Showing 75001 words to 78000 words out of 99112 words

Chapter 26 - Mijin Marigayiyya Part Complete Hausa Novels.docx

17 Sep 2025

83

189

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Yayi shiru da bakinsa a bude yana kallon Khadeejan ta cikin mudubi; to a gaban Antin tata zai sakar mata aikin gida da na yara bayan ga danyen jego sannan kuma ga Khadeejan tana kallo? Kuma ace ita ce zata tashi ta shirya masa yara, duk da dai kusan sun iya shirya kansu amma dai idan ba a tsaya a kansu ba haka zasuyi ta shiririta har su makara. Gashi Afaf ta shiga SS 3 yanzu tun 7:15 am ake tare su makara. Ya san idan dai ba a tsaya a kansu ba to kullum sai dai ya dawo da Afaf. Ya rasa ma me zai ce mata, domin ya san kusan ko me yace tana da amsar bashi kuma ya tabbatar fitnar da bata yi bace a lokacin da Baffanta yace ta dinga taya Naja aiki take shirin biyan bashinta yanzu.

Ta mike ta kwashi mayukanta da ta gama shafawa ta karasa gaban mudubin ta ajiye. Ta dan tsaya daga gefensa tana kallonshi fuskarta cike da walwala kamar ba yanzu ta hadiye bacin rai ba, tace ‘Kuma ni na yafe nawa kwanan ka hada mata, idan kuka yi arba’in sai mu cigaba da rabon. Ka ga ita da Baby suna bukatar lokacinka da kulawarka sosai a wadannan kwanakin.’

Ta wuce ta nufi gaban wardrobe domin saka kaya.

PAGE 190

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Yana nan zaune a gaban mudubin ta shirya ta fice ta barshi a dakin; nan da nan ta hada masa breakfast ta jera a kan table sannan ta dawo dakin ta sameshi ya riga ya gama saka kaya. Tana tsaye daga bakin kofa tace ‘Na yi serving breakfast.’

‘Ok.’ Ya amsa.

Ta juya ta fice ya biyo bayanta.

Suka zauna tare suna cin abincin. Har suka ci kusan rabin abincin babu wanda yace wani abu; kowa da abinda yake ransa. Ya ajiye kofin shayinsa bayan da ya kurba sannan ya dauki fork dinsa ya tsikari dankalin baturen da yake gabansa, ya dan ajiye fork din ya kirawo sunanta a hankali kamar ma baya so ta ji kiran. Ta daga kanta daga kallon kwanon abincinta ta amsa tana kallonsa. Yayi gyaran murya sannan yace ‘Um, da-Allah kiyi hakuri ki cigaba da girki akalla har zuwa lokacin da Antin Naja zata gama yi mata wanka ta tafi, tunda kinga ga Hafsa nan tana taimaka miki kuma na san Afaf din ma yanzu duk abinda kika gwada mata zata iya tayaki da shi.’

Saura kadan dariya ta kwace mata; wato yanzu Afaf ta kai ta taimaka wajen girki kenan tunda ya auro matar so? Ashe ma ya san kunya tunda ga shi baya so yaji kunyar iyayen Naja. Ta ajiye cokalinta ta kurbi shayinta sannan tace ‘Don Allah Abban Afaf mu bar wannan maganar, hidimar gidannan ta wata takwas na karbar mata. Ai nayi ko? Yanzu sai ta cigaba daga inda ta tsaya. Kwanan kuma da nace na bata da gaske nake, kuje kuyi jegonku na masoya kwana arba’in; watakila dai a kwankin da suka kama nawane na yi aikin gidan idan ina nan in ya so ita sai ta kwana da angonta.’

Cike da jin zafin abinda ta fada yace ‘Khadeeja ni kike gayawa wannan maganar?’

A cikin abinda ta fada bata san menene ya bata masa rai haka ba tunda ita dai a iya saninta ba rashin kunya tayi masa ba, amma ta ga ya fusata yana faman yi mata muzurai. Ita da ya kamata ace itace ranta ya baci haka saboda nauye-nauyen da yake nema ya dora mata wadanda karara suke nuna rashin adalci.

Ta kalleshi ta kawar da kai tace ‘Allah ya baka hakuri.’

Ta kurbe ragowar shayinta ta mike da kofin da kwanonta ta wuce kitchen.

PAGE 191

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Tana ajiye kwanukan ta fito ta wuce dakinta, tana turo kofar dakin hawayen da take rikewa suka kwace mata, ta karasa ta zauna a kan kujerar gaban mudubi. Ta zubawa mudubin ido tana kallon yanda hawaye suke fita daga idanuwanta suna gangarewa ta kan kumatunta. Wai me Mustapha ya dauketa ne? mai aikin Naja? To da me yasa ya aureta ne? ko dama haka ake soyayya?

Bata sami amsar tambayoyinta ba karar fitar motarsa daga gidan ta katse mta tunani, ta tuna itama aiki zata tafi. Don haka ta mike ta wanke fuskarta ta karasa shiryawa ta fice daga gidan zuciyarta cike da damuwa.

……..

Kamar yanda Khadeeja ta fada bata sake kula hidimar yaran a ranar da ba itace da kwana ba, sai dai ranar kwanata tana fitowa ta sallami kowa sanna ta cigaba da harkarta. Idan kuma dare yayi ta shiga dakinta tayi kwanciyarta don ta tabbatarwa Mustapha cewa ta bashi kwanan.

……..

Ranar asabar ce don haka yara babu makaranta duk suna gida, kamar yanda suka saba tunda Khadeeja taki hidimar yaran to duk ranar girkin Naja Anti Wiyya ce take abinci har yaran. Ita kuma Najan itace zata tsaya a kansu suyi wanka su shirya, sai dai ranar da bata tashi ba dole haka Mustaphan yake tashi yayi ta faman yi musu fada har ya samu su gama shiryawa a hankali.

Afaf ce ita kadai a parlor din Naja tana kallo saboda TV din parlor dinsu Startimes ce ita kuma ta fi son DSTV wadda take parlor din Naja; yayinda Anti Wiyya take ta kaiwa da kawowa tana kokarin dora a bincin rana. Ta wuce Afaf a parlor ta shige dakin Naja inda ta sameta a kwance a gefen gado; bayan ta amsa sallamarta ta karasa ta zauna a gefen karata kamar a fusace. Tace ‘Sannu Anti, kina ta hidima. Lallabata nakeyi idan ta koshi goyata zan yi na fito na tayaki. Salaman ma ina jin yau ba zata zo ba; ko wa take so yayi mana wanke-wanke da sharar oho ga girki.’

Tayi tsaki ta kawar da kai tace ‘Kin ganni a cike nake da haushinta, gashi kamar ta shirya wulakanci tunda yau wanke-wanken ya fi na kullum yawa sannan taki zuwa.’

‘Hmm! Ai sai hakuri masu aikin zuwa da dawowa basu da kirki, nima da na gama jegon nan me kwanan zan dauka.’

PAGE 192

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan Anti Wiyya tace ‘Ita kuma wannan ‘yar taki wallahi itama bata da mutunci; yaushe za ace budurwa kamarta ba zata yi aiki ba komai kankantarsa? Sai ai ta dinga bin mutane da kallo suna mata aiki sai kace ubanta sayenmu yayi. Gaskiya ku sake zama a gidan nan, haba! Idan banda ma rashin mutunci ya za ace mace tana jego kuma a barta da kula da gida da yara bayan tana da kishiya? Ai kamata yayi ta karbar miki aikin. Ko da yake wannan ‘yar mulkin kishiyar taki na kula daga ke har maigidan tsoronta kuke yi.’

Ta tashi zaune ta kwantar da Rukayya wadda ta riga ta yi bacci, ta kama haba ta dubi Antin tata tace ‘A’a shi dai yake tsoron matarsa, duk abinda ta ga dama tace ba zata yi ba haka zai yi ta kame-kame saboda ita ba a iya yi mata dole.’

Ta kalleta shekeke tana cewa ‘Kece karkatacciyar kukarsa mai dadin hawa ko? Shi yasa kina jego amma aka lafta miki aiki? Ita ko kunya bata ji? Sai ta sauko ta ishi mutane da gaishe-gaishe kamar wata musulmar ta kwarai.’

Cikin damuwa tace ‘Haka take fa, da an hadu tayi ta haba-haba da mutum amma mugun halinta yana nan fal cikinta sai mu da muke zaune da ita muka san halinta.’

Anti Wiyya ta dan yi kasa da muryarta tace ‘To gaskiya dai dole ayi aiki a kan wannan matar, yanda ta kama maigidan nan tana juya shi ai ba fin mu iyawa tayi ba. Kema idan kika zo yawon arba’in da kaina zan kai ki inda za a taimaka miki a kwato miki daraja. Wannan kwarjinin da take dashi take yiwa kowa har maigidan kema a samo miki shi. Taimako ne da ayar Allah ina da malamina a hannu kudi kawai zaki bayar. Har yaran ma don ubansu ko su biki su zauna lafiya ko kuma su koma ‘yan kallo.’

Tana ta jijjiga kai saboda gamsuwa tana cewa ‘Babu komai Anti, in sha Allahu zamu je. Don nima wallahi zaman haka ya isheni. Kuma dama Yaya ma tace zamu je ban san me ya dauki hankalinta ba.’

Nan suka zauna suka gama kulla yanda za ayi sannan suka fito suka kama hidimar gidan.

PAGE 193

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Haka suka cigaba da yi har Naja tayi arba’in; duk wata kalma da Mustapha zai yi amfani da ita ya sa Khadeeja ta karbi hidimar nan bata yi amfani ba har ya gaji ya sakawa sarautar Allah ido.

Sai da Naja tayi arba’in sanna suka cigaba da rabon kwana. idan Khadeeja ce da kwana sai Mustaphan yaje dakinta yayinda ita kuma Naja take zuwa dakinsa. Kwanci tashi har ya zama ta mayar da saman nasa kamar nata, ya zama kullum tana ciki ko parlor dinsa ko dakinsa.

Bata dade da yin arba’in din ba kuma Khadeeja ta gama bautar kasa; sai dai duk yanda ita da Baffanta suke kokarin samar mata aiki bai samu ba. Inda tayi bautar kasar ma ta so su riketa amma suka nuna mata basa bukatar ma’aikata. Bata son zaman gidanta, domin ta san in dai ya zama Naja zata tafi aiki ta barta a gidan da yara to dole Mustapha zai yi duk yanda zai yi ya tursasa ta ta dinga kula da yara. Ya zama shi da matarsa sun yawon neman kudi ita tana musu hidimar gida da ta yara. Don haka ta sanar da manager zata dinga zuwa litinin zuwa juma’a tana yi musu aiki kyauta. Da yaji haka sai ya sa aka dorata a kan tsarin internship da suke da shi; inda duk wata za a dinga bata naira dubu goma sha biyar har zuwa lokacin da za a sami wani gurbi a gidan rediyon kawai sai a dauketa. Sosai hakan yayi mata dadi, kuma ba tare da wata fargaba ba ta sanarwa Mustapha sun riketa aiki, ta cigaba da zuwa.

Kusan wata takwas kenan da haihuwar da naja tayi; kuma kamar yanda suka tsara an kaita wajen malami. Bayan malamin ya ji bayaninsu ya bata wani abu mai kama da gishiri yace tayi sati tana zuba musu a abnci duk gidan kowa yaci har Khadeeja. Haka ta dage tayi amfani da abun nan sai dai bata da tabbcin Khadeeja ta ci abun marmarin da take girkawa tana aika mata, shima Habib bata da tabbacin cinsa domin ya fi cin abinci a wajen Khadeeja.

A hankali ta fara ganin sauyi, kamar dai duk yaran da Mustaphan suna saurararta; tunda wasu lokutan idan ta sa Afaf aiki haka zata tashi tayi ko bata so kuma Mustaphan ya daina hanata.

PAGE 194

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Sun gama magana da ita a kan zai siya mata mota, amma gashi lokaci yana ta kurewa yanzu ya ma ce mata shi ba alkawari yayi mata ba; shi kawai ce mata yayi zai yi tunani.

Cikin damuwa suke waya ta sanar da Anti Wiyya halin da ake ciki; tace ‘Wallahi Anti nema yake ya canza maganar. Kuma dama na gaya miki aikin malamin nan ba kullum yake ci ba, tunda ko Mustaphan ya fara saurarar maganata da an kwana biyu sai ya sake komawa kamar da. Gani ma nake kamar duk lokacin da matarsa ta karbi kwana sai ta warware min aiki, shi yasa nake ta fama da shi.’

Daga daya bangaren Anti Wiyya tace ‘Au haka ne? To barni da su, ai ba mu za a yiwa bariki ba. Akwai wani malamin aikinsa yana da zafi sosai, in kin sami lokaci kiyi min waya sai muje wajensa. Ke kanki sai kin yi mamakin aikinsa.’

Suka karasa hirarrakinsu sukayi sallama. Ta jefa wayarta a kan gadonta cike da kwarin gwiwa; ta san Mustapha yana kokari wajen kyautata mata amma ita gani take kamar tsoron khadeeja yake yi. Kuma ma ita so take ya zama gaba daya gidan sai abinda ta fada za ayi. Tana ganin yanda maza suke yiwa matansu kyauta ta burgewa, itama haka take so ya dinga yi mata, duk abinda ta nema ya bata kawai tunda ta san yana da kudin. Idan ma ta sami yanda take so to ko ganin Mustapha yaran basu isa suyi ba sai da izininta, domin ta kula da yanda yake saurararsu yana bin ra’ayinsu kamar su suka haifeshi. Sai an yi magana yace su marayu ne. Tabbas dole gidan nan gaba daya ya dawo tafin kafarta don ta gaji da wannan mulkin da ake mata ana kasa mata hankalin miji tsakanin uwargidansa da yaransa.

………

Kwanci tashi sai da Khadeeja ta kwashe shekaru biyu tana aiki a gidan rediyon nan a matakin internship sannan aka sami gurbi aka dauketa cikakken aiki, aka saka mata albashinta Naira dubu saba’in.

Ba karamin dadi ta ji ba da samun wannan ci gaban domin tun da ta fara service ya zama wasu hidimomin nata ita take yiwa kanta kamar kayan shafe-shafe, turare wani lokacin ma har da sutura. Bata sani ba ko haka yake yiwa Najan ma tunda itama tana da albashi ko kuma ita kadai yake yiwa hakan.

PAGE 195

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Sai dai bata da lokacin da zata bincika ko kuma ta tambaya don haka take rayuwarta yanda taga zata iya.

Afaf ta shiga Jami’ar Bayero ta Kano inda take karantar Computer Science yayinda Habib yake SS3 yayinda Nasreen take JSS3 ita kuma Shukra tana primary 5.

Zuwa yanzu duk bakon da yayi kwana daya a gidan zai gane cewa gidan ya kasu kashi biyu; Shukra da Halifa wadanda su ‘yan dakin Khadeeja ne da kuma Afaf da Nasreen wadanda su ‘yan dakin Naja ne. ko a wajen tarbiyya ‘yayan dakin Khadeeja sun fita da ban da ‘yayan dakin Naja. Domin ita Khadeeja tarbiyyar take basu da kulawa saboda Allah kamar yanda take yiwa Hammad, ita kuma Naja hankalinta yana kan yanda zata kwace gida ta mallake maigidan don haka duk abinda zai saka shi farin ciki shi da yaransa shi take yi; ko da kuwa abun ba daidai bane.

Lokuta da dama idan taje wajen malamanta tana samu ta fara juya Mustapha, sai dai abun bai fiya dadewa ba. Da zarar ta fara samun yanda take so sai kuma ta sake rasa kan maigidan nata. Tayi iya bakin kokarinta ganin ta inda zata samu ta hadashi fada da Afafa amma ta gagara; saboda son da yake yiwa Afaf ba kadan bane. Kuma kusan duk wani abu da zai yi to da Afaf yake shawara. Haka aka yi a farkon shekarar nan da zai canza mota; da kansa yake fada Afaf ce ta zabar masa motar bayan ita bata ma san zai canza motar ba sai da aka kawo motar gidan. Haka kuma aka yi da zai canza fentin gidan; Afaf ce ta zabi wanda take so aka yi, sai daga baya matan gidan suka ji labari.

Lokuta da dama Naja ta so su hade kai da Khadeeja ko da su samu su kwaci Mustapha daga hannun ‘yayan ne, amma bata sami hadin kai ba. Domin har yanzu zaman nasu dai babu yabo babu fallasa. Shi yasa ma Najan takewa Khadeeja kallon bata san me take yi ba saboda yanda ta bari yara suke controlling miji.

Ita kuwa Khadeeja bata taba daukan alakarsa da yaransa a matsayin matsalarta ba, matsalarta daya da shi rashin adalcin da yake nuna mata tsakaninta da Naja. Idan dai abun a nuna kulawa ne da kauna to Naja yake nunawa, amma idan abu ne wnda za ayi masa hidima shi da yaransa to sai yace a kaiwa Khadeeja.

PAGE 196

MIJIN MARIGAYIYA

A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)

Duk wani kokari da zata yi ta ga ya nuna mata so da kauna tayi amma abun ya ci tura; har ta gaji ta zuba masa ido. Lokuta da dama idan tayi magana sai dai ya dinga kokarin nuna mata cewa ya fi sonta kuma ya fi trusting dinta shi yasa yake saka ta hidimarsa da ta yaransa. Ta gaji da jin wannan tatsuniyar shi yasa ma ta hakura ta daina korafi; kawai dai duk abinda zata yi zata yi, abinda ba zata yi ba kuma haka zata zuba masa ido ya karaci barazanarsa amma bata yi.

Haka rayuwarsu ta cigaba.

--------

Tun kafin ta yaye Hammad al’adarta ta dawo, don haka kai tsaye ta tafi asibiti ta karbo kwayoyin family planning; ko Mustaphan ma bata gayawa ba sai da ta karbo. Ba wai haihuwar ce bata so ba, kwai dai bata da tabbas din zaman auren. Kullum Mustapha nuna mata yake itace jakar gida yayinda Naja itace matar gida; don haka duk da yana kula da yaransa sosai kuma yana son su amma bata jin zata iya tara masa wasu yaran balle ma azo inda zata yi magana a ce tayi hakuri ta zauna don yaranta.

Tunda ta karbi kwayar nan bata taba yin fashi ba kamar yanda likita ya sanar da ita, ko da kuwa ba itace da kwana ba haka take shan kwayarta. Amma a ‘yan kwanakin nan gaba daya ta rasa gane kan jikinnata; wasu abubuwa take ji kamar na mai laulayi.

A hanyarta ta dawowa daga office ta tsaya a chemist ta siyo pregnacy test strip, har ta zo gida tana fargaba saboda duk wasu alamu na ciki sun gama bayyana a tare da ita. Sai da ta bari tayi baccin dare sannan ta dauki fitsarinta na sassafe ta gwada da shi; kafin sakamakon ya bayyana a jikin ‘yar takardar gaba daya ta gama rudewa. Ko da taga layukan guda biyu sun bayyana batare da wata matsala ba sai da zuciyarta ta kusan bugawa, ta muttsike ido ta sake kalla amma har yanzu layukan suna nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login