Showing 42001 words to 45000 words out of 99112 words
fara komai ba kika tsaya kina kallona?’
‘Uhm ai ban san me zan fara ba.’
‘Me kuke yi ke da ita idan zata shirya ‘yan makaranta?’
‘Um, ai itace take yin abincin ni tayata nake yi, kuma yanzu ban san me zata dafa ba.’
PAGE 106
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
‘Mtsewww!’ Ya ja tsaki sannan ya juya kamar zai fice sai kuma ya dawo yace ‘Ki dora ruwan shayi mana da abincin tafiya makaranta.’
Ya juya zai fita tace ‘Um to abincin makarantar me za a dafa?’
Ya kalleta cike da takaici; wai wannan wacce irin dakikiyar yarinya ce? Yace ta dafa abincin ma sai kuma ya gaya mata abincin da zata dafa. Kamar zai fice kuma sai ya tsaya yace ‘Ki dafa indomie.’
‘To.’ Ta amsa jikinta na rawa ta juya ta shige store domin dauko indomie.
Yana dawowa parlor din ya jiyo Afaf tana hayaniya da Shukra a kan shiryawa, har ya nufi dakin sai kuma ya fasa ya wuce kofar daki Khadeeja ya kwankwasa kofar a hankali yana cewa ‘Khadija ki bude mana.’
Babu wanda ya bashi amsa don haka ya koma parlor din ya zauna yana jiyo hayaniyar yaran a dakinsu suna shiryawa. Jimawa kadan ya tashi ya nufi dakin inda ya sa hannu ya fara kokarin tayasu shiryawa. Nan da nan suka gama sannan ya tasosu a gaba suka fito inda ya saka su a gaba suka sha shayi da burodi sannan a gurguje Rashida ta zuba musu indmie dinsu a flask ya tasa su a gaba suka fice.
Khadeeja tana jin fitarsu da mota ta fito daga dakin a shirye ta sallami Rashida ta sanar da ita idan ya dawo ta fice ta tafi makota in ya so idan zai fita sai yayi mata magana ta dawo; Haka suka saba tunda Shukra ta shiga makaranta; idan dai ba tare da yara zai fita ba sai dai Rashida ta je makota ta jira idan ya gama zai fita sannan ta dawo ta shiga gidan.
Bayan ta gama sallamar Rashida ta fice ta tafi makaranta.
………
Suna dab da karasawa makarantar aka rufe gate din, gaba daya masu gadi da sauran ma’aikatan suka shige ciki suka rufe kofa; wanda hakan yake nufi babu yaron da zai sake shiga. Ya tsaya ya cije lebe na dan lokaci sannan ya kunna motar suka kama hanyar komawa gida.
Nasreen tace ‘Mun makara, gashi bamu taba makara ba.’
Yace ‘E, kun tsaya kuna ta fada baku shirya da wuri ba.’
Afaf tace ‘Abba Anti bata lafiya ne?’
Ya shafa kansa yana cewa ‘Eh, bata jin dadi.’
PAGE 107
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Suna Shigowa gidan suka tara da Rashida a tsaye a bakin kofa kamar yanda ta saba jiransa, tana ganin su ta bisu suka shige. Shi kuma Abbansu ya karasa kofar dakin Khadeeja ya fara kwankwasawa yana yi yana cewa ‘Khadeeja daAllah ki bude mana.’
Rashida ta fito daga dakin su Afaf tace ‘Antin ta tafi makaranta.’
Ya kalleta da mamaki yace ‘Makaranta? Yaushe?’
‘Bayan kun fita.’
Ya wuce dakinsa ya barta a nan.
To me Khadija take nufi ne? Daga yin abu ta ma ki ta zauna ayi magana tana ta wulakanci, gashi har ta sa yara sun rasa makaranta. Yanzu gashi dole ya fita ya barsu a gidan su kadai abinda baya so. Amma wannan wulakancin na Khadeeja fa ya fara yawa, ta ma ki ta saurareshi gaba daya. Yanzu ya take so ayi?
Haka ya wuce dakinsa ya zauna ya fara kiran wayar Khadeeja amma har ya gaji da kira bata dauka ba. Ya duba lokaci yaga karfe takwas da rabi, gashi yana da meeting karfe tara. Don haka a gurguje ya tashi ya shiga wanka ya shirya. Ko abinci bai tsaya ci ba ya fice ya bar yaran.
……….
Babu wanda ta gayawa yanda suka yi da Mustapha, don ko su Rahma bata cewa komai ba; su kuma da suka kula bata son magana sai kawai suka kyaleta. Haka tayi zamanta a makaranta har wajen karfe biyar na yamma sannan ta kamo hanya ta dawo gidan. Tana shigowa yara suka fara yi mata oyoyo; da murnarta ta amsa sannu da zuwansu kamar yanda ta saba. Ta kalli Afaf tace ‘Bari na je daki na sha magani na huta, kaina ciwo yake yi.’
Ba tare da ta saurari amsarta ba ta shige dakin ta turo kofa.
……….
Sai bayan sallar isha’i sannan ya dawo, lokacin Afaf ta sa Rashida ta dafa musu taliya sun ci abncin dare saboda Khadeeja tace kada wanda ya sake buga mata kofa.
Yana shigowa gidan ita ya fara tambaya suka ce masa tana daki, sai dai ga mamakinsa yana taba kofar ya jita a rufe. Nasreen ce ta sanar da shi cewa tace a dina buga mata kofa bata lafiya. Don haka shima sai kawai ya kyaleta ya cigaba da harkokinsa har sai da yara suka kwanta.
Wajen karfe goma na dare ya sake kwankwasa mata kofar, tayi banza da shi bata ce komai ba. Ya matsa jikin kofar yace ‘Wallahi Khadeeja idan baki bude kofar nan ba zan balla ta.’
PAGE 108
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Tana daga ciki ta dauki ‘yar saman rigar baccina ta saka sanna ta zo ta bude masa kofar tana rike da wayarta tana chatting. Ta koma ciki ta karasa kan gado ta zauna ta mike kafarta ba tare da ta ce masa komai ba. Yana daga tsaye ya kare mata kallo sannan yace ‘Wai wanne irin wulakanci ne wannan kike yi ne Khadeeja? Kin bar min yara sun makara a makaranta kuma kin fice kin bar gida ba tare da wani bayani ba?’
‘To ai ka san dai yau ina da lecture ko?’ ta bashi amsa sannan ta sake mayar da hankali a kan wayarta.
‘To don me baki tashi kin shirya yara ba kuma da kika dawo kika sake rufe kofa kika barsu.’
‘Au wai Najan bata zo ba? Ai na zata tayi musu komai tunda yau itace da aiki.’
Ya cije lebe sannan ya ja dogon tsaki ya fesar da iska saboda yanda Khadeeja take kureshi ‘Na gaya miki babu komai atsakanina da ita sakatariyata ce kawai, don Allah wai me kike so nayi miki ne a kan wannan maganar. Idan kuma don taje makarantar yara ne to kiyi hakuri ba zata sake zuwa ba, babu wata alaka tsakanina da ita dama sai ta office.’
‘Ai naga alama.’ Ta fada ba tare da ta daina kallon wayara ba.
A fusace yace Khadeeja ni nake miki magana kina danna waya ko kallo ban isheki ba?’
Ta ajiye wayar a gefenta ta kalleshi tace ‘Shike nan, na ji duk abinda ka fada.’
‘Please kada ki sake rufe kofar nan, kuma ga yara can sun kwanta da safe ki tashe su da wuri kada su makara.’
‘Ok.’
Har ya juya zai fita ya dan tsaya yace ‘Kuma kin san kema ba a nan kika saba kwana ba.’
‘Ok.’
Ya fice ya barta.
Ta murguda baki kamar yana kallonta tace ‘Dan rainin hankali, baka yi laushi ba tukunna kaje ka dauko Naja ta zo ta dinga yi maka hidimar kai da yaran.’
Yana fita ta zame tayi kwanciyarta sai dai bata rufe kofar ba. Tana jinsa ya dawo dakin ya leka fuskarta tayi kamar bacci take, don haka ya fice ya barta bayan ya kashe mata fitila.
PAGE 109
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Yayi zaton kamar yanda ta amsa masa da daddare zata tashi ta shirya yara, sai dai abinda tayi jiya shi ta sake maimaitawa. Ta saka mukulli ta kulle dakin, ya buga har ya gaji bata bude ba; don haka ba tare da bata lokaci ba ya tsaya a kan yara suka shirya ya kwashesu ya kai su makaranta. Kafin ya dawo ta fice ta bar masa Rashida a gidan. Takaici ne ya sake kamashi; to me Khadeeja ta mayar da shi ne? wannan wane kalar taurin kai ne take yi haka? Kuma me take nufi? Yanzu me take so yayi mata; yaya ma zai yi da ita don gaskiya idan ba so take ya doketa ba bai san me zai yi mata ba.
Haka ya shirya ya fice ya nufi office.
Har ya kusa karasawa office din dabara ta fado masa; ya karkata kan motar ya nufi gidan su Khadeeja. Gara yaje ya kai kararta waje Baffa in ya so su tsawatar mata don shi yanzu idan ba duka ba bai san me take so yayi mata ba. Ya ci sa’a ya sami Baffa yana shirin fita, bayan sun gaisa Baffa yace ‘Lafiya kuke dai na ganka da sassafe ko?’
Nan ya mayar masa da abinda ya faru da kuma yanda Khadeejan take rufe kanta a daki, sai dai ce masa yayi ya rasa Khadeejan ne a waya shiyasa ya tura sakatariyar tasa.
Baffa yayi dariya yace ‘Kishi ne nasu na mata ya motsa, ka san a kan wata macen komai son da matarka take maka to za aji kanku. Kada ka damu bayan Magriba ka daukota ku zo nan. Zan kirawota don ma kada tace zata yi taurin kai.’
‘To Baffa, na gode.’
Yayi musu sallama ya fice yana jin dadin matakin da ya dauka tunda ya san ko babu komai Baffa zai yi mata fada kuma ya san dole ta shiga hayyacinta.
_____
Suna shirin shiga lecture wayarta tayi kara, tana dubawa taga Baffanta ne don haka ta ja da baya ta nemi waje ta amsa. Bayan sun gaisa yace ‘Khadeeja, na cewa Mustapha ku zo bayan magriba ke da shi kin ji ko?’
Tace ‘Um Baffa yau? Wani abu ya faru ne?’
‘Babu abinda ya faru, ku dai zo din.’
‘To Baffa in sha Allahu zamu zo, in ya dawo zan gaya masa.’
‘Kada ki damu na gaya masa ma, yanzu ya bar nan.’
Ta amsa suka yi sallama da Baffa tana dariya, don ta san inda zancen ya dosa, ta gane Mustapha kararta ya kai duk da bata zata haka ba.
Page 110
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ta jiyo motsin shigowar Mustapha gidan amma bata yi zaton zai yi saurin tafiya ba, don haka ma ta jira sai da ta gama abinda takeyi tunda ta jiyoshi da Baffa a tsakar gida. Sai dai ga mamakinta ko da ta fito Baffa ta tarar shi kadai, yana shirin shigewa mota tayi sauri ta karasa. Tace ‘Naji kamar kai da Mustapha ne, ko har ya tafi ne?’
Ya tsaya yana rike da murfin mota yana cewa ‘Shine, matar tasa ce ta fara gwada masa tutsun nata shine ya taho kawo kara da sassafe.’
‘Ikon Allah, Khadija Iya-rigima. Me tayi kuma?’
Ta Nan ya bata labari kamar yanda Mustapha ya bashi, ya kara da ‘Na ce su zo bayan Magriba don itama yanzu zan kirawota na sanar da ita kada tayi taurin kai, kin san hali.’
Tayi dariya ‘To Allah ya kaimu, ai an auna arziki ma da aka dauki lokaci haka bata fara rigimar ba.’
Suka yi dariya ta yi masa a dawo lafiya ya wuce sannan ta koma ciki.
………
Sai da yamma tayi sannan ta kirawo Khadeeja a waya, bayan sun gaisa tace ‘Me ya hadoki da Mustapha ne ya kawo kararki da sassafe ne?’
Tayi adriya sannan ta bata labari, bayan ta gama ji tace ‘Ikon Allah, to neman mata Mustaphan yake yi kenan ko kuwa dai aure yake nema?’
‘Nima ban sani ba Mommy, amma dai ko ma menene ai da akwai cin fuska ace ina yawo a taxi ita kuma tana yawo a motar mijina; at least ya bari ta aureshi sai ya bata wannan ikon. Kuma sannan idan itace zata dinga yi masa hidimar yaransa ai sai ta karba gaba daya ni kuma na huta gaba daya.’
Mommy tace ‘Um! Da wannan, amma dai ki bari abi abun a hankali. Saura kuma idan kun zo kiyi shiru ki ki yiwa Baffa bayani ya yanke miki hukunci in ma ya ga dama yace ki bawa Mustaphan hakuri.’
Tayi ‘yar dariya ‘Ba zan yi shiru ba Mommy.’
Suka yi sallama suka ajiye wayar.
………
Sai dab da magriba ya dawo gidan, ya yi mamaki da ya jiyo Rashida da Afaf a kitchen suna kokarin dafa abincin dare; a tunaninsa tunda ya san Baffa ya gaya mata yana nemansu ya kamata ace ta shiga hankalinta.
Bayan ya amsa sannu da zuwansu ya wuce dakinta; kofarta a rufe take, ya saka mukullinsa yaji har yanzu bata cire mukullin ba don haka ya daure ya kwankwasa.
PAGE 111
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Sai da ta gama yaukinta sannan ta bude ta rige hannun kofar ta matsa ya shige. Ya so ya zare mukullin kofar to amma sai ya ga idan ya zare ai duk da haka ba lallai ta dinga fita daga dakin ba balle ma ta dinga yin hidimar da ta saba; tunda dai wulakanci ne kawai ta shirya zata yi.
Don haka ya bi bayanta suka shige dakin, tun kafin ta gama zama a inda ta tashi yace ‘Baffa ya gaya miki muje yana nemanmu ko?’
Cikin halin ko in kula tace ‘Karfe nawa zamu je?’
Ya so ace ta bashi dama suyi magana su kashe wannan rigimar in ya so ya kirawo Baffa yace masa sun shirya amma sai dai ga alama ta fi so suje wajen Baffan.
Yace ‘Da na dawo daga masallaci sai muje.’
Ya juya ya fice daga dakin ba tare da ya saurari amsarta ba.
Ta bi bayansa da harara tana dariya; wato shi uban ‘yan son kai har yanzu bai ga laifinsa ba don haka ita yake tsammani ta bashi hakuri kenan. Tabbas yau sai ta kure wannan son zuciyar na Mustapha duk da har yanzu wata zuciyar tana gaya mata kada taje ta yiwa mijinta tonon asiri a wajen iyayenta.
………
Yana dawowa daga masallaci ya sameta a shirye, ko zama bai yi ba suka sallami yara suka fice daga gidan.
Suna shiga gidan suka sami Mommy wadda ta basu umarni su karasa parlor din baki domin Baffa yana can yana jiransu. Yana zaune a kan kujera 3-seater don haka Mustapha ya zauna daga gefen damansa jikin 2-seater ita kuma Khadija ta koma daya gefen jikin single seater ta zauna. Bayan Baffa ya amsa gaisuwarsu ya dubi Khadeeja yace ‘Dije, me ya hadaki da maigidanki ne kika daina kula shi shi da yaransa?’
Ta sunkuyar da kai cikin sanyin murya tace ‘Baffa ba daina kulasu nayi ba.’
Kafin Baffa yace wani abu Mommy ta shigo da sallama Nabila tana biye da ita dauke da tray wanda aka jera ruwa da lemo a kai, don haka Baffa ya tsaya ya amsa sallamarta. Ta nunawa Nabila inda zata ajiye tray din daga kusa da Mustapha, ta ajiye ta gaida Mustaphan sannan ta mike ta fice daga parlor din ita kuma Mommy ta kara ta zauna a kan kujerar da Khadija take zaune a kasanta.
Ya juya ya gaida Mommy, bayan ta amsa Baffa ya sake duban Khadeeja yace ‘Ya aka yi Dije ina saurarenki.’
PAGE 112
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Tace ‘Baffa ba daina kulasu nayi ba fa.’
‘To ai yace kusan kwana uku kenan ba kya kula kowa sai dai kawai ki kulle kanki a daki kin bar yara da mai aiki sannan kuma gari yana wayewa sai ki fice ki tafi makaranta. Kawai saboda ya tura sakatariyarsa taje makarantar yara kun hadu.’
Ta faki ido ta share kwalla; ya riga ya bawa Baffa kanun labaran don haka duk yanda take son ta kare mutuncinsa ba zai yiwuba domin itama dole ta kre kanta a wajen mahaifinta. Ta gyara zama tace ‘Wallahi Baffa ina bakin kokarina wajen kula da gidan da yaran, kuma babu laifi duk mun sami fahimtar juna da yaran gaba daya. Duk wata hidimarsu ni nake yi, kuma nice nake daukosu daga makaranta ranar da bana nan kuma sai mai-aikina ta daukosu. To shine ranar Monday suka yi open day a makaranta; nice na saba zuwarmusu don haka tun weekend suk gaya min, shi kuma na manta bamu yi maganar ba. Don haka gari na wyewa da na shirya zan tafi school sai na tsaya makarantarsu. Shine sai na ga har ya tura sakatariyarsa taje musu.’
Baffa yayi dariya yace ‘To ai babu komai Dije, watakila don baku yi maganar bane kuma kin ga ita din ai sakatariyarsa ce zai iya sakata wannan aikin duk da dai personal ne.’
‘Ni Baffa ba zuwanta ne ya bata min trai ba…’ nan ta bashi labarin yanda taga sakatariyar a motar Mustapha din da kuma yanda tunda ta aureshi sau daya ya taba kaita makaranta a motarsa da kuma yanda ko ta shirya baya yarda ya fita da ita. Da kuma yana wasu lokutan tana tsaye a bakin titi yake dawowa daga kaisu; bata sani ba ko yana ganinta amma ita dai tana ganinsa.
Baffa ya kalli Mustaphan ya kalli Mommy sannan ya kalli Mustapha wanda yayi tsamo-tsamo don bai zata Khadija zata kawo wannan maganar ba; shi da yaga ta daina damuwa ya rage mata hanya ma ya zata ta hakura gaba daya don haka bai san tana jin haushinsa a kan wannan ba.
Yace ‘Ikon Allah, yanzu a ce a ki ragewa mutum hanya sai kace wani wanda ake jin haushi? Ko dai akwai wata matsalar ne Mustapha?’
PAGE 113
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Nan da nan ya fara gyara zama kansa a kasa cikin rawar murya yace ‘Babu wata matsala, em… dama yawancin lokutan ne ai bata shiryawa da wuri su kuma yaran idan 7:30am tayi rufe musu gate za ayi. Umm.. shi yasa dole muke tafiya, kuma wasu lokutan ma idan na kaisu gidan nake dawowa sai daga baya nake fita.’
Tace ‘Baffa ai ko ya dawo zai fita idan nace ya rage min hanya sai ya san abinda zai fada wanda zai sa ba zai tafi dani ba don haka