Showing 57001 words to 60000 words out of 99112 words
by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ta sunkuyar da kanta tana duban cinyarta domin tana tsoron kada idanuwanta su bada ita ta hanyar tunkuda awaye a daidai wannan lokacin. Hajia ta kama hannunta sanna ta kamo hannun Naja ta dora ta hada ta rike tana kallon Khadeejan tana cewa ‘Ga amanar kanwarki nan, ki riketa amana ku zauna lafiya ku samarwa da mijinku nutsuwa. Allah ya hada kayuwanku.’
Mata suka kaure da amshi ‘Amin. Amin.’
Wata cikin iyayen amaryar ta karbe ta cigaba ‘Eh gata nan amana, a yi hakuri uwargida sarautar mata ku zauna cikin amincin Allah domin kayan Alah na annabi ne.’
Aka sake kaurewa da guda.
So take ta zare hannunta amma hajia bata basu dama ba; bugun zucuyarta kara sauri yake yayinda take jin hanunta kamar ta rike wuta. Kokari take ta dafe bakinta saboda kada abinda yake zuciyarta ya fito; Amana! Ita za a bawa amanar matar Mustapha? Ina ruwanta da ita? Ko sunyi mantuwa ne? shi da yaga zai iya da amanar ai yayi gammo ya dauko. Don me zasu ce ita aka bawa amana? Tabbas wanna amana ce da bata karba ba kuma ba zata taba iya karba ba.
Sai da aka gama addu’oi sannan Hajia ta saki hannuwansu, cikin dabara Khadeeja ta faki ido ta goge kwallar da ta taru a kwarmin idonta.
Ba dadewa kuma aka fara mikewa aka kama hannun amarya aka nufi dakinta, a haka ne Khadeeja ta samu ta sulale ta haye sama, yayinda su kuma matan suka bi bayan amarya.
Haka ta koma cikin su Yaya Mama ta cigaba da dagewa, su kuma suna ta bata baki da nasiha. Wajen 9pm gayya ta fara watsewa, aka kirawota ta yi sallama da Hajia, ba dadewa kuma su Yaya Mama suma suka yi mata sallama suka barta ita da Nabeela.
Tana zaune a gefen gadonta tana jiyo yara wajen 11pm suka hawo saman, gaba dayansu sai da suka leka dakinta suka yi mata sai da safe amma banda Afaf, suka wuce dakinsu inda suke kwana tare da Hafsa. Basu dade ba kuma Nabila ta fito daga dakin bakin da yake saman ta turo kofar dakin a hankali ta shiga, ta wuce Khadeejan a gefen gadon ta zagaya ta kwantar da Hammad a gafe ta lullubeshi. Ta zagayo ta zauna a kusa da Khadeejan, bata motsa ba kamar ma bata san an zauna a kusa da ita ba.
PAGE 144
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ta mika hannu ta dafa nata hannun da yake kan cinyarta tana kallon fuskarta tana cewa ‘Yaya Khadeeja ga Hammad fa na kwantar miki da shi.’
Ta kalleta suka hada ido, ba tare da tace komai ba ta sake kawar da idonta saboda ta tokare hawayen da suke neman kwace mata. Nabila ta dan matsa hannunta tana cewa ‘Ya Khadeeja.’
Kafin tace wani abu hawayen ya fara bin idonta, gaba daya ta sakesu saboda yanda take faman rikesu tana jin kamar an dora mata dakon wani kaya mai nauyi. Gaba daya ta fada jikin Nabeela wadda ta rungumeta gaba daya suka sa kuka. Ita Nabeela auren ma gaba daya ya kara bata tsoro’ kuma ta tabbatar ko da wanne lokaci za a iya daura nata auren; tunda da ba don Ahmad ya tafi UK karo karatu ba da tuni ta shekara a daki. Ita kuma Khadeeja gaba daya komai ma ya tsaya mata; tana dai fatan Allah ya sa Mustapha ya zama mai adalci.
A hankali suka fara lafawa, Khadeeja ta zare jikinta ta kalli Nabeela. Suna hada ido suka tuntsire da dariya duk da hawayen da suke fuskokinsu. Suka rike hannun juna suna murmushi. Khadeeja ta dubeta tace ‘Sorry.’
Itama murmushin tayi mata tana cewa ‘Its’s ok, you will be fine in sha allah. Komai zai wuce kamar ba ayi ba.’
Murmushi ta sake mayar mata sanna tace ‘Kije ki kwanta, na san yanzu Abbansu zai shigo.’
Ta sake rungumeta sannan tayi mata sallama ta fice ta rufe mata kofa.
Ba tare da bata lokaci ba ta mike ta shiga bandaki inda ta yiwo wanka sannan ta fito da alwala, ta shirya ta sa kayan bacinta sannan ta kabbara sallar isha’i.
A nan ya shigo ya sameta tana zaune a kan dadduma tana gyangyadi; kallo daya tayi masa taji zuciyarta ta sake komawa cikin damuwa wadda ta fi ta da. Sai wani faman yage baki yake yana muzurai a lokaci guda; a sanin da tayi masa ta san murnace da doki yakeyi na amarya kuma yana kokarin tabbatarwa ita din bata kawo masa cikas ba. Nan da nan ta danne duk wata damuwa da take ranta ta kakalo murmushi tayi masa sannu da zuwa.
A tsaye ya amsa yayi mata bangajiyar biki sannan yace ‘Um ni bari naje, na ga kema bacci kike ji. In ya so da safe na shigo da kanwar taki ku gaisa.’
‘To Allah ya kai mu.’
PAGE 145
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ya juya ya fice ya rufo mata kofa.
Ta ji dadi sosai da ya sanar da ita ba zai shigo da atarsa a wannan daren ba, domin gaba daya a gajiye take. Ba jikinta ba har ruhinta ma ji take ya gaji, fatanta kawai wadannan kwanakin su wuce ko kuma ma ta farka taga mafarki takeyi. Taga rayuwarsu ta dawo kamar yanda take a farkon aurensu; ko da yake a farkon auren ma babu wani abun kirki da zata dorar; kamar dai gara ma tace rayuwarsu ta dawo yanda ake kafin aure.
Sai da bacci ya fara dibanta sannan ta tashi ta kwanta a kan ganto ta kashe fitila.
………
Cike da doki ya shiga dakin amaryarsa rike da ledarsa ta kayan ciye-ciye; tana zaune a can a kuryar gado. Ko da ace ta amsa sallamarsa to shi dai bai ji ba, amma ya riga ya san yanda amare suke. Har inda take ya karasa ya sameta bayan ya ajiye ledar hannunsa a kan mudubi. Ga mamakinsa bayan ya daga fuskarta kuka takeyi sosai da hawaye kamar wadda aka yiwa auren dole, don haka nan take ya shiga aikin lallashi. Sai da suka kusan minti talatin sanna ya samu ta goge hawayen ta saurareshi.
‘Wai me ya faru ne kike ta faman kuka haka sai kace wadda aka yiwa auren dole?’
Ta balla masa harara ta dauke kai sannan tace ‘Ni da ka kawo na zabi dakin da nake so a sama kusa da nka dakin shine za a kawoni a ajiye ni a nan, ka sa ina nema nayi musu da masu kawoni.’
Ya yi murmushin yake ya sake kamo hannunta wanda ta riga ta fizge yana cewa ‘Haba ke kuwa? Ai na zata da suka zo kafi sun gaya miki.’
Ta zumbura baki ‘Ni babu wanda ya gaya min, sai da aka kawo ni kawai naga an ajiyeni a kofar gida kamar wata wadda ba a so zuwanta ba.’
Nan ya shiga faman bata hakuri da bayani tana faman fizgewa har dai ya samu ta sauko. Ta kalleshi tace ‘Amma gaskiya ni fa ba zan zauna a nan ba, matarka da yaranka da kai kuna sama. Kenan fa duk ranar da ba kwana na ba ni kadai ce a kasa bakin kofa. Gaskiya wannan tysarin bai yi min ba, ko dai a bani sama ko kuma gaskiya ka nema min wani gidan. Wannan ai duk wanda ma ya zo ya san matsayina.’
PAGE 146
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ya kara matsawa ya janyota jikinsa ‘Kin ga, kada wannan ya dameki. Ko da ban kama wani gidan ba zaki iya komawa saman in ya so ko ni sai na dawo kasan ku kuma gaba daya kuyi zamanku a saman.’
‘Ni dai ba haka nace ba, amma gaskiya ka cika min alkawari don ba zan yarda wata tana sama ni ina kasa ba.’
Haka yayi ta lallabata har ya samu ta amince masa. Ya tattara musu kayansu suka wuce sama dakinsu wanda da farko ta so ta ki zuwa, sai kuma ta tuna gara itama ta hau saman ta ga yanda Khadeejan zata yi.
……..
Da yake dama Hammad bai saba barinta baccin safe ba yau din ma tun wajen 6am ya tashesu, bata bude dakin ba saida tayi wanka shima ta shirya shi. Ta riga ta ji motsinsu tun dare don haka ta san a dakin Mustaphan suka kwana. tana fitowa ta taso Hafsa suka shiga kitchen. Ya siyo burodi kamar yanda ya saba duk dare, don haka nan da nan ta soyawa kowa kwai ta hada kayan shayi tsaf ta bawa hafsa ta sauko da shi kasa. Kafin karfe takwasa ta jera komai da suke bukata ita da yara na breakfast a parlor din kasa. Tana shirin hawowa bene Hafsa ta biyota da wayarta ta mika mata tana ringing. Tana dubawa taga Baffa ne.
Bayan sun gaisa ya kara yi mata nasiha sanna yace mata nan da awa daya Nabeela ta shirya Ahmad zai zo ya dauketa.
Bata ji wata damuwa ba saboda dama ta san halin Baffa, ba tare da bata lokaci ba ta taso Nabila ta sanar da ita. Nan da nan ta hada kayanta don ko wanka cewa tayi idan taje gida tayi abunta, haka ma breakfast cewa tayi idan taje gida ta ci kosai don tabbatar yau lahadi kosai Mommy tayi.
Wajen 9am suna zaune a dining table ita da yara in banda Afaf wadda bata tashi ba ko kuma bata fito daga dakinsu ba. Breakfast sukeyi suna ta hirarrakinsu Shukra sai labari take basu suna dariya gaba daya. Da sallama ya sauko daga benen ya karasa gaba table din yana cewa ‘Ina can ina nemanki a dakinki ashe kina nan ke da yara kuna ta jin dadinku.’
Tayi murmushi ta kwara da kai. Ita da yaran duka suka gaishehi, bayan ya amsa ya dubeta yace ‘Idan kun gama cin abincin ki zo ki bani nawa breakfast din ni da kanwarki.’
PAGE 147
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Tayi murmushin yake tace ‘Da yake mu ma bread da shayi muka sha ba wani abu ba, amma dama naga bread din da yawa ka siyo gashi can mun bar muku guda daya ka dauka ka haye muku da shi. Ko a nan zaku yi breakfast din?’
Ya kalleta da dan mamaki ya cije lebe don baya son ya ja zancen a gaban yara yace ‘Um, idan kin gama dai kya hawo da shi.’
‘Ok.’ Ta amsa cigaba da cin abincinta.
Sai da suka gama cin abincinsu tsaf sannan ta dauki bread din ta haye sama, tana shiga babu kowa a parlor din don haka ta karasa kan dining table ta ajiye bread din ta shige dakinta.
Kamar tare suka shiga dakin don ko zama bata yi ba ya shigo ya tura kofar, yana daga tsaye a jikin kofar yace ‘Wai ya na ganki a nan ina breakfast din namu ni da kanwarki?’
Ta karasa ta zauna a kan gadon ta jingine ta mike kafarta tana cewa ‘Oh, ga bread din can na ajiye muku ai ko akwai wani abun ne?’
Da mamaki yace ‘Ai na zata zaki dan dafa wani abu ko don saboda ganin ga bakuwa kin kwana da ita a gidan.’
Bata san lokacin da dariya ta kwace mata ba, haka kawai maganar tashi sai ta bata dariya musamman da ta kalleshi kuma yana cewa wai “kin kwana da bakuwa”
Ta dan gintse tana kokarin saita fuskarta sanna tace ‘Na kawana da bakuwa ko ka kwana da ita? Tea and bread muka ci fa kuma gashi can na ajiywmata ita bakuwar tawa, ina ga kamar ai dafa ruwan zafi bai kamata ya zama matsala ba ga wanda aka bawa burodi ko?’
Ya bata rai saboda kwat-kwata bai zata haka ba; a iya saninsa sai sun kwana bakwai da amarya Khadeeja tana yi musu girki sannan sai araba kwana amma gashi tana nema ta kawo masa raini. ‘Ba fa na son raini Khadeeja, duk wanda ya kara aure matarsa ta gidan itace take yiwa amarya girki har sai ta kwana bakwai amma zan zo ina miki magana kina min wani zancen banza. Ai ko bazawara na aura kin san ya kamata kiyi mata abinci na kwana uku balle budurwa.’
PAGE 148
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ta kalleshi ta kawar da kai; babu yanda za ayi ta yiwa Naja girki sai dai duk abinda zai yi ya yi; ta tsani Naja ta tsani jin sunanta. Watakila da ace ya biyo ta hanyar da ta dace wajen sanar da ita zai kara aure da wadda zai aura da haushin da take ji bai kai haka ba, amma gaskiya babu abinda zai sa ta yiwa wata Naja girki. Ya auro matarsa ya gama more kwanan amarci sanna ita kuma bayan bacci da bata yi cikin nutsuwa ba kuma ita yake so ta tashi da sassafe ta hada musu breakfast na warware gajiya, bata taba ganin rainin hankali irin wannan ba. Ta bata rai sannan tace ‘Ba a biya mana wannan hadisin ba a islamiyya.’
Mamaki ya kamashi ya bude baki amma ya rasa abinda zai gaya mata. Yana kallo ta zame ta gyra kwanciyarta ta juya masa baya. Bai shirya da wannan mahaukacin taurin kan nata ba wanda idan ta fara shi sai duk garin kowa ya ji. Ya dan tausa muryarsa yace ‘Bana son wasa Khadeeja, don Allah ki tashi ki samarwa yarinyar nan abinci. Next week ai zaku raba girkin kowa ta dinga yin nata, amma for now ki tashi ki bamu breakfast.’
Ta sake gyara kwanciya ba tare da tace masa komai ba. Ya kalli kasa yana jijjiga kai don ya san ta gama magana; takaici ya kamashi. To yanzu ya za ayi tana amarya ya bata bread ruwan zafin ma ace sai ta dafa. Haka ya fice daga dakin yana wasi-wasi.
Yana ficewa ta juyo ta harari kofar kamar yana wajen ta ja dogon tsaki tace ‘Dan rainin hankali!’
………
Yana shiga ya tara da ita ta fito daga wanka tana shirywa. Tun kafin ya gama shiga dakin tace ‘Allah ya sa dai an gama abinci don wallahi yunwa nake ji kamar an min sata a ciki.’
‘Akwai dai bread, sai dai idan kin fito ki dafa ruwan zafi da kwai haka sai mu karya.’
Da mamaki ta kalleshi tana cewa ‘Ruwan zafin ma sai na dafa? Yau ne fa kwanana na farko a gidan, haba! Kitchen din ma ban san inda yake ba.’
Cikin damuwa yace ‘To ko order za a yiwo?’
‘Ni ban gane ba, wai ita matar gidan bata girki ne?’
PAGE 149
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ya karasa kusa da ita yana kokarin kama dogon gashinta da take tajewa yana cewa ‘Ki bar wannan maganar, ki zo muje na nuna miki kitchen dinki sai ki samar mana ruwan zafi mu karya. Idan kuma akwai inda zaki iya yiwo mana order a kawo nan da awa daya haka to sai na tura kudin.’
Ta jijjiga kai ‘Gaskiya babu, sai dai ko na rana don wallahi kwana bakwai din nan sai na yi su ba tare da na dora tukunya ba. Don ni abinda na sani matar gida ko ‘yar gwal ce idan aka yi amarya ita take girki kafin a zauna a raba.
Haka yayi ta bata hakuri yana lallabata, daga karshe ta shirya suka sauko parlor dinta ta dafa musu ruwan zafi sanna ya debo kwai ta soya musu.
Wajen 12pm ya hadasu a parlor dinsa yayi musu introduction; ita naja amarya sai muzurai takeyi tana wata yanga, ita kuwa khadeeja cike da walwala tayi mata maraba suka gaisa babu laifi. Ya sanar da su idan an kwana bakwai zasu raba kwana kowacce kwana biyu.
Ba karamin mamakin Khadeeja yayi ba, ko da yake wannan ba bakon abu bane a wajensa. Tayi masa rashin kunya mintuna kadan kuma ta koma kamar ba ita ba. Shi yasa a lokuta da dama yake kasa fassarata.
Ganin walwalarta ya saka ya sa rai cewa zata yi abincin rana da su, amma gudun kada akuma ya sa ya bita don ya tabbatar. Sai dai ta tabbatar masa da cewa ta figa ta dafa abincin rana tun da safe kuma nasu ne ita da yara, sauce ne kawai a fridge zata dumama ta hada musu salad su ci. Ko amsa bai bata ba ya fice ya barta a dakin, tabi bayansa da harara tana dariya.
Don haka da rana tayi sai akwai ya yiwo order din abinci aka kawo musu har gida, haka ya kirawo yaransa gaba daya suka hadu da Naja suka ci suka koshi. Ita kuma Khadeeja ko damunta abun bai yi ba, taci abincinta ta zubawa hafsa sannan ta bayar da ragowar.
A haka aka karasa wannan amarcin. Kullum Khadeeja zata dafa abincinta shi kuma zai ywo order su ci su koshi tare da amarya da yarasa. Babu wanda ya taba yiwa Khadeeja tayi ita kuma bata taba tambayarsa nata kason ba.
PAGE 150
MIJIN MARIGAYIYA
A HAUSA NOVEL BY SAKINA YAZID (INNAR SU AMAL)
Tayi zaton ranar da kwana zai dawo kanta zata ji tana cikin yanayin murna, sai dai ba hakan ya kasance ba. Yau ne zata karbi kwana amma sai taji kamar ma ba zata iya bari ya kusanceta ba saboda lkamar dai har yanzu kokari take ta saba da cewa su biyu ne matansa. Haka dai ta tashi ta gama duk wata hidima da takeyi. Ya riga ya sanar da su cewa da daddare za adinga karbar kwanan don haka tun yamma ta shirya abincin dare; duk da bata cikin walwala amma haka ta girka baincin da ta tabbatar yana so; tuwo miyar kubewa danya. Ta hada komai ta jera a table din sama. Sai dai ga mamakinta har wannan lokaci Naja tana dakinsa na sama, don haka ma bata ko je kusa da dakin ba tana jiran ya dawo taji ko shine zai biyota dakinta tunda dai kwananta ne.
Da yake bayan ya ci abincin rana ya sake fita sai wajen 8pm ya