Showing 93001 words to 96000 words out of 99112 words

Chapter 32 - Mijin Marigayiyya Part Complete Hausa Novels.docx

17 Sep 2025

89

zaton zai yi kewara rigimar Khadeeja ba amma yanzu tabbas kewar rigimar tata yake yi.

Karfe daya da rabi daidai suka idar da sallah a farfajiyar office din su. Yana shiga office dinsa ya auna a kan kujerarsa ya turata baya kadan yana juyawa ya dauki wayarsa wadda take kan tebur din ya lalubo lambarta ya dannan mata kira, ya kara a kunnensa bayan da ta amsa yace ‘Hello.’

Bayan sun gama gaisawa yace ‘Kina ina ne?’

Da mamaki a muryarta tace ‘Ina office mana, akwai wata matsala ne?’

Murya a sanyaye yace ‘No, babu matsala kawai dai ina son ganinki. Zan iya zuwa office din yanzu?’

‘Umm! Akwai matsala ne?’ Ta sake tambaya.

PAGE 234

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Yayi ‘yar dariya ‘Babu matasala fa, akwai dai maganar da nake so muyi. Zan iya zuwa, minti talatin kawai ya isa.’

‘Ok, ina jiranka duk da dai na kusa tashi.’

Ya ajiye wayar ya mike ya dauki mukullan motarsa ya kama hanya.

…….

Yana sane yaki ya kirawota da ya sa don so yake ya shiga ya sameta a office din nata, don haka bayan ya ajiye motarsa sai ya fito ya shiga gidan talabijin ya tambaya. Ba tare da bata lokaci ba aka nuna masa office din nata.

A hankali ya kwankwasa kofar, daga ciki muryarta ta bashi amsa ‘Shigo a bude kofar take.’

Ya tura kofar ya shiga da sallama.

Tana zaune a kan kujerar zaman mutum daya wadda take gefe guda, da jakarta a gefenta tana ta danna waya; da alama ta gama shirin tafiya gida. Bayan ta amsa sallamarsa ya mayar da kofar ya rufe sannan ya karasa yayi kansa mazauni a kujerar da take kusa da wadda take zaune a kai. Bai san dalilin da yasa ganinta ya saka shi jin dadi ba amma dai ya san ya ji dadin ganinta. Cikin girmamawa ta gaisheshi kamar babu wata damuwa a tsakaninsu.

Bayan ya amsa tace ‘Allah ya sa dai ba wata matsala don tunda kace zaka zo nake ta tunani.’

Yayi murmushi yace ‘Babu wata matsala, kawai dai ina son ganinki ne.’

Ta dan yi gajeren murmushi tace ‘Uhm, to gani.’

Yayi dariya yace ‘Kamar dai kina korata.’

‘Ba korarka nake ba, kawai dai ina son na tafi gida don wallahi na gaji.’

Ya gyara zama; yarasa ma ta inda zai fara domin ganinta ya goge masa duk zantukan da ya tsaro zai zo ya gaya mata. ‘Yara suna kewarki.’ Ya fada bayan ya gama nazarin ta inda zai fara.

Nan da nan murmushinta ya kara fadi, tace ‘Allah sarki ni da Hammad ma muna kewarsu. Don ma Yaya Habib yana zuwa gidan Mommy yana gaishemu.’

Ya girgiza kai domin Habib bai taba gaya masa yana zuwa wajen Khadeeja ba, bai ma taba yi masa maganar Khadeejan ba tun bayan da suka rabu.

‘Ya Hammad? Baya kukan makaranta?’ Ya tambaya.

‘Baya yi, ka san ya hada wayon yayyinsa gaba daya.’ Ta fada tana dariya.

Suka yi shiru na dan lokaci; ita duk ta kosa domin so take ta tafi gida yayinda shi kuma ya gyara zama yana kwaso hira.

PAGE 236

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan yace ‘Khadeeja.’

‘Na’am.’ Ta amsa tana kallonshi.

‘Wai me yasa kika ce na sakeki?’ ya tambaya yana tsareta da ido.

Ta sunkuyar da kai tana murmushi, ta dago ta kalleshi suka hada ido sannan ta sake yi masa wannan murmushin nata wanda yake dauke da ma’anoni daban daban tace ‘Right question at the wrong time; amma dai zan baka amsa.’

Ta sunkuyar da kai a daidai lokacin da murmushin fuskarta ya gushe, ta dago suka sake hada ido sannan ta gyara zama tace ‘Gajiya nayi Musatapha. Ka san idan mutum wanda bai iya swimming ba ya fada ruwa to zai yi ta kokarin ganin ya fita da rai ko, amma duk dadewa zai gaji. To haka ce ta faru da ni. Soyayya ce ta saka na aureka, amma idan dai ba na manta lissafin ba tun a shekarar farko na rasa soyayyarka. Haka na dinga kokawar janyo attention dinka ko zaka fahimceni amma baka ko kalli inda nake; kai dai abinda kake so kawai shi kake so. Na hakura ina zama da kai a haka saboda I was ok with just sleeping behind you every night; sai kuma ka dauko aure. Duk wani abu da nake so daga wajenka a lokacin ka dauka ka bata ina kallo. Haka na cigaba da kokawar samun attentin dinka, ina kokarin ganin kayi mana adalci amma hakan bai samu ba. Na tuna tun ina ni kadai ma ka fara kasa yi min adalci to balle yanzu mun zama mu biyu; ni da rabin ranka. So I gave up, ba zan iya ba, na gaji da fadan da bashi da ranar karewa don na gane bana ma gabanka. Shi yasa na nemi saki kuma Allah ya taimakeni ka bani kuma ka barni har na gama idda.’

Idanuwansa suna kan fuskarta har ta gama tayi shiru, ya cije lebe yace ‘Kuma baki gaya min ba Khadeeja? How did I not see all this?’

Tayi dariya tace ‘Da wanne yaren zan gaya maka?’

Suka sake yin shiru na dan lokaci. ta danna wayarta ta kalli agogo sannan tace ‘Time yana tafiya, wallahi so nake na tafi gida don na gaji.’

‘Oh, sorry’

PAGE 237

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid Innar su Amal

Suka sake yin shiru na dan lokaci sannan yace ‘Khadeeja yi hakuri mu mayar da aurenmu, in sha Allahu haka ba zata sake faruwa ba.’

Ta mike tsaye tana dariya tace ‘Kayi hakuri Mustapha amma aure ba zan sake yi da kai ba, babu wannan zance don Allah kada ka sake yinsa. Shekarun da muka yi Allah ya amfana su kuma Allah ya sa kaffara ne amma kada Allah ya maimaita mana.’

Ya dafe kansa da hannuwansa biyu na dan lokaci sannan ya sauke hannuwan ya mike tsaye. Ta bude kofar ya fice sannan ta biyo bayansa suka fito daga office din. Suka jero suka fito harabar office din. Nan suka tsaya yana ta faman lallabata ta bari ya kaita gida amma ta ki; yana ji yana gani ta tare taxi ta hau. Sai da ya tabbatar ta zauna a bayan motar sannan ya zagaya ya bawa direban taxi din kudinta. Suka ja mota shima ya koma ya shiga motarsa ya kama hanya.

Ya dai ji tace ba zata taba sake aurensa ba amma tabbas bai yarda ba, yana ji a jikinsa in sha Allahu zata yarda su mayar da aurensu. Yanda zai yi da baffa ne ma yafi damunsa domin ya san tabbas Baffa ba zai saurara masa ba. Haka har ya isa gida yana wannan tunanin, sai dai yana saka kafarsa cikin gidan ransa ya kara baci. Bai san a yanda zai je ya sami yaran ba sannan kuma ita kanta Najan yana jin haushinta do ba zai taba bata dama ta wulakanta masa yara ba.

____

Ana cikin kiran sallar magriba ya shiga gidan, don haka ko zama bai yi ba ya daura alwala ya ja Habin suka wuce masallaci. Ko da aka idar da sallar a can ya tsaya wajen magidanta unguwar suna hira, har sai da suka yi sallar isha’i sannan suka tashi daga hirar kowa ya koma gida.

A parlor din kasa ya sami yaran suna harkokinsu, ya wuce ya haye sama. Tana zaune a parlor tana jiransa saboda bata son yanda tun da safe ya ki ya ko kalli inda take. Ita idan ana fada ta fi so ayi hayaniya kowa ya fadi abinda yake ransa, amma ya ma ki ya tambayeta me yasa ta yiwa yaran haka balle ta samu tayi masa bayani. Ba ta jin ya amsa sannu da zuwan da ta yi masa, idan kuma har ya amsa to tabbas ita dai bata ji ba. Ba tare da ya kalli inda take ba ya shige dakinsa. A fusace ta mike ta bi bayanshi.

PAGE 238

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Yana tsaye a gaban mudubi yana rufe durowa ta shiga ta turo kofar, ta tsaya a bayan kofar ta rungume hannu tace ‘Ga abinci can a dining table.’

Ba tare da ya kalleta ba yace ‘Ki sauka da shi kasa a can zan ci ni da yara.’

ta sunkuyar da kai ‘To bari nace su hawo sai kuci a nan, duk da suma na zuba musu nasu abincin kuma duk tuwon ne dai.’

‘Ba sai sun hawo ba ni zan sauka, ki dauka ki kai can.’ Ya fada sannan ya juya ya zauna a gefen gado.

Ta karasa ta zauna a kusa da shi, ta dafa gwiwarsa ta dan marairaice tace ‘Don Allah ka bawa Hajia hakuri, wallahi abinda ta gani ba haka bane. Kai ma ka san babu yanda za ayi na ci wani abu na hana yara. Hawowa ne basuyi ba na ajiye musu nasu a kitchen kuma da ka shiga zaka gani.’

Ya kalleta shekeke yace ‘Ai ba yau kika fara ba, kuma ba yau na fara yi miki magana ba. Babu wani akuri da zan bata idan kin gyara halinki su yaran zasu gaya mata ai. Mugun halin da kike nuna musu kuma ki cigaba kada ki fasa.’

Ya mike zai fita, ta kama hannunsa itama ta mike tana cewa ‘Don Allah kayi hakuri, yaran da nake hidimarsu tun kafin na aureka kuma yanzu ribar me zan ce idan nayi musu mugunta?’

‘Nima shine abinda nake mamaki, watakila daman ba don Allah kike yi ba ko kuma zugaki aka yi kika canza hali ni ban sani ba. Abinda na sani kawai shine kusan tun da Khadeeja ta bar gidan nan kika dage sai kin raba rayuwarki da ta yaran nan, ina kula da yanda kike kokarin ganin basu hawo benen nan ba saboda tsabar samun waje…’

‘Don Allah ka dai wannan maganar, wallahi kai ma ka san ba haka bane. Naga dai ko gidan waye akwai part din mai gida inda ba a bari yara su shiga, amma in sha Allahu ba zan sake hakan ba tunda na ga kai ba haka ne tsarinka ba.’ Ta katseshi cikin kosawa.

Ya zare hannunsa da ta rike ya mike yana cewa ‘Ki kawo min abincin parlor din kasa yanzu.’

Ya fice ba tare da ya saurari amsarta ba.

Haka ta gama zumbura baki ta sauko ta kawo masa abincin nan parlor din kasa inda a zauna suka ci da yaran; duk da sun nuna msa suma tuwo aka basu irin nashi.

PAGE 239

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Haka ya kafa mata dokar idan dai yana gidan to a parlor din kasa zai dinga cin abinci wajen yara, babu rokon da bata yi masa ba a kan ya bari yaran su dinga hawowa saman ana cin abincin tare amma ya ki ya saurareta. Ya kula cewa ganin saman bene take kamar wani abu na musamman don haka ya yanke shawarar bar mata saman benen ita kadai. Ya yanke shawarar a kasa zai dinga zama hira kuma a nan zai dinga kallo yana cin abinci, in ya so idan zai yi bacci ya dinga hawa saman ya kwanta. Tayi yanda take so da saman ita kadai.

…….

Yana sane ya ki zuwa gidan Hajia a ranan sai washegari; ya san idan ya je zancen nan bai huce ba Hajia da Alaji haduwa za suyi a kansa har sai ya rasa binda yake masa dadi. Don haka washegari yana tashi daga office ya wuce gidan Hajia.

Bayan sun gaggisa ya sami Alhaji a parlor, yana gama amsa gaisuwarsa yace ‘Mustapha me yake faruwa ne a gidan naka? Ban ji dadin bayanan da na samu daga wajen Habib ba kuma sai ga Hajia ta je ta gani da idonta. Me yake faruwa ne?’

Ya gyara zama ya shafa kansa sannan yace ‘Wallahi Alhaji ‘yar matsala ce aka samu kuma na ma yi mata magana in sha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba.’

Ya tashi daga kashingidar da yake yana cewa ‘Yar matsala? ‘yar matsala fa kace Mustapha? An bar yara a kasa kamar masu zaman kansu amma kana cewa ‘yar matsala? Gidan naka har ya kai an raba tukunya, ta marayun yaranka da ban ta matar gida da ban. Anya kuwa Mustapha? Rashin uwa ai ba hauka bane da zaka wulakantasu saboda Allah ya dauki ran mahaifiyarsu.’

Ya sake shafa kansa ‘Wallahi Alhaji akasi aka samu kuma in sha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba.’

Ya kawar da kai cike da damuwa yayi shiru, jimawa kadan ya cigaba ‘Ita Khadeeja ya wajen nata da Muhamadun? Kana zuwa dai?’

Ya gyara zama yana murmushi ‘Eh, ina zuwa. Jiya ma na je.’

‘To ya kamata dai ka san yanda za ayi ku daidaita tsakaninku tunda dai ka ga ita ba a taba samun wata matsala tsakaninta da yaran nan ba, hadawa tayi ta rikesu tun kafin ma ta sami nata. Kuma da ta sami natan ma babu abinda ya canza. Ka ga itace ta zama uwa ta gari a wajensu tunda gasu kalau da tarbiyyarsu.’

PAGE 240

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

‘Hakane Alhaji, in sha Allahu zamu daidaita.’

‘Ya kamata dai ka san abun yi tunda ka san dai yanzu a kasuwa take, idan baka maida hankali ba wani zai iya yi maka shigar sauri.’

Suka karasa hirarrakinsu sannan yayi musu sallama ya wuce office.

PAGE 241

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Dole tana ji tana gani ya kafa mata doka idan dai har zai ci abinci to parlor din kasa zai ci. Babu yanda bata yi da shi ba yaran su dinga hawowa sama amma yace ba zasu hau ba tunda ita saman take so a bar mata, haka ta hakura ta saka masa ido saboda abun yana nema ya zama matsala a tsakaninsu.

Duk wani taimako da aiki da malamai zasu yi mata tana kan yi sai dai abun yaki yi, idan yayi kamar zai kama sai kuma ya sake botsare mata. Idan dai tana son ganin walwalarsa to ta yiwa yaran nan yanda suke so kuma ba tare da ta yi masa wani korafi ba.

Burinta daya yanzu a aurar da Afaf domin haka ne kawai take ganin zata sami natsuwa a gidan nan. Don a halin da ake ciki komai zai yi da Afaf yake shawara, wasu lokutan ko ta bashi list din cefanen gidan sai ya tambayi Afaf abinda take bukata ita da kannenta ya siyo musu. Idan kuma ya kawo kayan sai ya tsaya a kasa Afaf din ta ware nasu kayan sannan ya hau mata sama da sauran. Haka dai take hakuri, musamman da yake ya iya lallabata ya tsarata kawai dai ya nuna mata yaran nan nasa ba zasu tabu ba.

Haka rayuwarsu ta cigaba.

¬-------

Duk yanda yake jin zai samu Khadeeja ta saurareshi ya gagara, gashi kuma sai a yanzu Allah ya jarrabeshi da kaunarta.

Kusan kullum sai yayi mata waya, idan ta ga dama ta dauka idan kuma ba ta ga dama ba taki dauka. Ya mayarwa kansa duk Juma’a da yamma sai ya je gidan duba Hammad, sai dai hakan bai bashi damar ganinta ba. Domin idan yaje ko da yayi mata waya haka zata saka a bude masa parlor din baki ta turo masa Hammad, har ya gama hirarsa da Hammad ya tafi ba zata fito ba. Don haka wasu lokutan sai kawai ya rutsata a office inda dole ta zauna su gaisa har su dan yi hira.

Abu daya ne yake hanashi zakewa a kan maganarta saboda har yanzu yana jin kunyar Baffanta, baisan da wane bakin zai je yace masa ya sake bashi auren Khadeeja ba. Shi yasa ya dage yake kokarin ganin ya gamsar da Khadeejan ta jewa Baffan da maganar da kanta.

PAGE 242

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Kwanci tashi har shekara ta zagayo.

Tun da ya gama hada takardun yake cike da farin ciki, haka ya kwana cike da zakuwa sabodan yanda yake son gari ya waye ya jr ya sami Khadeeja yayi mata albishir.



Yana fita office dinta ya fara tsayawa, yayi sa’a kuwa ta riga ta zo.

Kamar yanda ya saba a cikin office din ya sameta tana zaune tana editing script din da zata yi amfani da shi wajen gabatar da show dinta.

Yana shiga ya tura kofar sannan ya yiwa kansa mazauni a kujerar gabanta cike da walwala. Bayan sun gaisa yace ‘Kina jin dadinki fa, kin ga yanda kike sheki kuwa.’

Tayi dariya tace ‘Don Allah ka bari, haba. Ko waya ma baka yi min ba kace min zaka zo to da ka zo na riga na shiga studio fa?’

Shima dariyar yayi yace ‘Sai na jiraki mana. Ai idan kina son na daina zuwa wajen nan to ki yarda mu mayar da auren mu mu huta, in ba haka ba dole kullum na zo nan nayi attendance don duk masu shirin yi min shigar sauri su ganni su san ina nan ba fashi.’

Ta sunkuyar da kai don bata san me zata ce masa ba, amma dai yawana zuwan nashi office din ya fara gundurarta. Ba wai don bata so a ganshi bane kuma ba wai tana jin ya isa ya hanata kula wanda take son kulawa ba; kawai dai tana so ya dana bata space tunda ita dai ta gama magana a kan lallai ba zata koma gidansa ba kuma har yanzu hakane a ranta.

Muryarsa ce ta katse mata tunanin da ya kirawo sunanta, ta dago ta kalleshi suka hada ido sannan ta kawar da kai.

Yace ‘Ki sauwake mana wahala ki yarda mu mayar da aurenmu, duk wani abu da ya bata miki rai a baya nayi miki alkawarin ba zaki sake gamuwa da shi ba a zamanmu.’

Ta jijjiga kai ‘Na fahimceka Mustapha, amma dai kayi hakuri. Ba wai kaine ba zan aura ba, auren ne gaba daya ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login