Showing 78001 words to 81000 words out of 99112 words
guda biyu. Haka ta hakura ta mike ta dauro alwala sannan ta fito daga bandakin ta tayar da sallar asuba.
Bayan ta idar da sallar ta zauna a kan daddumar ta yi shiru; ta daga hannu zata yi addu’a amma ta rasa ta inda zata soma. Gaba daya ma bata san me take ji ba. ‘Alhamdulillah.’ Ta fada a fili kamar me yin rada.
PAGE 197
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Haka ta karasa azkar dinta sannan ta mike ta shiga hidimarta.
Dole ta hakura ta daina shan kwayar family planning din da take sha saboda kada taje ta cutar da abinda yake cikinta.
Sai bayan kwana biyu ta dan sami natsuwa sannan taje asibiti aka sake yi mata gwajin, aka tabbatar mata tana dauke da ciki na sati shida. Bayan ta dawo daga asibitin sannan ta sanar da Mustaphan.
Wannan gwajin da ta yi kuma sai ya zama kamar ta kunno laulayin gaba daya. Babu inda yake mata ciwo amma tana fama da kasala sosai sannan kuma ga rashin son cin abinci. Haka dai ta cigaba da lallabawa.
…………
Ranar kwananta ne don haka Mustapha a dakinta zai kwana. Yaran duk sun kwanta a dakinsu yayinda Hammad da Shukra suke kwance a dakin bakinta wajen Hafsa.
Yana zaune a gaban mudubinta yana aiki a computer dinsa yayinda ita kuma take kwance a kan gado tana game a waya. Ya bar aikin ya juyo yana kallonta ya kirawo sunanta, ta bar gane din ta mayar da hankalinta kanshi sannan ta amsa.
Yace ‘Umm! Ina so dama na sanar dake bana zamu je aikin Hajji da Naja. Da dake zamu je amma kin ga ke laulayi ya saka ki a gaba don haka na cire sunanki na saka nata sunan.’
Ta dan yi shiru saboda yanda maganar ta zo mata a ba-zata; idan dai ba wai bata ga dai-dai ba ma kamar dai ganin da ta yiwa Najan shekaran jiya ta ga kamar itama tana dauke da yaron ciki; ko da bai fito ba dai amma ita Khadeejan taga wasu alamu. Domin a lokacin har ta ji kunya tana fatan Allah ya sa ba ganewa Najan tayi ita tana dauke da ciki ba taje itama tayi. Kallon da ya kafeta da shi ya sa ta yi firgigit ta dawo hayyacinta tana cewa ‘Ma sha Allahu, Allah ya nuna mana. Amma ai ana zuwa da masu ciki kuma zan iya; in dai an yi niyyar kaini to a bani kujerata zan je.’
Yayi dariya ‘Haba aikin hajin fa ba wasa bane kuma ba akwabce ake yi ba, ko so kike muje wahala ta sa ki sami miscarriage? Kuma ya za ayi na daukeku mu tafi saudiyya gaba dayanmu? Mu bar yaran a wajen wa? Kin san Hajia yanzu ba lafiya ce da ita ba.’
‘Hakane, to ai sai Najan ta zauna ni naje tunda ni ka fara yin niyyar biyawa.’
PAGE 198
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
‘To ai na gaya miki ke ga ciki, da ace baki sami ciki yanzun ba dake zamu je amma ki yi hakuri sai shekara mai zuwa in Allah ya nuna mana.’
Ta tashi zauna ta kara marairaicewa tace ‘Idan na mutu a haihuwa fa?’
Ya harareta yace ‘Ka fadi alkhairi ko kayi shuru.’
Ta sunkuyar da kai tana murmushin yake; yayinda ya juya ya cigaba da aikinsa.
Ta zame ta koma ta kwanta; tabbas ba kuskure tayi ba ciki ne da Naja, ko da kuwa bai kai sati shida ba. Kuma tabbas ta san ba ita Mustapha yayi niyyar biyawa Hajji ba, Najan ya so biyawa. Kawai dai cikin ya zo masa ne a matsayin uzuri da kariya. Ya wanke kansa daga zargi. A hankali ta zame ta gyara kwanciyarta ta janyo abun rufa ta rufe jikinta sannan ta rufe idonta kamar mai bacci; haka ta kwana zuciyarta tana kuna.
Me Mustapha ya mayar da ita ne; shikenan idan dai abun karuwa ne ba zai iya sakata a ciki ba sai bayan ya saka Naja amma idan dai wahala ce itace a kan gaba? Yanzu yana nufin yace da matarsa zai tafi aikin Hajji; wadda itama cikin ne da ita sannan ita kuma ya barta ta kular masa da yara da gida duk da itama cikin ne da ita. Zata iya wahalar kula da gida amma ba zata iya wahalar ibada ba kenan? Sai yau ta gane girman rainin da Mustapha yayi mata da kuma yanda ya dauketa.
PAGE 199
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Tun ranar da Mustapha ya sanar da ita zai tafi Saudiyya da Naja taso ta je gida wajen Mommy, amma saboda kada abun yayi kama da zata yi reporting dinsa sai ta hakura.
Tun dare ta sanar da shi zata je gida kuma ya bata izini, don haka gari yana wayewa da yake ba itace da girki ba ta shirya. Hafsa ta kama hannun Hammad suka sauko, suka fice tsakar gida suna jiranta yayinda ita kuma take rufo part dinta. Ta saba duk lokacin da zata fita idan Naja tana nan sai ta leka ta sanar da ita ta fita, don haka yau din ma tana saukowa ta shige parlor din Naja.
Tun kafin ta hango fuskokinsu ta dauki muryar Yaya Jidda, bata yi mamaki ba tunda yanzu sun saba zuwa gidan su wuni a wajen Naja idan bata sauko ba babu mai hawa nemanta kuma ko yara ba za a tura ace ta zo ba. Ta karasa ta zauna a kan hannun kujera ta gaida Yaya Jidda cike da girmamawa sannan suka gaisa da Naja. Har ta mike zata fice Yaya Jidda ce ‘Sai muka ji abun arziki kuma, Mustapha yace da shi da Naja zasu je aikin Hajji.’
Ta dan koma ta zauna tana murmushi tace ‘Eh, haka yace.’
‘To Allah ya sa suje a sa’a, muma ‘yan baya Allah ya kirawo mu.’
‘Amin ya Allah.’ Ta amsa sannan ta mike tayi musu sallama ta fice.
Har taje gida abun yana yi mata ciwo a rai; wato harma ya gayawa ‘yan uwansa da Naja zai tafi Hajji kenan an fara zuwar mata murna ta kuma ana yi mata Allah ya kaow na ‘yan baya. Kuma wannan ganin da ta yiwa Naja ya kara tabbatar mata da cewa Najan tana dauke da ciki domin yawu ne a bakinta irin wanda masu ciki suke tarawa.
Tun da ta shiga gidan Mommy ta san da matsala, amma dai bata tambayeta ba saboda bata son ganin kukanta. Ta san yanzu da ta tambayeta damuwarta sai tayi kuka mai isarta sannan zata gaya mata damuwar.
Sun zaune a parlor din Mommy bayan sun gama cin abincin rana suna hira yayinda Hammad yake ta kaiwa da kawowarsa, Mommy ta dubeta tace ‘Ki bar min Hammad a nan ya kwana biyu ki samu ki dan huta, naga duk kin yi wani zuru-zuru.’
Tayi gajeran murmushi tace ‘Gashi nan Mommy an bar miki, idan na shirya sai Ahmad ya mayar da ni gida ya karbo masa kayansa.’
PAGE 200
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Tayi dariya ‘Dama neman kai ake da shi.’
Jimawa kadan tace ‘Momy wai Abbansu ne zai tafi Hajji shi da Naja.’
Nan da nan fara’arta ta karu, tace ‘Kai ma sha Allahu, Allah ya amsa ibada.’ Ta kalli Khadijan suka hadu kuma kamar wadda aka tunawa wni abu tace ‘Ah, to ke me yasa ba za a hada dake ba ko kuma a fara kaiki, ko kinyi halin naki ne ya bata miki rai kin ce ba kya son kujerar?’
Ta sa yatsanta ta goge kwallar da ta fado a kwarmin idonta, ta kawar da kai sannan tace ‘Haka ya zaba ya fara tafiya da ita.’
Da mamaki ta zaro ido tana tambaya ‘To ke me kika yi masa, tunda dai ai kece babba ke ya kamata ya fara tafiya dake ko kuma ya tafi daku dukanku a lokaci guda.’
‘Yace wai ciki ne da ni don haka ba zai tafi da ni ba sai dai ko wata shekarar zuwa lokacin na haihu.’
Ta kalli cikinta sannan ta kalli fuskarta ‘Ciki? To ai karami ne kuma naga har yanzu ana zuwa da masu ciki sai dai idan basu da lafiya. Ni ban ma san kina da cikin ba ai.’
‘Nima bai fi last week na gane ba, ban ma sa rai da shi ba kawai na ganshi.’
Mommy ta dafa hannunta tace ‘To ai shikenan tunda ya zo sai muce Allah ya raya, amma dai masu ciki suna zuwa aikin Hajji har yanzu. Ana ta dai cewa za a hana amma ba a hana din ba tukunna. Kawai da yace bai so zuwa dake ba.’
Ta sake share kwalla tace ‘Tabbas Mommy bai so ba, don itama Najan ai ciki ne da ita. Kawai dai ya zata ban san tana da cikin bane shi yasa yake so ya raina min hankali kamar yanda ya saba.’
‘Ikon Allah.’
Suka yi shiru na dan lokaci; itama Mommy abun ya daure mata kai. Duk gidajen da ta sani na mata biyu ko sama to idan irin wannan damar ta samu babba ake fara kaiwa. Tabbas abun ya sosa mata rai to amma babu yanda zata yi. Ta dafa hannun Khadeejan wadda itama tayi nisa a nata tunanin tace ‘Kuma baki gaya masa Najan ma ciki ne da ita ba?’
PAGE 201
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
‘Ban gaya masa ba Mommy, kuma ba zan gaya masa ba. Yana sane da abinda yake yi Mommy, tsaf ya san tana da ciki. Ita da take tara yawu idan tana laulayi, kuma ko yau ma da na shiga wajenta da yawuna bakinta. Kawai dai da ita yayi niyyar zuwa, ko na gaya masa kuma ba canzawa zai yi ba sai dai kawai yayi ta kawo hujjoji.’
‘Uhm, to ai shikenan. Kin ga dama shi Hajji kiran Allah ne, kema in sha Allahu Allah zai kirawoki nan ba da dadewa ba ta hanyar da ya so. Kada ki sa wata damuwa a ranki balle ki illata dan da yake cikinki.’
Suka yi sshiru na dan lokaci, jimawa kadan ta gyara zama tace ‘Wallahi ni Mommy na ma gaji da auren nasa gaba daya. Tabbas ko shekara nawa zan yi da Mustapha ba zai taba canzawa ba, ba zai iya yi min adalci ba. Watakila ya daina so na, watakila kuma iya son da yake min kenan. Amma dai gaskiya na gaji Mommy.’
Ta dafa hannunta cike da kulawa tace ‘To ai hakuri zaki yi, dama shi aure ya gaji haka kuma ribar aure ta me hakuri ce. Baki sani ba ko ita abokiyar zaman naki wani abun take yi na biye-biyen malamai, ai duka ana yi.’
Tayi murmushin yake tace ‘Ai wallahi babu wani biye-biye Mommy, a hayyacinsa yake yi. Kawai dai idan hidima za ayi masa to ya fi so ni ya saka ni aiki, idan kuma morewa zai yi da harkar soyayya to wannan ita ta iya. Amma babu wani asiri haka ya tsarawa kansa.’
Ta sake kama hannunta tarike tana kallon fuskarta tace ‘Ki dai yi hakurin, in sha Allahu zaki ga ribarsa. Kuma idan dai Hajji ne da izinin Allah kema zai kirawoki.’
‘Uhm.’
Nan suka dauki lokaci Mommy tana bata baki. Can zuwa yamma ta shirya Ahmad ya mayar da ita gida ta barwa Mommy Hammad.
--------
Shirye-shiryen tafiya aikin Hajji sun kankama domin ana maganar saura sati uku alhazai su fara tashi. Duk wani abu da suke bukata na kula da gida Mustapha ya tanada ya kawo musu, kuma yayi mata bayanin abokinsa wanda dama ta san shi; shine zai kawo musu raguna kuma ya tsaya a yanka.
Yanzu kullum sai yamma tayi sai ya dauki Najan a mota su fice wai sun tafi bita, haka ta zuba musu ido tana ta bawa kanta hakuri.
PAGE 202
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Gaba daya maganar tafiyar ta fita daga ran Khadeeja, kuma Mustaphan ma gaba daya ya fice mata daga rai; ji take yi kamar matsayinta a wajensa bai wuce na mai aiki ba. Zuwa yanzu ta san wanda ma bai san halin da suke ciki ba ya san Naja tana da ciki domin tara yawunta ya karu kuma tayi fari tas irin na masu ciki. Sai dai har yanzu ita Khadeejan bata sanar da Mustapha cewa ta san Najan tana da ciki ba. Sai shirye-shiryensa yake yi yana zuwa sallama da mutane domin Hajia ta gama gayawa kaf dangi Mustapha zai tafi Hajji da matarsa. Danginsa da na Naja sai zuwa suke sallama, duk wanda ya zo sai ya cewa Khadeeja Alah ya kirawo ‘yan baya. Wannan kalmar ba karamin bata mata rai take yi ba, amma haka ta share ta kawar da kai.
Tun jiya bata jin dadi sai dai bata gane me yake damunta ba, haka take ta fama. Da yake ba itace da aiki ba kuma Hammad baya nan haka ta wuni a kwance. Daf da magriba ta fara gane abinda yake damunta; marata ce take ciwo ga wani amai da yake taso mata amma ya ki fitowa. Haka ta sha panadol ta shige dakinta ta kwanta. Wajen 9pm Mustaphan ya shigo dakin domin sanar da ita ya dawo kamar yanda ya saba. Har ya juya zai fita ya dan tsaya yace ‘Wai ya na ganki a kwance ne? kamar baki da lafiya.’
‘Uhm, mara tace take dan ciwo.’ Ta amsa a gajiye.
‘Ok, Allah ya sauwake. Ko kina bukatar wani abu?’
Tace ‘No ina jin zai daina don na ma sha panadol.’
Ya sake yi mata sannu sannan ya juya ya fice.
Can wajen 10:30pm ciwon ya matsa mata, tun tana daurewa har ta kasa. Ta lalubi wayarta ta kirawoshi, ba tare da bata lokaci ba ya shigo dakin nata. Kafin ya shigo ma ta riga ta shige bandaki saboda yanda take jin kamar zata yi kashi, kafin ta karasa toilet din abinda yake shirin fitowa daga jikinta ya riga ya fito sai jini da ya biyo baya gaba daya da aman da ya tokare mata kirji.
A tsugune ya sameta a bandakin, ya karasa da sauri ya duba halin da take ciki. Ya kamata ta mike sannan ta karasa ta zauna a kan toilet. Tace ya jirata ta wanke jikinta sai suje asibiti.
PAGE 203
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Nan da nan ta wanke jiki ta gyara sannan ta tattare zanin nata da bainda ya fita daga cikin nata gaba daya ta saka a leda sannan ta fito ta shirya suka kama hanyar asibiti. Babu wanda yayi magana sai shi da yake mata sannu lokaci zuwa lokaci; a haka har suka isa asibitin.
Ba tare da bata lokaci ba likita ya dubata kuma ya tabbatar da cewa cikin jikinta ya fice gaba daya, don ko wankin ciki ma ba sai an yi mata saboda komai ya fice. Aka rubuta mata magunguna aka sallamesu.
Tun a mota ta gane Mustapha bai ji dadin zubewar cikin ba, duk da ita ta fi shishiga damuwa da zubewar cikin; amma dai ta kula ba haka yayi ba wancan lokacin da tayi bari. Har yanzu tana jin ciwon mara don haka ba zata iya surutu ba.
Bayan sun dawo gida ta haye samanta ta sake yin wanka sannan ta sha magungunanta ta saka Hafsa ta hada mata indomie da shayi mai kauri ta zauna taci. Sai da taci ta koshi sannan ta kirawo Mommy da Yaya Mama ta sanar da su. A daren Momy ta so zuwa sai da Khadeejan ta hanata ta sanar da ita cewa ta sami lafiya su bari da safe sa zo; don haka suka hakura.
Can wajen daya saura ya sameta a dakin; tana kwance a gefen gado tana shirin yin bacci. Ya zauna a gefenta yace ‘Sannu.’
‘Yauwa.’ Ta amsa tana daga kwance.
Suka yi shiru na dan lokaci, ta san da zance a bakinsa don haka tayi kasake tana jiran taji me zai ce. Jimawa kadan ya gyara zama kamar wani mara gaskiya yace ‘Um wai ni me ya faru ne? Me ya kawo wannan miscarriage din? Ko wani abun kika sha ne?’
Tayi ‘yar dariya tace ‘Babu abinda na sha, Allah ne dai ya kawo kamar yanda ya kawo wancan.’
Ya dan yi jim yace ‘Allah ya sauwake.’
Ya sake yi mata sannu sannan bayan ya tabbatar babu abinda take bukata sannan ya fice ya barta.
Washe gari tun da safe Mommy da Yaya Mama suka zo, nan suka zauna suka zube mata kayan dubiyar da Baffa ya aiko mata. Mommy ta ji dadi yanda ta ganta ta riga ta mike kamar ma ba daren jiya tayi bari ba, sai kaiwa da kawowarta take yi ana hira da ita. Har sun fara shirin tafiya suna zaune Yaya Mama tace ‘Kinga idan dai ciki ne zai sa a fasa tafiya dake ai yanzu sai a baki kujerarki ko.’
PAGE 204
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Tayi dariya tace ‘Dama kujera ba tawa bace, babu ruwan ciki niyyar bani ne ba ayi ba.’
Mommy ta dafa ta tana dan zare ido tace ‘Khadeeja in ce ko dai ba wani abu kika sha kika fitar da cikin nan ba saboda kujerar Makka.’
Ta dan zaro ido ta kalleta suka hada ido tace ‘Mommy! Me yayi min zafi? Wallahi babu abinda na sha, sai kace wata marar hankali? Ai na gaya miki fa ba ciki ne ya sa ba zai bani kujerar ba kawai haka yayi niyya, yanzu kuma barewar cikin ba zata sa ya fasa tafiya da ita ba. Ni ce kawai ba zashi da ni ba.’
Yaya Mama tace ‘Haba Mommy, a kan wata kujera zata barar da ciki?’
Ta gyara zama ‘To ai abun naku ne sai a hankali.’
Suka karasa hirarrakinsu suka yi mata sallama suka kama hanya.
Ta zauna tana tunanin dalilin da yasa Momy zata yi wannan tunanin; to ko tunanin da Mustapha ma yayi kenan yake tambayarta me ya faru bayan sun