Showing 63001 words to 66000 words out of 99112 words
shima ya juya ya fice zuciyarsa cike da wasi-wasi saboda ya san wannan murmushin nata ba wai yana nufin zata kula da su bane, amma dai ya tafi yana addu’ar Allah ya sa ta kula masa da su.
PAGE 158
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Sai bayan la’asar suka dawo tare kamar yanda suka fita, a lokacin yara suna islamiyya. Don haka cikin wallwala ya karas ciki don ya san Khadeeja ta kular masa da yaran. Sai da ya leka parlor dinta ya gaya mata ya dawo sannan ya wuce dakinsa.
Yara suna dawowa daga islamiyya suka wuce parlor din Naja inda suka jiyosu ita da Abbansu. Kafin wani yayi magana Shukra ta fada jikin Naja tace “Yauwa Anti kin dafa bana abinci ko? Wallahi yau gari muka sha mu da Anti, tace idan kin dawo zaki dafa mana abinci.’
Ta kalli Mustapha sanna ta sake kallon Shukran, kafin tace wani abu Mustaphan ya janyo Shukra jikinsa yace ‘Gari kuka ci Shukra?’
Ta daga masa kai. Nan take ragowar yara suka tabbatar masa da haka aka yi.
Ya kalli Afaf wadda shigowarta kenan tana kokarin zama yace ‘Ke ba sai ki dafa muku ko indomie bace?’
Ta zumbura baki ta kawar da kai ba tare da tace komai ba.
Yayi gajeren tsaki sannan ya dubi Nasreen yace ‘Ina Hafsa? Ita ba sai ta dafa muku ba?’
‘Itama garin tace ai, Anti bata ce ta dafa komai ba haka tace mu jira Anti Naja ta dawo itace da girki.’
Ya kalli Najan wadda take ta fama cika tana batsewa, ya mike a fusace ya fice daga parlor din.
Tana zaune a parlor dinta tana shan kunun alkama ya sameta, kafin ta gama amsa sallamarsa ya fara magana a fusace ‘Khadeeja wane irin raini da wulakanci ne zai saka ki bawa yara gari, ke ba zaki girka musu abinci ba kuma ba zaki saka yarinyarki ta girka musu ba.’
Ta ajiye kofin kununta ta kalle shi tana jijjiga kai sannan cikin halin ko in kula tace ‘To ai mai girkin bata bar musu abinci ba kuma bata barwa yarinyar tawa wani abu tace ta dafa musu ba, shi yasa da aka ji yunwa na hada mana gari duka muka sha. Ina laifi?’
Ya fesar da iska mai zafi saboda yanda takaici ya kamashi, baya son yanda idan Khadeeja zata yi masa fitna take zama da nutsuwarta shi kuma tana saka shi yana yin spark. ‘Khadeeja, don Allah me kike so ne kike min wanna wulakancin.’
PAGE 159
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
‘Ba wulakanci nake maka ba. Abu daya kawai nake so shine kayi adalci, yanda nake bukatar hutu daga kwana saboda jego haka nake bukatar hutu daga hidimar gida da ta yara, don dama wallahi dagewa nakeyi. Idan kuka gama arba’in din muka fara rabon kwan sai na dinga hadawa ina karba.’
Yaja dogon tsaki ya yarfar da hannu, har ya bude baki zai yi magana kuma sai ya fasa. Ya juya ya fice daga parlor din.
……..
Duk yanda yake tunanin Khadeeja zata saurara masa hakan bai samu ba. Yana so ya mayar mata da kwananta da ya karab ya bawa Naja amma kuma yana son karin lokaci don ya kara sabawa da Najan. Haka dole ya hakura ya zuba musu ido; sai dai duk wani jin dadi da yake sa ran zai samu daga wajen Najan baya samuwa saboda yanda take wuni a gajiye saboda hidima. Suna kwanciya bacci yake kwasheta; gashi kullum cikin yi masa mita take a kan ita ya mayar da hidimar yara wajen Khadeeja. Duk da kusan Khadeejan ta sallama musu Hafsa tana tayata.
Ita kuwa Khadeeja gaba daya haushinta yake ji don gaba daya ya daina kulata, a yanda yake ji yanzu ma baya jin zai kulata koda tayi arba’in din idan dai ba itace ta kawo kanta ta bashi hakuri ba.
PAGE 160
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Duk yanda Naja ta zata kula da yaran nan zai yi mata sauki abun ba haka bane, domin da kyara take kaiwa yamma saboda gajiya. Gashi Khadeeja ta sallama musu Hafsa kullum cikin taimaka mata take; abu daya da Khadeeja ta hana Hafsa yi mata shine girki. Ta so kwarai ace ta dinga barwa Hafsa tana yi musu girki idan ta fita, amma Khadeeja ta ki bari. Don haka kullum kafin ta fita aiki sai ta dafa musu abincin rana kuma idan ta dawo sai tayi na dare. Gashi duk da suna shiri da Afaf ta gane Afaf ta fita son jiki, don duk yanda take jin zasu tayata aiki hakan ma bai samu ba.
…….
Yau satinta biyu da tarewa; yana zaune a parlor dinta shi da yaransa kamar yanda suka saba suna kallon TV bayan sallar isha’i. Ita kadai ce a tsaye tana kokarin jera abincin dare a dining. Tana jerawa tana mita a ranta yanda yaran basa tayata aiki, ko da zata ce su tayata to fa idan dai yana nan ba zasu tayata ba; sai dai tayi aikinta ita kadai. Gashi kuma baya son Hafsa ta dinga yi masa girki. Bayan ta gama jera abincin suka taso gaba dayansu suka zauna harda ita suna cin abinci.
Jollof sphagetti ce da kifi; ana cikin cin abincin Shukra ta daga kifin da yake kwanonta tace ‘Abba a cire min kaya.’
Har ta bude baki zata ce Afaf ta cire mata yayi sari yace ‘Ki mikowa Antinki ta cire miki.’
Haka Afaf wadda take zaune a tsakanin Najan da Shukran ta dauki plate din da yake gaban Shukran ta mikawa Naja. Ba tare da ta ce komai ba ta sa hannu ta bara kifin gida biyu ta cire kayar sannan ta mikawa Afaf wadda ta sake mikawa Shukra.
Haka har suka gama cin abincinsu babu wanda Naja ta sake yiwa magana.
…….
Tana zaune a gefen gado tana shirin kwantaw bacci ya tura kofar ya shigo da sallama, da kyar ta amsa sallamarsa saboda yanda take jin haushinsa. Gani take kamar da gayya ya bari matarsa ta sallama mata yaran sannan kuma sun kai su kula da kansu amma komai sai yace sai tayi musu.
Ya karasa ya hau gadon ta bayanta ya kwanta, tana kwanciya ya janyota jikinsa. Ta dan tureshi tana cewa ‘Bacci fa nake ji Habibi, wallahi na gaji. Kuma ka ga gobe yara zasu makaranta kuma zan je aiki.’
PAGE 161
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ya kara kankameta yana laluba jikinta yana cewa ‘Sannu, bari nayi miki massage yanzu gajiya zata sauka.’
Ta dage ta janye jikinta ta zauna a kan gadon, hakan ya sa shima ya tashi ya zauna a kusa da itayana kallon fuskarta kamar mai neman amsa a fuskar tata. Kafin yayi magana ta langabe kai tace ‘Habibi ni dai don Allah ka mayarwa da maman Hammad kwananta, in ya so mu cigaba da yi kwana bibbiyu yanda tsarin yake.’
Da mamaki ya kalleta suka hada ido sannan yace ‘Kin gai dani kenan Baby.’
Ta mika hannu ta shafi gefen fuskarsa tana murmushin yake sannan tace ‘Ya za ayi na gaji da kai, ni kama ai ban ki ba ace ni kadai ce matarka kullum muna tare. Amma ka ga aiki yana yi min yawa sosai, yiwa yara abinci kadai ya isheni da shiryasu makaranta. Kullum a gajiye nake kai kanka baka samun yanda kake so a wajena. Amma ka ga idan zan dinga samun kwana biyu a tsakani na huta ai ina ga hakan zai fi mana sauki ko? Tunda nace a daukar min mai aiki kace Hafsa ta ishemu; ita kuma wannan yarinyar wallahi karin aiki ce saboda ta fi su wasa da son jiki. Ni ban ma san yanda akayi Khadeejan take zama da ita ba. Kawai dai kace ta karbi kwananta.’
Har ta gama maganar yana binta da kallo ba tare da yace komai ba, sai da ta gama ta numfasa sannan yace ‘Um haka ne, amma dai ai kinga kula da yaran yanzu fa ba wani aiki bane tunda gaba dayansu kowa ya iya kula da kansa. Kusan za a iya cewa abinci ne kawai sai an dafa musu.’
Ta kalleshi suka hada ido. Har ta bude baki zata yi magana kuma sai ta fasa; ta kula ba so yake ya karbi uzurinta ba. Yaran da hatta kula da kan nasu ma da yake cewa sun iya idan dai bata tsaya a kansu ba babu wanda zai yi, idan kuma aka barsu haka yace zai yiwa mutane fada. Ta ja numfashi sannan tace ‘To ka dai mayar mata da kwananta don Allah, a fara rabon haka tunda ka ga yanzu saura kusan sati uku ta cika arba’in din.’
PAGE 162
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ya numfasa ya zame sannan ya janyota jikinsa ta gyara mata kwanciya yana shafa bayanta sanna yace ‘Kada ki damu, in sha Allahu da safe zan yi mata magana. Ai na san kina kokari wajen kula da yaran nan kuma suma zaki ga suna jin dadin zama a wajenki, nagode sosai da kike kula min da su.’
A haka dai ya samu ya lallabata suka kwanta.
Ya san wulakancin Khadeeja, tabbas idan yaje yace mata za a fara rabon kwana yanzu ba lallai ta saurareshi ba. Baya jin ma zai iya tunkarata da wannan maganar idan dai ba so yake tayi masa dariya ba.
Haka ya cigaba da lallabar Naja don baya ma son ya tayar da maganar mayarwa da Khadeeja kwanata da ya kwace.
………..
Tunda ta kwana ashirin da bakwai da haihuwa ta yada wankan jego, kuma da yake ita din mace ce wadda ta damu ta fatarta sai ta mayar da hankali wajen gyaran fata da gahsin kanta wadanda ruwan zafi ya bata. A zaman da sukeyi da Mustapha ta san yana jin haushinta saboda ta ki ta cigaba da kula da yara shi da amarya suyi amarci, ta san ba lalli ya barta wasu kudi ba. Don haka ‘yan kudadenta da ta samu a barkan Hammad su ta fito da su ta nemi Baffanta ya kara mata dubu goma sannan ta hado kayan gayarn fata. Nan da nan cikin sati guda haske da santsin fatarta ya fara dawowa.
……….
Kamar yanda ya saba kullum da safe zai leka su gaisa kafin ya fita. Yau din ma haka ya shigo parlor din da sallama. Suna zaune a parlor din ita da Habib suna cin abinci; ita tana zaune ta mike kafa da Hammada a kan cinyarta yayinda shi kuma Habin yake zaune daga gefenta yana cin nasa abincin. Funkaso ne ta soya da zafinsa tare da parpesun kaza suke karyawa da shi; don kanta ta dafa farfesunta amma ta riga ta saba shi Habib idan dai tana nan baya cin abinci a wajen Naja. Don haka idan dai ya shigo bata hanashi, domin wani lokacin ma ajiyewa take yi don ta san zai zo nema.
Ya karasa ya zana a kan kujera daga kusa da Khadeejan, bayan ya amsa gaisuwarsu yace ‘Nan kuka kule kuna cin dadi ashe shi yasa na ji shiru.’
PAGE 163
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Tayi dariya kawai ba tare da tace komai ba, Habib ne yace ‘To ai Abba Anti Naja tuwo ta dafa jiya na san dumame za a ci shi yasa na gudo.’
Sukayi dariya gaba daya. Ta san so yke yace zai ci domin yana son funkaso, ita kuma bata so yace zai cib saboda dafawa tayi har abincin ran tunda so take ta fita idan ta dawo kawai sai taci abunta. Ya dubeta tana cinye funkason karshen yace ‘Idan akwai funkason ki zuba min na dan ci, duk da dai nayi breakfast amma ya bani sha’awa.’
Ji tayi kamar tace masa babu, amma Allah ya sa bata iya rowar abinci ba, musamman ga mutumin da shi ya kawo cefanen. Don haka bayan ta cinye nata ta mike ta kwashi kwanukan ta shige kitchen bayan ta mikawa Mustaphan Hammad; Habib shima ya kwashi nashi kwanukan ya bi bayanta. Jimawa kadan suka fito tare, ta kawo tray din da ta riko ta ajiye a gaban Mustaphan sanna ta sa hannu ta karbi Hammad; shi kuma Habib ya fice daga parlor din.
Ya sauka kasa ya fara cin abincin sannan ya dubeta yace ‘Shine kinyi funkaso ko ki kirawoni.’
Tayi ‘yar dariya tace ‘Ai na san ka riga ka ci better ka cika cikinka shi yasa na sa yarona a gaba muna ci mu kadai.’
Yayi dariya ya mayar da hankali wajen cin abincinsa.
Jimawa kadan ta tahsi ta shige daki, bata dade ba ta fito tana rike da takarda a hannunta. Sai da ta zauna sannan ta mika hannu ta ajiye takardar a gafensa tana cewa ‘Ga posting letter dina, jiya na karbo. Anyi posting dina gidan talabijin na ARTV.’
Nan da nan ya bata rai, bai ce mata komai ba sai da ya karasa cinye abincin sanna ya dubeta yace ‘Kin san dai bana son aikin jaridar nan ko, sai da mace ki saka ayi posting dinki makaranta amma shine kika je kika saka aka kai ki gidan talabijin don ki dinga fitowa a TV.’
Ta kawar da kai tana mamakin Mustapha. Tana karatunta na aikin jarida ya ganta ya aurota amma tunda yaga ta kusa gamawa yake ta faman gaya mata aiki daya zai bari tayi shine koyarwa. Watakila ma da ace bai kara aure ba da ta hakura tayi koyarwar amma yanzu kam babu yanda za ayi ya auro amaryarsa tana aikin office duk da dai ba na TV bane; sannan ita yace koyarwa zata yi.
PAGE 164
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Tace ‘Ni bani nace su kaini can ba, sun duba abinda na karanta ne kawai. Kuma idan nace a kaini makaranta naje na koyar dasu me? Ni da na karanci aikin jarida.’
Cikin halin ko in kula yave ‘Ko hausa ba sai ki koyar ba ko English, amma kin san babu yanda za ayi na barki kina fitowa a gidan TV duk duniya suna kallonki kina iya yi ko?’
‘To yanzu ya kake so ayi?’
‘Kije kawai su canza miki, idan kuma ba haka ba ni zan je a canza amma ba zakiyi aikin TV ba matukar da aurena a kanki bana so.’
Ta dan gyara zama tace ‘To ai ko naje gidan ARTV din ma ba lallai na dinga fitowa a TV ba tunda aiyukan suna da yawa kuma ba duk ma’aikatan ne suke fitowa a TV ba.’
‘Ni dai bana son kije wajen kwata-kwata tunda idan dai kana wajen wata rana za a sakaki a wani shirin kuma babu yanda zaka yi. Kawai kije su mayar dake makaranta ko kuma ki bani takardun ni naje.’ Ya fada yana mikewa tsaye.
Bata ce komai ba yace ‘Ni na tafi gidan Hajia.’
‘A dawo lafiya, ka gaishe min da su.’ Ta fada ba tare da ta kalleshi ba, kuma da yake shima ba kallon nata yekeyi ba bai ma san yanayin da tae ciki ba.
Ta bi bayansa da kallo bayan da ya fice daga parlor din; ta ma rasa me zata ce masa. Koyon aikin jarida ya ganta tana yi ya aurota, kuma sau da dama ta sha gaya masa cewa babu abinda take so take buri kamar ace yau gata a gidan talabijin tana karanta labarai ko kuma gabatar da wani shiri. Sai da ta kusan gama karatun sannan yake sanar da ita shi baya son matarsa ta dinga fitowa a TV, kuma duk lokacin da ya gaya mata ana gaya masa cewa ita kuma burinta daya kenan a duniya. Daga baya nema ta fahimci cewa da ba don ya auro Naja a ma’aikaciya ba to da tabbas ba zai barta tayi aiki ba ma gaba daya. Yanzu kam ma sai taga kamar yana dai so ya takurata ne saboda bata yi masa yanda yake so ba, amma zata san yanda zata bullowa lamarin.
……….
Sai da ta bari dare yayi lokacin ta san Baffa yana zaune a gida sannan ta kirawoshi, bayan sun gaisa ta sanar da shi abinda Mustapha din yace game da inda aka kaita bautar kasa.
PAGE 165
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Bayan a saurari bayaninta yace ‘To ke kije makarantar mana, ai ba shine aikinki ba tunda bautar kasa shekara daya ne kawai.’
Tace ‘To ai Baffa idan naje ina fatan ne su rikeni su bani permanent aiki, kuma ka ga Baffa gaskiya ba zan iya aikin koyarwa ba don za a dinga samun matsala dani.’
‘Um hakane, to bari mu gani. To ko gidan rediyo zaki je a mayar dake? In ya so sai na yiwa Mustaphan bayani.’
‘Baffa ni dai da ka yi masa magana ya barni naje gidan TV din.’
Yace ‘A’a, kiyi hakuri ki yi a gidan rediyo tunda dai yace baya son a dinga nuna matarsa a TV kinga kuma hakan ya nuna yana kishinki. Kije kiyi a gidan rediyo ta yanda ko da an saka ki a wani shiri to muryarki kawai za a ji ba za a ganki ba.’
Ta so kwarai ace Baffa ya goya mata baya ta tafi gidan TV domin shi ya san tun tana yarinya burinta kenan, amma ta san tunda yace haka ba zai goya mata baya ba; sai dai idan ta matsa ranta ya baci. Don haka sai kawai ta hakura. Suka yi sallama da Baffa suka ajiye wayar.
Sati yana zagayowa ta fara bautar kasa a gidan radio na Freedom Radio bayan da Baffa ya kirawo Mustaphan yayi masa bayani sanna ya bashi hakuri a kan ya barta tayi a nan din. Haka ya bari ba don ya so ba.
………
Tunda ta fara zuwa aiki kuma sai aikin gida da na yara suka kara taruwa suka yiwa Naja yawa. Domin sai ya zama kullum idan Khadeeja zata fita da hafsa take fita saboda rike mata Hammad a wajen aiki. Gani haka ya sa Naja ta