Showing 90001 words to 93000 words out of 99112 words

Chapter 31 - Mijin Marigayiyya Part Complete Hausa Novels.docx

17 Sep 2025

78

ka dai yi hakur ka zo ka kwanta tunda ka ga yanzu dayan dare ta kusa, zuwa wayewar gari sai a nemoshi a bashi hakuri a gaya masa ya barwankin.’

‘Mtseww! Wai kin san me kike fada kuwa? Na zo na kwanta saboda ke kin kwanta ko?’ ya sake jan tsaki sannan ya fice daga dakin ya rufe mata kofar da karfi, rufe kofar da sai da ya farkar mata da Baby daga barci.

Ta juya a fusace tana gunguni ta dauki yarinyarta ta saka mata nono.

Yanda yaga rana haka yaga dare, yana zaune a parlor shi kadai. Sai dai idan bacci ya daukeshi yayi firgigit ya farka, ya sake buga lambar Habib amma a kashe. Yana fara jin kiran sallar asuba ya kirawo Alhaji ya sanar da shi ba a ga Habib ba.

A shirye ya fice masallaci, bayan an idar da sallar asuba ya sanar da su bacewar habib. Yana dawowa gidan ya dauki mukullin motarsa ya fice ya nufi gidan Hajia.

Suma a tsaye ya samesu cikin tashin hankali, nan suka zauna suna jira gari ya kara wayewa suje police station su sanar.

Suna zaune a parlor din Alhaji cikin tashin hankali Hajia ta dubi Mustapha tace ‘Kuma ka tuntubi kakanninsa, can gidan su Ma’u da ma ita Khadeejan ko wajensu ya tafi?’

Ya gyara zama yana cewa ‘Khadeeja dai na tambayeta itama bata ganshi ba, amma gidan mama ma ni na manta da su. Bari na kirawosu na ji.’

Kafin ya gama laluben lambar suka jiyo bugun kofa, gaba dayansu suka nufi kofar saboda Alhaji ya bada sanarwa a masallaci yayi zaton ko an sami wani labari ne.

PAGE 228

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ga mamakinsu Kawu Auwal ne wato kanin Ma’u tare da Habib din. Suna hada ido Mustapha ya kai masa duka yana cewa ‘Shine zaka fice ba tare da ka gayawa mutane ba saboda raini ko?’

Alhaji yace ‘Ka barshi mana ya zauna yayi bayani.’

Suka karasa cikin gidan suka zauna a parlor din Alhaji.

Bayan sun gaggaisa Kawu Auwalu yace ‘Wallahi nima da asuba Mama ta kirawoni tace na zo na dawo da shi, itama ta yi zaton an san yana gidan shi yasa ma bata nemi kowa ba. Sai dazu bayan sallar asuba Antinsa Khadeeja ta kirawota tana cigiyarsa. Shine ta kirawoni tace na kawo shi nan nayi bayani.’

Alhaji yayi masa godiya sannan ya dubu Habib yace ‘Mutumina ya haka kuma? Me suka yi maka a gidan da zaka bi dare ka gudu? Kuma madadin ka zo ka gaya min sai ka tafi ka dagawa Mama hankali.’

A nan ne ya sami dama ya gayawa Alhaji abinda ya faru, sannan ya sanar da shi irin zaman da ake yi a gidan.

Hajia tace ‘Dama Aminan Jidda ta fada, tace wancan zuwan da suka yi gidan basu ma ga Najan ba. Kamar yaran suna kasa su da mai aiki suna rayuwarsu ita kuma tana sama ita da nata yaran, kuma yanda ya fada haka Aminana ta fada tace shi kanshi Mustaphan yaran basa ganinshi sai dai idan ya sauko.’

Shima Auwalu ya tabbatar musu da cewa duk wadannan maganganu yaran sun dade da yiwa Mama bayani, sai dai da yake ta dauka ba huruminta bane shi yasa ma bata ce komai ba. Amma dai gaskiya da akwai matsala, tunda ai da ba a taba samun matsala irin wannan ba.’

‘Hakane, in sha Allahu za a duba kuma a dauki mataki.’ Alhaji ya fada.

Suka karasa tattaunawa Auwalu yayi musu sallama ya tafi.

Shima Mustapha ya mike ya sa Habib a gaba don su tafi, sai dai shi habib din ya nuna ba zai koma don ya fi so ya zauna a nan wajen Hajia. Alhaji ne ya saka shi a gaba da nasiha yana nuna masa gara ya zauna saboda kannensa, kada ya tafi ya barsu su kuma bai san me zai faru da su ba.

Sai wajen karfe tara sannan Hajia ta shirya suka kama hanya tare da Habib din da Mustapha suka koma gidan.

PAGE 229

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

A cikin tashin hankali suka sami yaran, Nasreen da Shukra suna sanye da uniform dinsu; don saida suka fara shirin makaranta sannan Naja ta sauko ta sanar da su ba zasu makaranta ba Habib ya bata Abbansu kuma ya tafi nemansa.

Babu wanda ya ji shigowarsu gidan saboda Mustapha a waje ya ajiye motarsa saboda Hajia tace yanzu zata fito ya mayar da ita. Da sallama suka shiga parlor di, Nasreen ce da Shukra suna zaune a parlor din da flask din shayi a gabansu da katon bread. Sai dai sun kasa shan sahyin sun yi tsuru-tsuru.

Da gudu suka mike, Shukra ta fada jikin Habib tana dariya yayinda Nasreen ta matsa kusa da Hajia. Suka karasa ciki suka zauna.

Hajia tace ‘Ina Afaf?’

Nasreen tace ‘Tana dakinmu.’

‘Antin fa da Rukayya?’

Nasreen ce ta sake sunkuyar da kai tace ‘Basu sauko ba.’

Hajia tace ‘To kije ki kirawo min ita kice ta zo.’

Shukra tace ‘Yanzu fa ta leko kuma tace kada wanda ya hau mata sama ya dameta, ko menene a jira sai ta sauko.’

Hajia ta jijjiga kai, ta kalli Mustapha.

Ya dan diririce sannan yace ‘Hajia tasowa zakiyi muje saman ai.’

Ba tare da wani musu ba ta mike ta tasa Nasreen da Shukra a gaba tana biye da su yayinda Mustapha da Habib suke biye da ita.

Anti Wiyya ce a zaune a kan kafet da kwanuka a gabanta suna cin abinci ita da Rukayya yayinda Naja take zaune a kan kujera tana cin nata abincin suna hira. Da yake kicin a buda yake ana hango mai aikinta da goyon baby tana goge-goge.

Shukra ce ta fara shiga tana surutu don haka a fusace Anti Wiyya tace ‘To sarkin tsurku, ba cewa aka yi ku zauna a kasan ba shine kika shigo kina….’

A lokaci guda kuma Naja tace ‘Ai sai nayi maganin wannan yar…’

Sallamar Hajia ce ta katse musu zantukan, ta karsa ciki yayinda Shukra ta zagaye ta koma bayan Abbanta. Suka karasa ciki suka zauna yayinda Naja da Wiyya suka diririce.

Naja tayi wuf ta mike ta kwashi kwanukanta tana cewa ‘Bari na wanko hannu.’ Ta nufi kicin cikin sauri.

Itama Wiyya ta kwashi nata kwanukan ta mike tana cewa ‘Sannu da zuwa Hajia, bari na kawo miki abinci.’

PAGE 230

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Rukayya tace ‘Anti ban koshi da naman ba.’ Bata ko saurareta ba ta wuce kichin yayinda ita kuma ta tashi ta bi bayanta da sauri.

Sai dai duk saurinsu kowa ya riga ya ga abinda yake cikin kwanukan nasu; farfesun kaji ne wanda suke hadawa da burodi da shayi suna ci.

Bayan sun zauna Hajia ta dubi Mustapha sannan ta dubi Nasreen tace ‘Nas ku ina naku naman naga kuna cin gayan burodin.’

Tayi darya tace ‘Ba a bamu ba, dama kullum abincin sama da ban da na kasa har garama idan Abban yana nan.’

Hajia ta sake kalloshi tace ‘Allah ya sauwake.’

Naja ce ta dawo parlor din ta zauna a kan kafet ta gaida Hajia, bayan ta amsa ta dubi Nasreen tace ‘Jeki kicin ki taya Anti Wiyya ta daukowa su Hajia abinci.’

Hajia ta daga hannu tace ‘Ki ce ta barshi, ku barshi ma, abincin da naga bai isa an raba da yara ba ai ba zai isa har a bawa bako ba. Ni na ci abincina ku barshi na koshi.’

‘A’a Hajia ai akwai, suma hawowa ne basu yi ba nake jira Jummai ta gama wanke-wanke ta mika musu.’

‘To me zasu shigo suyi, su da zaki yi maganinsu. Ai sai dai kawai a cigaba da addua kada a wayi gari kin korosu daga gidan kamar yanda kika koro dan uwansu cikin dare.’ Hajia ta bata amsa.

‘Wallahi Hajia babu wanda ya koroshi.’

‘Allah ne kawai zai gane gaskiya, amma dai ke kiji tsoron Allah. Kin bani kunya, wallahi kin bani kunya! Ban taba zaton haka daga gareki ba. Gaba daya mun zata zuwanki gidan nan zai sa yaran nan su sami kulawa ta musamman ashe ba haka bane. Ke da uwarki da ‘yayanki kuna sama kuna cin kaji yaran suna kasa suna fama da burodi. Kuma ma har sharadi aka kafa musu cewa kada su hawo su dameki. Kamar dai ba gidan ubansu ba.’

Suka yi shiru kamar ruwa ya cinyesu.

Hajia ce ta karya shirun ta dubi Mustapha tace ‘Kai dai baka kyauta ba, yanzu rayuwar da kuke yi kenan? Su wadannan da uwarsu ta mutu kun barsu a kasa kuna sama kuna jin dadi. To kaji tsoron Allah. Kema kuma ki ji tsoron Allah. Bana jin sun taba ganin haka a wajen Khadeeja, ashe dama jira kike ku koreta daga gidan ki cuzgunawa marayun Allah.’

PAGE 231

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta sunkuyar da kai kamar wadda zata dungura. Habib yace ‘Ai tunda suka dawo daga Saudiyya aka hanasu hawowa na, dakinsu ma da koamai nasu ya koma kasa.’

Hajia ta dubi Mustapha duba na takaici har sai da ya sunkuyar da kansa cike da kunya. Ta mike tana cewa ‘Ai shikenan, amma tabbas ba zan bar wannan zaluncin ba. Kuma ko da kin ga kamar kin yi nasara to Allah yana kallonku gaba daya.’

Yaran suma suka mike, Hajia ta dubi Mustapha wanda kunya ta hanashi mikewa tace ‘Za ka samu ka mayar da ni gida ko sai ta baka izini.’

Ya mike kamar wanda aka tsikara.

Naja tace ‘Don Allah Hajia kiyi hakuri. Wallahi ba haka abubuwan suke ba rashin fahimta kawai aka samu wallahi ana kula da su.’

Ta dubeta tace ‘Allah ya sa, ai nima haka nake so. Sai dai kowa yayidon Allah ai ya sani ko, Allah kuma yana sane.’

Ta wuce yaran da Mustapha suka bi ta a baya suka fice.

Har suka isa gida tana faman caccakar Mustapha a kan yanayin da ta gani a gidansa kuma tana tuna masa girman hakkin yaran nan a wuyansa da shi da matarsa. Bashi da binda zai gaya mata sai hakuri kawai yake bata; shima baya jin dadin yanda gidan ya koma tun bayan rabuwarsa da Khadeeja. Ba da son ranshi ba ta mayar da yara kasa kuma wannan raba abincin ya sha yin magana a kai. Amma ta iya abun ganin ido ne kawai, idan yana nan sai tayi kamar komai normal amma da zarar ya fita sai ta tsawatarwa yaran kowa ya shiga hankalinsa. Abinci kuwa dama idan dai ba a gidan zai ci ba tabbas abincin da ake dafawa a sama da ban kuma abincin da take bawa mai aiki ta dafawa yaran da ban ne. Duk wani dadi a sama suke ci ita da yaranta da ‘yan uwanta su kansu yaran har sun saba. Gashi ta hanasu kula ubansu sosai, domin in dai yana saman nan bata barinsu su ganshi. Har sun gaji da yanda take musu sun hakura sun ma daina cewa suna son magana da shi.

Haka ya karasa gidan ya ajiye Hajia a bakin gate ya dawo saboda baya son ya shiga ciki saboda ya san ba zai ji da dadi ba a wajen Alhaji.

PAGE 232

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Suna fita Anti Wiyya ta fito daga kitchen jiki a sanyaye, ta zauna kusa da Naja ta kama haba tana cewa ‘Ikon Allah, kin ji mutane ko? Ko motsin shigowarsu bamu ji ba sai kace shiri.’

Ta tabe baki ‘Hmmn! Su suka sani. Dama tafiya yayi ya kai rahoto shi yasa ya bi dare su kuma basu yi tunanin su kirawo mutane su sanar cewa ya isa can ba saboda sun shirya tsiya. A kansu zata kare in sha Allahu.’

Ta mike kamar an tsikareta tana cewa ‘Bari ki gani na hada kayana na bar gidan nan kafin ya dawo ya koreni da kansa.’

‘Haba Anti, saura sati biyu dama fa ki tafi tunda kin ce ba zaki yi mim arba’in ba. Kiyi zamanki babu abinda zai yi.’ Ta fada tana gyara zama.

‘Wallahi tafiya zan yi, da wanne idon zan kalleshi ya riga ya gama rainani. Ina nan ina yagar kaza na bar masa yara suna fama da gayan burodi.’

Ta marairaice ‘Anti idan kika tafi ma in ya dawo ai sai yace bani da gaskiya.’

Ta nufo kasa don hada kayanta tana cewa ‘Ku kwashe kalau amma ni da mijinki ba zamu sake haduwa ba in sha Allahu, ko a kwararo balle ma a gidansa.’

Tana ji tana gani Anti Wiyya ta fice ta bar mata gidan.

Bata dade da fita ba Mustapha ya dawo.

Yana shiga parlor din kasa ya tara da Afaf ta fito tana shan bakin shayi da burodi yayinda sauran yaran suke zaune suna kallon TV.

Bayan ya amsa sannu da zuwansu ya karasa ya zauna a kusa da Shukra, ya kalli kofin shayin Afaf wanda ta ajiye a kusa da ita tana kokarin sake yago burodi. Yace ‘Ya kike shan bakin shayi Yaya?’

Tace ‘Um, babu madara a nan dama idan nayi canjin kudin makaranta ne nake siyo mana kuma yanzu ka ga ina hutu shi yasa bani da kudi.’

Takaici ya cikashi, yanzu da ransa da lafiyarsa madarar shayi ace sai Afaf ta tara kudin makarantar da yake bata ta siya sannan zasu sha. To wai ina kansa ya shiga hakan take faruwa a gidansa? Tunda yake a rayuwarsa bai taba ganin Khadeeja ta hana yaranshi wani abu da ya siyo ba, sai dai ma ya san lokutan da take sayen abu da kudinta su ci ita da yaran. To wai yaushe ma Khadeeja ta bar gidan?

PAGE 233

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ba a fi wata takwas ba fa da rabuwarsa da Khadeeja amma gidan duk ya zama haka? Ita da take zama cin abinci a tsakiyar yaran balle a ce ta boye wani abu ta hana su.

Ya bi fuskar yaran da kallo gaba dayansu babu wadda take da cikakkiyar walwala, tabbas yanzu ne zasu ji nauyin maraicinsu. Shi kanshi sai ya ji kwalla tana neman kwace masa, sai da yayi da gaske sannan ya mayar da kwallar. Ya dubi Nasreen yace ‘Nas dauko min kofi nima na sha shayin.’

Ta tashi ta shiga nan kichin din kasan ta dauko masa tsohon kofin tangaran ta kawo masa da sugar a ‘yar roba. Ya kalli kofin duk ya dafe ya dubi Nasreen din da ta ajiye kofin yace ‘Kije sama ki dauko min wani kofin mai kyau.’

Tace ‘Abba Anti Naja fa tace kada mu hau kuma wallahi idan na hau zagina zata yi in nayi magana tace na mata rashin kunya, sai dai ko yaya Afaf taje ta dauko.’

Haka ya karbi kofin ba don ya so ba ya hada bankin shayi ya sha tare da ragowar burodin da suke ci. Sai da ya gama sannan ya tashi ya haye sama domin ya shiryo ya fita aiki.

……..

Ta ji dawowarsa tunda ya shigo da motarsa, sai dai da ta ji shiru ta saka rai ya tsaya a wajen yaransa don ya kara jin abubuwan da zasu gaya masa a game da ita. Don haka a parlor ya sameta tana ta cika tana batsewa ita a dole kada yayi mata fada. A gajiye yake sannan bashi da karsashin hayaniya da ita, don haka ko inda take bai kalla ba ya shige daki ya fara shirinsa.

A shirye tsaf ya fito dauke da jakarsa, tana nan zaune a inda ya barta. Ya dauke kai ya nufi kofa bayan ya amsa a dawo lafiyar da Rukayya tayi masa.

Ta mike ta nufoshi fuska babu walwala tana cewa ‘Ga abincinka can zaka fita baka yi breakfast din ba.’

Ya kalleta a fusace ba tare da ya daina tafiya ba yace ‘Abincin da kike hana yarana? Ni na koshi ki kirawo ragowar ‘yan uwanki ku cinye.’

Ta bude baki zata yi magana sai dai kafin tace wani abu ya ci rabin kafar benen, tana nan tsaye kamar zata hadiyi zuciya ta jiyo ficewar motarsa daga gidan.

Dole itama ta shirya ta fice ta tafi wajen aiki domin a hakan ma ta san sai an harareta tunda ta makara.

PAGE 234

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Kansa a cike yake saboda rashin bacci ga damuwa, don haka yana shiga office din ya rufo kofar ya kwanta a kan 3-seater din da take wajen.

Yana rufe ido ya fara nadama; ya aka yi ya saki Khadeeja? Ya aka yi ya bari har ta gama idda bai mayar da ita ba? Tunda dai ai da ya mayar da ita ya san bata da wani zabi dole ta zauna da shi tunda ba zata saki kanta ba. Tunda yake da Khadeeja bai taba ganin wata damuwa game da yaransa ba, gashi wata takwas kacal da ta barsu gidan yana neman ya gagareshi. A da yayi zaton Naja zata fita kulawa da su musamman yanda yaga tana nuna kauana garesu kafin ya aureta; to me ya canza mata ra’ayi har aka kai inda basu da damar da zasu ci abinda suke so a gidan ubansu? Lallai dole ya dau mataki.

Haka ya wuni a office din cikin rashin sukuni; yana tunani halin da yaransa suke ciki a gida sannan kuma ga shi zuciyarsa taki ta kyaleshi da tunanin Khadeeja. Tabbas da Khadeeja tana nan da babu yanda za ayi ya wuni a office yana tunanin halin da yaran suke ciki. Domin ya tabbatar duk halin da suke ciki to itama tana cikin wannan halin a tare da su. Ya tuno lokacin da tace ba zata yi musu girki ba yanda suka gaya masa gari suka sha kuma garin ma tare da ita suka sha. Yayi dariya a fili; tabbas Khadeeja tana da rigima amma ta iya rigimarta. Ya tabbatar babu yanda za ayi taci kaza ta bar yara da bakin shayi. Haka ya zauna yana aiki yana tuno rigimarsu da Khadeeja yana murmushi shi kadai. Bai taba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login