Showing 6001 words to 9000 words out of 99112 words

Chapter 3 - Mijin Marigayiyya Part Complete Hausa Novels.docx

17 Sep 2025

66

amma fa hawayenta ya ki daina zuba harda shesshekar. Ta cigaba da shafa bayana tana lallabata yayinda Nasreen ta koma ta kwanta har bacci ya fara daukanta. Abbansu ya ya turo kofa ya shigo dakin, Shukra ta leko ta kafaradar Khadija cikin shessheka tace ‘Abba tea zan sha.’

Ta kwace daga jikin Khadijan ta sauko ta taho wajensa, ya rage tsawo ya dauketa ya rungumeta yana cewa ‘Ya isa, Anti bata baki shayin ba?’

'Tace sai da safe.’ ta fada tana shessheka.

Ta mike ta rungume hannuwanta a kirjinta ta kalleshi da fuskar tausayi tace ‘Babe, ka barni da ita zata koma bacci kuma a hankali zaka ga ta ma daina farkawan shan shayi da daddaren. Ka barni na lallabata idan tayi bacci zan taho.’

Kallonta yake da mamaki a fuskarsa, sai da ta gama sannan yace ‘Yunwa fa take ji, haka zata kwana da yunwa. She's only 3, idan ta girma da kanta zata daina duk yayyenta ma haka barsu take raininsu.’

Cikin kosawa tace ‘Kai dai ka barni da ita mana, I promise you she will be just fine.’

Ta karaso kusa da shi, ta mika hannu ya dafa kafadarta yana cewa ‘Kin ga, ki yi hakuri ki hado mata shayi kada ki sakata kwana da yunwa tunda bata saba ba. A hankali zaki ga da kanta zata daina.’

Murya kasa-kasa tace ‘Ohkk!’

Ta wuce ta barshi a nan ta nufi kitchen; tea at 1pm, wannan wane irin tashin hankali ne? Idan da ya kyalesu ta san tabbas zata rabata da wannan shan tea din amma har wani cewa yakeyi kada ta barta da yunwa. Ta karasa kitchen din ta hado mata tea a kofi ta daukonta fito.

Tana zuwa ta sameshi zaune a gefen gadon ragowar yaran duk suna ta baccinsu yayin da yake zaune rungume da Shukra; har bacci ya fara dibanta amma tana shiga ya dagata yace ‘Yauwa Baby tashi ga shayinki.’

Ta tashi tana muttsike ido, ya mike tsaye ya nunawa Khadijan wajen ta yana cewa ‘Zauna sai na ajiye miki ita idan kin gama bata tayi bacci kya taho.’

Ya ajiye mata ita a kan cinyarta ta fara bata shayin sannan ya fice ya barsu.

Bayan ta gama bata shayin ta sakata tayi fitsari sannan ta kwantar da ita ta dan jijjigata bacci ya fara kwasarta sannan ta wuce dakin. Ko da ta shiga dakin ya riga yayi bacci, don haka ba tare da ta kunna fitila ba ta lalubi waje ta kwanta a gefen gadon. Motsin kwanciyarta ne ya farkar da shi, ya dan matso ya rungumota ta baya yana sumbatar bayan wuyanta. Ta dan motsa tace ‘Mmmm!’

Yace ‘Kin San gobe yara zasu school ko? Sai ki tashi da wuri don ki shirya su.’

A take jikinta yayi sanyi; gaba daya ma ta manta da wannan tunda ita ta riga ta sanar da kawarta su yi mata attendance ba zata koma ba sai tayi sati.

Ya cigaba da lalubenta tana kokarin zamewa, saboda ita gaba daya ma komai ya fita daga ranta; a halin yanzu ma kuka take son yi. Sai dai haka ta hakura ta barshi yayi yanda ya so sannan ta kwanta tana fargabar yanda zata tashi nan da awowi kadan ta cigaba da hidima.

Ana fara kiran assalatu ya tasheta daga bacci, sai da tayi da gaske sannan ta iya saukowa daga kan gadon. Tayi alwala ta wuce kitchen tunda da dan sauran lokaci kafin a tada Sallah. Ta tsaya a tsakiyar kitchen din tana tunanin inda zata fara; a hankali dabara ta fado mata; macaroni da sauce zata dafa musu in ya so sai ta dafa indomie da kwai suyi breakfast. Nan da nan ta dora sannan ta debo tsofaffin flasks dinsu da ta gani a store ta wanke sannan taje tayi Sallah.

Ta zata idan ya dawo daga masallaci zai tsaya ya tayata shiryasu amma ga mamakinta sai ya wucesu a parlor ya koma daki ya kwanta ya cigaba da baccinsa.

7:15 am ta gama komai duk ta yi musu wanka sun shirya, suka zauna a dining table ta kawo musu abinci ta zubawa kowa Indomie da dafaffen kwai guda daya. Daga fuskokinsu ta san ba indomie suka so ci ba, suna cikin cin abincin yayinda ita kuma take zaune a table din tana bawa Shukra a baki Nasreen ta kalleta tace ‘Anti da ma dankali da kwai kika soya mana.’

Ta kalleta tana murmushi tace ‘Saboda kar ku makara shi yasa nayi sauri na dafa Indomie, but in sha Allah weekend idan babu makaranta sai a soya muku dankali kin ji. Yanzu maza ki cinye kafin Abba ya fito ya kai ku school.’

Suka cigaba da cin abincinsu. Jimawa kadan Abbansu ya fito yana rike da mukullin mota, suka hada baki gaba daya suka gaisheshi. Bayan ya amsa yace ‘Maza ku gama mu wuce a school kada ku makara.’

Ya kula da ragowar kwai a plate din kowa banda Habib, ya dubeshi yace ‘Kai ina naka kwan.'

Yace ‘Shi na fara cinyewa Abba.'

Nasreen tace ‘Abba ni ina son dankali, Anti tace ba za a dinga soya dankali ba sai weekend.’ Ta langabe kai kamar abun tausayi.

Ba tare da ya kalli Khadeejan ba yace ‘No, za a dinga soyawa kada ki damu, maza ki ci abinci mu tafi.’

Tana jinsu ta kawar da kanta, don sai dai idan shi zai dinga tashi ya soya ita bazata iya soya dankali da sassafe ba. Nan da nan suka gama; Habib ne ya fara mikewa har ya juya tace ‘Dauke plate dinka da cup din ka kai kitchen.’

Ya dauke plate din ya tafi da shi, suma ‘yan uwan da suka ga haka kowa idan ta mike sai ta dauke plate dinta ta wuce da shi.

Suma ‘yan uwan da suka ga haka kowa idan ta mike sai ta dauke plate dinta ta wuce da shi. Suka karasa shiryawa suka fice tare da Abbansu.

Kafin ya dawo ta soya dankali da kwai ta jera a dining table sannan ta wuce daki; wanka zata shiga sai kuma ta tuna ko da ta yi wankan dai kitchen zata shiga tayi wanke-wanke ga shara, don haka taga gara ta bari idan ta gama aikin ta yi wankan.

Sai da yayi wanka ya shirya sannan ya fito a shirye, kai tsaye ta riga ta shirya abincin a dining table don haka suka zauna. Yana bude kwanon yace ‘Sai da suka tafi kuma kika soya dankali? Sun fi son soyayyen abinci idan zasu tafi school.’

Ta dan langabe kai ‘To ai Babe ba zan iya soya wani abu before 7am ba, da ace ma dai ina da mai aiki ne. Amma hakan ma weekend zan soya musu in sha Allah.’

‘To ai da kin bari sai weekend din ma ci gaba daya, yanzu idan sun dawo ai zasu ga bawon ba dadi ai kuma ma Shukra zata gaya musu tunda ita taci. Mai aikin ma kuma za a dauka.’

'Uhm.'

Suka cigaba da cin abincin ba tare da kowa ya ce komai ba.

Gaba daya ma abincin sai ya fice daga ranta; kenan duk abinda ba zata bawa yaransa ba baya so ita ta ci. Haka tunani kala-kala suka yi ta yawo a kanta.

Ya gama cin abincin ya fice ya barsu ita da Shukra.

Sai wajen 10am ya kirawota a waya, bayan ta dauka yace ‘Mantawa nayi ban gaya miki ba idan 1pm tayi sai ki je ki dauko yara daga school.’

Ta dan yi shiru don ta zata shi zai daukosu, tace ‘Ohk, but zan iya zuwa a kasa?’

'No, kin san school din ai ba nisa sosai amma dai ku hau a dai-daita sahu sai ki tafi da Shukra.’

'Ok.'

Suna gama wayar ta mike ta dora abincin rana don ta gama da wuri. Lokaci yana yi ta dauki Shukra suka tafi suka dauko yan makarantar. Suna dawowa bayan sun huta ta shiryasu suka tafi islamiyya.

Dab da magriba ya dawo. Bayan ya huta yana zaune a parlor shi da yaran tana jiyoshi yana tambayar Afaf abinda aka yi da baya nan, an dauko su da wuri daga school? Sun ci abincin rana? Me suka ci? Sun makara a islamiyya? Haka dai ya cigaba da tambayoyinsa tana kitchen tana jiyosu, kamar ta fito tayi magana sai kuma ta share ta cigaba da abinda takeyi.

PAGE 20

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

A haka suka karasa satin nan tana bakin kokarinta wajen kula da yaran nan gaba dayansu.

Ranar Juma'a suna gida da yake yara babu islamiyya; ranar ne kuma suke gyara gashin yaran mai kitso zata zo. Tun da wuri Afafa ta tsefe nata kan, ita kuma Shukra da yake tun suna makaranta Khadeejan ta tsefe mata babu wanda ya ji kansu. Tun da suka gama cin abincin rana take faman lallaba Nasreen ta bari a tsefe mata amma har aka kusa kiran la'asar guda biyu suka tsefe. Bata son a taba gashinta kwata-kwata don haka taki ma zama a tsefe.

Khadeeja ta kamo hannunta tace ‘Zo kin ji Nas, kin ga fa Shukra zata fi ki kwalliya tunda ta tsaya an gyara mata nata.’

Ta zauna, har an fara tsifar ta zame kanta ta matsa tana zumbura baki. Afaf tace ‘Anti wallahi idan baki zare mata ido ba haka za kiyi ta fama da ita, sai ayi sati ana tsefe kanta a gidan Mama.'

Ta cigaba da lallabata amma sam ta ki tsayawa; don haka ta kama hannunta ta zaunar da ita tana cewa ‘Idan kika sake tashi sai na zaneki Nasreen, ko na sa almakashi na aske gashin kan ya koma kamar na Yaya Habib.' Ta dubi Afaf tace ‘Yaya Afaf dauko min slippers mai zafi idan bata tsaya an tsefe ba zaneta zan yi.’

Da sauri Afaf ta dauki slippers ta zo ta ajiye a gaba Nasreeen wadda ta fara shesshekar kuka tana fizge-fizge. Khadeeja ta dan rike gashin tace zan dake ki fa Nasreen, ki rufe min baki bana son jin kukanki.’

Nan da nan ta hadiye kukanta tana shessheka aka cigaba da tsifa Shukra tana mata dariya.

……….

Daga masallacin Juma'a ya wuce gida don ya gaida Hajia, da ya gaisheta sai ya wuce gida don Khadeeja tace idan ya dawo zai kaisu saloon ita da yara a wanke musu kai da yamma kuma akwai mai kitso a makota dama ita take musu.

Yana shiga gidan ya sami Yaya Jidda da yaranta biyu ‘yan mata Naja da Farida, bayan sun gaisa gaba daya Yaya Jidda ta dubeshi tace ‘Gidanka fa zamu tafi yanzu ni da yara, Hajia tace muje mu dubo su Afaf.'

Yace ‘To ai sai ku tsaya mu tafi, don nima gaisawa kawai zamu yi na wuce.’

Kafin minti goma sun gama, suka shiga mota ya ja su suka kama hanya, suna tafe suna hira.

'To ya yaran? Ana kula da su dai ko?’

PAGE 21

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta tambayeshi.

'Ah Alhamdulillah, gaskiya tana kokari.’ Ya fada cike da fara'a.

'To ai haka ake so, Allah ya sa ta dore.’

Tun a bakin gate yayi honk, gaba daya yaran suka fito banda Nasreen. Habib ya tayashi bude gate, bayan ya shigo da motar gaba dayansu suka yi masa sannu da zuwa.

A nan suka fara gaida Yaya Jidda, bayan ta amsa tace ‘Ina Nasreena?’

Afaf tace ‘Tana ciki tsifa Anti Khadeeja take mata.’

Suka wuce gaba daya suka shiga gidan; kafin Khadeeja ta amsa sallamarsu Nasreen ta fizge kanta wanda saura daya a gama tsefeshi ta tashi tana share hawaye tace ‘Abbaaa.’ ta fada tana zumbura baki.

Da sauri ya rungumeta ‘Ya haka na ganki wujiga-wujiga? Wa ya taba ki?’

Shukra ta tintsire ta dariya ta daga slippers din da aka ajiye tace ‘Kukan tsifa take Abba shine Anti zata zaneta da slippers, kaga nawa Anti yalash din ko kuka ban yi ba har aka tsefe yanzu za mu je saloon smma banda ita. Anti tace tunda bata so a taba kanta askeshi zata yi kamar na Yaya Habib.'

'Sannu da zuwa Yaya.’ Khadija ta fada tana karkade jikinta.

'Yauwa.' ta amsa ba yabo babu fallasa.

Ta kare musu kallo tana kokarin zama tana cewa ‘To yanzu Kuma tsifar ce sai an yi zaniya ni ‘ya su?’

Kafin Khadeeja tace wani abu Afaf tace ‘Anti wallahi idan aka biye mata sai an yi sati ana wannan tsifar, kullum haka ake fama da ita.’

Khadeeja tace ‘Ai ba a ma yi zaniyar ba ta bari an tsefe.’

Ta tsuguna ta gaida ita yayinda shi kuma ya ja hannun Nasreen din suka shige ciki.

Sai da ta kawowa Yaya Jidda ruwa sannan ta bi shi dakin. Tana shiga ta sameshi a tsaye yana cire kaya yayinda Nasreen take kwance a kan kujerar dakin, kafin tace wani abu yace ‘Wai me yasa ne sai an yi duka sannan za a yi tsifar? naga tun tuni dama ana mata kitson ban taba ji an doketa ba.’

Tace ‘Yanzun ma ba a doketa ba, ko Nasreen? Ta dai ki tsayawa a tsefe ne na takurata na tsefe mata, amma ba ayi duka ba.’

Ya kawar da kai ‘Ni dai bana son dukan yara, don Allah duk abinda yaro yayi kada a dokar min shi. Uwarsu ma bata dukansu, bana bari gaskiya.’

Ta sunkuyar da kai cikin kosawa tace ‘In sha Allah za a kiyaye.’

PAGE 22

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ta ajiye masa ruwan da ta kai masa tana cewa ‘Lunch dinka yana nan a table.’ sannan ta fito ta barshi a dakin.

Bayan ta dawo parlor din ta tarar Yaya Jidda tana ta yiwa Afaf tambayoyi, ta wucesu ta shige kitchen.

Ta tsaya a tsakiyar kitchen din gaba daya kanta ya kulle; daga shigowarsu suna nema suce ta doki Nasreen, to yanzu haka suke so a bar Nasreen din ta dinga yawo da kanta? Gashi Afaf tace makarantarsu ana duba kitso duk ranar Monday. Ta jijjiga kai ta karasa ta dauki saucer ta zuba cake da cin-cin ta debo lemo a fridge ta jera a tray ta kawowa Yaya Jidda da yaranta, bayan ta ajiye a gabanta tace ‘Ya wajen su Hajiya?’

'Lafiya kalau.’ Ta amsa ba yabo babu fallasa.

Sukayi shiru sai surutun Afaf da take ta bawa Naja labari. Shukra ta matso ta kwanta a jikin Khadeeja tace ‘Anti nima lemon.’

Ta shafa kanta ta dubi Afaf tace ‘Yaya ki dauko mata lemon wanda babu sanyi.’

Ta mike, har ta kama hanyar kitchen din Yaya Jidda tace ‘Ku ba zaku sha lemon ba?’

Afaf tace ‘Ai da shi muka je school.’

Shukra tace ‘Anti tace idan an kawowa baki abinci mutum ya daina cewa zai ci, ni ma dai kawai lemon zan sha.’

Khadeeja tace ‘Ki dauko muku lemon idan kuna so.’

Jimawa kadan Abbansu ya fito daga dakin ya wuce dining ya zauna ya fara cin abinci; yana cikin cin abincin ya juyo yace ‘Kai Habib kun ci abinci ne?’

Yace ‘Tun dazu Abba, acici har tayi round 2.’ Ya fada yana zungurar Nasreen.

Khadeeja ta mike ta shige daki, don gaba daya jikinta yayi sanyi. Ta kula kiri-kiri neman laifinta ake yi; kamar ma Yaya Jiddan zuwa tayi ta binciketa. Ta karasa ta zauna a kan gadonta ta zuba tagumi.

Bayan ya gama cin abincin ya shiga daki ya fito da mukullin motarsa, ya dubi Khadijan yace ‘Idan kun shirya muje na Kai ku saloon din.’

Gaba daya suka fice harda su Yaya Jidda, ya ajiyesu a hanya sannan ya wuce.

………

Tun daga wannan lokacin kuma sai Yaya Jidda ta mayar da shi dabi'a, duk Juma'a sai ta zo gidan. Haka zata zauna a parlor tayi ta kare musu kallo tana kula da duk wani motsinsu, ga tambayoyi wadanda idan ta gama yiwa yaran zata bi Khadeeja da neman karin bayani.

.........

PAGE 23

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Ranar talata ce Kuma a ranar Khadeeja take sa ran zata koma makaranta, tun dare ta sanarwa Mustapha. Ya amsa mata ba tare da wata matsala ba.

Haka ta tashi tun kafin asuba ta shirya yaran tsaf, suna tafiya makaranta tayi Maza tayi wanka sannan ta dan rage aiki don tana da lecture 9am.

Bayan sun gama breakfast ta mike daga dining table tana tattara plates din tana cewa ‘Babe bari na saka hijabi na sai kayi dropping dina a school.’

Yace ‘Ok, but kada ki bata lokaci don kada ki makarar da ni.’

Kusan a lokaci guda suka fito daga dakin kowa a shirye, sun kawo tsakiyar parlor ta dubeshi tace ‘Yau Kai zaka dauko yara ko? Don ni Ina da lectures 9am to 4pm.’

Ya dan bata rai cikin nuna damuwa yana cewa ‘I thought Zaki dawo ki daukosu, kin san ni sai 5pm nake tashi daga wajen aiki.’

'To ai ka ga nima sai 4pm.zan tashi, Kuma I can't miss these lectures don last week ma ka ga ban je ba. Gara dai ka sami wani ya dauko su kawai.’

Ya Bude motar ya zauna yayinda itama ta zauna a kujerar gaba, yace ‘To ai ko an daukosu ma wajen wa za a kawo su tunda ba kya gidan?’

'Haka ne fa, most days ma lectures dina har 4pm ne.’

Suka yi shiru na dan lokaci; gaba daya ma shi ya manta tana wata makaranta. Yanzu ya take so yayi da yaran? Wa zai daukosu Kuma wa zai zauna da su? Wannan ai shine an gudu ba a tsira ba.

Muryarta ce ta katse masa tunani tana cewa ‘Babe ka ga da muna da Mai aiki sai ta daukosu ta shiryasu su tafi islamiyya kafin na dawo; musamman idan Babba ce.’

Cikin jin dadi yace ‘kwarai kuwa, zan yiwa Yaya Jidda magana sai a sami Mai aikin kafin next week.’

'No, ka bari idan na yiwa Mommy magana zata sa a sami kla garinsu, mutanen suna da Amana sosai ga aiki.’

Ba tare da ya kalleta ba yace ‘Ki bari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login