Showing 72001 words to 75000 words out of 99112 words
tare yazo ya ga gidan. Nan da nan ta tashi ta fice don zuwa ta taryi Baffan nata. Sai da ta shiga kitchen ta jera ruwa da lemo a faranti sanna ta fito, ta dubi Habib wanda yake zaune a parlor din yana rike da Hammad tace ‘Yaya ku taso ku gaida Baffa gashi nan a parlor din Abbanku.’
Tana shiga parlor din ta sameshi da Shukra da Nasreen yayin da Abban nasu yake zaune daga gefe a kan kafet; yanayi zaman da Mustaphan yayi kawai ta kalla ta sha jinin jikinta. Ko da bai kai kararta gida ba to tabbas ta san a wannan dan zaman da Baffan yayi ya gaya masa laifinta. Ta karasa ta ajiye ruwan a gaban Baffa a daidai lokacin da Naja wadda itama ta shigo ta gaisheshi take ficewa daga parlor din. Ta zauna daga gefen kafarsa sannan ta gaisheshi ya amsa cike da girmamawa.
Sai da ya gama raha da yaran sannan ya zaro sababbin kudi a aljihunsa ya bawa kowa naira dubu sannan ya sallamesu suka wuce suka barsu daga shi sai Khadeejan da Mustapha.
PAGE 182
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ya dubi Khadeeja yayi gyaran murya sannan yace ‘Deeje, garin yaya kika ce ba zaki taimaka ki karbarwa abokiyar zamanki hidimar gida ba bayan bata da lafiya? Haba Khadeeja, hakan ai shine zaman tare tunda dai Allah ya hadaku.’
Ta yi shiru ta sunkuyar da kai tana tunanin ta inda zata fara, inama da Baffa ya zo da Mommy. To ta ina zata fara gayawa Baffa yanda Mustapha yayi mata lokacin tana nata laulayin? Kuma ya za ayi ta gayawa Baffa cewa ita bata bin Mustapha dakinsa kuma duk ranar da bata bishi dakinsa ba Naje yake kira ta tayashi kwana? To ai Baffa ma sai dai ya sake yi mata fadan kin zuwa dakin miji domin tabbas abu ne da haka aka saba; kuma ta sani mata biyu ne da kakanta mahaifin baffa. Wanda da wayonta kafin dukansu su rasa ta san matan ne suke zuwa dakinsa. Wannan kam ai sai dai ta kara kai karar kanta.
Muryar Baffa ce ta katseta yana cewa ‘Deeje me yasa ba zaki taimakawa abokiyar zamanki ba?’
Ta dan yi firgigit kamar wadda aka tasa daga bacci sannan tace ‘Uhm Baffa wallahi nima daurewa nake ina yin hidimar ranar girkina, tunda ga jego ina yi sannan kuma ina zuwa aiki.’
‘Eh, ai wannan ba zai gagareki ba tunda kinga da ace ke kadai ce a gidan ai duka zaki hada ko?’
Suka yi shiru na dan lokaci sannan daga baya tace ‘Baffa nima fa haka nake hada nawa laulayin da aikin gidan babu wwanda yake tayani. Kuma ka ga Baffa akwai mai aiki fa wadda zata iya yi mata duk abinda take so idan tayi mata bayani.’
Baffa ya dan yi murmushi sannan yace ‘Na fahimceki Khadeeja, amma dai kiyi hakuri ki karbar mata aikin. Tunda kin ga yanzu kema idan kika kuma samun wani cikin ai zata karbar miki ko? Kiyi hakuri Deeje, bana son taurin kai da yawa. Allah zai baki lada har kashi biyu, ladan biyayya wa miji da kuma ladan taimakon ‘yar uwarki musulma wadda take neman taimakon naki. Kiyi hakuri kin ji, tunda ga yarinyarki nan tana taimaka miki ki zauna lafiya tunda dama yara duka naki ne tun kafin ma a aurota.’
Haka Baffa ya dauki lokaci yana bata hakuri, daga karshe kuma ya bata umarnin lallai ta taimakawa Naja ta karbi hidimar gidan.
PAGE 183
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid Innar su Amal
Bayan ya mike duka suka mike gaba daya, a nan yayi sallama da Khadeeja yace ta koma ciki. Suka fice shi da Mustapha wanda yayi masa rakiya har wajen motarsa sannan yayi masa sallama ya tafi.
Ya san ko da ya koma wajenta a yanzu ba zata saurareshi ba sai dai ma ta gaya masa maganganun da baya son ji, don haka ya wuce wajen Naja tunda dama kwananta ne.
……….
Har turiri take ji yana taso mata a kirjinta saboda tsabar yanda zuciyarta take tafasa; sai da tayi da gaske sannan ta kai kanta dakinta ba tare da tarushe da kuka ba. Ya za ayi ace ta karbarwa naja girki saboda kawai tana da ciki? Bayan ita a lokacin da tana da nata cikin hakaya dinga barinta da duk wata hidima yana hana yaranshi su tayata. Sannan kuma idan tayi magana ya dinga nuna mata cewa laulayi ba komai bane kamar ma dai itace take son nuna raki. Yanzu kenan haka zata kwashe wata takwas ko tara tana kula da yara yayinda Naja take kwana da miji tunda laulayin bai hana idan ta sameshi shi kadai a dakin ta kai masa kanta ba?
Tana shiga ta murza mukulli ta rufe kofar, sai da karasa kan daddumar da ta tashi sannan ta zube da gwiwoyinta tarushe da kuka. Shikenan ita ta zama baiwar Mustapha ne? ya iya nunawa kowa kauna da tausayi a duniya amma banda ita? Anya zata iya wannan rayuwar a gidan Mustapha kuwa? Amma ta san dole ne ta bi umarnin Baffanta, musamman da yake a gaban Mustapha ya bata umarnin. Ta kifa goshinta a kasa ta sake rushewa da kuka.
…..
Ya so kwarai kamar yanda ya saba lekawa da daddare ya yiwa wadda bata da kwana sai da safe ya leka wajen Khadeeja, amma da yake bai shirya rigimarta ba sai kawai ya kyaleta suka shige daki shi da Naja suka yi kwanciyarsu.
Ba karamin dadi ya ji ba da ya dawo daga masallaci sallar asuba ya jiyo motsinta a kitchen, tabbas ya san ta ji maganar Baffanta. Ba tare da bata lokaci ba ta shiryasu sannan ya fito ya kaisu makarantar.
Kafin ya dawo daga kaisu makaranta ta gama nata shirin, a zaune ya sameta a parlor dinta tana karyawa. Babu yabo babu fallasa suka gaisa, sai dai daga gaisuwar bata sake ko da kallon inda yake ba.
PAGE 184
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Jimawa kadan ya mike zai fice, tace ‘Idan na tsahi daga aiki zan je gidan Mommy.’
Ya dan tsaya yana kallonta yana kokarin su hada ido ko zai karanto wani abu a fuskarta, sai dai bata bashi damar ba. Daga tsayen yace ‘Ki gaishe min da mutanen gidan.’
Ya fice ita kuma ta cigaba da cin abincinta ba tare da ko da ta kalli inda ya wuce ba; gaba daya ma a halin yanzu ko son kallonsa bata son yi.
……….
Tun wajen 12pm ta nemi izini a wajen aikin nata ta fice, kai tsaye gidansu ta nufa. Ta ci sa’a ta sami Mommy da Yaya Mama suna zaune a parlor suna hirarrakinsu. Bayan sun gaisa Khadeeja ta dubi Yaya Mama tace ‘A nan kika kwana Yaya.’
Tayi dariya tace ‘Ga jakata a kusa dani kina kallo amma kike min wannan tambayar, to ni yanzu ma zan tashi saboda 2pm zan dauko yara a makaranta sannan mu wuce gidan.’
Itama tayi dariyyar, ta umurci Hafsa da ta shida dakin Nabila ko taje kitchen wajen masu aikin gidan ta zauna.
Tun kafin tace wani abu Mommy ta dubeta tace ‘Lafiya dai na ganki kamar a fusace, sarkin rigima.’
Ta zumbura baki ta sunkyar da kai tana kallon hannunta kamar me kunkuni, sai da ta gama zumbura bakin sannan cike da takaici tana kokarin danne hawayen da ya taso mata tace ‘Mommy ni Mustapha zai mayar ‘yar aiki, kuma Baffa ya goya masa baya.’
Mommy ta gyara zama ta fuskanceta sosai tana kallon fuskarta da mamaki sannan tace ‘Ban gane ba, kuma me kawo Baffanki a cikin mayar dake ‘yar aiki? Shi Mustaphan me yayi miki?’
Tana bude baki zata yi magana hawaye ya kwace mata, ta sa bayan hannunta ta goge sannan ta labartawa Mommy abinda ya faru. Zuwa lokacin hawayenta ya gama kwacewa yana zuba kamar ana zubar da ruwan famfo, Mommy ce ma take kokarin goge mata. Tace ‘Mommy yanzu shikenan haka zan yi wata tara ina mata hidimar gida tana kwana da miji, bayan ni haka nayi nawa laulayin ko tausayina baya ji. Ko haihuwar Hammad fa ana gama suna dole na mike na koma hidimar gidan saboda ban ma ga fuskar cewa ba zan iya ba. Amma yanzu saboda ya auro ‘yar gwal shine zan karbar mata aiki ita kuma tayi laulayi.’
PAGE 185
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Yaya Mama tace ‘Nifa gaba daya ban gane. To ke me yasa bakya zuwa dakin kike barinta taje, ai da sai kije ki yi wanciyarki a can kiga ta inda marasa kunya zasu kwana tare.’
Kafin tayi magana Mommy tace ‘Gaskiya nima dai ban gane dabarar yin hakan ba, ai dakin ya kamata ki gyara ki tare har sai kin gama kwananki.’
Ta sa bayan hannunta ta goge hawayenta sannan tace ‘Mommy ba zan iya ba, ya kwana da wata matar a kan gadon sannan nima ya kwana dani a kan wannan gadon. Watakila ma da yayi aurensa ba tare da ya ci min mutunci ba abubuwa da dama zau zo min da sauki, ama gaskiya ba zan iya ba. Tunda ko bayan ta tare ranar da zan karbi girki bayan da ta gama kwana takwas dinta na shirya tsaf zan shiga dakin, amma har magriba bata fito daga ciki ba. Lokacin shi kuma ya riga ya fita. Don haka na kyaleta na shirya masa abincin dare tunda na gama kintsawa. Amma yana dawowa ko kallon abincin bai yi ba ya sameni wai tunda ina jego na bashi kwanakin ya kaiwa amaryarsa in ya so idan nayi arba’in sai a fara rabon kwanan. Kinga kenan ita ta riga ta san ba zai bani kwnan ba shi yasa ta ki fita ma daga dakinsa. Daga wannan lokacin dakin da me dakin suka karasa fice min daga rai gaskiya. Idan yana bukatata ya sameni a dakina, kuma yana zuwa din.’
Mommy wadda take binta da kallo tana jijjiga kai tace ‘Lallai Mustapha, ni na rasa ma me zan ce. Ni fa mamakin da nake Baffanki ko gaya min bai yi zai je ba balle da ya dawo ya gaya min, watakila jiya bayan ya fita da magriba Mustaphan yayi sa’a ya sameshi a gate suka gama magana.’
Yaya Mama tace ‘Hmm! Ai komai dadinki da miji idan dai wata macen ta gifta to sai abinda kika gani. Watan hakurinki ne ya kama har ya gama yayinta.’
Mommy tace ‘To yanzu ya za a yi? Kinga Baffanki ya riga ya sa baki a maganar ba tare da kin gaya masa ainahin abinda yake faruwa ba..’
‘To Mommy ya za ayi nayi masa duk wannan bayanin ya gane, ai ban ga alamar zai ma gane ba tunda ko a lokacin ma yace amfanin mta biyu kenan daya ta taimakwa daya. Kuma ya za ayi na zauna ina gaya masa Mustapha yana satar min kwana saboda na ki zuwa dakinsa?’
PAGE 186
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
‘Umm, hakane kuma. To Allah ya kyauta. Yanzu kam sai dai kiyi hakuri a ga abinda hali zai yi tunda dai babu wanda zai je ya kwance maganar baffanki. Ina ga kula dayarn wanda kika yi a baya bai kashe ki ba bana jin na wata tara nan gaba zai dameki.’
Haka suka zauna suka yi ta bata hakuri; sai daga karshe Yaya Mama tace ‘Kuma kema idan kin gaji kawai kiyi pretending ki kwanta masa, wallahi da kaina zan zo na taho dake na kawowa Mommy tayi jinyarki idan kin huta kya koma.’
Mommy ta kai mata duka tana cewa ‘Allah ya shiryeki yayar kwabo.’
Suna nan zaune wajen 1:30pm Baffa ya shigo gidan da sallama, bayan ya amsa gaisuwarsu da sannu da zuwa ya dubi Mommy tana zaune a tsakiyar su Khadeeja yace ‘Gulmar wa kuke yi suka saka ki a tsakiya haka.’
Itama dariyar tayi tace ‘Ba dai gulmarka muke yi ba.’
Yaya Mama tayi musu sallama ta fice yayinda Khadeeja ta mike ta nufi dakin Mommy ba tare da tace komai ba.
Baffa ya bi bayanta da kallo sannan yayi dariya ya dubi Mommy yace ‘Wannan iya rigimar karata ta kawo ko?’
Ta harareshi tace ‘Ashe ka san kayi mata laifi?’
Yayi dariya yace ‘Rabu da ita da-Allah, ya za ayi ace mutum yana da mata biyu ace daya ba zata karbi daya aiki ba idan bata da lafiya? Ai itama bata so a zauna lafiya ba.’
Nan ta kara yi masa bayanin yanda zaman nasu yake, sai dai ta kasa gaya masa cewa Mustaphan yana bawa Naja kwanan Khadeeja saboda Khadeejan bata yarda taje dakinsa. Yanda ta san shi ta san tabbas ba zai dauki wanna ba, tunda shima tashi uwar har ta koma ga Allah turaka take zuwa ranar kwananta.
………
Haka dole Khadeeja ta hakura ta cigaba da hidimar gida da ta yara.
Shima Mustapha da ya gama zagaye-zagayen haka ya sameta a dakinta yana nuna mata jin dadinsa ganin yanda take kula da yaran sai dai baya jin dadin yanda idan ta jera abinci take komawa daki ta barsu shi da ‘yayansa.
PAGE 187
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Duk yanda ya so ta bashi hadin kai su tattauna maganar ta ki, da ya dameta da zance ma sai tace ‘Don Allah ka bari! Kai dai ba so kake na cigaba da hidimar gidanka da yaranka ba amaryarka tana hutawa? To ai ina yi ko? Ina ga duk a inda na zauna naci abinci ma wannan bai kamata ya zama damuwa ba tunda dai ku kun ci naku.’
Kafin ya bata amsa ta fice ta bar masa dakin. Dole ya hakura ya zuba mata ido tunda dai tana yin abinda yake so kuma duk ranar da ya kai mata kwananta bata hanashi bukatarsa.
000000
Da fari lokacin da Mustapha ya kara aure Khadeeja taga ‘yan uwansa basa wani damunta tayi zaton tunda an mata kishiya sun fita harkarta. Sai dai tunda suka ji labarin Naja tana da ciki sai suka kama zarya gidan; babu yanda za ayi Yaya Jidda tayi sati bata zo gidan ba. Haka zata taho da girki a flask wai Hajia ce tace a kawowa Naja saboda kwadayin mai ciki. Gashi idan ta zo a wajen Najan zata sauka, sai dai idan Khadeejan tana nan ta shiga su gaisa sai ta koma wajen Najan. Sai kuma tayi ta aiko yara; a bata abinci. Idan ta cinye kuma tace a bata wani dan abun tabawa. Ranar da bata zo ba kuma sai a turo yaranta da abincin; haka zasu zo ta wuni surutu da hidima da su bata taba jin wani yace Hajia tana gaishwta ba. Kuma shima Mustaphan kuma yana kallo ana yi amma bai taba cewa komai ba; sai dai yawan godiya da zata ji shi yana yiwa mutan gidan nasu.
Haka ta kawar da kai ta cigaba da duk wannan hidimar tana ganin rawar kai kala-kala.
Haka ta cigaba da dagewa har Allah ya sauki Naja lafiya, aka sami yarinya mace wadda tun ranar da aka haihu Mustapha yayi mata huduba da suna Rukayya.
Basu tsara zata tafi gida ba don haka sai aka kawo kanwar mahaifiyarta Alawiyya waddad suke kira da Anti Wiyya ta zo yi mata zaman dabaro.
Tun Khadeeja tana saka ran zata ji Mustapha yace zai hade mata kwanan saboda Naja tana jego har dai ta fitar da rai.
Ranar da aka kwana takwas da haihuwa ranar ta kama kwanan khadeeja ne sai dai a daren ranar zata fita daga girki.
PAGE 188
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Da yake a dakinta suka kwana a nan yake shirin fita office; musamman tunda bandakin dakinsa ya kwana biyu rabon da a wanke saboda Naja ba zata iya wankewa ba kuma Khadeeja ta ki ma shiga dakin; gashi kuma yana kyashin ya saka Afaf ta wanke tunda baya son damuwarta.
Yana zaune a gaban mudubinta yana shafa mai ta fito daga wanka, ta dauki kayan shafawarta ta koma gefen gado, suna yi suna taba hira.
Jimawa kadan tace ‘Yauwa, tazarce zamu yi ko? Sai na hade kwanakin tunda Naja tana jego har zuwa tayi arba’in ko?’
Ya dan yi dum, alamar maganar ta shammaceshi; tun ranar da Naja ta haihu ta gaya masa ba zata bayar da kwanata ba saboda ko ba zata iya biya masa bukatarsa ba tana so ya kwana da su ita da Baby, in ya so kwana biyu sai su hakura. Ya riga ya amsa mata hakan domin shi ma hakan yayi masa; duk da dai shi ba mutum ne mai son jarirai ba domin ko daukan yaro baya son yi har sai yaro ya iya zama sosai. To amma dai tunda ta nuna tana so shima sai ya ji hakan yayi masa ko hira ce sa yi, musamman da yake bai taba tsammanin Khadeeja zata nemi wani karin kwana ba duk da ita ta bada nata kwanan an bawa Najan.
‘Um, no ina ga ba haka za ayi ba. Na riga nayi magana da ita amma bata bada kwanan nata ba, tunda kin ga kema tambayarki nayi kika bayar ba tare da nayi miki dole ba. To ita bata bayar ba, don haka sai a cigaba da kwana bibbiyun kawai.’ Ya fada cikin in-ina yana satar kallon Khadeejan ta cikin mudubi.
Sai da tayi da gaske sannan ta hadiya malolon da ya tokare mata makogoro; duk da dama hakan ta sa rai zai fada amma sai da abun yayi mata ciwo. Ita bata ma yarda Naja ce ba zata bada kwananta ba, ta fi yarda shine di ba zai iya bata kwana arba’in ba ba tare da ya ji dumin rabin ransa ba. Ta daure tayi murmushin yake sannan tace ‘Allah sarki hakane kam, to babu damuwa Allah ya raya mana Rukayya ita kuma mai jego Allah ya kara mata lafiya. Shikenan ai tunda ta haihu lafiya idan ta karbi kwana yau to ta hada da sauran hidimar gida da yara da nakeyi nima na samu na huta.’
PAGE