta kular masa da yara? To ai ita ko ‘yayan da ta haifa ma haka ko tana so ko bata so zata dinga barinsu da mai aikin ta tafi makaranta tunda dai haka taga masu yaran suna yi. Ko kuwa da yake ta auri tuburarre hakura zata yi da komai ta zauna sai yanda suka yi da ita?
Haka suka kwana a wannan daren kowa da abimda yake ransa.
Ko da gari ya waye tun asuba ta tashi uta da Rashida wadda ta tayata nan da nan suka shirya yara sannan suka hadawa kowa abinci. Kamar yanda ya saba sai karfe bakwai da kwata sanna ya fito, zuwa lokacin sun shirya suna jiransa; ya kwashesu ya kaisu ya dawo.
Sai wajen karfe tara da rabi sannan ya gama shirinsa, lokacin fitowarta kenan daga wanka saboda sai da ta tsaya ta gama abincin rana ta juye a flask sannan ta fara shirin. Ya sameta a daki tana shafa mai rike da mukullin motarsa, yana daga tsaye a bakin kofa yace ‘Ni na fita.’
Ta juyo da sauri tana cewa ‘La! Babe don Allah bari nayi sauri na saka kayana sai ka bani lift.’
‘No ba ta hanyarku zan bi ba, ki wuce kawai sai na dawo. Kada ki manta min da yara.’ Ya fada yana ficewa daga dakin.
Tabi bayansa da kallo da baki bude; lallai ma mutumin nan. Kiri-kiri dai shi baya son ya dauketa a motarsa idan dai makaranta zata, in banda haka ai ko ba hanyar makarantarsu zai bi ba ya sauketa a bakin titi ya rage mata tafiya. Ta juya ta cigaba da shiryawa cikin sanyin jiki tana tunanin son kai irin na Mustapha. Allah ya so ta ma Baffa ya tura mata kudi kuma ya sanar da ita duk wata zai dinga turo mata kudi saboda karatunta, idan tana son wani abu sai ta yi masa magana.
PAGE 88
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Tabbas ta san da ace da Mustapha ta dogara da sai dai ta hakura da karatunta ta zauna ta kular masa da yara.
Nan da nan ta karasa shiryawa ta fito ta sallami Rashida wadda ta barsu tare da Shukra bayan ta yi mata duk wani bayani da take bukata sannan ta kama hanya zuciyarta cike da damuwa da wasi-wasi.
Kafin sha biyu ta gama duk wani abu da take yi a makarantar sai dai bata son ta dawo ta dauko yara; ba wai yaran ne bata son daukowa ba amma bata son ta daukosu Mustapha yaga kamar fadansa ne ya sa don haka duk lokacin da zata fita ya zata zai yi mata fada ta dauko masa yara. Don haka suka nemi inuwa ita da kawayenta suka zauna suna hira, sai wajen 1;30pm sannan suka karasa masallaci suka yi sallah kowacce ta kama hanyara gida.
Ko da ta zo gida bata tarar da wata matsala ba, Rashida ta kai Shukra gidan su Ummi ta dauko Nasreen daga makarantar kamar yanda ta bata umarni. Su kuma Afaf da Habib kusan tare da ita suka shiga gidan.
Ko da ya dawo tana jin sa yana tambayar taran wanda ya daukosu daga makaranta suna ba shi amsa, musamman Shukra wadda yake ta tambayarta me suka yi ita da Rashida a gidan bayan Anti ta fita. Haka tayi banza da shi ta cigaba da harkokinta.
Haka suka cigaba da yi, sai ya zama kuma da yake ba a fara lecture sosai ba sati biyun farko kullum Khadeeja bata fita da wuri sanna kuma tana dawowa kafin ya dawo gidan, don haka matsalarsu da sauki tunda zai zo ya tarar da ita tana ta hidimar yara.
…….
Sati daya da komawa aka kafewa su Khadeeja timtable, kuma da yake babu lokaci sosai timetable din a matse take. Haka dai suka cigaba da karatun.
Ranar Alhamis shine take da lecture 8am to 6pm, don haka ta san dole ta shirya ta fita tare da yara. Tun dare ta gama komai, tayi rabin aikin abincin safe sannan ta fitowa da kowa kayansa. Ta yiwa Rashida duk wani bayani da take bukata tunda yaran idan sun dawo daga makarantar boko babu islamiyya don haka nan zasu wuni a gidan.
Tun kafin asuba ta tashi suka fara aiki tare da Rashida.
PAGE 89
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Bayan Mustapha ya dawo daga masallaci sallar asuba ya sameta a kitchen, tana ta fama kaiwa da kawowa tsakanin dankalin da take soyawa da kuma hadawa yara abincin makarantarsu a lunch box. Bayan ya amsa sannu da zuwanta yace ‘Wai kin yi sallah kuwa? Na ga kamar a nan na barki fa.’
Tayi ‘yar dariya tace ‘Haba dai, nayi sallah mana. Sauri nake na gama saboda yau 8am to 6pm ne da ni kuma 8am din nan idan Prof. ya rigani shiga aji rufe min kofa zai yi wallahi shi yasa nake ta sauri don kullum sai yayi attendance.’
‘Oh kenan yau sai 6pm zaki dawo gidan?’
‘Eh.’ Ta amsa a gajarce tana kwashe dankalin da ya riga ya soyu.
Ya kara hade girar sama da kasa sanna yace ‘To a ina zaki bar yara wuni guda?’
Bata son hayaniyarsa don bata son abinda zai bata mata rai, ba tare da ta bar abinda take yi ba tace ‘A nan mana gidansu; Rashida zata dauko Nasreen su kuma su Afaf idan suka dawo zasu sameta a gidan sai suyi zamansu kafin na dawo, they will be just fine.’
‘Haba ai dadewar tayi yawa, kenan haka zasu zauna suyi duk abinda suka ga dama ba tare da wata kulawa ba.’ Ya fada a fusace.
‘Kada ka damu Rashida zata kula da su.’
Kafin ya bata amsa suka jiyo ihun Nasreen daga dakinsu tana cewa ‘Wayyo Anti.’
Ta riga ta san rigimar Nasreen, idan dai aka tasheta da sasafe zuwa makaranta sai tayi kuka ko ma waye ya tasheta, shima kuma ya san da haka. Amma ba tare da bata lokaci ba ya nufi dakin da sauri. Ganin haka itama Khadeejan ta ajiye abinda take yi ta bi bayansa, kusan a lokaci daya suka shiga dakin.
Nasreen tana zaune a kan gadonsu da hawaye shabe-shabe a idonta yayinda Rashida take tsugune a gaban gadon tana rike da towel.
‘Me aka yi miki kike kuka Nasreen?’ Ya tambaya kafin ya karasa shiga dakin.
Khadeeja tana shiga dakin ta sauko daga kan gadon ta rungumeta tana cewa ‘Anteee.’
Ya shafa kanta ‘Me aka yi miki?’
Cikin shagwaba tace ‘Rasheeda ce.”
Ya juya ya dubi Rashidan a fusace yace ‘Me kika yi mata?’
Nan da nan jikinta ya hau rawa tana gyara tsuguno, kafin tayi magana Khadeeja ta shafa kan Nasreen tace ‘Nas me Rashida tayi miki?’
‘Tashi na tayi daga barci.’
PAGE 90
MIJIN MARIGAYIYA
A HAUSA NOVEL by Sakina Yazid (Innar su Amal)
‘To ai kin ga shiryaki zata yi ki tafi school ko? Ko kina son ki makara Uncle ya koroki gida ne?’
Yayi tsaki ya fice daga dakin ba tare da ya sake cewa komai ba.
Ta lallaba Nasreen ta tura ta bandaki sannan ta juyo zata fito, kafin ta fito ta jiyoshi yana dawowa dakin yana cewa ‘Dankalin da kika bari a wuta ya kone, kije ki duba na kashe miki wutar.’
Ta wuceshi ta karasa kitchen din da gudu inda ta sami dankalin ya kone, ta kwashe sannan ta sake kunna wutar ta dora. Ya karaso ya tsaya a kofar kitchen din, ya dan dauki lokaci yana kallonta tana zubawa yara abincin rana wanda ta sauke a babban flask. Jimawa kadan yace ‘Kin ga irin abinda yasa bana son ki barsu da yarinyar nan ita kadai ko? Ya za ayi ta iya kula da yara tunda gashi nan bata ma iya tashinsu daga bacci ba?’
Ta kalleshi cike da mamaki tace ‘Nasreen ce fa, ko kaine ma ka tasheta sai tayi rigima, ko ka manta ne? Kuma kaine kace baka son Rashida ta dinga yi maka girki kuma ka ga dole abu daya zan yi a lokaci guda ba zai yiwu ina girka muku abinci ba kuma ina shirya yara.’
Ya juya ya fice ba tare da ya ce komai ba.
Ta ja tsaki ta share kwallar da ta taru a gefen idonta sannan ta cigaba da aiki. Bata ma san me take ji ba, kokari kawai take ta fita daga gidan idan taje makaranta ta samu tayi tunani ta fahimci me take ji.
Bayan ta gama abinci ta wuce daki ta sameshi bayan ta zubawa yara abinci suna ci, yana kwance a gefen gado yana fama latsa waya ta wuce har ta kusa shiga wankan yace ‘Idan na kai yara dawowa zan yi kin sani, sai wajen 10am zan fita, ita wannan yarinyar taki haka zaki bar min ita a gidan daga ni sai ita?’
Cikin halin ko in kula tace ‘Eh, ita da Shukra zasu zauna idan zaka fita kawai ka gaya mata don ta san cewa ka fita ta cigaba da aikinta.’
Har zata shige bandakin yace ‘Gaskiya bana so, kuma kema kin san bai dace ba ki barni a gida daga ni sai mai aikinki mace. Irin hakane kuma idan an ce za a auri mai aikin kuce baku yarda ba.’
Duk bacin ran da take ciki sai da ya bata dariya, duk da dai dariyar takaici ce tace ‘to ai gaka nan gata nan ka aureta mana, ai itama mace ce.’
PAGE 91