Showing 21001 words to 24000 words out of 99112 words

Chapter 8 - Mijin Marigayiyya Part Complete Hausa Novels.docx

17 Sep 2025

67

abincin.

PAGE 54

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Yana yi yana kallon lokaci saboda kar a akirawo assalatu. Haka ya ci abincinnan yayi sauri ya kwankwade shayinsa rabin kofa sannan ya dora da ruwan sanyi duk a loakci guda. Yana ajiye kofin aka fara kiran assalatu, ya kwantar da kansa a jikin kujerar yana mayar da numfashi.

Shukra da take kan kujera tana gyangyadi bayan ta shanye shayinta ta taboshi tana cewa ‘Abba kashi zan yi.’

A dan zabure ya dubeta yace ‘Kashi Shukra?’

Cikin halin ko in kula tana murje idonta tace ‘Um.’ Ta fara kokarin sauka daga kujerar da take zaune.

Ya jijjiga kai cike da takaici; su wai yara ba a hutawa da hidimarsu ne? tunda ya dawo daga asibiti ake abu daya gashi duk yana neman fita daga hayyacinsa amma babu alamar sauki. So yake ma ya sami natsuwa ya turawa Khadeeja message ta whatsapp yaga ko tana online amma basu bashi time ba, a halin yanzu ma kansa ciwo yake ga bacci duk kansa ya cushe bai ma san ta ina zai fara ba.

Haka ya bi bayanta har bandaki, Allah ya taimakeshi bata ma nemi fo ba ya taimaka mata ta hau toilet tayi kashinta. Yana zaune a gefen gadonsu yajiyota daga bandakin tana cewa ‘Abba na gama.’

Gaban shi ya fadi da ya tuna wai shi take sa rai yayi mata tsarki; ya juya ya kalli Afaf wadda take baccinta hankali kwance. Ya san idan ya tasheta zata yi mata tsarkin to amma fa itama bata kwanta da wuri ba. Ya jijjiga kai ya mike bayan da ta sake maimaita masa ta gama a karo na uku. Haka ya tashi ya shiga bandakin ya wanke mata kashin ya wanko hannunsa ya fito ya canza mata kaya ya mayar da ita ya kwantar da ita a kusa da Habib saboda katifar kan gadon ta jike; zuwa lokacin masallatai duk sun riga sun tayar da sallah.

Yana fitowa daga dakin yayi alwala ya tada sallah a dakinsa, yana zaune a kan dadduma yana azkar Nasreen ta turo kofa ta shigo dakin, ta karaso ta fada jikinsa tana cewa ‘Abba na tashi, baka dawo mana da Anti Khadeeja ba?’

‘Eh, sai an jima.’ Ya fada yana tureta.

‘Ki je kice Ant….’ Sai kuma ya tuna Antin bata nan don haka ya gyara zance yana kokarin mikewa ‘Muje na wanke miki jiki ki canza kaya sai kiyi sallah.”

‘Abba ni yunwa nake ji.’

PAGE 55

MIJIN MARIGAYIYA

A HAUSA NOVEL BY SAKINA YAZID (INNAR SU AMAL)

Ya bata rai yace ‘Sai an canza kaya kuma kinyi sallah.’

Haka yayi ta fama da yaran nan, gashi ita Afaf ma fushi take da shi saboda bai tasheta sahur ba tunda Anti tana tashinta tana yin azuminta. Sai wajen karfe takwas na safe sannan ya tashi ya koma ya roko Baban Ummi ta shigo ta karbi yaran don yana son ya tafi asibiti wajen Khadeeja.

Yana shiga dakinsa ya zauna a gefen gado ya dannan mata kira.

------------

Haka Khadeeja ta kwana a asibitin karkashin kulawar Anti Iyami.

Tun dare likita ya gama da ita aka bata duk wasu magungunanta, ya sanar da Anti Iyami za a iya tafiya da ita gida. Don haka gari yana wayewa karfe takwas na safe Anti Iyami ta gama aiki zata tafi gida ta shiga dakin da Khadeejan take. Bayan sun gaisa tace ‘Yanzu akwai inda yake miki ciwo Khadeeja.’

Ta jijjiga kai tace ‘A’a, ko ina ya warware, yanzu ma na gama breakfast din da kika aiko min da shi.’

‘Ok, so ki kirawo Mustapha kice masa zan wuce dake gida sai mu tafi na kaiki gidan Mommy din.’

Bata son tayi magana da shi sai ta je gidansu don haka cikin sauri tace ‘Ai yanzu na kirawoshi bai dauka ba, ina jin yana bacci ko baya kusa da wayar amma na san da ya gani zai kira. Mu wuce kawai tunda tun jiya na gaya masa zamu wuce gidan.’

‘Ohk, to tashi mu tattara kayan mu wuce. Nima tun dare na kirawo Mommyn naki na sanar da ita, da safe ma munyi waya. Na dai ce mata kada ta kirawoki ne don duk lokacin da na shigo sai na sameki kina bacci, shi yasa nace ta bari idan kin tashi zan kirawota kuyi magan. But ba komai idan mun je zata ganki tunda mun shirya.’

Nan suka hada kayan Khadeejan wadanda daman ba yawa ne da su ba suka shiga motar Anti Iyami suka kama hanya.

PAGE 56

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Khadeeja tana zama a mota ta lalubo wayarta ta ska ta a silent ta jefa a jaka don bata so Mustapha ya kirawota a gaban Anti Iyami domin bata san me zai ce ba idan ya ji ta wuce gidan Mommy. Duk inda suka je checkpoint aka tsayar da su da anga uniform din Anti Iyami kuma ta nuna ID card sai a barsu su wuce, haka har suka isa gidan Mommy.

Tun suna asibitin Anti Iyami ta snar da Mommy zasu taho don haka kafin su isa an dorawa Khadeeja ruwan wanka, suna shiga ta wuce dakin Mommy inda Azumi mai aikinsu ta sirka mata ruwan a bandaki. Ba tare da bata lokaci ba ta fada wanka.

A parlor Mommy suka zauna da Anty Iyami; bayan sun gaisa sun jajantawa juna Mommy tace ‘Ina Mustaphan? Ai na zata tare kuke da shi.’

Ta gyara zama tace ‘Bai zo ba ma yau da safen duk da dai tace ta gaya masa nan zamu huto, amma don Allah kawata a duba yarinyar nan.’

Cike da kulawa Mommy tace ‘In sha Allahu kuwa, kema kin san ba zan barta haka ba ko akwai wata matsala ne da ta samu ko rashin lafiya.’

Ta jijjiga kai ‘Babu fa, kawai dai tace min tana son dawowa gida. Duk dai wasu tambayoyi da zan yi mata nayi ta nuna min babu komai, to amma kin ga akwai yaransa guda hudu. Watakila hidimar gida da ta yaran ce take mata yawa ga ciki shi yasa ta sume masa. Baccin da ta dinga yi kawai ya tabbatar min da cewa bata samun isasshen bacci wallahi, don shi yasa ma naki tashinta kuyi waya. Gaskiya ku bincika, ya nema mata mai aiki ko ya san yanda zai yi da yaransa.’

‘Umm! To kinga dai idan ma da wata matsala bata fada ba, koda yake kwanaki tace mai aikinsu bata nana abata aron Nabila amma Baffansu yaki amincewa. Watakila saboda babu mai aikin ne abun yayi mata yawa ga laulayi.’

‘Gaskiya dai ku duba, ko da zata koma ku barta ta huta ta sami natsuwa sannan kuma a daukar mata mai aiki.’

Suka karasa hirarrakinsu daga baya suka yi sallama Anti Iyami ta kama hanya.

.......

Bayan ta fito daga wanka ta tarar da farfesun kaza mai rai da lafiya wanda Mommy ta dafa mata sannan ga shayi mai kauri Azumi ta hada mata da burodi a gefe, cikin sauri ta gyarajikinta ta sa kaya sannan ta shimfida dadduma a gaban gado ta mike kafafu ta zauna ta fara ci.

PAGE 57

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

A nan Mommy ta shigo ta sameta itama ta zauna, sai da ta gama cin abinci sanna ta fara yi mata tambayoyi.

Bata boyewa Mommy komai ba ta sanar da ita halin da ake ciki, ta tabbatar mata cewa idan dai da mai aiki musamman babba wadda ba zata sata surutu ba. Sai dai ta kasa gayawa Mommy cewa gaba daya ma ko da da mai aikin ita ji take kamar ma Mustaphan baya kaunarta, gani take kamar yanda take zama kullum cikin hidima ya sa bata gane kulawarsa a gareta. Don haka ta bar wannan a ranta tana fatan idan an sami mai aiki ya zama suna samun lokaci a tare to zata fuskanceshi.

Muryar Mommy ce ta katseta tana cewa ‘To yanzu yaushe zai zo ya daukeki?’

Ta kalleta suka hada ido ta sunkuyar da kai sanna cikin muryar shagwaba tace ‘Mommy kin ga yanzu mai aikin bata dawo ba, kuma na gaya miki shi ba zai tayani komai ba kuma ba zai bari yaransa su tayani ba. Kawai ki barni sai bayan sallah ko kuma duk lokacin da mai aikin ta dawo ko aka sami wata.’

Mommy ta jijjiga kai tace ‘Na fahimceki, amma me kike so na gaywa Baffanku? Shi kuma Mustaphan wane dalili za a bashi na rike ki a nan din. Tunda dai ciki ya fice an riga an wake; kuma gaki nan kowa yana ganinki ras.’

Ta karyar da kai kamar abin tausayi tace ‘Umma ni dai don Allah ki san yanda zaki yi a barni na huta.’

‘To bari mu gani. Idan kuma akwai wani abun da Mustaphan yake yi miki wanda kike so a yi masa magan to kiyi gaya min.’

‘Babu komai tunda ma bai hana a dauki mai aikin ba, in sha Allahu da ta dawo ko kika samo min wata zan koma.,

Ta gyara zama ta kafa tagumi ‘Hmma, bari muga yanda zamuyi da Baffan naki tukunna.’

………

Sai da suka gama wannan hirar sanna ta tuna tunda suka shigo bata ma nemi wayarta ba, ta san yanzu haka Mustapha yana ta faman kiranta. Cikin sauri ta mike ta dauko wayarta daga jakarta, ai kuwa tana dubawa taga missed calls dinsa har guda goma sha daya.

PAGE 58

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Tana gani danna masa kira, ko ringing bata yi ba ya dauka ‘Hello, wai ina kika shiga ne naje asibiti ina ta nemanki? Na rasa mai bani tsayayyiyar amsa, sai ce min kawai ake kin tafi da Anti Iyami, na zata gida zata kawo ki na dawo gidan kuma baku zo ba. Kin san ina neman haukacewa na rasa wanda zan kira don ban san me zan ce musu ba.’

‘Subhanallah! Kayi hakuri Babe, wallahi ka ganni nan ai gidan Mommy ta kawo ni. Na kirawoka bata shiga ba kuma shine na jefe wayar a jaka na manta sai yanzu da na fito daga wanka na tuna.’

‘Amma shine baki gaya min ba? Kin san wulakancin da aka dinga yi min a checkpoint kuwa?’

Ta tausasa murya ‘Sorry Babe, wallahi laifina ne don tun a asibitin Anti Iyami tace na kirawoka sai wayar ta ki shiga.’

Ya dan saki numfashi ‘To me yasa baku taho nan ba ko kuma a jirani na zo? Me ya sa za a kai ki gidan Mommy?’

Ta dan yi shiru, shima bai yi magana ba yana sauraronta; ta murgude baki kamar yana kallonta tace ‘Ai ka san dai idan an haihu ana zuwa wanka gida, may be shi yasa da suka yi waya Mommy tace a kawoni gida.’

‘To kuma shine aka rasa wanda zai gaya min.’

Cikin kosawa tace ‘To ba gashi na gaya maka ba, kuma ai nace maka mantawa nayi.’

Ya dan ja numfashi ‘Uhm! To ya jikin naki? Shike nan an gama yi miki alluran?’

‘Na sami sauki, ga ragowar magungunana na taho da su daman yawanci na kwana bakwai ne. amma na sami sauki.’

‘To idan an bude gari sai na zo na daukeki, inaga ranar Saturday zasu dan bude mu, nan da kwana uku kenan.’

‘Uhm, to ka dai zo amma gaskiya sai bayan sallah zan dawo kafin nan na dan huta na gama arba’in tunda ka san shima barin ai sai an yi wanka.’

‘Barin, gaskiya ban taba ji ba. Ma’u ma fa su biyu tana yin barin amma na biyun babu wanda ma amuka gayawa a nan tayi zamanta ta cigaba da hidimarta. Hutawa kawai tayi na kwana biyu.’

‘idan ka zo dai mayi maganar.’

Ta tamabye shi yaran ya bata su suka gaisa sannan suka yi sallama suka ajiye waya.

……….

Tunda yake bai taba ganin son zuciya irin wannan ba, ya za ayi a dauke masa mata kuma ace sai bayan sallah zata dawo? Kawai saboda tayi bari. Asma’u ma ai tayi bari har sau biyu ma;

PAGE 59

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Asma’u ma ai tayi bari har sau biyu ma; na farkon shine bayan haihuwar Habib, bayan anyi mata wankin ciki a ranar suka dawo gida. Ko maganar taje gidansu ma ba a yi ba kawai dai an kawo mata kanwarta tunda dama tana da mai aiki. Na biyun kuwa ma bayan haihuwar Nasreen babu wanda suka gayawa, suna zuwa asibiti aka ce musu ya fice gaba daya ba sai an yi wankin ciki ba aka basu magunguna suka dawo gida. Kawai dai ya san ba zata koma dakinsa ba sai bayan kwana arba’in, kuma bashi da matsala da wannan. Amma su iyayen Khadeeja saboda son zuciya sai akwai su dauke ‘yarsu? Kuma ko gaya masa ba za ayi ba.

Haka ya gaji da sake-sakensa ya sake daga wayar ya kirawo Alhaji ya gaya masa, don bai gaya musu cewar a asibiti ma ta kwana ba yana so yaje da safen ya gani tukunna. Shima Abban ya nuna rashin jin dadinsa da aka tafi da ita, musamman da ya gaya masa basu ma tambaye shi ba suka tafi da ita. Bayan sun gama waya da Alhaji ya kirawo Ummansu itama ya sanar da ita.

Suma su Afaf saida yayi musu bayani don tunda ya dawo basu ganshi tare da Khadeeja ba suke ta faman yi masa tambayoyi.

Babu yanda za ayi ya iaya brin Khadeeja ta zauna a gidansu, ya suke so yayi? Ga lockdown an hana mutane fita sannan kuma su dauke masa mata. Kwana ukun nan ma da zai yi da yaran bai san ta ina zai fara ba don yana tuna yanda a kwana dayan nan suka gama firgitashi; ga gari a kulle balle ya kaisu gidan Umma. Gaskiya da an bude gari ranar asabar zai je ya dauko ta tunda dai ko shi ya tambayeta jiki ta ce da sauki.

Sai can da yamma dabara ta fado masa; ya dauki waya ya kirawo Baffan Khadija, bayan sun gaisa ya jajanta masa jikin Khadeejan sannan ya sanar da shi cewa ranar asabar idan aka bude gari zai zo ya dauki Khadeejan. Ba tare da matsala ba kuma Baffan ya amsa masa da hakan yayi, don haka cikin walwala ya karasa wuninsa. Bayan Ummi ta gama hada musu kayan shan ruwa shi da yara ta wuce ta tafi gidansu ta barsu.

---------

PAGE 60

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Tun bayan dawowar Khadeeja gidan sau daya Baffanta ya shiga dakin Mommy ya sameta yayi mata sannu.

Yana zaune a parlor bayan ya dawo daga sallar tarawih Mommy ta shiga ta sameshi, ta zauna a gefensa suna kallon labarai a tashar Aljazeera tare. Bayan sun dan taba hira yace ‘Dazu Mustapha ya kirawoni yana duba Khadeeja, ya ma ce min idan an bude gari ranar asabar zai zo su tafi.’

Ta dan gyara zama ‘Ranar asabar fa kwana uku kenan, haba ai sai ta kwana arba’in.’

‘A’ah to ai ni na zata sun gama magana da ita ne a kan hakan.’

Ta jijjiga kai tace ‘Gaskiya dai basu yi wata magana ba don da kanta tace min tana so tayi arba’in din. Suna zuwa da na sa ruwan zafi nayi mata wanka ta ji dadin jikinta da kanta tace a barta tayi arba’in din. Haba, kuma haka za a mayar da ita haihuwar fari babu wani gyara? Sai kace ‘yar tsana.’

‘To ai naga bari ne ba haihuwa ba.’

‘To ai Baffan Nabila bari ya fi haihuwa wahala sosai ma, sannan kuma na fari ne haka za a bashi matar ya ma kasa daga mata a kwana arba’in din.’

‘To naga dai ai matarsa ce ko? Ina laifi, kuma ma ai shima ba zai ce bai san wadannan hukunce-hukuncen ba tunda ga yara nan har hudu an haifa masa.’

Ta sake gyara zama ‘Ku dai yi hakuri Baffa a barta tayi kwana arba’in ko akalla talatin, kafin nan ta ji daidai a jikinta sai ta koma.’

Ya daga wayarsa ya cigaba da dubawa yana cew a’To ai shikenan idan ya zo sai kuyi masa bayani, ni bani da matsala da hakan.’

‘Yauwa, ai lalacewar zamanin ba ta kai an daina wanka da gyara a haihuwar fari ba. Amma dai idan ya zo sai kayi masa bayanin idana kana nan tunda ka ga kai ya nema, gara ku cigaba da magana man to man.’

Yayi dariya yace ‘To babu laifi.’

Ya san halin matarsa da kishi, yanzu haka haushi taji shi Mustaphan bai kirawota ya duba Khadeejan ba ko akalla ya gaya mata zai tafi da Khadeeja ranar asabar tunda ya san iatace zata shirya Khadeejan amman ya kirawo Baffa. Jimawa kadan kuma fice ta bashi waje.

______

Shi da yara suka zauna suka gama shan ruwan sanna ya sa Afaf ta kwashe kwanukan, nan suka zauna suka cigaba da kallo suna wasannisu.

PAGE 61

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Har lokacin kwanciyar bacci babu wanda ya bashi matsala a yaran.

Ya tasa su a gaba ya raka su dakinsu domin suyi shirin bacci; yana shiga dakin zarni ya doki hancinsa. Ya dubi Afaf yace ‘Ba naga Ummi ta fitar da katifun nan ba? Me yasa suke zarni?’

‘Ta fitar Abba, sai da yamma sannan ta shigo da su gaba daya. Ban sani ba ko katifar Habib ce bata bushe ba don bamu san anyi fitsari ba sai wajen la’asar sanna ya gaya mata Shukra tayi masa fitsari bayan asuba da ka kwantar da ita. Shine aka shanya, to ina jin itace bata gama bushewa ba.’

Ya karewa dakin kallo, ko shimfida ba ayi ba a kan gadon don haka ya sa Afaf ta yi musu shimfida yayinda shi kuma ya wuce dasu bandaki don suyi brush. Nan da nan kowa ya shirya bayan sun fito sun kwanta ya cewa Afaf ‘Wai sai yaushe katifun nan zasu daina zarni ne?’

‘Nima ban sani ba Abba, kuma fa idan baka saka su sunyi fitsari da daddare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login