Showing 48001 words to 51000 words out of 99112 words

Chapter 17 - Mijin Marigayiyya Part Complete Hausa Novels.docx

17 Sep 2025

76

gama wayar ina nan.’

Ta shige kitceh ta barsu.

Tana shiga ta karasa ta bude freezer ta duba sannan ta ce masa ‘Zata isa ma, amma dai idan zaka dawo sai ka siyo wata don gaba daya zan kwashe na dafa muku yanzun.’

Suka yi sallama ta katse wayar.

Sunan da ta gani a jerin chats din kan wayar shi ya ja hankalinta ta fasa fitowa daga kitchen din tana karewa sunan kallo; Anti Naja aka rubuta da alamar zuciya ta emoji. Daga haka da take kallon hoton da yake kan sunan kuma tabbas Naja ce sakatariyar Abbansu. Ba tare da tayi wani tunani ba ta danna kan sunan ya bude mata chats din, har zata yi sama sai kuma wani sako da yake cikin jerin sakunan dake kasa ya ja hankalinta. Afaf ce ta turawa Naja sakon kamar haka

“Congrats Anti, Abba ya ce min an kawo kudin auren ko?”

“Eh my girl, sun kawo harda sadaki ma. Saura kawai ya gama gyaran sabon gida mu shikenan.”

“I can’t wait to have you here with us Anti.”

“Soon my girl. Amma dai ta daina baki matsala ko?”

“Ta daina, tunda ta ga babu riba. Yanzu ba sosai ma take kulani ba dama ni haka nake so. Habib ne kawai sarkin rawar kai ya manne mata.”

PAGE 121

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

“Kada ki damu kwanan nan zan zo na gyara mata zama.”

Motsin da Khadeejan ta jiyo ne ya sa tayi sauri ta rufe sakinnin ta dire wayar a kan teburin da yake kusa da freezer din ta kama murfin freezer din ta daga kamar a lokacin ta rufe.

‘Anti ina wayar?’ Afaf ta fada bayan da ta karasa shigowa kitchen din.

‘Kin ganta nan a kan tebur, dauki.’

Ta karasa ta dauki wayarta ta fice ta koma parlor din.

Cikin sanyin jiki Khadeeja ta tsaya a ta jigina da freezer din ta kafa tagumi. Kusan wata takwas da suka wuce Mustapha ya kalli tsabar idon Baffa da Mommy yace musu ba auren Naja zai yi ba, amma gashi daga wadannan chats din da ta karanta yanzu har an kai kudin aure da sadaki. Wato ma Afaf ta san komai itace kawai bata san mijinta zai kara aure ba kenan; kuma kamar dai bashi ma da niyyar gaya mata. To me ta yiwa Mustapha ne? me yake tunanin zata yi a akna kara aurensa da yake boye mata? Ita dama da ya kai ta gidan da ya siya yanda taga gidan ta san sai ya kara aure, kawai dai bata zata Naja zai auro ba don kwata-kwata bata sake ganin wata alama da take nuna yana tare da Naja ba tun bayan da suka je wajen Baffa. Wato dama da take zargin Yaya Jidda ce take hure mata kunnen yara ashe Naja ce, tunda gashi nan ta gani har tana gayawa Afaf cewa zata shigo ta gyara mata zama. Ta jijjiga kai, ta goge gumin da ya fara tsattsafowa daga goshinta sannan ta tuna ce mata fa yayi nan da awa daya zasu zo.

Jikinta a sanyaye ta koma cikin gidan ta kirawo Rashida sannan suka fito suka kama aiki. Haka ta hadiye duk wani bacin rai tayi ta haba-haba da abokinsa, sai bayan sallar isha’i sannan yayi musu sallama ya tafi.

Ta san cewa ya kula da yanayinta yanda ya sauya, amma bai yi mata magana ba. Duk da dai ko da yayi mata maganar ma zata gaya masa gajiya ce kawai. Haka dai suka kwana shi yana baccinsa ita kuma Khadeeja duk lokacin da tayi juyi sai ta kalleshi tana tambayar kanta wai me tayi masa ne yake mata abubuwa kamar wata wadda aka aura ba don soyayya ba?

Haka ta hakura tayi ta danne zuciyarta har gari ya waye

PAGE 122

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Sai karfe biyu na rana take da lecture amma haka ta shirya da wuri lokacin da Mustapha ya shirya zai tafi office tace ya wuce da ita ya kaita gidan Mommy, in ya so daga can sai ta wuce makarantar ta kuma dawo gida. Haka kuwa aka yi.

Tunda ta shiga gidan Mommy ta karanta damuwa a fuskarta, ta dai kyaleta har Baffa da Nabila suka gama shirinsu suka fice. A nan parlor din inda suka barsu Mommy ta zuba mata ido na dan lokaci, har ta ji a jikinta Mommy din kallonta take. Tana juyowa kuwa suka hada ido; ta danyi dariya tace ‘Mommyy.’

Itama tayi dariyar tace ‘Ya aka yi ne? kamar dai kina da damuwa. Ko kuma ba kya jin dadi ne?’

Ta jijjiga kai tace ‘Mommy Mustapha aure zai yi.’

Ta dan zaro ido ‘Aure? Ikon Allah.’ Sai kuma ta saki fuskarta ta cigaba ‘Ko da yake wannan ba abin mamaki bane ai don haka kada ma ki sakawa kanki damuwa.’

Ta sunkuyar da kai cikin damuwa tace ‘Mommy nima ba damuwa nayi ba, kawai dai yayanyin abun ne.’

‘Ban gane ba.’

Nan ta sanar da ita wadda zai aura sannan ta sanar da ita a inda taga labarin auren da kuma irin sakonnin da Afaf take turawa Najan da kuma yanda take fama da Afaf din a ‘yan kwanakin nan.

Duk da Mommy bata yi mamaki ba amma dai ta ji babu dadi, musamman yanda Afaf ta zama ‘yar rahoton Naja. Tace ‘Ikon Allah, to shi me yasa yake boye miki auren?’

Tace ‘Wallahi ban sani ba, ko da wasa bai taba gaya min ba kuma danginsa ma babu wanda ya gaya min. Amma kin ga yaran har sun sani, tunda gashi har ana gaya musu za a zo a gyara min zama.’

‘Lallai mutum sai a barshi.’

‘Dama na gaya miki Mommy tunda naga gidan da ya saya nace miki gidan nan ba na mace daya bane, kin ga maganata ta tabbata.’

Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan Mommy tace ‘To da ce mata aka yi baki zauna daidai ba da take cewa zata gyara miki zama ko me? Amma kafin ta gyara miki zama ke ce zaki bi dare ki gyara zama ta hanyar addu’a, idan gari ya waye kuma ki dora da sadaka.’

PAGE 123

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta sunkuyar da kai tana koakrin boye kwallar da ta gangaro a kwarmin idonta; wannan kalmar ta za a gyara mata zama ta tsaya mata a rai. Domin dai kalma ce da zata iya daukan kowacce ma’ana. Amma kamar yanda Mommy ta fada hakan zata yi tunda ta san bata da gatan da ya wuce Allah.

Haka suka cigaba da hira Mommy tana ta bata baki kuma tana yi mata alkawarin daga nan ma zata dinga yi mata addu’a kuma da sadaka, ta tabbatar mata ba za tayi nasara a kanta ba.

Da wuri Mommy ta sauke abinci saboda Khadija taci kafin ta tafi makaranta, tana daga kitchen din ta kwalawa Khadeejan kira. Tana shiga kitchen din ta fara gatsina fuska tana cewa ‘Mommy wannan wane irin kifi ne kika dafa me azabar karni? Allah ya sa dai ba da shi kika yi abincin ba.’

Mommy ta kare mata kallo na dan lokaci sannan tace ‘Wane kifi da aka dafa tun jiya da daddare aka cinye, ni shinkafa da wake ma na dafa.’

Nana da nan fara’arta ta karu, ta dauki plate ta matsa tana mikawa Mommy tana cewa ‘Yauwa Mommy zuba min na fice don wallahi kitchen din nan karni yake.’

Ta karbi plate din tana cewa ‘Cikine da ke ko?’

Ta kalli Mommy da baki a bude, suka dan zubawa juna ido sannan ta rufe bakin tace ‘Anya kuwa Mommy, tunda dai ni ban ji wani sauyi na azo a gani ba.’

Ta zuba mata abincin ta mika mata tana cewa ‘To ki dai bincika tukunna kafin kiyi saurin cewa a’a, don tunda kika shigo nake kula da ke gaba daya ma na dauka abinda ya kawo ki kenan.’

‘To ban sani ba gaskiya Mommy, amma zan duba yau din nan kuwa.’

Bayan ta gama cin abincin tayi sallah sanna ta fice ta kama hanyar makaranta. Sai da ta tsaya a chemist ta sayi abun pregnacy test sannan ta wuce. Ta riga ta san su Rahma suna jiranta a hostel don haka kai tsaye can ta wuce, tana ajiye jakarta a dakin ta fice ta fada toilet. Tana tsoma abin nan a fitsarinta ya nuna radau positive; wato tana dauke da ciki. Tayi murmushi tana ji kamar ta daka tsalle saboda murna, nan da nan idonta suka ciko da kwalla saboda jin dadi. A take kuma jikinta yayi sanyi da ta tuna cewa Mustapha ne yayi mata ciki kuma shine yake shirin auro matar da ta ke ikirarin zata shigo ta gyara mata zama.

PAGE 124

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta sunkuyar da kai ta saki takardar a kasa sannan ta fito daga bandakin cike da damuwa.

Yanayin da ta shiga dakin ya tabbatar musu da akwai matsala, don haka tun kafin ta Zauna farida ta mike ta tareta tana cewa ‘Ya na ganki haka, lafiya dai ko?’

Ta zauna a kan gado Rahma kamar wadda aka jefa, ta kalli farida suka hada ido sannan ta saki murmushe wanda yake hade da takaici tace ‘I am pregnant Farida.’

Nan da nan su Rahma da Amina da ke zaune suka dako tsalle suka fada jikinta sun ihu. Sai da suka fahimci ita bata taya su ihun kamar yanda suka saba sannan suka tsaya suna kallonta.

‘Girl, wannan ai abun murna ne na ga kamar ke baki ni dadi ba.’ Amina ta fada tana rike da hannun Khadeejan.

Ta sunkuyar da kai ta zare hannunta ta goge kwallar da ta fado daga idanunta. Ta basu labarin auren Mustapha da kuma abinda ta gani da ma yanda yake boye mata.

Tace ‘Ban ma san wanne zan yi ba; murna ko bakin ciki? Ni da za a zo a gyarawa zama ina zan mike kafa na fara haihuwa; haihuwar da ni ban ma tabbatar zai yi murna da ita ba. A yanzu ma gaba daya kai na ya kulle. Mommy dai tace kada na kuskura nayi masa maganar kara aurensa, na barshi har sai ya zo da kansa ya ya gaya min, a lokacin sai ayi duk wadda za ayi. Amma wallahi ban sani ba ko zan iya jurewa. Gaba daya ma yanzu ban san matsayina a wajen Mustapha ba, kuma ga ciki.’

Suka yi shiru na dan lokaci.

Amina ce ta katse shirun nasu tana cewa ‘Gaskiya mutumin nan dan wulakanci ne, haba!’

Rahma tace ‘Amma gaskiya ina bayan Mommy, ki barshi kawai kada kiyi masa magana in ya so idan ya zo zai gaya miki da kansa sai ki yi masa wankin bargo tunda dai babu abinda zai sa ya fasa wannan auren da yayi niyya.’

Tace ‘Hakane.’

Nan suka daui lokaci suna bata baki, sannan daga baya Farida da Rahma suka fice suka tafi lecture din suka barsu a dakin itada Amina wadda ta tsaya ta tayata zama don tace ba zata iya zuwa lecture din ba.

PAGE 125

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Duk yanda take cikin damuwa da yanda take so ta yiwa Mustapha tijara game da yanda ya boye mata maganar aurensa da Naja haka ta hakura ta danne zuciyarta. Domin ita kanta ta kasa ganin maslahar yi masa maganar; tunda dai itace baya so ta sani gara ta rabu da shi ta gani ko za a dauro auren ne a kai amarya sama jannati saboda kada ta sani. Cikin da take dauke da shi ma kasa gaya masa tayi, domin bata ga alamar yana farin cikin kasancewarta matarsa ba. Gaba daya ma cikin ya zo mata a wani lokaci ne da take jin cewa da bata same shi ba zata iya hakura da haihuwa a gidan Mustapha har sai ta fahimci inda auren nasu ya sa gaba. Ko da yake dai ta san ana cewa idan namiji zai kara aure matarsa da take gidan sai ta yi matukar hakuri; to tabbasa ta ji a jikinta cewa lokacin nata hakurin ne ya kama yanzun.

Da kansa ya kula da yanda take mu’amalarta kwana biyu cikin kasala gashi bata ma son magana, don haka ya tasata a gaba ya kaita asibiti. A nan aka tabbatar masa da cewa tana dauke da ciki sati shida.

Suna zaune a mota yana tukosu a hanyarsu ta dawowa ya dubeta yace ‘Kin gani ko, kin sami cikin a kwanciyar hankali ba tare da kinje nemansa a asibiti ba ko? Allah ya sa dai ba mai wahaka bane?’

Ta dan yi gajeran murmushi tace ‘Smin ya Allah.’

Suka yi shiru na dan lokaci, ya dubeta yace ‘Wai ya naga duk kin yi wani shiru ne? kamar ba abin nema ne ya samu ba?’

Ta kawar da kai tana murmushin yake tace ‘Bana jin dadi ne, bacci ma nake ji.’

Ta kwantar da kanta a jikin kujerar motar ta rufe ido, don haka shima ya kyaleta ya mayar da hankali a wajen tukinsa.

……

A haka Khadeeja ta dage ta cigaba da mu’amalarta tana yin duk wata hidima da ta saba. Ko a wanne yanayi ta tashi haka take daurewa tayi duk wata hidimarta don bata shirya drama da Mustapha ba. Ta riga ta san idan dai tana numfashi a gidan nan to duk wata hidima da matar gida take yi ba yafe mata zai yi ba; don haka ta daure ta cigaba da dagewa tana yi. Musamman da yake duk wani aiki da ta saba yi a gidan ta riga ta koyawa Rashida kuma ta iya sosai, gashi yarinyar bata da kyashi ko daya, don haka abubuwa suka zo mata da sauki sosai.

PAGE 126

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Sai dai fargabarta daya iyayen Rashida suna maganar ko da wane lokaci za a iya zuwa a dauki Rashida saboda aurenta ya kusa; duk da dai an ce za a kawo mata kanwarta to amma ta san akwai aiki.

Haka ta cigaba da rayuwarta tana goyon cikinta.

A hankali ta fahimci lokutan da yake zuwa zance wajen naja, kuma da yake shi yake kaita makaranta da ta shiga motar take gane Naja ta fita a motar ko kuma sun fita tare.

……..

Daidai lokacin da zasu fara jarrabawar karshe a lokacin cikinta ya shiga wata na takwas; ga hidimar gida, ga karatu kuma gashi tana kokarin hada project dinta. A dai-dai lokacin ne kuma Mustapha ya gama gyara gidansa wanda yake fatan da zarar sun koma za ayi bikinsa da Naja. Sau biyu yana kaisu gidan ita da yara, kuma duka zuwa biyun sai ta tambayeshi ko aure zai yi ne yake yin gidan kamar d zubin mata biyu. Amma duk lokacin da ta tambaya sai yace mata ko da zai yi auren to ba yanzu ba; ta rasa gane dalilin da yasa yake son boye mata aurensa da Naja. Don haka ma ta daina tambayarsa gaba daya.

Ranar asabar ce kuma tun dare ya sanar da ita da safe yara su shirya zai fita dasu, don haka tun wajen tara na safe ta bayan da suka ci abinci ta sallamesu ta koma ta kwanta. Ya dai ce mata gidan Hajia zasu je kuma suma yaran haka suka gaya mata; amma a ‘yan kwanakin nan yana yawan fita da yaran ranar da babu aiki yace wajen Hajia zai kaisu. Ta riga ta gane wajen Naja yake kaisu, sai dai bata ga dalilin da zai sa tayi masa magana ba tunda ‘yayansa ne sannan kuma gaya musu da yake suce mata gidan Hajia suka je su yake cutarwa ta hanyar koya musu karya.

Gaba dayansu suka fice banda Habib, wanda dama ya riga ya saba duk lokacin da za suyi wannan fitar shi baya binsu. A gida yake zama tare da Khadeejan da Rashida.

Sai wajen karfe biyar na yamma sannan suka dawo, lokacin ta riga ta gamamabincin dare ta zuba a flask tana kwance a daki. A dakinta yaran suka sameta tana kwance tana hutawa, suka sanar da ita sun dawo. Shukra kuwa sai ta wuce ta haye gadon ta kwanta kusa da ita tana cewa ‘Bacci kike yi Anti?’

PAGE 127

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta dan matsa jikinta tana gyara kwanciya, Khadeejan ta dan gyara kwanciyarta tana kawar da Shukran daga cikinta. Tayi dariya tana cewa ‘Na matsa ko Anti, kada na lotsewa kanina hanci.’

Tayi dariya saboda itace ta saba gaya mata hakan a duk lokacin da take son kwanciya a jikinta tunda cikin ya fara girma; domin Shukra yarinya ce mai son jikin tsiya kuma ta samu Khadeejna bata tureta. Tace ‘Yauwa, ashe dai kin gane. Kada a dinga ce miki yayar mai lotsttsen hanci.’

Suka yi dariya gaba daya; Shukra ta ci gaba da wasa da hannun Khadeejan guda daya yayinda Khadeejan take rike da daya waya a daya hannun tana chatting. Jimawa kadan cike da damuwa tace ‘Anti.’

‘Umm.’ Ta amsa ba tare da ta bar abinda take yi ba.

Tace ‘Gaskiya ni ba zan koma wajen Anti Naja ba, a wajenki zan zauna ko?’

Ta ajiye wayar tace ‘To wa yace zaki koma wajen Anti Naja kuma? Ai muna nan tare, ko ba gamu ba a gidanmu.’

Cike da damuwa tace ‘Ai itama tace aurota Abbanmu zai yi ta dawo gidanmu. Amma sai mun koma sabon gida. Shine yau da muka je wajenta take cewa Yaya Afaf idan ta tare duk wajenta zamu koma. Gaskiya ni dai ba zan koma ba ko?’

Ta dan yi shiru tunani yana nema ya birkita kwakwalwarta; duk da bai gaya mata ba ta san yana kai yaransa wajen Naja, amma maganganun da Najan take gayawa yaran basa kama da maganganun da ya dace a gaya musu a daidai wannan lokacin. Sai dai ta san babu yanda zata yi tunda shi ya bata dama.

‘Anti.’ Muryar Shukra ta katseta tana kiran sunanta.

Bayan ta amsa Shukran ta cigaba cikin damuwa ‘Tace saura wata biyu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login