Showing 18001 words to 21000 words out of 99112 words

Chapter 7 - Mijin Marigayiyya Part Complete Hausa Novels.docx

17 Sep 2025

71

ta ambaci sunan nata. Cikin sanyin murya tace ‘Anti Iyami.’

‘Na’am, Khadeeja. Wa ya kawoki?’

‘Muatapha ne.’

Ta juya ta kalli abokiyar aikin nata tace ‘’Yata ce ai, itace wadda mukayi biki kwanaki fa yarinyar Habiba wadda nace miki chiildhood friend dina ce.’

Da fara’a tace ‘Aaah! Allah sarki, to abun ya zo kenan haihuwa yakin mata.’

‘Ai kuwa. Bari na kirawo Dr. Jamil ya zo ya duban min ita sai muje na kaita scanning din muga ko za a iya sallamrta a daren nan.’

Har ta juya zata fice Khadeeja ta riko hannunta, ta juyo tana cewa ‘Akwai wani abu ne Khadeeja?’

Tayi murmushin yake ta goge kwallar da ta gangaro daga gefen idonta tace ‘Kada ki sallameni Anti Iyami, ki yiwa Mommy waya ta zo ta daukeni gida zan tafi.’

Ta dan rankwafo tana shafa kanta tana duban fuskarta tace ‘Ok, kada ki damu, ki samu ki huta tukunna likita ya duba ki. In sha Allahu yanzu zan kirawota ko bata zo ba da safe idan na tashi daga aiki sai na tafi da ke gidan Mommy din. Kada ki damu.’

Ta juya ta fice yayinda Khadijan ta mayar da idonta ta rufe.

Tare da likitan suka dawo, bayan ya duba Khaddej aka je aka yiwo scanning tare da Mustaphan aka dawo. Bayan likita ya duba scanning din yace cikin jikinta ya lalace fita zai yi, don haka za ayi mata wankin ciki sannan akwai allurai da ruwa da za a saka mata.

Da kansa yaje ya siyo komai ya kawo sannan suka koma wajen Khadeeja tare da matron; a nan Khadeejan take sanar da shi cewa martron kawar Mommy ce.

PAGE 47

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ya sake gaisheta cike da girmamawa, bayan ta amsa ta dubi Khadeejan tace ‘Likita ya ce cikin jikinki ya lalace don haka za a yi miki wankin ciki, ga magunguna kuma ya rubuta miki sannan ga drip idan an gama wankin cikin zan saka miki kinga yau a nan zamu kwana da ni da ke.’

Tayi murmushin yake, ta dubi Mustapha tace ‘Ka tafi, ka bar yara a gida. Anti Iyami zata kirawoka idan akwai wani abu tunda ka ga tare zamu kwana ma, zuwa da safe zamu yi waya in sha Allah.

Matron ta fice ta basu waje. Bayan ta fice ya matsa kan Khadeejan yana saha fuskarta yace ‘Sannu, kin bani tsoro fa.’

Tayi murmushi.

Ya cigaba ‘Kafin safiyar tayi sai ki samu ki yi mi message din duk abinda kike so na taho miki da shi, idan kuma Allah ya sa da safen zasu sallameki ma shike nan sai kawai na zo mu tafi. Na yi maganar abici ma Anti Iyami tace na bari zata kawo miki, but in ana son wani abu kiyi min magana sai na saka miki kudi a account dinki ko transfer ne sai kiyi musu.’

Ya sa hannu a aljihunsa ya zaro wayarta ya mika mata yana cewa ‘Ga wayarki, ba zan kirawoki ba don kada na dameki ko na tashe daga bacci, but please da kin farka ki kirawo ni.’

Ta karba tana murmushi tana cewa ‘Ok, ka gaishe min da su Yaya Afaf.’

Ya fice ya barta a kwance.

Yana fitowa ya sami Anti Iyami da abokan aikinta a station dinsu, yayi mata sallama bayan ta karbi lambar wayarsa sannan ya wuce.

………

Tun a daren Anti Iyami ta kirawo Mommy ta sanar da ita halin da ake ciki, sai dai bata gaya mata cewa Khadeejan tace gida zata taho ba. Ta dai sanar da ita cewa tana hannunta idan akwai wani abu zasu ji zuwa wayewar gari.

Tana tsaye aka yiwa Khadeeja wankin ciki sannan aka bata daki, ta saka mata drip da alluranta sannan ta hada mata sahyi mai kauri. Ta sakata a gaba bayan ta shanye sannan ta zuba mata shayi da kwai ta cinye sannan ta ajiye mata saucer da kankana da lemon bawo tace ta shanye kafin a jima.

Ta sha tambayoyi a wajen Anti Iyami wadda take kokarin gane dalilin da yasa Khadeejan take son tafiya gida; sai dai bata sami komai ba don da a tunaninta ko Mustaphan yana abusing dinta ne.

PAGE 48

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

ita kuma ta sanar da ita kawai bata da lafiya ne sannan kuma ga aikin gida da raino wanda yayi mata yawa shi yasa take son ta je gida ta huta.

_______

A gajiye ya shiga gidan wajen karfe tara na dare, yana shiga yaran suka taso da gudu gaba daya tun kafin ya gama rufe kofar motar suba cewa ‘Abba ina Anti Khadeeja?’

Ya dauki shukura ya kana hannun Nasreen yana cewa ‘Tana asibita, likita ya kwantar da ita, amma gobe in sha Allahu zan je na taho da ita.’

Ya tattara su suka shige cikin gidan.

Yana shiga bayan Ummi tayi masa sannu da zuwa ya sallameta ya fito ya rakata sai da ta shiga gida ta kirawo masa babanta yayi godiya sannan ya koma gida. Sai da ya biya sallar Magriba da Isha’I duk da yunwar da yake ji sannan ya zo ya zauna a parlor a gajiya, ya dubi Afaf wadda take kwance tana yin game a tab dinta yace ‘Afaf dauko min flask da kayan shayi.’

Ta mike ta shiga kitchen din, jimawa kadan ta futo dauke da kayan shayin bayan ta ajiye tace Abba babu ruwan zafi a flask ka jira na dafa maka, wanda Anti ta zuba mun sha shayi dashi mu da Ummi.’

‘No, barshi kawai. Dauko min zobo ki kawo min ragowar abincin da kuka ajiye na ci, yunwa nake ji.’

Kafin ta bashi amsa Habib yace ‘Abba ai tun kafin ku fita zobon ya bare a nan, ka manta? Kuma dama shi kenan wanda Anti ta zuba ragowar na jiya ne.’

Kafin yace wani abu Afaf tace ‘Abba babu fa abincin ma sai dai ragowar rice and stew, gaba daya dankalin muka cinye kuma da peppersoup din, amma akwai ragowar watermelon a fridge. Ko na dafa maka indomie?’

Ya kalleta yana shafa kai na dan lokaci, ya ma rasa me zai ce mata sabod yanda gaba daya ya jigata saboda yunwa, coke kawai ya samu a asibiti da wani guntun burodi ya ci. Ya zata zasu rage abincin amma wai duk sun ciye.

Muryar Afaf ce ta katse shi tana cewa ‘Bari kawai na dafa maka indomie din Abba.’

‘No, bari na shiga kitchen din na gani.’ Ya fada yana mikewa tsaye.

Ya dan dauki lokaci yana kallon kitchen din bai ma san ta inda zai fara ba; har ya dauki tukunya zai dafa indomie sai kuma ya tuna ai akwai cereal, don haka ya mayar da tukunyar ya ajiyeta a muhallinta. Ya zuba ruwan zafi a kettle ya jona

PAGE 49

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ya zuba ruwan zafi a kettle ya tafasa ya hada cereal, ya ajiye ya fiddo kankana daga fridge ya yanka sannan ya dauko ya dawo parlor din.

Yana zama Shukra ta matso tana dariya ‘Abba zan sha golden morn din.’

Ya bita da kallo da cokali a hannunsa; bata taba bashi takaici ba kamar a wannan lokacin don ya tabbatar sun koshi tunda gashi sun cinye duk wannan uban abincin da Khadeeja ta dafa. Ya dubi Afaf yace ‘Tashi ki dauko cereal, ki hado min da tea flask da komai na hada mata.’

Kafin Afaf ta dawo Nasreen tace ‘Abba nima zan sha.’

Don haka tana kawowa ya sa ta koma ta karo kofi, ya hada musu cereal din su biyun.

Babu wadda ta sha cokali uku a cikinsu, suka tashi suka bar masa a nan. Kafin ya gama cinye nasa abincin duk sun fara gyangyadi don haka ya sa Afaf ta dauko musu kayan baccinsu ya shiryasu bayan ya rakasu sunyi brush sun yi fitsari. Bayan sun kwanta sannan Afaf da Habib suma suka shirya, Afaf ta zauna a gefen gado tayi tsuru-tsuru shima Habib sai ya hau katifarsa ya kwanta yana zare ido.

Yana tsaye daga bakin kofa yace ‘Yaya dai Afaf? Ki kwanta mana, ko akwai wata damuwa ne?’

Ta jijjiga kai tace ‘Kawai tunawa nayi da Mommy, itama muna bacci ta mutu.’

Ya gaji sosai ga kansa yana sarawa, babu abinda zai iya yi musu na lallashi, ya bude baki a gajiye yace ‘In sha Allahu babu abinda zai sami Anti, kuyi addu’a ku kwanta kuyi bacci kawai.’

Halifa shima ya tashi zaune yana share kwalla ‘Wallahi Abba ni ba zan ma iya baccin ba, Allah ya sa dai kada Anti Khadeejan ma ta mutu ta barmu. Har yanzu idan na tuna Mommynmu sai na yi kuka.’

Kafin yayi magana itama Afafa din hawaye ya fara bin fuskarta, ta sunkuyar da kai ta sa masa kuka harda shassheka.

Ji yayi kamar ya dora hannu a ka ya sa ihu; ina ma yaran nana zasu barshi ya huta, yanzu ya zai yi da su? Manyan cikinsu da yake ganin sune ba zasu bashi matsala ba sune suke so su hanashi bacci. Ya karasa ya zauna a kusa da Afaf ya rungumota yana cewa ‘In sha Allahu babu abinda zai sameta, ku daina kuka kuyi mata addu’a Allah ya bata lafiya. Goben nan ma zaku ga an sallamota.’

PAGE 50

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta fara share hawayenta, Habib wanda shima ya taso ya dawo kusa da ita yace ‘Abba to ka kirawo mana ita a waya mu yi mata sannu.’

Ya zaro wayarsa daga aljihu yana cewa ‘To ai da bana son kiranta saboda kar na dameta don an yi mata allurai, ban sani ba ko harda ta bacci a ciki. Amma bari na kirawota sau daya idan ta daga shikenan idan kuma bata daga ba sai mu hakura da safe ma sake kira.’

Ya lalubo lambarta ya danna mata kira, sai da wayar ta kusa tsinkewa sannan ta daga. Murya kasa-kasa tace ‘Hello.’

Yace ‘Hello, Khadeeja ba kiyi bacci ba?’

‘Na dan yi, farkawa dai nayi kuma naji wayar tana ringing. Ai tun dazu aka gama wankin cikin har na dan ci abinci.’

‘Sannu. Wankin cikin ba wahala kenan?’

‘Hmmm! Akwai wahala ba kadan ba, kawai dai da an gama aka bawa mutum maguguna sai ya sami relief.’

‘Sannu. Afaf ce dama ita da Habibi wai ba zasu iya barci ba sai sun yi miki sannu.’

Tayi murmushi mai sauti domin ta ji dadi har cikin ranta, ta tabbatar cewa yaran nan suna kaunarta kuma da zai barta da su komai nasu zai zo da sauki amma shi komai gani yake kamar zata cuce su. Muryar Afaf ce ta katseta bayan da Abbanta ya bata wayar ‘Anti.’

‘Na’am Afaf, ya aka yi ba kiyi bacci ba.’

‘Babu komai Anti, ya jikin naki? Ke ya aka yi bakiyi baccin ba?

Tayi ‘yar dariya tace ‘Yanzu zan yi Afaf, kuma na sami lafiya don likitan ma ya ce gobe za a sallame ni.’

Suka dan taba hira sannan tayi mata sallama ta mikawa Habib wayar. Bayan sun gama gaba daya ya karbi wayar ya katse yayi mata sai da safe. Ya yi musu sai da safe suka kwanta, har zai kashe fitilar Afaf tace ‘Abba kada ka kashe mana fitilar, in an jima ka zo ka kashe.’

Haka ya bar musu fitilar ya fice.

Can bayan awa daya ya gama abinda yake yana so ya kwanta saboda ya gaji ya zo zai kashe musu fitilar, yana kashewa Afaf da Habib suka hada baki a lokaci guda suka ce ‘Abba kada ka kashe fitilar.’

Da mamaki yace ‘Kai! Me kuke baku yi barci ba?’

Afaf tace ‘Abba to ni dai na kasa bacci, da ma zaka taya mu kwana.’

Habib yace ‘Eh wallahi Abba don ni wallahi tsoro nake ji.’

Takaici ya kamashi, to yanzu ya zai yi? Taya su kwanan zai yi ko kuwa barinsu zai yi a haka su

PAGE 51

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Takaici ya kamashi, to yanzu ya zai yi? Taya su kwanan zai yi ko kuwa barinsu zai yi a haka suna zare ido yaje ya kwanta? Wannan wacce irin fitna ce a daren nan gashi ya gaji.

Baya son barinsu su kadai don haka ya wuce dakinsa yaje ya shirya ya rufo gidan sannan ya dawo nan dakin; katifar Habib karama ce ya san ba zata ishesu ba don haka kawai ya gyarawa Nasreen da Shukra kwanciya ya dan sami waje a gefen gadon ya kwanta bayan Khadeeja ta kwanta a daya gefen. Yayi addu’a ya tofa musu sannan yace kowa ya rufe idonsa kada ya sake jin motsinsu.

Tunda ya kwanta yake jin wani dan doyi haka, idan iska ta busa sai ya ji kamar doyin ya buso cikin daki idan iskar ta wuce kuma sai ya daina ji. A haka bai san lokacin da bacci ya daukeshi ba.

‘Subhanallahi!’ ya fada bayan yayi firgigit ya tashi, ya kai hannunsa ya taba inda yake kwance daidai duwawunsa yaji shi a cikin ruwa sosai. Ya daga hannun yana kallo da tsananan mamaki ‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.’ Ya sake fada a fili.

to fitsarin kwance yayi ko me? Gashi yaran duk sunyi bacci balle yace wni ne ya zuba masa ruwa; tunda shi dai ya san baya fitsarin kwance. Motsin Shukra da yaji a kusa da shi ne ya tabbatar masa da cewa itace tayi fitsarin, ya mika hannu ya tabata ya jita a jike amma tana ta baccinta hankali kwance. Ya kai hannu zai janye Nasreen daga kusa da ita ya jita itama a jike ‘Tab!’ ya fada a fili. Kenan duka su biyun suke fitsrin kwance ko kuwa yau suka fara? Don shi tunda Khadeeja ta tare a gidan nan sau daya ya taba ji an ce Shukra ta yi fitsari. Ya kalli Afaf wadda ita tana can ta takure a karshen gadon tana baccinta, ya danna wayarsa ya kalli lokaci yaga karfe biyun dare. Ba zai iya tashin yaran nan ba don haka ya lallaba ya sauka daga kan gadon ya fice ya shiga dakin Khadeeja ya samo zanin gado ya zo ya rufe su saboda kar sanyi ya dinga kadasu ga danshi.

PAGE 52

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Bayan ya gama rufesu ya zo ficewa daga dakin doyin da yake ta ji ya sake dukan hancinsa; wannan doyin ai sai ya kymburawa mutum ciki. Kamar daga bandaki doyin yake fitowa don haka ya koma ya bude kofar bandakin ya shiga, ya karasa ya leka toilet din ya tarar babu komai a ciki duk da haka dai ya danna flushing ya juya zai fita. A daidai bakin kofa daga jikin bango ya ci karo da fo din Shukra wanda dazu Afaf ta cire wandon Shukra mai dauke da kashi ta jefa a ciki. Pant din yana nan da kashin a yanda ta ajiye har ya fara bushewa amma duk ya dumame bandaki da doyi.

Ya dan ja baya kamar a firgice, to wa Afaf ta ajiewa wannan kashin? Yanzu ya zai yi da shi gashi duk ya dumame gidan da wari. Ya daga hannuwansa ya zuba a aljihu, danshin da yaji ya tuna masa cewa wandon a jike yake da fitsrin Shukra ce ko Nasreen shima bai sani ba. Yayi tsaki ya fito daga bandakin ya wuce dakinsa yana tunanin yanda zai yi da kashin, gashi a jikin pant yake balle ya sa a toilet yayi flushing.

PAGE 53

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Saida yayi wanka ya canza kaya sannan ya fito daga dakin, yana fitowa yaji warin kashin nan har parlor din saboda ya bar kofar a bude. A fusace ya wuce kitchen ya dauko katuwar bakar leda ya zo ya dauki fo din ya kulle a ledar, ya sake dauko wata ledar ya kara kullewa sannan ya dauki mukulli ya bude kofa ya fice ya jefa a shara; gari yana wayewa zai sami yaro ya fitar masa da sharar. Ya san dai Shukra ta iya hawa toilet yanzu, duk da idan ta so rigima sai tace sai ta hau fo amma shi dai ya zubar don ba zai iya wankin kashi ba kuma ba zai iya bari Afaf tayi ba ta zo ta yi musu jagwalgwalo da kashi.

Yana dawowa cikin parlor din ya kalli agogon bango yaga karfe uku har ta wuce, abinda yayi masa saura bai fi awa daya da rabi ba ayi assalatu. Sai a lokacin ya tuna bashi ma da abincin sahur, gashi kuma ko a lokacin ma yunwa yake ji balle yace zai yi dore. Kai tsaye ya wuce kitchen ya dora indomie sannan ya tafasa ruwan shayi; nan da nana ya juye indomie din a plate ya dumama stew ya zuba sannan ya hada shayi, ya kwaso ya dawo dining table ya fara ci.

Tun kafin ya hadiye lomar farko ya fara jiyo hayaniyar Shukra a dakinsu, yana zuba loma ta biyu ta budo kofar dakin ta fito tana kuka tana ‘Antiiii..’

Ya ajiye cokalin yace ‘Menene Shukra?’

‘Shayi zan sha Abba’

Har cikin zuciyarsa takaicinta ya kamashi, to amma ya zai yi da ita? Haka ya kirawota ya zaunar da ita a kan kujera, tun kafin ya gama gyara mata zamanta zarni ya cika masa hanci; sannan ma ya tuna tayi fitsarin kwance. Ya gyara mata zama yace ‘Bari na gama sahur sai na hada miki shayin.’

Ya dauki cokali ya zuba loma a bakinsa yayinda ita kuma ta fara mutssike ido tana kuka.

‘Menene kuma?’ ya tambayeta

‘Yunwa nake ji, shaaayiii.’ Ya duba agogon wayarsa, saura bai fi minti goma sha biyar ba a yi assalatu ga shi baya jin zai kai azumin nan idan bai yi sahur ba, ya kalleta yanda take ta kuka kamar wadad aka ciza. Bai taba jin haushin Shukra kamar yau ba, amma babu yanda zai yi. Haka ya juye mata rabin shayin da ya hada zai sha ya saka mata madara da milo ya mika mata sannan ya cigaba da cin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login