Showing 60001 words to 63000 words out of 99112 words

Chapter 21 - Mijin Marigayiyya Part Complete Hausa Novels.docx

17 Sep 2025

75

shigo gidan.

A dakinta ya sameta tana mike a kan gado da Hammad a kwance a kan cikinta yana wutsil-wutsil dinsa. Bayan ya amsa sannu da zuwanta ya karasa ya zauna gefen gadon.

Suka dan taba hira sanna tace ‘Um ga abinci can a dinin fa, idan ka shirya sai mu je mu ci. Yara dai sun ci nasu don yau tun magriba Nas ta fara jin yunwa.’

‘Oh,Ok.’ Ya amsa kamar mara gaskiya.

Tace ‘Kuma na ga amarya har yanzu tana dakin naka fa, ko a nan zamu kwana ne?’

Kamar wanda aka tayar daga bacci yace ‘Umm. No, umm kin gane? Dama ina so nayi miki magana don da na san zaki dafa abincin darem zan ce ki dakata.’

Ta kalleshi da mamaki tana jira taji karashen bayanin, suka hada ido yayi sauri ya kawar da idonsa. Suka dan yi jim sannan ya cigaba ‘Ina ga ya kamata tunda ke kina jego ki bar mata kwnakin naki zuwa lokacin da zaki cika arba’in ko?’

Ta dauke Hamma daga kan cikinta ta tashi zaune tana karewa Mustapha kallo ko zai sauya maganarsa, kamar bai fahimci sakon ba don sai ya kara hade rai yana wasu muzurai. Tayi murmushin yake tace ‘Oh, yanzu kenan kwanan gaba daya na amarya ne har sai na cika arba’in da haihuwar Hammad?’

‘Eh, to ai kinga kina jego. Menene amfanin kwanan?’

Ta sunkuyar da kai, ta dago ta kalleshi sanna tayi gajeran murmushi tace ‘Hakane, Allah ya kai mu arba’in din.

PAGE 151

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Kamar wanda aka tsikara ya mike yana yage baki yana cewa ‘Yauwa, to bari naje sai da safe ko.’

Cikin sauri ya fice daga dakin kamar wanda yake tsoron kada ta rikeshi tace ta fasa.

Tabi kofar da kallo bayan ya fice; wasu hawaye masu zafi suka gangaro kan fuskarta a daidai lokacin da wani malolo ya taso ya tokare mata makogoro take neman kasa numfashi. Sautin rufe kofar ya dawo da tunaninta cikin dakin bayan da ta kifta idonta; tayi murmushi mai ciwo tare da sunkuyar da kai. Wato dai yanzu Mustapha yayi sabuwar amarya har ya fara gudunta, tunda ai lokacin da tayi bari sai da ya nuna bacin ransa a kan tafiyar da tayi gida. To me yake nufi da ita? Wato idan wahal ce taje ita kadai tayi ta sha kenan, lokacin da zai iya morarta shine lokacin da zai bata kwana. Lallai akwai aiki amma dai ba zata fasa addu’a duk da zuwa yanzu duk dan wani karsashin kyautatawa Mustapha da take so tayi ya zirare.

Sai da Hammad ya fara kuka sannan tayi ajiyar zuciya ta sa bayan hannunta ta share hawayenta sanna ta mika hannu ta daukoshi daga inda yake kwance ta saka masa nono. Har ya gama shan non ya saki tana ajiyar zuciya, ta shiryashi ta goya shi sannan ta fice daga dakin. Da yake dare yayi tana jiyo muryarsu kasa-kasa sun hira tunda dakin nasa yana jikin nata dakin. Haka ta wuce da yaje a parlor dinta ta jera musu abincin daren can ta wuce taje ta kwashe ta mayar kitchen tana kwafa. Ta dawo suka kwanta ita da Hammad.

PAGE 152

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Duk yanda take jin bacci a wannan daren kasawa tayi, sai dai da yake bacci barawo ne sai da ya faki idonta ya sace ta; sai ji kawai tayi ana assalatu. Duk da ba sallah zata yi ba sai da ta tashi ta wanke fuska sanna ta zauna tayi azkar dinta sannan ta koma ta kwanta.

Tun kafin a daura aurensa da Naja ya riga ya gaya mata amarci zasu yi na kusan kwana talatin domin lokacin da zata tare zai yi daidai da kwanan Khadeeja goma sha biyu da haihuwa. Don haka ya sanar da ita gaba daya kwanan nata ne har sai Khadeeja ta gama jego kwana arba’in. Ita Khadeejan ce bai gayawa ba shi yasa ma ta zata za ayi yanda aka saba ne ta karbi kwananta bayan kwana bakwai.

Ba karamin dadi yaji ba da Khadeeja ta amsa masa ko da yake dama bai sa ran zata bashi matsala ba tunda dai ta san ba zata biya masa bukatarsa ba wadda a wannan lokacin ko allah ma bai haramta masa ya kaiwa daya matar tasa bukatar ba. Cikin walwala suka kwana shi da amaryarsa, ko da ya fito da asuba zai tafi masallaci ya hango fitila ta kasan kofar dakin Khadeeja don haka ma ya san ta riga ta tashi.

Da sallama ya shigo parlor din bayan ya dawo daga masallaci, kai tsaye ya nufi kitchen din don ya jiyo motsinta a can. Tana tsaye da goyon Hammad tana zuba ruwan zafi a flask. Bayan ta amsa sallamarsa ta gaisheshi; yana ta wani kau da kai yana muzurai kamar yanda ya saba idan yana so ya gwada mata son kai haka ya amsa gaisuwar tata. Ta mayar da kettle din inda take sanna ta bude fridge don ta dauko ragowar peppersoup dinta. Yace ‘Ina yaran? Basu taso ba.’

‘Eh.’ Ta amsa a gajarce ba tare da ta bar abinda takeyi ba.

Ya kula da yanayinta idan ya takurata zata iya birkice masa a safiyar don haka yace ‘Ok, idan sun shitya kice su biga min kofa please.’

‘Ok.’ Ta sake bashi amsa a gajarce.

Ya juya ya fice daga kitchen din.

Ta karasa dumama soup dinta ta juye a flask, ta dauki ruwan zafinta ta hada ta kai daki sannan ta dawo ta dauki kayan shayi duka ta shigar daki. Ta zauna ta ci burodi da soup ta sha shayinta mai kauri sannan ta koma ta kwantar da Hammad itama ta kwanta.

PAGE 153

MIJIN MARIGAYIYA

A HAUSA NOVEL by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Bata dade da kwanciya ba kuwa bacci ya dauketa saboda dama na jiya ba isarta yayi ba.

Kamar a mafarki taji ana buga mata kofa, tayi firgigit ta bude ido. Ko ba a gaya mata ba ta san wannan bugun Habib ne don haka ta tashi zaune ta janyo wayarta ta duba lokaci; 8:25am. Ta janyo zanin goyon Hammad dake kusa ta rufe jikinta sanna tace ‘Shigo Habib.’

Ya turo kofar ya shigo da sallama, tun kafin ta gama amsa sallamar tasa yace ‘Anti yau makara kika yi ne? Yanzu har past 8 fa kinga bamu tafi makaranta ba.’

‘To me yasa baki tafi ba, ni ai na zata kun tafi tuni.’

Ya karasa ya zauna a bakin gadon da mamaki a fuskarsa yana cewa ‘Anti baki tashemu ba fa; nima bayan mun dawo daga masallaci da Abba har nayi wanka fa na dan kwanta don na san zaki tasheni shine bacci ya kwasheni. Su Afaf ma gasu can ko sallah ma basu yi ba sai yanzu na taso su har Hafsan.’

Ta kama haba tana cewa ‘Ikon Allah. To ai ba nice da girki ba Habib, Antin ku ce. Itace zata tashi kowa ta shirya shi yasa ma ka ga ban fito ba.’

Ya tabe baki yana zare ido ‘Tab, to ai kuwa daga ita har Abban babu wanda ya fito.’

‘To Allah ya sa dai lafiya, kaje ka buga musu kofa. Ka murda kofar parlor din a bude take sai ka kwankwasa dakin kaji.’

Ya mike ya fice daga dakin yayinda ita kuma ta zame ta gyara kwanciyarta da niyyar komawa bacci.

……

A tsakiyar parlor din Habib yaci karo da Abban nashi yana fitowa da gaggawa, suka hadu a tsakiya suka yi cirkocirko. Abban nasu yace ‘Kai Habib meye haka? Na cewa Anti ku taso ni idan kun shirya me yasa baku taso ni ba? Kai ko uniform ma baka saka ba.’

Yace ‘Abba ai makara muka yi, Anti Najan bata tashemu mun shirya ba.”

Kafin ya bashi amsa sauran yaran suka shigo kowa da kayan bacci, ya kallesu sannan ya mayar da hankalinsa kan Habib din yana cewa ‘Wace Anti Naja kuma, ko dai Anti Khadeeja?’

‘To ai itama Antin bacci takeyi yanzu naje tashinta tace min ba itace da girki ba Anti Naja ce zata shirya mu.’

Mamaki ya kama shi; ya za ayi Khadeeja ta gayawa yaro wannan maganar? Wane irin wulakanci ne bayan itace ta saba shirya yaran kawai kuma yanzu sai tace Naja ce zata shiryasu?

PAGE 154

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ba tare da yace komai ba ya wuce yaran ya nufi dakin Khadeejan. Habib ya dubi ‘yanuwansa yace ‘Yau dai mun yi mising school, ni yunwa nake ji ma kuzo muje kasa bread yana can ko shayi sai mu hada.’

Ya wuce suka bi shi suka sauka kasa.

Kusan a fusace ya tura kofar, hangota da yayi a kwance tana bacci ya kara harzuka shi. Sautin bude kofar ne ya farkar da Hammad daga bacci. Ta tashi zaune tana mittsike ido sanna ta mika hannu ta daukeshi. Ta dubi Mustapha cikin halin ko in kula tace ‘Ohhh! Abba ka tayar min da yaro yanzu babu sauran bacci.’

Ta daga shi yayi mika sannan ta saka masa nono yayinda Mustaphan yake cewa ‘Me ya faru naga baki tashi kin shirya yara ba bayan yau akwai makaranta, kuma fa ko da asuba sai da na ce miki idan sun shirya kice suyi min magana?’

Tace ‘Oh! Ai basu zo sun ce min sun shirya ba na zata ma sun gaya maka kun wuce sai da Habib ya gaya min yanzu sannan na sani.’

‘Ban gane ba, wai wace magana kike yi ne? to me yasa baki tashi kin shirya su ba?’

‘Oh to ai wadda take da kwana itace da gida musamman ma da yake ni ina jego. Na zata da kai mata kwanan ka gaya mata abinda aka saba yi na running gidan.’

Mamakin da yake fuskarsa ya karu ya hade da takaicin Khadeeja, yace ‘Ban gane wadda take da kwana itace take da gida ba Khadeeja. Ke kika saba shirya yaran nan kullum kuma kin san haka, shine yau saboda ganin ido zaki ce ita zata shiryasu? Idan kina jin haushina ai sai ki gaya min tunda ba dole nayi miki kika bar mata kwanan ba ko? Zaki fara wulakancin naki ko Khadeeja?’

Tayi dariyar yake tace ‘Wallahi ni duk ban gane ba. Ai ni a yanda na sani duk matar da take da kwana da girki itace take duk wata harka ta kula da gida, nima idan na karbi girki sai na hada gaba daya nayi.’

‘Khadeeja, bana son wulakanci. Yaran nan a hannunki suke kuma da ke suka saba, ya za ayi tana zuwa ki dora mata kula dasu ita da yau zata koma aiki.’

PAGE 155

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

‘Amma dai ba dasu na zo ba a nan na samesu ko? Kuma idan ban manta ba nima daga zuwana aka hada ni da su, kamar ma ita an daga mata kafa. Hidimarsu ta makaranta ma wadda ta riga ta saba yi tun ma kafin ta auri ubansu balle yanzu da ta aureka, ai inaga wannan ma karamin abune.’

Ya gama kulewa har wani huci yake, ya cije lebe sannan yace ‘Khadeeja bana son wulakancinki fa, yanzu me kike nufi da yaran nan?’

‘Alkhairi nake nufi da kowa, kawai dai duk wadda take da kwana ta hada duk har gidan da yaran ta kula da su. Shikenan.’

Har ya juya zai fita ya juyo ya nuna ta da yatsa yana cewa ‘Yanzu shikenan kintura mata yara har tsawon sati hudu?’

Ta dago ta kalleshi cikin halin ko in kula tana cewa ‘Na tura mata mijin ma?’

‘Mtsewww!’ ya ja dogon tsaki ya fice ya maka mata kofar.

Tayi ‘yar dariya ta cigaba da wasa da Hammad.

……..

Har ya koma dakin tana kwance tana baccinta domin office din da zata ta riga tace sai wajen sha daya zata tafi saboda an canza mata branch sakamakon aurensu da Mustapha; ta san tunda yau zata fara reporting tana da damar makara. A hankali ya bude kofar ya shiga saboda kada ya tasheta daga bacci, ya karasa ya zauna a gefen gadon. Ya zuba fuskarsa a tafukan hannunsa yana shafa fuskar, gaba daya kansa ya kulle. Yayi zaton yaran nan tunda suna wajen Khadeeja shikenan a wajenta zasu cigaba da zamansu ko da ya kara aure. Gaba daya ma shi bai taba zama sun yi maganar yara da Naja ba, kawai dai yana sakata hidimarsu idan ta kama kuma yana nuna mata cewa yana so su sami kulawar da yake jin sun rasa daga wajenta. Baya jin zata bashi matsala saboda yanda yaga tana kulawa da su tun ma kafin ta aureshi balle yanzu da zata yi da hujja.

Ya juya ya dan tabata. Ta bude ido ta kalleshi tayi murmushi sannan tayi mika. Tace ‘Honey har ka dawo?’

Ya dan kawar da kai sanna yace ‘Daga ina?’

‘Umm! Na zata ‘yan makaranta ka kai.’

‘No, ban kaisu ba sun riga sun makara sosai sai gobe.’

‘Ok, Allah ya kaimu.’

Ta zuro kafafunta kasan gadon ta kwanta a kafadarsa tana cewa ‘Bari naje na yi wanka sai na fito na hada mana breakfast. Ina jin ma kawai sai na shirya ka bani lift.’

PAGE 156

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Yace ‘Ai kuwa sai kiyi sauri don ga yara can ma ke suke jira ki zo ki bamu abincin gaba daya.’

Ta daga kafadarsa ta dan kalli fuskarsa da mamaki ‘Antin bata nan ne?’

Ya kawar da kai daga kallon da ta kafeshi da shi, yace ‘Tana nan. To ai kin ga kece da kwana don haka kece zaki dinga yin baimcin duka gida kina kula da yara, in ya so idan ta karbi kwana sai ta cigaba. Duk wadda take da kwana itace da gida.’

Ta sake leka fuskarsa da mamaki a kan fuskarta tace ‘Ban gane ba, ai ni ban karbi girki ba, kwana ne kace ka tambayeta ta bamu har tayi arba’in. kuma yara ai na zata tunda a wajenta suke sai suyi zamansu duk abinda ya kama ai zan saka hannu.’

‘A’a, wadda take da kwana itace zata dinga hadawa tayi komai kawai. Kiyi sauri kiyi wankan ki zo ki bamu abinci.’

Shiru tayi kawai tana binshi da kallo. Jimawa kadan ya kalleta suka hada ido, ya gyara zama ya kama hannuwanta duka biyun ya rike sanna yace ‘Kin ga wannan fa ba wani abun damuwa bane, ai dama kin san duk inda ake da mace sama da daya ai dama duk wata hidima rabawa ake yi. Idan yanzu kika ki yin wani abu ai sai ki janyo kwanan amarcin ya kare tunda kin ga dole ne na koma kan tsarin kwana bibbiyu don tabbatarwa an yi adalci ko?’

Ta sunkuyar da kai tana kallon kasa don gaskiya ita bata zata haka ba; ba wai ba zata kular masa da yara ba amma dai ta sa rai zasu yi zamansu a wajen uwarsu itace zata dinga hidimarsu ta kullum in ya so ita duk wanda yazo inda take a cikinsu zata yi masa duk wani abu da ya kama.

Ta dago ta kalleshi tace ‘To yanzu kenan duk wadda take da kwana itace zata dinga tashi tana yiwa yara komai?’

Ya daga mata kai alamar e.

‘To idan zani aiki fa.’

Ya kama habarta ya dago fuskarta, suka hada ido yayi mata murmushi sannan yace ‘Ki bari wannan a hankali zamu ga yanda za ayi.’

Ta dan ja baya zata tashi, ya rike fukarta ya sake tsareta da ido har saida tayi murmushi, ya sumabi lebenta sannan ya mike yana cewa ‘Muna kasa muna jiranki ni da yara.’

‘Ok.’ Ta amsa sannan ta shige bandaki.

Ya tashi yafito daga dakin.

PAGE 157

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid Innar su Amal

A parlor ya tarar da yaran suna zaune suna shan shayi da burodi wanda Hafsa ta dafa musu ruwan zafin. Ya nemi waje ya zauna ya dauki remote ya canza channel.

Ya fi minti tallatin da zama shi da yaran suna ta hira sannan ta sauko, ta sha kwalliya sai kamshi takeyi. Bayan ta amsa gaisuwar yaran kai tsaye ta wuce part dinta, nan da nan ya tashi ya bi bayanta yayinda Nasreen da Shukra suka rufa masa baya. Nan da nan ta soya kwai ta hada musu da shayi suka zauna shi da ita a dining table suka karya.

Suna gama karyawa shima Mustaphan ya shirya suka fito tare. Har zasu sauka daga bena sai kuma ya bata mukullin motar yace ta fito ta jirashi zai yi sallama da Khadeeja.

A parlor dinta ya sameta tana kwance a kan doguwar kujera da remote a hannunta yayinda Hammad yake cikin baby rocker dinsa yana ta wutsil-wutsil. Tana daga kwance ta amsa sallamarsa, ya karasa kusa da kanta yace ‘Zamu fita ni da Naja, itama yau zata koma aiki.’

Tace ‘Ok, a dawo lafiya.’

Har ya juya zai fita tace ‘Ta dai barwa yara abincinsu ko? Ga shi zasu je islamiyya ko da yake na san sun yi wanka in lokacin yayi ko Hafsa sai ta tayasu shiryawa su wuce.’

Ya juyo ya tsaya ya zuba mata ido na dan lokaci; ya ma rasa ta ina zai fara. Ya kan rasa yaren da zai yiwa Khadeeja magana da shi idan ta fara wannan taurin kan nata, lokuta da dama ya kan dauka cewa tana jin tsoronsa amma fitnar da yake gani a kwayar idonta idan tana wannan taurin kan tana bashi tsoro. Ya cije lebensa sanna yace ‘Fita fa nace miki zamu yi, ya kike so tayi da abincin ranansu?’

Ta tashi zaune ta gyara zamanta sannan tace ‘Yanda nakeyi idan zan tafi makaranta ko?’

Ya jijjiga kai sanna yace ‘Khadeeja please kada ki saka min ciwon kai da safen nan, ga yara nan ki basu abinci in ya so idan mun dawo ta basu na dare. Idan kuma kin ga dama ki barsu da yunwa.’

Ta kalleshi suka hada ido tayi masa gajeran murmushin yake ta zame ta kwanta ba tare da ta ce masa komai. Haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login