Showing 84001 words to 87000 words out of 99112 words
kenan.
PAGE 212
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Suna hada ido dashi hawayen da ta kasa fitarwa ya kwace, ta saki akwatin da take ja. Ahmad wanda yake tsaye a kusa da shi ya karasa ya rike akwatin yayinda ita kuma ta karasa ta fada jikin Baffa wanda yake binta da kallon mamaki. Ya rungumeta sannan ya dafa kanta wanda ta kwantar a kirjinsa yana cewa ‘Subhanallahi! Me ya faru da ku Khadeeja?’
Ta kasa magana sai kuka kawai take har da shessheka.
Baffa ya fara shafa bayanta yana cewa ‘Ya isa haka, ya isa, ki gaya min me ya faru?’
‘Ya sakeni.’ Ta fada a cikin shesshekar kuka kamar mai rada.
Take fuskar Baffa ta canza, ranshi yayi matukar baci. Yace ‘Mustaphan ya sake ki?’
Ta daga masa kai.
Ya sake shafa kanta cikin yanayi na lallashi yana cewa ‘To shikenan, ya isa haka.’
Ya ja hannunta suka shige gidan; da yake Mommy tana dakinsa kai tsaye can ya wuce da Khadeeja. Mommy tana kokarin yi masa sannu da zuwa ta kula da Khadeeja, tace ‘A’a, Baffa a ina ka samo wannan?’
Ya zaunar da ita a gefen gadonsa yace ‘Mustapha ya saketa.’
‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Saki kuma? A yau din? Na dauka ce min kika yi yau jirginsu zai tashi?’
Ta share ragowar hawayenta ta ajiye jakar hannunta sannan tace ‘Eh, kafin su tafi airport din ne ya sakeni saki daya.’
‘Lallai Mustapha, to me kika yi masa ya sake ki? Ko kuwa dai tsabar wulakanci ne yaga gara ya sakeki kafin ya wuce yayi ibada?’ Mommy ta tambaya tana daga tsaye.
Bata yi tunanin wata amsa da zata bayar idan an yi mata wannan tambayar ba, amma dai tana jin gara ta fadi gaskiya don ma kada ya zo shi ya bada amsa da ta bambanta da tata. Ta daga fuskarta suka hada ido da Mommy sannan ta sunkuyar da kai. Mury kasa-kasa tace ‘Ni nace ya sakeni.’
Saura kadan wayar da take hannun Mommy ta kufce ta fadi, ta rike wayar sannan tace ‘Kika ce ya sake ki Khadeeja? Saboda rashin hankali ko saboda me?’
Baffa da yake tsaye a gaban wardrobe dinsa yana rataye babbar rigarsa ya zagayo ya zauna a kusa da ita yana kallonta yace ‘Dije me yasa kika ce mijinki ya sake ki?’
PAGE 213
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Kafin ta yi magana Mommy tace ‘Saboda wulakanci mana, ko kuma saboda yace ba zai je da ita aikin Hajji ba sai ya je da amaryarsa.’
Kallonta kawai Baffa yayi ta yi shiru, ta gyara tsayuwarta tana binsu da kallo. Ya dubi khadeejan ya sake cewa ‘Deeje me yasa kika ce mijinki ya sake ki?’
Ta kalleshi suka hada ido sannan ta sake sunkuyar da kai tace ‘Baffa na gaji, wallahi Baffa baka ga zaman da muke yi a gidan nan ba. Tun kafin ya auri matarsa Baffa dama hakuri nake, matsayina a gidan da kadan ya wuce matsayin ‘yar aiki. Kuma bayan ya aurota ma ya kara tabbatar min da hakan; duk wani abu na walwala da jin dadi da ita ake yi amma wallahi idan aiki ne da wahala Baffa ni zai kawowa kuma dole na yi. Ita kanta matar tasa haka yake saka ni nayi mata aiki babu sannu bare na gode. Shi yasa kwanaki da nace ba zan yi ba ya zo ya kawo maka karata. Wallahi Baffa a lokacin sai da nayi wata takwas ina mata aikin gida da girki da kaomia kuma kullum shi a wajenta yake kwana.’
Ta sake sunkuyar da kai ‘Na gaji Baffa, baya sona, wulakancin da yake min suna da yawa, gara na hakura kawai shi yasa nace ya sakeni.’
Ya kama hannunta wanda take wasa da shi a kan cinyarta ya kalleta suka hada ido yace ‘To ya isa, kuka ya isa haka. Ki je ki kai kayanki daki ki huta mayi magana wani lokacin.’
Ta gyada kai ta mike ta fice daga dakin.
A fusace Mommy ta bi bayanta, cikin sauri Baffa yace ‘Zo mana.’
Ta juyo a daidai lokacin da Khadeejan ta rufe kofa, ya nuna mata inda Khadeejan ta tashi ta zauna. Sai da ya dauki lokaci yana kallonta sannan yace ‘Ki bita a hankali tunda dai kin ji bayaninta. Ni da na bashi aurenta ai ba ‘yar aiki na bashi ba ko? In ya dawo ya zo yayi bayani in ya so sai a san matakin da za adauka. Shi a zaman aure ma wani lokacin hutu kawai mutum yake bukata; kada ki je ki daga mata hankali. Ki barta ta huta karshenta in ya dawo sai dai kiji da kanta tana gaya miki ya mayar da ita zata koma. Da-Allah kada ki daga mata hankali tunda dai ita ta kawo mutumun nan tace tana so ai ba laifi bane idan ta dawo tace bata son shi. Ki bata lokaci ta sami nutsuwa tukunna.’
PAGE 214
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ta sauke numfashi sannan tace ‘To.’
Ta tashi ta fice ta barshi a dakin.
………
A nan gidan Hajia ya ajiye motarsa ya samar musu taxi wadda zata kaisu airport, ya shiga gaban mota ita kuma ta shiga baya. Suna kama hanya ta zaro wayarta ta lalubo lambar Anti Wiyya ta tura mata sako ta wahtsapp tana sanar da ita an saki Khadeeja. Bayan sun gama hirarrakinsu na murna da nuna jin dadi Anti Wiyya ta turo mata sako kamar haka “Kije kiyi ta addu’a Allah ya sa kada kuna dawowa ya dawo da ita. Nan ma in sha Allah akwai wani malami da zan kaiwa abin sadaka yayi miki aikin da ba zata taba dawowa gidan ba, kin ga ki ci gida se yanda kika yi.”
Ta turo mata emoji na dariya ta rufe wayar, ta mayar da hankalinta kan hanya zuciyarta fes cike da fatan Allah ya sa kada ya dawo da Khadeeja tunda ya ce saki daya ne; in ya so sai ta ji da yaran kawai.
………
A hankali Khadeeja ta baje kayanta a gida; ta sanar da Baffa ko da ya dawo ma ba zata koma ba domin ko ya mayar da aurenta to kotu zata kaishi ya saketa. A haka dai aka bar maganar domin shi Baffa gani yake kamar idan aka bata lokaci ta huce zasu yiwa kansu sulhu ita da shi.
Tun Baffa yana sa rai zai ji kira daga wajen iyayen Mustapha sun biyo sawu har ya fitar da rai. Saura kwana biyu babbar sallah suna zaune a parlor shi da Mommy suna hira yace ‘Mutanen nan dai shiru, babu wanda ya biyo sawun Dije. Na san dai babu yanda za ayi suce basu san ya saketa ba tunda ai zasu ga ba ita ya barwa yaransa ko?’
‘Uhm, ni abun har ya isheni ma wallahi. To amma ko tuntubarsu zaka yi ka ji, tunda ai ba zamu taru mu zama daya ba ko?’ Mommy ta bashi amsa.
Yayi ‘yar dariya yace ‘Babu wanda zan tuntuba tunda ai da zan basu aurenta ba ni na tuntubesu ba su suka zo har gida suka tuntubeni. Idan na tuntubesu hakuri zan basu ko me? Ni aka yiwa wulakanci aka saki ‘yata ko ma don wanne dalili ne amma kuma ni ake jira nayin magana? To su cigaba da zamansu kada ma su zo inda nake.’
A haka suka bar zance domin Mommy ta san in dai Baffa ne yanda ya kafe ba zai yi magana ba to tabbas ba zai yin ba.
PAGE 215
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Suma daga can gidansu Mustapha a tunaninsu Baffan Khadeeja ne ya kamata ya nemesu don ya kamata idan ta je gida a bincika a ji, sai dai har aka shiga hidimar bikin sallah babu wanda ya neme su. Sai suka bar maganar kawai suna jiran Mustaphan ya dawo su ji ko shi yayi magana da iyayen nata.
...........
Suna daga cikin na farko-farkon dawowa a alhazai. Tun kafin su baro masaukinsu ta gama magana da shi a kan ba za adauko yara ba sai tayi kwana biyar tana hutawa, don Rukayya ma tace kada a dawo da ita sai bayan sati biyu. Abokinsa ne ya daukosu daga airport ya kaisu har gida, da yake ya saka Habib ya bude gidan an gyara tsaf suka sami ko ina.
Da safe suka sauka don haka kafin su shiga gidan sai da suka yi order din abincin rana. Sai can da yamma bayan sun gama hutawa sannan ya shirya ya wuce gidan Hajia. Nan ya zauna suka yita hira a wajen Hajia. Duk da ya gaya musu ba yau zai tafi da su ba amma Shukra ta kafa a kan ita a ranar take son ta bisu, don haka yace su shirya tare da su zai tafi.
Sai bayan sallar magriba sannan Alhaji ya dawo, bayan sun gaisa suka cigaba da hirarrakinsu. Alhaji yace ‘Yauwa, ya wajen Khadeeja kuwa? Kun yi magana ne?’
Yace ‘A’a ni ban nemeta ba kuma ba zan nemeta ba Allhaji, itace fa tace na saketa kuma na saketan, taje ta dana zaman gidan.’
Alhaji ya dan bata rai yace ‘Kai! Ba a yiwa mata haka, idan jira kake ta nemeka to ba lallai ta nemeka ba gara ma kaje idan da wani abu ka yiwa iyayenta bayani su yi mata fada ka mayar da aurenta.’
Ya jijjiga kai ‘Alhaji ni ba inda zan je, idan tana son auren nata zata nemeni tunda ai da kanta ta nemi sakin.’
Haka Alhaji ya saka shi a gaba yayi ta yi masa nasiha, daga baya yayi musu sallama ya kwashi yaransa suka wuce.
………..
Ba shi kadai ba hatta yaran ma saida suka gane bata ji dadin dawowarsu a ranar ba, haka dai suka gaggaisa suka yi mata sannu zuwa kowa ya shiga harkarsa. Inda Allah ya taimaketa ma shine ya siyo musu abincin dare.
Ta rigashi kwanciya saboda gaba daya bata ma jin dadin jikinta, sai da suka gama hira shi da yaransa sanan ya rufe gidan kowa ya tafi ya kwanta.
PAGE 216
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Motsin shigarsa daki shi ya tasheta daga bacci, sai da ta bari ya gama shirins ya kwanta sannan ta gyara kwanciya tace ‘Kai da muka yi da kai ka bar yara sai mun huta shine ka taho da su?’
Ya gyara kwanciyarsa yace ‘To sun ce zasu taho, suma fa ba dadin zaman suke ji ba a wani wajen kin san kowanne yaro ya fi son gidansu.’
Ta kula idan dai a kan yaransa ne ba zai saurareta ba don haka ba tare da ta ce komai ba ta juya masa baya ta cigaba da baccinta; amma dai ta san tabbas dole ta dauki mataki don babu yanda za ayi ta bari ya kori kishiyarta kuma ya mayar da yaransa kishiyarta. dole ta dauki mataki.
Sai da tayi sati da dawowa sanna taje gidansu ta taho da Rukayya, don ko ‘yan gidan nasu ma da zasu zo musu sannu da zuwa cewa tayi kada a zo da ita don idan ta zo ba zata yadda ta koma ba.
Bayan ta gama hirarta a gidan ta wuce gidan Anti Wiyya; nan suka zauna tayi mata bayanin ayyukan da ka yi mata, sannan ta bata wasu layu guda biyu tace ‘Gasu nan hatimi ne aka rubuta da ayoyin Allah, ki sami waje ki konesu kurmus sai ki zuba masa tokar a miya. In dai ya sha miyar nan to ba zai sake yi miki musu ba. Wannan aikin bana haufisa kamar yankan wukane sai dai idan baki aikata ba.’
Ta karba ta mayar cikin ledarsu ta kulle ta jefa a jaka tana cewa ‘Ai dai kin ce ayoyi ne ko?’
Tace ‘Wallahi ayoyi ne, ke malamin fa har almajirai gareshi suna karatun allo. Ai idan kin haihu zamu je ki gani da kanki idan har kina da wata matsala.’
‘Hmm! Ai dole ma nayi Anti Wiyya, daga dawowarmu ya fara neman ya nuna min iyakata a kan yaransa, gashi su baka isa ka saka su aikin komai ba sai dai kai ka kare a hidimarsu. Ai yau din nan zan aikata wannan layun kowa ya shiga hankalinsa. Ko nan ma fa da zan taho shi so yayi na taho da su wai saboda kada na barsu su kadai, ki ji don Allah sai kace wasu jarirai.’
‘Ya zata kema Khadeejan ce.’
Suka yi dariya gaba daya.
Sai gefin magriba sannan ta dauko Rukayya suka dawo gidan. Tana zuwa tadora abincin dare imda ta dafa tuwo miyar kuka.
PAGE 217
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Tsaf ta hade tokar layun nan ta juye masa a miya ta juya komai ya shige, tayi sa’a kuma ya sami tuwon nan yayi masa cin koshi.
A hankali ta fara ganin kyawun aikin da Anti Wiyya ta yi mata. Cikin wata daya da dawowarsu ta tattare kayanta ta koma sama part dinshi, bata son tayi maganar part din Khadeeja sai ta bari wata uku ya cika saboda kada ma ta tuna masa yaje ya dawo da ita. Yanzu ta samu idan suna sama shi da ita ta hana yaran hawa kuma ya kasa yi mata magana. Ta san bai ji dadi ba don yana nuna mata a fuska amma wannan ba damuwarta bace, kuma idan shi ya zauna a kasan da zarar ta kirawoshi haka zai tashi ya bi bayanta su koma saman da shi da ita da Rukayya, sauran yaran suna kasa. Sai dare yayi idan zasu kwanta ne suke hawa saman da yake dakinsu yana can. Suna hawa sai ta kadasu su wuce daki su kwanta.
………..
Tun ranar da ta koma gida take lissafi, duk da dai tana jini a lokacin amma dai sai da ta lissafa jini uku, kuma jiya ne ranar da ta fita daga jini na uku bayan rabuwarsu da Mustafa.
Tana zaune a gefen karamin gadonta wanda shine dai gadonta tun kafin ta auri Mustapha, ta rufe fuskarta da tafukan hannunta tana tunanin yanda rayuwarta zata cigaba; tabbas ta ji dadin rabuwa da Mustapha, bata yi nadama ba kuma ba zata koma ba. Domin ko babu komai yanzu ne ta tabbatar tana cikin nutsuwa. Duk wani abu na kulawa da Hammad yake bukata zata iya yi masa don haka ba zama ta nemi Mustaphan da maganar Hammad din ba saboda ma kada yace ta bashi yaronsa. Fatan ta daya Allah ya tabbatar mata da alkahiri a cikin rayuwarta ta nan gaba; duk da bata tunanin akwai namijin da zata sake aure. Ba zata yarda a sake yi mata yanda Mustapha yai mata ba kuma bata fatan ta zama dalilin da zai saka wani namijin ya mayar da matarsa kamar yanda Mustapha ya mayar da ita bayan ya kara aure.
A hankali ta mike ta fito daga dakin. Ta ji dadi da ta sami Baffa da Mommy a parlor suna zaune suna cin abinci. Bayan ta gaishesu ta dubi Baffa tace ‘Baffa ian so a debo min kayana na gidansu Hammad.’
Ya ajiye cokalinsa yace ‘Ikon Allah, bai nemeki ba kenan?’
PAGE 218
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
‘Eh Baffa, duk da ma ko ya neme nin ba zan koma ba. Jiya ne na gama iddata ka ga auren ma ya kare kenan.’
‘Hakane, Allah ya sa haka ne ya fiye muku alkhairi gaba dayanku. Gobe sai kaninki ya shirya suje a kwaso miki kayan, kiyi masa bayanin abubuwan da zasu kwaso.’
‘To Baffa.’
Mommy tace ‘To ya za ayi da Hammad? Ai dai ya kamata ayi magana da Mustaphan ya dinga turo abinda za a kula masa da yaron ko?’
Tace ‘Eh bamu dai yi magana da shi ba, amma da bari nayi sai zai shiga makaranta tukunna.’
Baffa yace ‘A’a tun yanzu zai dauki nauyin dan sa, ni zan nemeshi in sha Allahu.’
Mommy tace ‘Hakane kam, ba sai daga baya ba azo ana sa toka sa katsi.’
Suka karasa hirarrakinsu sanna Khadeeja tayi musu sallama ta tafi office.
……….
A mota suke tafe yana tukasu, zai sauke Naja a wajen aikinta sannan ya wuce. Wayarsace ta fara ringing, kusan a lokaci guda suka kalli screen din wayar “Babe” shine sunan da yayi saving lambar Khadeeja da shi tun kafin aurensu kuma rabuwarsu ma bata saka ya goge ba. To me ya manatar da shi Khadeeja ma da bai ko da kirawota a waya ba tun bayan dawowarsa daga aikin Hajji? Ko da yake ba mantawa yayi ba jira yake ta kirawoshi ta bashi hakuri idan ba haka ba ma ya kyaleta ta dandana zawarcin daga baya ya koma a sake daura musu aure idan ta gane shayi ruwa ne. to menene take kiransa yanzun? Ko har zawarcin ya isheta ne? Watakila kuma ta ga taba daf da gama idda ne bai nemeta ba shine ita take nemansa ya zo a daidaita.
Ya dauki wayar ya amsa sannan ya kara a kunnensa a daidai lokacin da ya kaucewa hada ido da Naja wadda take ta faman binshi da kallo saboda ta san lambar wacece yayi saving da sunan Babe.
PAGE 219
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Babu wata alamar nadama ko kuma damuwa a muryarta, cike da walwalarta suka gaisa kamar babu wani abu na rashin dadi da ya taba hadasu. Bayan sun gaisa tace ‘Na gama idda jiya, so in sha Allahu idan babu damuwa gobe zan turo Ahmada zasu zo su debar min kaya na. kayan da suke bedroom din kawai za a dauka tunda dama duk na sabon gida ne ka saka, amma akwai food flasks dina a kitchen guda uku da kuma tea flask da zasu hado min da su shikenan. Ina fatan babu wata damuwa.’
Sai da ya bude baki da niyyar bata amsa sannan ya gane yawun bakinsa ya riga ya kafe, ya kifta ido ya dan lalubo yawun bakin nasa sannan ya kalli Naja wadda take ta faman binsa da kallo kamar