Showing 66001 words to 69000 words out of 99112 words

Chapter 23 - Mijin Marigayiyya Part Complete Hausa Novels.docx

17 Sep 2025

90

saka Mustapha a gaba sai da ya bari ta dauki mai aiki wadda take zuwa kullum tana tafiya da yamma; tunda ya ce ba zata rabawa su Afaf wanke-wanke da gyaran gidan su dinga yi idan sun dawo daga makaranta ba.

Babu yanda bata yi da shi ya mayarwa da Khadeeja kwananta ba amma ya ki; saboda ki-fadi. Duk da shi dinma yanzu zai so ace sun fara kwana bibbiyun tunda yanzu yana son shiga harkar Khadeejan; amma dai ya san Khadeeja ba zata karbi kwanakin nan da ta bayar ba tare da son ranta ba sai ta saka masa ciwon kai.

PAGE 166

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ita kuma ta so ta yiwa Khadeejan magana amma ba zata yi ba, saboda kusan tunda ta zo gidan ba wata magana da take hadasu da Khadeejan bayan gaisuwa; da yake ma Khadeejan ba mai son fitowa bace sai ya zama idan dai ba aiki zata je ba to zasu iya kwana biyu ma basu hadu ba.

Haka suka cigaba da rayuwarsu.

………

Ranar Juma’a ce ta kama ranar da Khadeeja ta cika arba’in. Duk wani shiri ta gama yinsa, ta gama gyaran jikinta kamar yanda duk wata maijego take yi. Sai dai bata sa rai zai bata kwanan ba kuma ta ci alwashin ba zata taba kai masa kanta ba sai dai shi ya kawo kansa.

Bayan ta idar da sallar asuba sai ta sake bin gado ta kwanta tunda ta san Hammad ba zai taba wuce karfe takwas yana bacci ba zai tasheta. Bata san iya tsawon lokacin da ta dauka tana bacci ba bugun kofar da ake mata ne ya tasheta, a tare suka farka da Hammad wanda ya sa kuka. Ta lalubo wayarta ta duba lokaci inda taga 8:30am; nan da nan ta mutssike ido don ya kamata ace kafin karfe tara ta fita ta tafi gidan rediyo. Sai da ta dauki Hammad sannan ta mike ta bude kofar. Hafsa ta gani a tsaye; bayan ta gaisheta tace ‘Anti na gama aikin gaba daya na ga baki fito ba kuma jiya kin ce min na shiya da wuri zamu fita.’

‘Hmm! Bacci ne ya kwashe ni. Zauna ki jirani na shirya Hammad na miko miki shi nima na shirya mu tafi.’

Nan da nan ta shirya Hammad ta mikashi wajen Hafsa suka zauna a parlor sannan ta koma dakin ta shiga wanka.

A gurguje tayi wankan ta fito daure da karamin farin tawul dinta, tana rike da wani tawul din tana goge jiki. Mustapha ta hango yana zaune a gefen gadonta ya mike kafa yana kallo a waya. Ba karamin mamaki tayi ba domin gaba daya ta kasa tuna me yake jira. Ba wai baya shiga dakin bane amma dai tunda Naja ta tare bai zauna a dakin ba sai dai ya shiga ya gaya mata abinda zai gaya mata yana daga tsaye ya fice. Ta dan tsaya kadan ta kalleshi sannan tace ‘Ina kwana.’

PAGE 167

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ya ajiye wayar ya amsa gaisuwar tata da fara’a. Ta karasa gaban mudubi tana goge jiki yayinda shi kuma Mustaphan ya mike tsaye ya nufota. Ya karasa ya tsaya a bayanta ya rungumota ta baya, ta kalleshi ta cikin mudubin suka hada ido tace ‘Fita fa zan yi ka ga ma na makara.’

Yayi murmushi ya saka bakinsa a kan kunnenta yace ‘Nima fita zan yi, amma diai kin san yau kinyi arba’in yau ko.’

Ta dan motsa saboda yanda yake kara shigewa jikinta tace ‘Um.’

‘Ok, ki karbi kwananki yau sai ki ajiye min dinner.’

Murya kasa-kasa tace ‘Toh.’

Ya sumbaci gefen wuyanta sannan ya saketa ya juya. Har ya kusa zuwa bakin kofa kuma sai ya juya ya dawo, kafin ya karasa inda take itama ta juyo don haka ya tsaya a gabanta. Cike da damuwa ya kirawo sunata, bayan ta amsa yace ‘Bana jin dadin yanda kuke zama da Naja kamar kuna gaba, please ki dinga dan zama a parlor din kasa saboda ku saba.’

Ta dan yi murmushi tace ‘Ba wata gaba da muke yi tunda muna gaisawa, kuma duk abinda ya kama na magana ai muna yi.’

Ya kalleta suka hada ido sannan ya rike kwayar idonta yana cewa ‘Duk da haka dai ki dinga dan zama a can kuna hira. Kinga idan kina nan ba zata shigo ba itama sai tayi ta zama a parlor dinta inda ke ba kya shiga.’

Bata son ta ja zancen saboda bata son ta makara, don haka tace ‘To shikenan.’

Ya sake tsattsareta da ido sannan yace ‘Please!’

Tayi gajeren murmushi ta daga kai.

Ya fice bayan tayi masa a dawo lafiya.

Ta ja tsaki bayan da ya fice; bata jin zata iya rabar Naja, ta tsaneta. Watakila hakan yana da alaka da yanda Mustaphan ya bata mata rai a kan Najan tun kafin aurensu da kuma maganganun da ta gani a wayar Afaf da suna chatting da Naja. Gaskiya ba zata iya hira da wata Naja ba, gahi kuma bata iya munafurci ba balle taje ta yi na karya. Shi dai da yaga Naja yana so ya aurota suje can su karata.

Cikin sauri ta karasa shiryawa suka fice ita da yaranta.

PAGE 168

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Tun kafin Magriba ta gama abincin dare, don haka Habib yana shigowa daga masallaci sallar magriba ta turashi ya kirawo kannensa a wajen Naja. Nan suka zauna a parlor dinta suka ci abinci inda ta dafa macaroni da miyar hanta da salad. Suna gama cin abinci Afaf wadda dama bayan sallama bata ce mata komai ba ta tashi ta fice daga parlor din. Sauran yaran kuma suka zauna a nan aka cigaba da hira ana kallon TV. Wajen 8:30pm duk suka fara jin bacci don haka da kanta ta tashi ta rakasu dakinsu, ta shirya shukra sannan ta tsaya Nasreen ma ta shirya suka yi brush suka kwanta sanna ta koma nata dakin. Shima Habib yayi mata sai da safe sannan ya wuce nashi dakin.

Har zuwa lokacin Mustapha bai dawo ba, sai dai yayi mata waya ya sanar da ita sun fita da Alhaji don haka sai ta ganshi.

Don haka bayan tayi wanka tayi shirinta na bacci sai ta koma ta jera masa abincinsa a table din parlor dinta sannan ta wuce dakinta ta kwanta.

……….

Sai wajen 9:30pm sannan ya shiga gidan. Kai tsaye bayan ya kulle gidan parlor din Naja ya shige tunda itace a kasa.

Tana zaune a kan kujera tana shan cornflakes ranta a bace. Ya karasa bayan ta amsa sallamarsa ya sumbaci kumatunta sanna ya zauna a kusa da ita yana cewa ‘Cornflakes kike sha a daren nan?’

‘Um. To me gidan ce da girki kuma bata bani nawa abincin ba shine na hada cornfakes nake sha tunda ban saba zama da yunwa ba.’ Ta fada tana kara shan kunu.

Ya dan shiga duhu, yace ‘Umm, Khadeeja bata yi abinci bane?’

‘Ta yi, amma nan ta turo aka kirawo yara suka je samanta suka ci abinci. Da suka gama cin abincin ma a can suka yi zamansu Afaf ce kawai ta sauko ta tayani hira.’

‘Um! To ai na zata kowaccenku dama girkinta zata dinga yi ko?’

Ta harareshu sanna tace ‘A ina ake haka? Tunda wadda take da girki itace zata dinga kula da yara ai gikin ma gaba daya zata dinga yi. Shi yasa nima idan nayi abinci nake fitowa dashi nan parlor din inda kowa zai iya diba, itace bata fitowa ta diba saboda bata son ganina.’

PAGE 169

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

‘Wa ya gaya miki? Ba haka bane. Bari zan yi mata magana in ya so sai ta dinga yi da ke, kema ranar naki girkin sai ki dinga yi da ita kun ma ragewa kanku aiki.’

Ta zumbura baki ‘Ah to don ni dai haka na san duk masu mace sama da daya suna yi.’

Yayi mata sallama ya wuce sama. Bata taba sanin idan Khadeeja ta karbi kwana abun zai sosa mata rai ba sai a wannan lokacin. Gaba daya zucuyarta tayi kunci, haka tabi bayansa da kallo har ya fice daga parlor din ya rufe mata kofa. Nan take hawaye ya wanke mata fuska; ta ajiye kofin da yake hannunta akan tebur ta hada kai da gwiwa ta sa kukan da ta kasa gane me ya kawo shi. Haushin Khadeeja ta karbi kwana ko kuwa haushin an barta da yunwa?

………..

Yana karasa shiga parlor dinsa ya kalli dining table, bai ga alamar abinci ba. Kamar ma ko taba wajen ba ayi ba tunda ya fita da safe. To me Khadeeja take nufi? Duk wannan dokin da yake na zuwa wajenta ita ashe bata gama fushin ba kuma bata gaya masa ba?

Cikin sanyin jiki ya karasa ya shiga dakinsa. Ga mamakinsa dakin ma ba a gyara ba. Yanda Naja ta fita ta barshi da safe yana nan a haka, babu ma alamar da take nuna mutum ya shiga dakin bayan fitarsa. Khadeejan ma da yake sa ran zai gani a dakin bata ciki. To ina take? Me take nufi bayan ya sanar da ita yau itace da kwana? Gaba daya ranshi ya gama baci; baya son fitnar Khadeeja don ita rigima da ita ba ta karewa, musamman a yanzu da yake da bukatarta.

Har ya juya zai fita kuma ya fasa, ya tsaya ya canza kaya ya shirya sannan ya dauki wayarsa ya fito ya nufi dakin khadeejan.

PAGE 170

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Yana shiga parlor dinta ya kai hankalinsa kan dining table, yanda ya ga wajen a jere da kwanuka ya tabbatar abincin ne ta dafa ta ajiye masa. To me yasa tayi hakan? Ya karasa kan tanle din ya bude kwanukan ya ga abinda ta dafa, sannan ya taba flask din ruwan zafi ya jishi a cike; tabbas ya san shayi ta dafa masa. Ya gyada kai ya juya ya nufi dakinta.

Duk da ita ba mace ce mai son mu’amala ta turaren wuta da humra ba amma dai tana son kamshi, tana da hadaddun turarkanta na jiki da nakaya wadanda idan dai ta zauna a waje sai ka ji kamshinsu. Yana tura kofar dakin nata kamshin turarenta yayiwa hancinsa maraba. Fitilar dakin a kashtake sai dai dim-light wadda take ajiye a kan durowar gefen gado itace a kunne; ga alama bacci ne ya kwasheta ba tare da ta kashe fitilar ba. Ya karasa kan gadon inda take kwance, ya leka fuskarta; bacci takeyi hankalinta a kwance gashi yanayin baccin ya yiwa fuskarta kyau. Kamar ya kyaleta sai kuma ya canza tunani, ya zauna a hankali a gefen gadon daidai inda kafafunta suke, ya daga abinda ta rufa dashi ya sosa mata tafin kafa a hankali. Ta janye kafarta da sauri sannan ta bude ido a hankali hankalinta gaba daya yana kan Hammad wanda yake kwance a cikin gadonsa na baby a gefen gadon nata.

Yayi dariya a daidai lokacin da ta ganshi, ya lakace mata hanci yana cewa ‘Yanzu mutum daya ne a rayuwarki wato Hammad ko? Ke na taba amma ba abinda ya tabaki kike nema ba yaronki kike nema kada a taba miki shi.’

Ta yi murmushi ta mutssike idonta tana gyara zama sannan tace ‘To ina laifi, nice gatansa kaga kuwa dole na kula da amanar Allah.’

‘Hakane. To a taso a bani abincina yunwa nake ji sosai.’

Ta zubo kafafunta daga kan gadon ta mike tana cewa ‘Bari na wanko baki.’

Ta wuce ta gabanshi ta nufi bandaki.

Ya bi bayanta da kallo yana yaba yanda jego ya karbeta. Ya dade bai ganta a haka sanye da rigar bacci kamar wanna ta jikinta ba sai yau kuma tayi matukar burgeshi. Yana nan zaune yana lissafi ta fito daga bandakin suka fito parlor din.

PAGE 171

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Sai daya zauna a table din sannan ta zuba masa abincin ta ajiye a gabansa, ta koma ta hada masa shayi kamar yanda yake so shima ta ajiye masa ta koma ta zauna a kujerar kusa da shi.

Tun kafin ta zauna ya fara cin abincin saboda da gaske yunwar yake ji; bayan ya cinye lomar bakinsa ya dubeta yace ‘Ke kin ci abincin ne?’

Tace ‘Um, mun ci ni da yara mun koshi tun dazu.’

Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan yana cin abincinsa yace ‘Wai me yasa baki saka abincin a parlor na ba kika kawoshi nan?’

Ba tare da wata damuwa ba tace ‘Ba komai, kawai dai nan din ya fi min kusa da kitchen saboda saukin aiki ko?’

‘Um hakane. Ki dinga sakawa a parlor din kawai kin ji can din zai fi yanda duk wanda yake son yaci zai iya diba.’

‘Ok, next time in sha Allah.’

Suka sake yin shiru na dan lokaci, jimawa kadan ya ajiye cokalinsa ya fara shan shayin. Bayan ya kurba ya ajiye kofin sannan yace ‘Kuma na ga baki gyara mana dakin ba, yanzu zaki gyara kenan ko a haka kike so mu kwana?’

Ta kalleshi da mamaki tana dan zare ido ‘Duk gyaran da nayi kuwa? Ko dai baka kalli dakin ba? Koda yake baka kunna fitila shi yasa ba zaka ga dakin sosai ba amma na gyara sosai fa.’

Ya kula da tana maganar hankalinta yana kan kofar dakinta kamar dai ta zata dakinta yake nufi bata gyara ba, yace ‘Ba fa dakinki nake nufi ba, dakina nake nufi tunda ai a nan zamu kwana.’

‘Oh,..’ sai kuma ta dan sunkuyar da kai kamar dai ta kasa fadin abinda take son fada ne. ya kurbi shayi ya bita da kallo yana jira ta karasa fadin abinda ta fara fada.

‘Gaskiya mu kwana a dakina, in ya so duk ranar kwana kai sai ka dinga zuwa dakina muna kwana.’

Da mamaki yake kallonta yana dariyar yake ‘Khadeeja a ina kika taba jin miji ya bi matarsa dakinta kawai saboda su biyu ne? shike nan yanzu duk wacce take da kwana nine zan je dakinta kenan?’

Ta dan bata rai ‘Nifa ba haka nace ba, ita idan tana so ta dinga zuwa dakinka bani da matsala da hakan amma ni dai sai ka dinga zuwa dakina.’

PAGE 172

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Dariya ma maganar tata taso ta bashi; tunda yake bai taba jin inda maigida yake bin dakin matansa ba sai dai a inda bashi da dakin saboda kankantar gidan ko kuma agidan haya. Amma ya za ayi yana da gida kamar wannan ga dakinsa da parlor dinsa amma ace shine zai dinga bin mace dakinta? Allah ma dai yasa Khadeeja wasa kawai takeyi.

‘Tunda kike don Allah kin taba jin inda aka ce maigida kamar wannan yana bin matansa daki saboda kwana madadin su suje dakinsa?’ Ya tambayeta yana nuna gidan, sannan ya cigaba ‘Kuma ma a wanne karatun aka biya miki haka bayan ga yanda kika taso kika ga ana yi?’

Ta kalleshi ta marairaice da fuska tana cewa ‘Don Allah ka bari mana, na ga dakin nawa ma duk gidanka ne ai meye don ka kwana a ciki. Itama Najan idan tana bukatar hakan ba sai kaje dakinta ka kwana ba?’

‘Oh, nine ma zan dinga binku ina kai muku kwanan kenan?’

‘To meye a ciki, abu ne fa wanda ya zo a tarihi ma.’

Ya dan zaro ido yana kallonta ‘Wanne tarihin Khadeeja? In ce ko dai tarihin tsumburbura ne?’

Ta kula dai so yake ya raina mata hankali, kuma idan bata yi da gaske ba so yake ta dinga zuwa dakinsa kwana. ita kuma gaskiya bata jin zata iya kwanciya gadon da ya kwanta da wata matar ko da kuwa ba Naja din bace. Gara kawai ya dinga zuwa dakinta. Ta kara bata fuska tace ‘To a islamiyya dai tunda ake buya mana sirah sai dai ace Annabi SAW ya je dakin Aisha, ko yaje dakin Hafsa da sauransu, duk bayanan da aka yi mana sun nuna shi yake zuwa dakin kowacce. Kuma tunda dai auren nan shi ake kwaikwayo SAW ai ba zai zama matsala ba idan an kwaikwayi wannan din ma.’

Bude baki yayi kawai yana kallonta; ya rasa yanda aka yi Khadeeja take lale shi haka har take samun damar gaya masa duk maganar da ta ga dama. Ya jijjiga kai yace ‘To idan nace ba zan zo ba fa sai dai ke ki zo dakin nawa?’

Tayi murmushinta wanda yake kara bashi mamaki; kana cikin magana da ita fuska murtuke sai kuma ta koma murmushi har kaga kamar da zuciyarta take murmushin, haka ma kuma idan tana walwala lokaci guda zata sha kunu ka zata kamar bata taba murmushi ba.

PAGE 173

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Muryarta ce ta katse masa tunanin tana cewa ‘Na san ma ba zaka ce hakan ba, kai da gidanka. Abinda ko a parlor ka kwana babu wanda zai nuna maka yatsa balle don ka kwana a dakin matarka?’

Binta kawai yake da kallo yana jijjiga kai, yace ‘Toh tsarani Khadeeja.’

Tayi dariya tana mikewa tsaye tana cewa ‘To ina laifi, yaushe rabon da a tsaraka.’

Kasa magana yayi kawai ya dinga binta da kallo har ta gama kwashe kwanukan. Bukatar ta yakeyi saboda shi kansa ya san yayi kewarta, don haka ma baya son yaja rigima a wannan daren da yake son ya huce gajiyarsa. Gashi sai kaiwa da kawowa takeyi tana kwashe kwanuka tana juya jikinta kamar da gayya, ya ma rasa me zai ce mata.

Bayan ta gama kwashe kwanukan ta dafa kafadarsa tace ‘Sai ka shigo.’

Bata ko saurari amsarshi ba wuce dakinta ta barshi a nan.

Sai yau ya tabbatar Khadeeja ta raina shi; tunda yake bai taba ganin matar da idan tayi niyyar abu sai tayi shi ba ko da tsiya ko da tsiya-tsiya sai Khadeeja. Anya kuwa ba wani abu Khadeeja tayi masa ba; idan taga dama ta gwada masa taurin kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login