Showing 24001 words to 27000 words out of 99112 words
ba haka gobe ma zasu sake yin fitsarin nan fa. Dama Anti ce kullum take tashinsu, Nasreen sau daya ita kuma Shukra sau biyu shi yasa basa yi a kwancen.’
‘To karfe nawa take tashinsu?’
‘Wallahi Abba nima ban sani ba, kawai dai tana tashinsu.’
Ya amsa sannan ya fito ya dawo parlo ya zauna; to shi yanzu ya za ayi ya san karef nawa zai saka su wani fitsari, gashi kuma ga dukkan alamu idan ya barsu suka cigaba da fitsarin nan a kwance to lallai gidan zai daina zaunuwa. To amma karfe nawa zai saka su? Watakila sai dai kawai idan ya tashi kwanciya bacci ya saka su shikenan.
Nan ya zauna a parlor din ya cigaba da kallonsa yana chatting, har ya sami Khadeejan ma online suka dan yi hira.
Basu fi awa daya da kwanciya ba ya jiyo kukan Shukra daga dakin, da sauri ya dire wayar da take hannunsa ya nufi dakin. Tana zaune a kan gadon tana ta faman kuka harda hawaye. Ya karasa ya zauna a kusa da ita yana cewa ‘Menene Shukra?
PAGE 62
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
‘Kashi zan yi.’
‘To ai ba sai kinyi kuka ba Shukra, sauko muje na saka ki a toilet.’
Ya sauketa daga kan gadon ya ja hannunta suka wuce bandaki, suna shiga ya cire mata wando ya fara kokarin daurata a kan toilet ta dafe duwawu tana juyi tana cewa ‘Ina Fo na Abba a shi zanyi.’
Cikin muryar lallashi yace ‘To ai ba ganshi ba ki yi hakuri ki hau toilet.’
‘Muje ka duba bandakin Anti fo dina yana nan Abba a shi zan yi kashin.’
Ya dauketa gaba daya ya dora a kan toilet yana cewa ‘To ki gama kashin kada ya fito in ya so idan kika gama sai muje mu dubo fo din.’
Kafin ya rufe bakinsa ta zame ta sauka daga kan fo din, tana kuka. Ta cigaba da bubbuga duwawunta tana shirin ficewa daga bandkin tana cewa ‘Fo na yana bandakin Anti bari na daukoa shi zan yi kashin.’
Cike da tsananin mamaki da takaici yake kallonta, ga dukkan alamu kashin ya matseta amma ita bata da niyyar zama a toilet din nan so take dole sai ya dauko mata fo; fo din da ya riga ya jefar ba tare da kowa ya sani ba. Ya kai hannu ya damkota tana shirin ficewa daga bandakin, ya mayar da ita kan toilet din ya zaunar da ita yana cewa ‘Anti ta kulle dakinta ta tafi da mukullinta sai ta dawo zata bude mana, kiyi kashin a nan.’
Ta sake direwa ta sauka daga kan toilet din tana buga duwawu harda juyi saboda yanda kashin ya matseta tana cewa ‘Ka zo na nuna maka Abba bata rufe ba, a bude dakin yake dazu nma na shiga.’
Kafin yayi wani abu kashin ya kwace mata, dan kadan ya fado ya zame daga duwawunta ya bata tsawon kafarta sanna ya dire a kasan toilet din. Yayi wuf ya dauketa ya daka mata tsawa yana cewa ‘Ki zauna a nan kiyi kashin nace, kalli yanda kika bata jikinki kika bata toilet din da kashi.’
Ta sake fashewa da kuka tana yi tana shessheka, takaici ya sa ko magana ba zai iya yi mata ba don haka ya kyaleta kawai yana tsaye tana rungume da kafarsa yana jira ta gama. Ko minti daya bata yi ba tace masa ta gama kashin, ya leka toilet din shi bai ga komai ba. Yace ‘Idan fa kika yi min kashi a wando zaneki zan yi Shukra gara ki gama kashin nan a nan.’
‘Na gama.’
PAGE 63
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ya dauketa cak ya ajiyeta a wajen wanka, ya dauki sprayer din yin tsarki ya fesa mata ruwan da karfi ta yanda ruwan ya wanke kashin jikinta, sannan ya sabi sabulu ya wanke mata da hannunsa. Ya dauketa ya fitar da ita ya shiryata ya kwantar da ita sannan ya koma bandakin; ya tsaya daga bakin kofa ya karewa bandakin kallo. Ga guntun kashin da ta jefar a kasa sannan gashi duk ta shafe na jikinta a jikin toilet din bandakin har ya fara wari. Ya yi tsaki ya juya ya fice, jimaw kadan ya dawo dauke da tissue paper, ya warware kusan rabinta sannan yayi amfani da ita ya dauke guntun kashin jefe a toilet din. Sannan ya sake warwarowa ya goge toilet din yayi flushin sannan ya fito ya dawo parlor ya zauna cike da takaici da gajiya.
A nan a parlor din bacci ya kwasheshi, watakila saboda tsabar gajiya domin bacci yayi mai nauyi sosai. Maganar Shukra ce ta farkar da shi wadda taje tashinsa tana sanar da shi zata sha shayi. Ya tashi zaune yana mittsike ido, ya lalubi waya ya duba lokaci; karfe ukun dare saura. Haka ya tashi ya hado mata shayin ya zo ya bata ta shanye sannan ya ja hannunta suka koma dakin. A nan ya tarar ita da Nasreen duk sun riga sun yi fitsarinsu a kwance; ya canzawa Shukra kaya ya lallaba ya kwantar da ita a gefen da bai jike ba kusa da Afaf. Ya dan tsaya ya karewa dakin kallo, sai kuma ya juya ya fice.
Gaba daya kansa ya kulle; wai dama haka yaran nan suke ko kuwa don sun ga mahaifiyarsu bata nan ne kuma Khadeeja bata nan suka saka shi a gaba suka hanashi sakat, domin wasu abubuwan da suke yi ma kamar da gayya musamman Shukra.
Har zai zauna a parlor din kuma ya tuna sai ya dafa abinda zai yi sahur don haka y wuce kitchen, ya janyo indomie ya debo park uku sannan ya nemi tukunya ya dora; Afaf da Habib sun yita fushi a kan jiya bai tashe su sahur ba don haka yau idan ya gama dafa abincin sai ya tashesu. Nan da nan ya dafa idomie din ya zubawa kowa a plate ya dora a dining table sannan ya hadawa kansa shayi. Bayan ya gama ya wuce dakinsu, ya kunna fitila sannan ya karasa ya tashi Afaf, ta zauna a kan gadon tana mittsike ido sanna ya wuce ciki ya tashi Habib.
PAGE 64
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Yana juyawa ya bude ido yace ‘Abba asuba tayi ne?’
‘No da saura, sahur zamuyi tukunna ga indomie can na dafa.’ Ya bashi amsa.
Ya gyara kwanciya yana janyo abun rufarsa yana cewa ‘Ni ba zan yi azumi ba Abba, sai gobe.’ Ya rufe ido ya cigaba da baccinsa ba tare da ya sake bi ta kan Abban nasa ba.
Afaf wadda take zaune a bakin gadonsu ta juyo tace ‘Abba wai sahur zamu yi.’
‘Eh.’
‘To Abba ai jiya ne ya kamata muyi azumi kuma baka tashemu ba, nima dai gaskiya yau ba zan yi azumin ba sai gobe. Dama haka mukeyi da Anti; muyi daya mu sha daya.’ Ta fada cikin halin ko in kula.
Bata ma tsaya ta saurari amsarshi ba ta koma ta kwanta ta rufe ido.
Nan ya tsaya yana kallonsu cike da mamaki; wai su yaran nan me yake damunsu ne? yanzu zasu ce zasu yi abu kafin wani lokaci sun canza ra’ayi. Gaskiya ya jinjinawa mata, ai idan ba mace ba babu wanda zai iya raino; jiya fa Afaf fushi tayi da shi saboda bai tasjeta ba amma yau kuma ita yake tashi tana ce masa wai yau bai kamata tayi azumi ba.
Yana fitowa daga dakin ya hada indomie din ya juye a tukunyar ya rufe ya ajiye musu a kan idan gari ya waye sa ci abincin safe, sannan ya dawo ya karasa sahur dinsa.
………
Kamar yanda suka saba yau din ma da tunasuba suka tasheshi a kan yunwa suke ji, haka ya shiga kitchen Afaf ta taimaka masa ya hadawa kowa cereal domin duk sunce ba zasu ci indomie ba don tayi sanyimkuma basa son dumame, da ya takura musu ma sai Nasree cewa tayi ‘Abba kai fa idan ka dafa indomie bata dadi, ka bari idan Anti ta dawo ta koya maka.’
Don haka kawai sai ya mayar da indomie din ya rufe.
………
Tun wajen goma na safe yake sa ran shigowar Ummi don ya riga ya gaya mata yau ma tazo, sai dai ga mamakinsa har wajen sha daya saura bata shigo ba; gashi har na fara yi masa korafin yunwa kuma ana bashi warning ba za aci indomie ba sai da taliya ko macaroni. Yana shirin fita ya je gidan su Ummin aka buga gate; kanwarta ce wadda suke kira Nana, wadda bata fi shekaru bakwai ba.
PAGE 65
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Bayan ta gaisheshi tace ‘baba yace na gaya maka Ummi ba zata sami zuwa wajen su Afaf ba yau don ta tashi da mura me zafi tana kwance, yace sai dai ko zuwa gobe idan ta sami sauki zata shigo.’
Jiki a sanyaye ya amsa ‘To, kice ina mata sannu kuma kice ina gaida Baban.’
Ya rufe komar ya koma cikin gidan gwiwarsa a sanyaye; ya zai yi da yaran ga gidan kace-kaca musamman kitchen din, ko ina kwanuka. Tukunna ma; mura fa aka ce Ummi take yi. Inna lillahi wa inna ialaihi raji’un! Allah ya sa yarinyar nan ba Covid-19 ta kwaso ba garin yawon tsiya, don tabbas idan ta kwaso to ta shafawa yaransa.
‘Subhanallah!’ ya fada a fili yana daf da karasawa cikin gidan.
Bayan ya shiga gidan yayi musu bayanin Ummi bata da lafiya.
Yana ji yana gani haka ya hakuri Afaf ta dafa musu jallof macaroni, bayan sun gama ci kuma ta kwaso wanke-wanke ta fice da shi waje ta wanko; duk da koakrinsa na hanata amma haka ta dage ta wankesu. Sannan ta umarci Halifa da ya share cikin gidan wanda shima nan da nan yayi, suka dawo suka zauna.
Wunin ranar haka yayi shi yana gyangyadi domin ko ya rufe ido da niyyar bacci haka wani zai rugo kai kara har Afaf din ma, ko kuma azo ace masa ana bukatar wabi abu; ita kam Shukra haka kawai ma da taga ya shiga daki binsa takeyi, idan kuam a parlor ne da ya rufe ido zata kirawo sunanshi tace ya bude ido ta nuna masa wani abu. Haka har aka kusan magriba sannan ya samu da taimakon Afaf ya soya musu dankalin bature kuma ya dafa musu indomie ta dan yi dadi.
Wuni yaran suka yi suna ciye-ciye amma ko da ka sha ruwa ma saka shi suka yi a gaba ana cin abinci suna masa surutu da rigingimu kala-kala; shi dai zai iya cewa ba a hayyacinsa ya ci abincin nan ba. Haka ya dinga ci yana kwarewa.
Ya cika bakinsa da dankali Shukra ta mike ta jefar da dankalin da yake hannunta tana dafe duwawu tana cewa ‘Kashi Abba.’
Ji yayi wani malolo ya taokare masa makogoro; wai ita Shukra bata tashi kashi ne sai mutum yana tsaka da wata sabga?
PAGE 66
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Lallai yanzu ya tabbatar Khadeeja tana da kokari don kusan tunda aka fara azumin nan sai ana tsaka da cin abinci sannan Shukra take cewa zata yi kashi kuma ta tashi ta sakata; idan ma tayi jinkiri shine yake nuna damwarsa.
Ya dubi Afaf wadda ya kula kamar ta bata rai me yace ‘Yaya Afaf ki saka kanwarki a toilet tayi kashi.’
Ta tashi a fusace ba tare da ta amsa ba ta dire kofin shayin da taje sha a kasa, tana daga kafa tayi fatali da kofin shayin ya zube ya fallatsa ya bata Habib wanda yake kusa da ita. Ya mike a fusace yana nunata ‘Dalla malama ji yanda zaki konani da shayi saboda kashin wata.’
Ita din ma a fusace tace ‘To ka matsa mana, ko baka gani ne?’
Abbansu ya bude baki zai yi magana Shukra tace ‘Kashi Abba.’
Ya tuna yanda suka yi cikin dare ya tabbatar bai shirya wanke kashi a parlor ba don haka ya mike ya wucesu ya ja Shukra ya nufi bandaki da ita. Saida ta gama kashin ya wanke mata ya fito sannan ya saka su a gaba yayi musu fada, ya sa Afaf ta gyara inda ta bara da shayi.
Ya kurbi shayinsa da ya bari yaji yayi sanyi, haka daiya hakura ya shanye ya dan kara cin abincin. Haka ya hakura ya nemi waje ya zauna yana tunani don zai iya cewa ba kkoshi yayi ba ya dai hakura da abincin ne kawai, haka ya dinga binsu da kallo sunata wasanninsu har loakcin kwanciyar bacci.
……..
A cikin wannan halin Mustapha ya karasa kwanaki biyu shi da yaran a jigace, gashi duk wanda yayi atishawa ko tari a cikin yaran sai ya firgita saboda gani yake kamar corona ce ta kwantar da Ummi kuma suma sun shafa a wajenta.
Kamar yanda aka sanar ranar asabar aka bude gari, ba karamin dadi wannan budewar ta yiwa Mustapha ba. Tun waje karfe takwas ya shirya sannan ya shirya yaran gaba daya, sai dai da ya duba lokaci yaga safiya ta yi da yawa ya bari zuwa wajen tara da rabi sai su fita; domin so yake su je su dauko Khadeeja sannan idan ya kawota gidan ya barsu ita da yaran ya wuce gidan hajia ya gaishesu.
Sai wajen goma saura sannan suka kama hanya.
PAGE 67
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid
Tun kafin ya gama tsayar da motar yaran suka balle kofofi suka fice suks shiga gidan da gudu, bayan sun gaida Mommy wadda take zaune a parlor tace su shiga dakin Anti Nabila su taso Antin tasu inda take barci.
Jinsu kawai tayi a kanta suna shewa, ba shiri itama ta mike. Nan take aka shiga bata labarin abubuwan da suke faruwa a gidan. Itama tayi kewar yaran kuma ta ji dadin ganinsu sosai. A farfajiyar gidan Mustapha ya tsaya sai da Mommy ta tura Nabila ta shigo da shi, ta bude parlor din baki tayi masa iso inda Baffa yake jiransa don shima fita zai yi jin isowarsu ya sa ya tsaya.
Bayan sun gaisa Baffa ya tambayeshi wajen su Alhaji sai yayi gyaran murya yace ‘Yauwa, ina ga zaka bar Khadeejan ta dan kara kwana biyu don mahaifiyarta tace akwai abubuwa suke yi na gyara wanda al’ada ta tanada. Don haka ina ga ka barta ta dan kara kwana biyu mu gani.’
‘Eh, kuma da zuwa mukayi mu tafi da ita Baffa.’
‘Allah sarki, ina ga a dan daga musu kafa su gama shirye-shiryensu, ba zasu dauki lokaci ba suma na sani in sha Allah.’
Babu yanda ya iya kwarjinin Baffa ya sa ba zai iya yi masa wani dogon musu ba, don haka sai kawai ya sunkuyar da kai. Baffa yayi masa sallama ya fice ya barshi a nan cike da takaici; yaya Baffa zai yi masa haka? Wannan din shawarar Mommy ce ko kuwa dai Khadeejan ce bata son ta koma? Amma dai bari Khadeejan ta fito ya ji daga bakinta. Ya gyara zama ya hadiye malolon da ya tokare masa makogoro ya dana saita fuskarsa da ya ji motsi ana taba kofar daga cikin gida, ya mike ya koma kan kujerar zaman mutum daya ya zauna.
Khadeeja ce ta shigo da sallama, bayan ya amsa ta nemi guri ta zauna a kan three seater ta gefen da ya fi kusa da shi, bayan sun gaisa tace ‘Ya kuke kai da yara? Sun ce min ku kadai ne a gida ko gidan Hajia baka kaisu ba.’
‘To ina zan kaisu gari yana kulle, dole haka muka zauna mu kadai; don ma dai Ummi tana taimakawa, jiya ne kawai da shekaranjiya aka ce bata da lafiya.’
‘Allah sarki ai iyayenta suna mana kirki gaskiya, Allah ne kawai zai biya su.’
PAGE 68
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Suka yi shiru na dan lokaci; idan ma da yana da niyyar gaya mata wasu kalamai masu dadi to Baffa ya goge masa haddarsu, yanzu haushin kowa ma yake ji. Sai dai fatansa daya ya ga ko zai iya tsaran Khadeejan ta canza wanna tsarin don yana jin idan tace tana son ta koma ba za a hanata komawa ba.
Yace ‘Uhm, da ni fa zuwa nayi mu tafi amma na ji Baffa yace kamar zakiyi wanka ne ko gyara wai sai an kwana biyu zaki dawo.’
Ta dan gyara zama ‘Eh, Mommy tace a barni sai nayi wankan jego kuma dai da ‘yan gyare-gyare na kara hutawa sai na komawa.’
‘Wai baki gayawa Mommy cikin bai karasa wata uku ba ma, na zata haihuwa ake wa wankan jego. Ke dai idan akwai wani dalili ki gaya min sai muga yanda za ayi.’
Tayi ‘yar dariya ‘Shine dai dalilin gashi na gaya maka, don kaga har yanzu ma ban gama jini ba kusan kwana biyar kenan.’
‘Uhm! To yanzu babu yanda za ayi mu koma yau, na san ai duk wani gyara ba zai gagare ki ba tunda kin sami lafiya ga laulayin ma yanzu babu.’
‘Gaskiya kayi hakuri kawai muyi yanda Baffa ya fada, kwana nawa ne zaka ga ma na dawo gidan.’
Ya sunkuiyar da kai; tabbas wannan tsarin na Khadeeja ne sai dai bai san laifin me yayi mata ba take son tayi purnishing dinsa haka. Muryarta ce ta katse masa tunani ‘Kada ka damu in sha Allahu zuwa bayan sallah zan dawo, ka ga kafin nan ma Mommy ta samo min mai aiki.’
‘Bayan sallah? Haba! Wajen sati uku fa kenan? Ai na zata duk inda aka kai nextweek kin gama hutawar. Kuma mai aiki ai Habi zata dawo bayan sallah ko?’
‘Ban sani ba, wai dai don kada ta bani mamaki gara a samo min wata runda ga aikin gida ga hidimar yara sannan ga makaranta zan koma idan an bude gari ka ga ina bukatar taimakon mai aiki ko.’
Sai a lokacin ma sannan ya tuna ashe tana zuwa jami’a; amma dai